Showing 75001 words to 78000 words out of 86122 words

Chapter 26 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

04 Jan 2025

8878

yayi yabar fauzynsa gashi yana da ayyuka sosai a office


Ta lallamasa akan yayi haquri sati daya kamar yaune amma yace yaji saida yamma zai tafi


Tunda rana suke tare dashi adakin baqi wai yazo suyi sallama zai tafi har aka kira laasar shiru


Abba yacema mama ina fauziyyah kam najita shiru kotaje unguwane


Mama tace tana wajen mijinta kasan yau zaikoma shine yazo suyi sallama


Abba yace amma kuwa ai zaiyi tafiyar dare har ankira laasarfa


Fitowa tayi tazo tayi sallah shikuma yaje masallaci bayan yadawone yayima Abba sallama zaitafi


Abba yamasa fatan sauqa lfy yace amma kuwa zakayi tafiyan dare kam


Yace anjima kadan zantafi ai


Abba yace aunan gabama sannan katafi


Dan sosa keya yayi yace aigida zankoma Abba babu damuwa


Nan Abba ya fahimci baison tafiya yabar matarsane saiyace jirani inaxuwa


Cikin gida ya shiga yace fauziyyah ta dauko kayanta tabi mijinta


Fauziyyah harda kukanta wai bazata tafiba


Mama tace banson gulma aidai kinzo kuma kinganmu kuma kema bakison barin mijinki tinda tunsafe kike wani bata rai sabida zai tafi


Abba ya tasata agaba har waje


Nan yamasu fatan alkhairi suka tafi


Papa kuwa zuciyarsa wasai dan murna sabida kwana biyun dasukayi baa tareba daurewa kawai yayi


Itakuma ta bata rai tawani tsume irin batason tafiyannan


Papa yadan dubeta kadan yace babyna yadai kika wani bata fiska inlaifi nayi inbada haquri


Turo dan qaramin bakinta tayi tace Allah one n only ya isheka hakannan karabu dani tunda dai kasa Abba ya hanani yin sati agida


Murmushi yayi sosai sannan yace haba yan matana nifa baruwana Abba dakansa yafahimci damuwar dansa yabashi magani amma bani ne nace mutafiba


Tace aidai yanzunkam shikenan tunda kamun alaska


Dariya yayi sosai yace nine me miki alaskan


Eh din tafada tana murguda masa baki cikin shagwaba


Yace toh naji na yarda amun haquri baby idan mun isa gida zan baki special haquri kinji my princess


Dahaka har ya lallamata suka shirya tun basu isa gida ba


Bayan dawowarsu da kwana goma papa yagama masu shiry shiryen tafiyansu *NEWZALAND* dagacan zasu biyo ta *QASA MAI TSARKI* suyi umra sannan su dawo


Ranan da zasu tafi su daddyne suka rakasu har AIRPORT


Basu tafiba saida jirginsu ya daga tukun suka dawo


Qarfe 3am suka sauqa acikin garin *NEWZALAND*




โœ๐ŸปFaty Mmn Faty








๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017






*Ina kira da babbar murya zuwaga wadda idannayi posting yake had'amun DOCUMENT, toh banaso adaina saiki/ka bari idan nakane kayi yadda kagadama, dafarko banyi maganaba amma yanzun anason abab'atamun tsarin littafina, maimakon adinga tambayar page nagaba sai adinga tambayar wai part 2, bayan nikuma littafina guda 1 ne kuma banma qarasaba yanzun nakeyinsa pls naroqi koma wanene yabarmun abina yadda yake inyaso daga baya idan ina ra'ayin maidashi DOCUMENT sai nayi da kaina inafata anfahimchi nufina!!!*




6โƒฃ9โƒฃ
Direct wani babban HOTEL suka nufa inda acan sukayi masauqi


Room nasu mai kyan gaske 2flat bedroom ne mai girma da tsari, suna hawa na 20


Agajiye suka shiga cikin dakin nasu dan sunsha zama a jirgi sabida tazaran dake tsakanin *Nigeria da Newzaland*


Akan bed ta zube tana cewa wash Allah


Dubanta yayi yana ajiye masu jakarsu yace yadai babyna?


