Showing 12001 words to 15000 words out of 86122 words
Chapter 5 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt
Abba ma miqewa yayi ya fice masallaci
Itama da kyar tasamu tayi sallah sannan ta koma ta kwanta, tinani take sosai aranta, tinani take ta ina zata fara cire son yasir daga zuciyarta
Sai dai zatayi iyaka qoqarinta ganin ta danne damuwarta, kodan kwanciyar hankalin iyayenta
Har ga Allah ta amince da auren Alamin, amma sai dai batajin zata iya jure yaci zarafinta ko kuma walaqancinsa
Sabida haka tsakaninsu, yimin inmaka koda ko zai kashetane, bazata dauki raini da walaqancinsa ba
********
Ranar asabar da safe su papa suka d'au hanyar dambam
Wajen 12pm suka shiga dambam, basu tsaya ko inaba sai gidan Abba
Mama kad'ai suka samu a falo, bayan sun gaisa tace bari tazo, key na falon Abba ta kawo masu tace ga shi ku isa barin yima Fauziyyah magana
Sai d suka fita sannan, ta shiga dakin Fauziyyah
A kwance tasameta, tace Fauziyyah kije falon Abbanki su Alamin sukazo
Amma kije kitchen kid'auka masu naman zabinnan da lemo kafin agama abinci
Toh mama ta amsa sannan ta miqe, black hijab nata ta zira sannan ta goga white gloss lips ta fice
Qaton tire ta riqo, da sallam ta shigo, ajiyewa tayi a gabansu sannan ta nemi waje ta zauna
TJ cikin sakin fuska y amsa inda papa yayi kamar bai ji shigowartaba
Ina yini tacema TJ, lfy lau amarya, munsameku lfy
Lfy lau
Kallon papa tayi wadda ya had'e rai kamar yaci ba dad'i
Ina yini ta gaisheshi
Dago kansa yayi mai makon ya amsa sai wani mugun kallo daya watsa mata
Aiko itama wani kallon raini mai nuni da kayi kad'an kuma ba barin bashi ta watsa masa..........
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
1β£3β£
Ganin irin kallon walaqancin datake masa yasake b'ata masa rai
Afusace yace keh, ni kikema wannan kallon da shegun idanuwa manya2
Cikin tsiwa itama tace dawani ido ka kallen har kasan ina kallonka
Eye lalle yarinyarnnan to kirubuta ki ajiye wlh sai nayi maganin fitsaran dake daminki, inace baki da kunyako
Tace gadon baya ce ni, qarshen rashin kunya tafad'a tana harararsa
Ganin abin nasu zaiyi tsayi yasa TJ yace haba Ameen meye haka wannan ba girmanka bane
Papa yace can't u hear abinda take fad'amun ni saantane, ko ce mata akayi dason raina nazo wajenta
TJ yace is ok man ai kaika fara dai ko, da baka faraba da abin baiyi tsayi ba tinda ita gaisheka tayi
Oh yes, yanzu nagane wato kana goya mata baya kenan ko that's good to inka gama kasameni awaje n ksani idan naga zaka wasting mun time wlh sai dai kabiyo motar kasuwa yana fad'in haka yayi gaba abinsa
Cikin takaici TJ ya cije lips d'inshi, duban Fauziyyah yayi wadda ko ajikinta yace pls Fauziyyah kiyi haquri da halin Alamin insha Allah Komai zai dai dai ta
Murmushin takaici tayi tace bakomai wlh, ya wuce gara katafi kada yamaka halinsa dan ba mutunci ke garesaba
TJ yace Allah dai ya kyauta amma dan Allah kidaina biye masa tinda kin fahimci halinsa sai kirabu dashi kawai
Insha Allah zan kiyaye gaba ta fad'a kamar gaske amma azuciyarta tace yanzu muka fara matuqar shi bai gajiba nima kazalika
Emvlope ya miqo mata mai d'auke da IV aciki yace amarya ga cards na biki sai kuma meda me kika shirya zakiyi na biki
Hannu tasa ta karb'a tace nagode sosai malam tijjani amma ni babu abinda zanyi ma wannan auren da har yau kallon arziqi bai had'ani da mijinba baran magana mai dad'i