Wlh am tired tafada tana bata fiska


Eyyer am sowwie barin muyi wanka muci abinci then saina maki tausa zakiji gajiyan ya gudu ko


Toh kawai tace dashi tana sake gyara kwanciyarta


Rage kayan jikinsa yayi ya rage dagashi sai boxer sannan ya nufuto


Dagota yayi ya rage mata kayan jikinta itama suka wuce toilet


Atare sukayi wanka sannan yana dota a towel suka fito


Dan cream da spray ya shafa mata ya sakamata doguwar rigar baccinta da qatuwar hijab sukayi sallolin da basuyiba sannan yayi masu ordern abinci


Bayan sunci abincine yadagota ya kwantar akan bed


Cikin salon kwarewarsa yake dan matsa mata jikinta aiko bada jimaba wani bacci mai dadin gaske yayi gaba da ita


Ganin tati bacci yayi murmushi ya rungumeta tsam ajikinsa shima bai dau wani lokaciba yabi bayanta


Washegari bayan sunyi breakfast sukayi waya da mutanen gida da yamma suka shiga gari dan zagawa


Baqarya sunajin dadin qasar sosai basu da aiki sai dai suci abinci su qoshi suyi bacci


Idan suntashi su shiga gari yawo


Hakan yasa wani shaquwa na musamman yasake shiga tsakaninsu sosai


Gawani matsanancin qaunar da suke nuna ma junansu


Cikin sati biyu sun wani irin canzawa hadi da kyau namusamman


Especially Fauziyya tasake wani haske da kyau wanda shikansa papa bai gajiya da kallonta


Rananda suka cika sati biyu suka wuce *SAUDI QASA MAI TSARKI*


Nanma sunji dadin zuwansu can dan sunyi ibada yadda yakamata


Haka sun zazzaga wuraren ziyara da dama


Kwanansu goma suka fara shirin dawowa gida


Inda suka shiga kasuwa suka jibgo tsaraba kamar ba gobe


Ranan da suka cika sati biyu cur ranan suka nufo gida Nigeria


Su momcyne sukaje taransu a Airport


Jirginsu na sauqa suna fitowa suka hangi su daddy da momcy harda Aunty Niima


Aifa dasauri fauziyyah ta qaraso ta rungume momcy


Cikin shagwaba tace nayi kewarki momcy


Momcy ma tace nima haka daugther gani nake kamar kun shekara bakunan




Haka ta rungume Aunty Niima tana cewa i miss u Aunty


Aunty tace nima haka ammafa honeymoon dinnan ya karbeku bakeba bashi ba masha Allah tafada tana murmushi


Sannan taje tagaida daddyma yana tasaka musu Albarka


Papa yace oh nikam yanzun andaina yayina babu wadda ya kulani


Dariya suka masa momcy tace bagashinan mungankaba


Shagwabewa yayi yace oh haka abin yakoma ko


Dariya daddy yayi yace muje gida babana dik munyi kewarku shikenan no more qorafi


Gidan momcy suka nufa sai dare kafin suka wuce gidansu


Ko ina tsaf suka samu dan aunty niima tazo da masu aiki angyaramasu ko ina shiyasa ko ina fess kanar dama suna nan


Bayan sungama abubuwan dasuka saba kafin sukwanta sannan sukayi shirin bacci




Aifa suna kwanciya papa yawani kanainayeta


Cikin shagwaba tace pls one n only kabari sai gobe agajiye nakejina
Dan tasan abinda yakeso


Cikin lallashi yace haba my princess kitausayinmana kema kinsanfa ina buqatarki sosai


Tinda mukaje saudi ba sosai bafa ummm


Kuma gaskiya inaso kiyi haquri kadan zanyi


Turo baki tayi tace um wai kadan aidai nasan kadan dinkafa


Yace gaskefa ainasan kingaji


Tace toh shikenan


Nan yafara aika mata da saqonni namusamman


Sunjima suna wasanni da junansu kafin ya zame hannunsa daga kan qirjinta yana qoqarin shiga


Aifa dasauri ta riqo hannunsa cikin wani yanayi tace pls kacigaba damin bangajibafa


Kallon fiskanta yakeyi yanda take wani lumshe idanu tana maida hannunsa kan qirjinta


Babyna ya kira sunanta da muryarsa kamar wadda mura ya kama


Umm ta amsa tana bude lumsassun idanuwanta


Meyasa kwana biyunnan kikeson naringa wasa da qirjinki sosaine?


Nidai kawai dadi yakemun kuma kana sosamun


Yace qaiqayine yake maki toh da kikeso nake sosa makin?


Eh sosaima yakemunfa amma idan kanamum sai inji yadaina


Murmushi kawai yayi danyafahimci kawai tanajin dadin abinne yaci gaba damata yadda takeso




******
Washegarin dawowarsu basu tashi da wuriba


Sabida momcy tace zata aiko masu da breakfast


bayan sunyi wanka sun shirya ta wuce dakinta dan tasaka kaya


Kwalbar humranta ta dauko tana budewa ta rufeda sauri saitaji tamata wani iri
Sai tayi tunanin kodan tajima arufe baa budewa ne oho




Wata doguwar rigar shadda tasaka light blue tasha aiki da zare dark blue


Kayan sun matuqar karbanta sosai ta kafa daurin dankwalin kamar wanda aka nadama gwagwgwaro


Dauko humranta tayi tasake budewa akaro na biyu namma taji qamshinta ya mata wani iri kamar zaisata amai saikawai ta ajiyeta


Tana cikin saka dankunnenta ya shigo


Wata farar boyel ce ajikinsa mai tsadar gaske dinkin boda


Ta matuqar fito masa da cikar zatinsa sai wani sheqi yakeyi


Juyowa tayi suna hada idanu suka sakarma junansu niimtaccen murmushi mai faranta zuciya


Kowa yana ganin kyan dan uwansa


Bude mata hannayensa yayi ya mata alama dakansa ta taho
Dan yadda ta birgesa kawai burinsa yajita acikin jiginsa


Tahowa tayi tashige jikinsa amma cikin sauri ta matsa baya tana riqe hannunsa dayake qoqarin rungumeta
Sabida shaqan qamshin turarensa datayi sai taji tashin zuciya kamar zatayi amai


Da mamaki afiskarsa yace baby lfy kuwa kodai zolayane ya tashi


Yatsina fiska tayi tace aa turarenkane banaso yayi qarfi dayawa


Turarena kuma? Ya fada yana kallon yadda take bata fiska


Taceceh wlh kai bakajisabane


Yace ammafa baby normal perfume nanefa dakika sani


Tace eh inaga dan sunjima a ajiyene baa amfani dasu shiyasa


Kai baby rigima dai kawai saikace mun shekara bamunan just fa one month ne mukayi bamunan


Tace Allah dagaske nake haka humrata ma tayi warin ajiya sai dai nacanza wata


Tabe baki yayi ganin dagaske takeyi yace anyway shikenan barin canzo kayan kifito muci abinci momcy ta turo


Toh kawai tafada ta biyo bayansa shiya wuce dakinsa itakuma tasauqa qasa


Baifi 5mins ba ya fito a dinning yasameta tana zaune


Murmushi yamata yace shikenan nacanzo inyaso saimu sake wasu turarukanko


Tace aa ai wadanda muka saya amakka suna da dadi


Ok shikenan yafada yana qoqarin zuba masu abinci


Zuba musu yayi a plate daya yace baby muci kona baki abakine dannaga yau rigimar ta tashi gara nayi lallami


Tace kai one n only harda tsokalane


Aifa tana shaqan qamshin abincin tajisa wani iri harma batasan yadda zata kwatantaba


Miqo mata yayi tabude baki saime kamar zai dawo haka ta hadiye da kyar tana jagula fiska