Tausayinta ne yakama shi dan Allah kad'ai yasan irin zaman da zasuyi, kuma har ga Allah jarumtanta ya burgeshi sabida shikansa yasan idan tabar papa abinda zai mata sai wanda yagani
Haba dai muda zamuzo da friends namu kice bazaki shirya mana komaiba, to tinda ke bakyaso Inyaso kidaure kiyi programs na jikin card d'in
Insha Allah nikuma 3days to biki zamu shigo domin shirya yadda abin zai kasance da kuma gyaran wajen da zaayi programs d'in
Toh nagode sosai tacema TJ dan sosai take ganin mutuncin sa, sabida shima yana mata mutunci shiyasa bazata iya musu ba
Hannu yasa a aljihunsa ya ciro kud'i, bundle na 1k guda biyu ya bata, yace pls kiyi manage da wannan, sauran su drinks da snacks wannan ba matsala dik zaa kawo so kada ki wahalar da kanki
Toh nagode amma kudinnan sunyi yawa gaskiya
No kada kidamu, ni barin wuce sai mun shigo kikuma qara haquri
Bakomai wlh nice da godia sosai, kuma gashi ko ruwa baka shaba baran akawo abinci
Yace kada kidamu nan ai gidane wataran zamuci
Toh dan Allah ko wani abu kaci mama bazata ji dad'iba idan na mayar baa ko tab'a ba
Hakane naman yad'anci agurguje yasha lemon exiotic sannan ya miqe toh madam mun wuce Allah ya qara maki haquri
Allah ya kiyaye hanya, agaida mutanen gida
Cikin gida tadawo inda suka bude cards din kuma sun yaba
Ana biki saura sati 1, inda Fauziyyah da khairy da amina suka kammala rabon kati
Mama kuwa ba qaramun dad'i tajiba ganin Fauziyyah ta ware ana hidima
Amarya kuwa tanashan gyara sosai a tunanin mama, batasan dik abinda tabata batasha ba, yanzun gyaran jiki aka fara mata cikin kwana uku ta wani irin kyau, fatan jikinta kamanta jaririya haka takoma dan sheqi da taushi, ga wani qamshi na musamman data keyi
Amma dik abinnan da ake aqasan zuciyarta takasa mantawa da yasir kuma har kwanan gobe tana kewarsa
Ana saura kwana uku biki su Daddy dasu mommy dasu aunty niima suka iso dambam, haka su papa da su TJ tare da wasu abokansu suka taho suma
Inda wasunsu sai Washegari wasu kuma sai ana gobe daurin aure dasu taho
Dik kuwa wanda suka zo babu wadda papa ya gayyata da bakinsa dik TJ ne ya raba masu IV
Akan haka sai da suka kai ruwa rana wai Yanason ya dizgashine yasa ya tara masa mutane akan bikin qaramar yarinya kuma ma *Budurwar Qauye*
Kamar yadda TJ yayi alqawari haka tinda sukazo bai zaunaba, cikin ikon Allah aka fara hidimar biki
Ranan laraba, da dare aka saka amarya a lalle, Washegari alhamis aka gudanar da kamu
Ranan jummu@ akayi walima kuma Komai ya tsaru yadda yakamata, amma dik abinda ake ango ba ruwansa, sai dai yayi wankansa yayi tatil da kayan maye abinsa
Kowa yaje wajen hidimar biki idan ya kalli amarya magana daya ake fad'a, papa yayi saan mata kyakykyawa sai dai qaramace
Su aunty Mubarakh sune akan gaba, wajen Komai
Bayan andawo daga wajen walima, aka turo wai ana sallama da Fauziyyah
Kai tsaye ta fita atunaninta TJ ne, amma data fita sai taga baqon fiska, bayan sun gaisa ya miqo mata wata leda mai kyau yace gashi ance ya bata amma da sharad'in kada afake bud'e sa Bayan biki inta amince y bata inbata amince ba ya mayar
Karba tayi tace ba Komai ta wuce gida tana zuwa ta ajiye acikin kayanta
Washegari asabar Dubbanin jamaa, suka shaida d'aurin auren Dr Muhammad Alamin Abubakar da Fatyma Fauziyyah Usman akan sadaki naira 100k lakadan ba a jalanba
D'aurin auren daya tara manyan mutane, sarakuna masu muqami a gomnati abin sai san barka, farin ciki a fiskar Daddy da Abba baa magana
Can na hango ango cikin manyan kaya farare sol, yasha hula mai tsadar gaske hakanan takalman qafarsa, kallo 1 idan kamasa saika qara dan papa ba qaramun kyakykyawan mutum bane ba
Shigar tasake fidda ainahin kyansa, ammafa sai d aka sha daga dashi kafin y aminta yasaka kayan
Anko sukayi shida TJ, Komai nasu irin 1, TJ sai gaisawa yake d jamaa iwa shine angon
Ango kuwa fiskannan ba yabo ba fallasa, hakama sai da TJ ya matso dafda kunnensa yace haba man kasake fiskan man kodan kada mutane su fahimci halinda kake ciki
Aranan su aunty mabarukha suka kawo lefe nagani na fada, wanda kowa ya yaba sosai dan annarka dukiya awajen
Bada jimawa ba daga daurin aure aka fara shirin tafiya d amarya
Kuka iya kuka Fauziyyah tayi haka aka wuce da ita, bayan laasar suka shiga bh, direct gidanta dake dasspark aka wuce da ita
Masha Allah gida yayi kyau dan kowa ya yaba sa fatan samin zaman lfy
kuma bada jimawa ba aka juya da yan dambam dan Abba yace kada wanda ya kwana
Tai kuka harta gode Allah
Su aunty niima ne suka zauna d ita, ahankali da kyar suka samu taci abinci wajen 9 suka mata sallama suka tafi
Nanfa tsoro ya kamata tana zaune yau ne gobe ne ba ango ba labarinsa har wajen 12
Can taji qarar mota, ta kuma sakejin fitar wata motar, tana zaune sai tunani take koda wani irin salo zai shigo, dan tasan batun mutunci babu dan bawadda zaa kawo masa amarya yakai wannan lokaci bai shigo gida yaga halin datake ciki ba
Papa kuwa TJ ne ya kawo shi gida, dan yayi tatil tafiyama tangad'i yake, bayadda TJ baiyi dashiba amma saida yasha shamma ya wuce misali dan ransa ab'ace yake kozai samu relief
Afalo ya tsaya yana kallon steps d'in, da kyar ya haura sai kuma ya tsaya dan yarasa inane hanyar side nasa dan sau biyu yazo gidan
Hakadai kansa na juyawa yayi left hand nasa, hannu yasa ya bude qofar sai yaji ta budu nan yafara tunani dama anbude yabar dakin
Ganin baisan damuwa ya shige dan buqatarsa ya kwanta ne kawai
Bedroom ya wuce yana bud'e qofar ya saka qafarsa har yana tangad'i kamar zai fad'i dan bashan wasa yayi ba
Jin anbud'e qofa yasa tai saurin d'ago kanta amma yanayin data ganshi aciki ya matuqar d'aga mata hankali lokaci 1 tsoro yasake rufeta.......
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
1β£4β£
Tangad'i yake har tsakiyan d'akin ya iso, da kyar ya bud'e idanunsa sai yaga kamar mutum ne atsaye
Sake bud'e idonsa yayi Da kyau, ganin wadda ke tsaye ta zuba masa idanu yasa ya murtuqe fiska
Keh meyakawoki d'akina yafad'a cikin muryar maye
Fauziyyah kuma dik masifarta Allah ya zuba mata tsoron masu shaye2
Jikinta na b'ari muryarta na rawa tace dan Allah kayi haquri nibansan d'akinka bane, su aunty mabarukha ne suka kawoni nan
D'aga kansa yayi kamar mai tunani sai anan ya fahimci sam ashe nan ba side nasa bane
Harya juya zai fita sai kuma ya tsaya cak, yace to dan ubanki kallona da kika tsaya kinayi akan baki sanni bane ko me
Ko rashin kunyar da kika saba zakimin?
Shiru tayi sai hawaye dakebin fiskanta
Wata tsawa daya daka mata saida ta razana, yace bada ke nake maganaba kin maidani d'an iska
Kayi haquri tafad'a cikin kuka
Banza qazama, yar qauye kawai yafad'a sannan ya juya ya fice
Tanajin fitarsa da gudu tazo tasaka key a qofar
Jikin qofar ta jingina ta fashe da wani sabon kuka mai tsuma zuciya
Tambayar kanta take dama ya Alamin yana shaye2?