Yaya dai ya tambayeta


One n only nikam banson wannan abincin gaskiya tafada kamar zatayi kuka


Riqo kafadunta yayi yace shikenan inbakiso aiba saikinyi kuka ba fadamun me kikeso kici


Nidai irin abincin makka nakeso


Tairkashi shine abinda yafada yana kallonta yace to wanne iri kenan


Tace koma wanne iri amma mai garlic aciki


Shiru yadanyi yace toh barin fita nasamomaki kinji ko


Maqe kafada tayi tace aa niba nasayarwa nakesoba




Yace toh nizan dafa maki kenan


Nanma tace aa


Dafe goshinsa yayi yace oh Allah toh wanne kikeso baby


Tace nidai nagidan momcy nakeso irin wadda talatu takeyi tafada ashagwabe


Takwana gidan sauqi yafada aransa yana ciro wayarsa ya shiga kiran layin momcy


Tana dagawa bayan sungaisa


Yace momcyfa yarkice takeson abincin gidanki


Momcy tace ah malam bala bai kawo bane ba?




Yace yakawo amma tace batason wannan wai mai garlic takeso irin abincin makka kinsan tasaba dashi kwana biyu


Momcy nan take wani farin ciki ya lillibeta tace toh shikenan dakainama zandafamata


Amma wanne iri takeso


Yace tacefa na talatu takeso kuma ko wanne iri


Momcy tace shikenan kabata haquri yanzun zaa dafa akawo kagaisheta




Tana ajiye wayar daddy dake gefenta yace ya dai kiketa faraa haka maman yara


Tace ai dolene daddy nida papane nan ta zayyane masa yadda sukayi


Ta qarashe da cewar aifa nitun a airport nafahimci kamar tana da pregnancy


Daddyma da faraasa yace Alhamdulillah Allah ya sauqeta lfy aisai amata abincin akai kada yunwa ya dameta


Momcy ta miqe tace yanzukuwa sannan tafice zuciyarsu fal murna


******
Yana ajiye wayar yace toh madam zaa kawo maki amma kafinnan me zakici umm


Dasauri tace popcorn din *BANILA* nakeso amma bamai milk acikiba


Dame kuma ?


Shikenan tafada, yace ok barinje nadawo toh


Nan ya dauko car key nasa ya fice


Manyan kwalaye biyar ya sayo mata


ahanyarsa ta dawowane yake tunanin


Meke damun babynsa kam dik tacanza haka


Tun a makka ya fahimci canzawarta iri daban daban


Gashi yaukuma irin abinda takeyi cikin qanqanin lokaci zuciyarsa ta amince masa lalle babynsa is pregnant




Aifa wani dadine ya lullubesa lokaci guda dan yanzu yafahimci tana nuna alamun masu ciki ta abubuwa da dama kawai zuciyarsa batakawo hakanba sai yanzun


Allah Allah yake ya isa gida yadauketa suje hospital ya cheking nata sosai..[truncated by WhatsApp]








๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017




7โƒฃ0โƒฃ
Tana kwance afalo ya shigo da sallamarsa


Dago kanta tayi ta amsa fiskarta dauke da murmushi


Babyna nabarki da yunwa ko yafada yana zama agefenta


Miqewa zaune tayi tana cewa umum ai baka jimaba


Riqota yayi ta zauna, ganan popcorn din yafada yana miqo mata ledar


Cikin sauri ta karba ta bude kwali daya tafara ci hannu baka hannu kwarya dan gani take kamar bazai ishetaba


Kallonta kawai ya tsaya yanayi ganin yadda take cinsa ba wasa


My princess ya kirata yana kallonta


Naam uum kawai tafada har wani lumshe idanu take sabida dadi


Murmushi yayi sosai dan ba shakka abinda yake zargi zai zama gaskiya


Babyna kigama cin popcorn din kirakani hospital


Tsayawa da cin popcorn din tayi tace hospital kuma?


Gyada kansa yayi yace eh hospital mana kobazaki rakani ba


Zanje mana ta amsa sannan ta tambayesa to wane ba lfy?


Kallon cikin idanunta yakeyi yace babyna zan duba naga lfyrta


Nikuma tafada da alamun tambaya


Yace yess ko inada wata baby baicin ke


To aini lfy ta qalau ta amsa tana kallonsa


Yace eh nasani kawai inason duba lfyr little babyna dake cikin kine yaqarashe maganar yana shafan cikinta


Aiko batasan sanda dariya ya kufce mata ba


Dariya yabata sosai tana dariya tace ah lallekam bayan kafitane kayi mafarkin hakan daiko


Matsowa yayi jikinta sosai yakai hannunsa yana shafan cikinta yafara magana ahankli


Baby bamarfaki bane gaskene kina dauke da ajiyata acikin cikinki


Jin yadda yake maganar da iyaka gaskiyarsa yasa ta natsu tana sauraronsa, saida tabari yayi shiru sannan tadago ta dubesa da kyau tace pls mubar wannan wasan


Baby am not joking fa dgaske nake alamunki sun nuna kina dauke da cikina ajikinki


Tace to meyasa kayi wannan tunanin baicin masu ciki bahaka sukeba


Yace baby kowacce mace da irin sign n symptoms dinta


Itadai jinsa take dan bata yardaba sam sabida haka yasa tace meye hujjarka nayin wannan tunanin


Murmushi yasakeyi yace haba baby bakiga yadda kika canzaba, abinda da bakiyi yanzun dik kinfarayi


Kinfara zaben abinci sannan kince bakison turarena da naki n kuma gashi kincin abinci sai popcorn da kika ritsa kamar dawani kukeci alhalin da ba haka kikeba sam


Sannan abinda ya tabbatarmum shine rabonki da yin mentruation yanzun 2months kenen


Saida ya qare tace ah lalle kuwa toh nikam banda komai batun menstruation nawa kuma ai dai kasan daman yanamun wasa


Yea i know baby but kituna rabonki da shan maganin ciwon cikinki tun bamu tafi newzaland ba, kuma watanmu guda bamunan dake cikim baiyi ciwoba shiyasa bamu ma tunaba


Tace oh yanzun kawai dan ciki yayi arha sai yazama inadashi


Yace nidai yanzun mubar magananan kawai muje hospital acan zamugani koma mene ne


Hankali kwance tace nifa ba inda zani kawai


Sassauta murya yayi haba babyna bafa jimawa zamuyiba kiyi haquri kirakani


Toh wai naga ikon Allah ni fatyma mutum lfyrsa lau acw saiya wanije asibiti


Aifa bance bakyada lfy ba rakiya nace kimun pla baby na kada kiqi


Da kyar yasamu ya lallamata ta amince amma da sharadin bazujimaba


******
Bayan gwaji da scarning ya tabbatar masu tana dauke da ciki har natsawon 7weeks


Habawa murna da farin ciki baa magaba papa bakinnan bai rufuwa


Mamaki kawai yake wai irin shima zaizama baba


Godia ya dingayima Allah da wannan kyauta daya masa wadda kudi bazai saya masa ba


Fauziyyahma yanzun ta yadda kuma ta amince da cikin dake jikinta wadda bata taba tunanin haka ba koda kuwa da wasa ne


Lokaci guda taji qaunar abinda ke cikinta yana ratsa ta


Tun daga asibiti papa ya ringa waya yana fadin fauzynsa nada ciki


Itakuma gaba daya kunya ya kamata yadda yaketa fadama mutane


Bayadda batai dashiba kada ya fadawa momcy amma fir yaqi saida ya fada masu


Su momcy jisuke kamar ba wadda yakaisu farin ciki


Haka suka dawo gida papa yarasa inda zaisaka kansa dan tsabar farin ciki


Wani tattali dabkulawa na musamman yashiga nunama babynsa


Ko kwakwkwaran motsi tayi sai tambayeta meta keso ko kuma ina ke mata ciwo


Tun abin nabata mamaki har yafara bata dariya


Bayan sun dawo driver daga gidan momcy ya kawo mata abincin datace takeso


Namma haka ya ringa lallmata yana bata abaki harta qoshi


Dubansa tayi cikin shagwaba tace my one n only nikam kabarni zanfa iya yin komaina da kaina cos ba inda kemun ciwo