Lalle da aiki na shiga uku, yanzuma dabadan Allah ya rufamun asiriba wayasan mai zaimun
Wasu hawaye masu zafi haka suka cigaba da zirya akan fiskanta, tana rakub'e ajikin qofar, gani take idan tamatsa zai sake shigowa
Har wajen qarfe 2 idanta biyu batai bacci ba kamar yadda batayi shiruba
Kafin haka da haka, fiskannan tayi jajur, idanun nan sun kumbura sunyi luhu2
Wajen qarfe biyu da rabi ta lallab'a ta kwanta, zuciyarta sai bugawa takeyi dan tsoro
Ga yunwa datake ji dan rabonta da taci abinci tun jiya sai d'azu da su aunty niima suka sata agaba taci kad'an
Ga gajiya na zirga2 dana tafiya da suka sha, had'i da kukan data rizga su suka saka tana kwanciya bada jimawaba bacci yayi gaba da ita
Ba ita ta farkaba sai wajen bakwai saura nasafe, aiko tana farkawa dasauri ta duba agogo ganin lokaci ya gudu yasa ta Shiga toilet dasauri ta d'auro alwala
Tana yin sallah akan sallayan bacci yasake yin gaba da ita, bata tashiba sai qarfe goma nanma wata irin yunwa ita tasheta
Wanka taje tayi, ta shirya cikin atampa super english wadda Abba ya dinka mata acikin kayan daya mata tasaka
Mai ruwan ganyen dorawa da baqi, dinkin riga da skert, sunmata cas dikda yatintanta, dan Fauziyyah Batada saurin girma amma inkaganta sai ka qara kallonta
Tasake gyara gashin kanta ta kafa dauri, turaruka tabi ta feshe jikinta dasu
Masha Allah tai kyau sosai
Amma haka ta koma bakin gado tazauna dan tsoron fita take kada ta gamu da ya Alamin ya shaqeta tunda ance yan shaye2 basa cikin hankalinsu har kinsan kai suna iya aikatawa
Haka ta zauna tana tunanin haka zata qare rayuwarta kenan da d'an giya, kullum tana d'aki anya kuwa hakan zai yiyu
Tana zaune ta saqa wannan ta warware wannan har lokaci ya fara tafiya
Wajen qarfe 11am, sai taji ana buga mata qofar falo aiko da tsoro ya kamata dan tasan ba mai zuwa inba shiba
Jin shiru bata bud'e ba yasa aka shigo har falon, aka fara kwankwasa qofar d'akin
Nanfa ta rakub'e ajikin gado, sai zare ido take, amma sai taji muryar mace tana cewa ko baku tashi bane kam
Jin muryar mace yasa tasauqo tazo ta bud'e qofar
Ganin aunty niima yasa tasaki ajiyar zuciya
Murmushin dole ta qaqalo tace Sannu da zuwa aunty niima
Yawwa kawai tace tana qare mata kallo ganin dik tayi wani iri kamar atsorace take, sannan idanuwanta sunyi ja sun kumbura alamun tayi kuka, dikda tayi kwalliya amma hakan bai hana ka fahimci wani abu atare da ita
Shigo mana tace da ita, ita kuma tanason ta fahimci wani abu yasa ta shiga d'akin
Ina kwana ta gaisheta, lfy lau ya baqunta
Murmushi kawai tayi batace komaiba
Ina papa ta tambayeta, sai da ta Zaro ido sannan asanyaye tace inaga ko yana d'akinsa
Tace ok, amma meyasameki idanunki suka canja haka? Ko papa ya maki wani abu ne?