Dubanta yayi yace tab sanadin kiwahalarmun babyna kenan ko


Hade fiskabtayi tace lallema yanzunkam ai nafara ganinma kafidon babynka dani


Jawota yayi jikinsa yace inji wane yace haka kadama kisake wannan tunanin dik abinda zanso abayankine so kada kidamu shima yana buqatar kulawan daddynsa ne kingane ai
Ya qarasa maganar yana shafan cikinta


Dahaka itakam bacci yayi gaba da ita


Gyara mata kwanciya yayi sai anan ya tuna ashe baiyi break ba


Sauqowa yayi yazauna amma sam yakasa cin abincin sai dan kadan yataba ya tashi


Da yamma momcy tasake aiko mata da abinci nanma lfy lfy taci


Sai dai me cikin dare matsanancin amai ya tasheta


Haka takwana tana abu daya


Gashi bata iya cin komai sai drip kawai daake saka mata


Cikin sati biyu ta re ta canza sai haske kawai data qara


Momcy tace ma papa ya maido mata da Fauziyyah gida ta ringa kula da ita tunda su kadaine agidan


Amma sam yaqi yarda yace aa abarta ai yana kula shima da ita


Amma idan ka kallesa zaka rantse kace shima baida lfyn sabida yadda yayi rama ko aiki ba kullum yake zuwaba


Hakan yasa daddy ya kirasa yace ya maido Fauziyyah gida tunda jikinnata yaqi dadi


Amma sam ya keqashe idanunsa yace aa shidai abar masa matarsa


Daddy yace toh kai haka zaka zauna bka zuwa ko aiki bayan bawai bayadda zakayibane


Toh umarni nake baka mom dinku zatazo ta dauketa


Aifa ba kunya papa yace toh saidai shima ya hada kayansa su taho tare......










โœ๐ŸปFaty Mmn Faty










๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ





๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017






7โƒฃ1โƒฃ
Daddy yana sauraronsa sai dayayi shiru tukun yace, Alamin waikai baka girmane kam?


Daddy me nayi to kawai dannace nima zan dawo gida shikenan


Daddy yace aifa ba kawai bane yakamata yanzun kagane da da yanzun the different is clear


What's the different daddy kunefa iyayena n nima kuma nine dai bacanzuwa mukayiba


Murmushi daddy yayi yace yess haka abin yake but now u r going to be a father, so kamata yayi kafara gane ka girma yanzun so kayi zamanka agidanku inyaso kana zuwa kana duba matarka babu wanda zai hanaka


Shikenan daddy dayamman zankawota dakaina yafada amma dai ransa baisoba babu yanda ya iyane kawai


Ransa ajagule haka ya dawo gida, bedroom nata ya nufa, bacci yasamu takeyi sai bai tashetaba ya wuce yafara hada mata kayanta


Motsinsane ya tasheta ahankali ta bude idanunta kallonsa takeyi sai faman shirya kaya yakeyi


Murya can qasa tace ya Alamin lfy kuwa ina zamuje?


Jin muryarta yasa yajuyo cikin sauri


Barin abinda yakeyi yayi ya nufota


Hawowa kan gadon yayi ya janyota jikinsa baby kintashine


Gyada kanta tayi tasake tambayarsa ina zamuje?


Baby gida zan maidake wajen momcy amma wlh ni raina baisoba kawai ba yadda na iyane umarnin daddyne


Tausayinsa ne yakamata jin yadda yake maganar cikin damuwa kuma koda bai fada bama tasan zai shiga damuwa sosai sabida bai qaunar abinda zai nesan tasu


Shiru tayi kawai ta kwantar da kanta ajikinsa tana son komawa gida sabida wannan gidan ta tsaneshi dama amma sai bata nuna masa hakanba


Baby ya zanyi ne, idan kikayi nesa dani, tabbas zanshiga damuwa amma inhar hakan yafi kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login