Girgiza kanta tayi tace bansamu bacci da wuri bane shiyasa
Toh meyasa kika kulle kanki ad'aki, baki fitoba najima ina buga qofa baki budeba sai da nayi magana
Kiyi haquri bansan kebace shiyasa amma bakomai
Aunty niima da gangan tamata wannan Tambayar dan alamu sun nuna papa bai kwana ad'akinba kuma ba abinda ya shiga tsakaninsu dan yana yinta ya tabbatar da hakan sai dai ko wani abu yamata taqi fada
Aunty niima tace to koma mene ne kada ki koya ma kanki shiga daki kirufe dan in aka gano kagwanki fa tom, miqewa tayi nikam barin tafi gacan break fast nakawo maki dama momcy tace nazo naduba lfynki tinda kina lfy shikenan
To nagode aunty kidaisu momcy,
Zasuji ta amsa sannan ta tafi
Itama falo ta fito, ganin qofa acikin falon yasa ta bude amma sai taga wani d'akinne, rufewa tayi ta bude dayan qofar sai taga kitchen ne
Plate ta dakko da spoon ta fito falo, abincin tabude taga soyayyar dankaline chips da plantain sai dayan kuma miyar niqaqqen nama ne da kwai
Dayan kulan kuma farfesun zallan naman ragone wadda yasha hadi sai qamshi yakey
Nan tazauna taci tayi nak sannan tasha ruwa, kwashe kwanukan tayi takai kitchen
Wayarta ta tuna datake cikin kayanta, tace barin dakko ko game nayi
Tana budewa taci karo da wannan ledan da aka kawo mata ana gobe daurin aurenta
Dakko Wa tayi tazauna abakin gado ta bude, wasu katina masu kyan gaske ne guda uku sai wani dan qaramun akwati aciki
Katinan dik na fatan alkhair ne na biki
Dan akwatin kuma wani agogo ne mai kyan gaske da gani kuma mai tsadane, nan taji ya burgeta tana ta juyashi sai murmushi take
Wayarta ta dakko sai taga message, tana budewa taga tunjiya dasafe aka mata shi batamasaniba
Ganin baquwar no yasa tafara karantawa kamar haka
*Aslm, Fauziyyah nasan narasaki har abada tunda yau zaa daura maki aure, ina maki fatan zaman lfy mai d'orewa agidanki, abinda yasa bana daukar wayanki nasan sake famamun gyanbon dake zuciyata ne amma bawai ina fushi dake bane*
*Inaroqin da kitayi da addua Allah ya bani haquri da* *juriyan rashinki, jiya ankawo maki saqo kiyi haquri bayawa ina maki fatan* *Alkhairy*
*Daga Yasir*
Nan taji wani kuka yazo mata, tayi harta gode Allah dan tasan tayi rashin masoyi har abada, da haka har wani bacci y d'auketa
*****
Papa kuwa tun da ya fice dakinsa ya zubu agado yake bacci bashi ya tashiba sai wajen 12
Subhanallah ya furta daya tuna ko sallan asuba baiba, agurguje yayi sallah sannan yayi wanka
Yana shafa mai yaji Wayarsa tana kuka, ganin momcy arubuce yasa yadauka yabar abinda yake
Hello momcy, yes papa kana ina ne?
Jifa momcy wani irin ina kuma, to ina gida
Kazo yanzun ina son ganinka, lfy momcy
Lfy nace kazo ko, to naji saina zo
Tab'e baki yayi yace koma mene zanji idannaje
Yana shiryawa yanufi gida, a Bedroom ya samu momcy fiskanta adaure
Yace gani momcy
Tace mekayima yar mutane daga zuwanta har kake neman maidata marainiya
Momcy wannan wani irin maganane ita tace namata wani abu
Ba ita tafad'a ba amma yanayinta shiya tabbatar d haka, niima ce ta fadamun dan taje dasafe
Hade rai yayi yace ok, ita didi niimace ta fadamiki wato ta shirya mata qarya da gaskiya kema anfada maki kinyarda ko
Bawani qarya da gaskiya akan Fauziyyah zamu bata dakai, kuma kada kabari maganan nan taje wajen Daddy dan bazai maka kyauba
Wai mommy daga anfadi maki qarya sai kihau kizauna kiyita ma mutum shouting
Namaka karama tinda baa fada maka gaskiya, kuma wlh wannan dan banzan shaye2n baya fada maka gaskiya
Fita kawai yayi adakin ransa abace idanunsa har wani qanqacewa sukayi dan bacin rai
Da uban gudu y figi motarsa, Allah Allah yake ya isa gida yaci uban yarinyarnan yanda gaba bazata qara shaawan kai gulmansaba.......
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
1β£5β£&1β£6β£
Bata jima da