Showing 51001 words to 54000 words out of 86122 words

Chapter 18 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

04 Jan 2025

8882

ranta yakeso nan yabasa labarin yadda sukayi


TJ yace ainafada maka ajiye fushi zakayi agefe har kasamu kanta dan wlh dama can kasanta yar zafin kaice baran yanzu data san ciwon kanta


Nan suka fito suka nufi shago inda TJ ke sayayya nan yasayi shaddodi da boyel kala ashirin sannan yasayi huluna masu kyau da tsadar gaske


Daganan suka wuce wajen tailor inda suka bashi dinkuna suka biya shi kudin express dan basason ya jima


Office ya maidashi akan sai da yamma zai shigo gida


Fauziyyah kuwa da wuri ta dawo gida yau da yamma ta shirya tsaf cikin wani sari sky blue wadda idan kaganta zaka rantse da Allah kace yar india ce


Nan tacema momcy zataje gidan khairy tinda tadawo batajeba


Momcy tace toh saikin dawo amma kada kiyi dare tinda ke kadaice zaki fita


Cikin ladabi tace toh momcy me abi ayaho (saina dawo)


Momcy tace Allah ya kiyaye hanya adawo lfy


Tana fita gidan khairy ta wuce cikin murna khairy ta tarbeta nan suka zauna afalo suka fara hiran yaushe gamo


TJ ne ya fito dan khairy ta fada masa zuwan fauziyyah


Zama yayi agefen khairy yana cewa hajiya fauziyyah ce agidanmu kodama bata gane mutane amma dai kekam nasan bata mantakiba yafada yana kallon khairy


Murmushi tayi dan tafahimci inda maganarsa ta dosa


Tace habaya Tijjani ni na isa nace banganekaba


Yace ah ranan agidan momcy kikayu kamar bakisanmuba


Tace kasan kazauna kusa da baqon fuska shiyasa kaima sai kabacemun amma yanzun bagashiba nazo har gidanka


Fauzy kenan kinzo dai wajen khairy


Tace dikkanku dai wajen ku nazo




Yace toh ya aiki da haquri damu


Tace aiki mungode Allah saita juta zancen da fadin banga mubeen bafa ko baccin yamma yake


Khairy tace aa baya nanma tun jiya yaje gidan hajiya (gidansu TJ)


Tace ayyah nan sukayi ta hiransu dik akan karatu nema dan khairyma tayi jamb admission take jira


Can wajen magriba fauziyyah tace bari ta tafi


TJ kuwa da tun dazu ya fita ashe suna tare da papa awaje


Nan sukayi sallama ta rakota har bakin mota tana cemata tagaida momcy itama zatazo


TJ kuwa ganin fauziyyah ta fito yasa yayi sallama ma papa ya wuce cikin gida dan dama yafadama papa tazo


Shima cikin sauri ya mufo inda take tana qoqarin bude mota ga hadari ya hadu baqiqirin ashe suna ciki basusan da hadarin ba




Assalamu alaikum yamata sallama juyowa tayi dan bata taba tunanin shibane tinda a iya tsawon zaman da sukayi har zuwa yau bai taba yimata sallama ba


Juyowa tayi dan ganin waye acikin gidan kuma dai ba muryar TJ ba kawai sai taga papa tsaye ya harde hannayensa aqirji


Tana ganin shine ta wani hade rai ta tsuke fiska tayi kamar bada ita yakeba ta bude motarta ta shige


Hannunsa yasaka ya riqe murfin motar yace pls ba danniba ba dan halina ba kiyi haquri kisaurareni


Dagoda manyan idanuwanta tayi ta watsa masa wani kallo batace masa qala ba tasa hannu ta jawo murfin motarta


Saurin janye hannunsa yayi da ta buge masa hannu


Key tayi ma motar zata wuce ta barshi


Shiru yayi yarasa abin ma zaice saiyaji sauqar yayyafa akansa hakan yasa ya juya ya shiga motarsa yabi bayanta


Suna fita ruwa ya kece kamar da bakin kwarya hakan yasa tafiya take ahankali shima yana bin bayanta har suka iso gida


Yana shigowa gate ko cikakken parking baiyiba ya fito ya nufi wajenta


Ita kuma tanayin parking tunani tafara ta fito acikin ruwanne ko ta zauna ya dan ragu


Kura idanu tayi tana ganin yadda ruwan ke sauka sai ta hango papa ya nufota


Cikin sauri ta bude qofar motar ta gwammaci ruwan ya jiqata than ace yazo wajenta


Aiko tana bude qofar motar ta zura qafarta kenan ya qaraso ganin haka yasa tajawo qofar zata kulle


Cikin azama ya saka hannu ya riqe, ganin haka yasa ta maida qafarta ciki batace masa qala ba


Shima baiyi magana ba sai ruwa dake dukansa haryafara diqa


Yakai 5mins ahaka yana tunanin mai zaima fauzy ta saurareshi kawai saiya durqusa awajen cikin ruwa ga kuma tasama ruwa na dukansa


Kallonsa kawai takeyi


Cikin murya mai rauni yace fauziyyah banida bakin da zan baki haquri akan abubuwan dana maki abaya wadda son zuciyata ya jani aikata hakan


Kuma nasani bacin ran abinda namaki ne yasa kike nuna baki sanniba


Amma kiyi haquri badan niba sabida Allah kiyafemun abinda namaki kozan samu salama arayuwata domin alhakinki yayita bibiyana kuma nagane kuskurena


Fauziyyah saima ta juyar da kanta dan bataji alamun zata sauraresa ba kuma ita dama matsa mata yayi ta wuce abinta dan batajin zata iya yafe masa abinda yamata




Ganin bata tankashi ba saima juyarda kanta datayi sake qasa da murya yayi kaman zaiyi kuka yace kefa musulma ce na roqeqi kiyafemun sabida Allah badan niba


Yadda ya marairaice murya saitaji tausayinsa ya kamata amma data tuna irin walaqancin daya mata abaya duka zagi azabtarwa sai taji wani sabon tsanarsa


Jakarta ta jawo afusace ta hankada murfin motar ta wuce tagefensa tayi cikin gida da gudu tana shiga falo wani kuka ya kubce mata direct dakinta ta wuce tana zubda hawaye


Papa kuwa yadda ta barshi awajen yakai minti goma baiko motsa ba yarasa wacce hanya zaibi ya samu yafiyarta wasu hawaye masu zafi yaji suna zuba akan fuskarsa


Kuma hakan datayi ko kadan baiji haushintaba sabida yasan abinda yamata bana kadan bane


Tashi yayi ahankali ya nufi cikin gida yana shiga shima ya wuce dakinsa cikin qunan rai ya dauko sigari ya kunna amma sam ko zuqa daya kasawa yayi haka ya kashe sabida alqawarin da yayima zuciyarsa yabar shan komai




Momcy da daddy suna tsaye jikin window suna kallon dik abinda sukeyi har suka shiga cikin gida


Momcy ta juyo tace daddy kaga papa ko tun bayauba nafahimci taketakensa kawai kallonsa nake naga iyaka gudun ruwansa




Daddy yayi murmushi yace aini tun rananda yafara ganinta nafahimci inda ya dosa sabida yadda lokaci daya ya birkice nan yafada mata yadda sukayi dashi




Momcy tace zaici qaniyarsa ai dan kuwa akwai wadda fauziyyah takeso har jiyama yazo da yamma


Daddy yace good haka nakeso Allah ya daidaita su shikuma zaigane kurensa




*****
Tana shiga daki ta kwanta akan gado tai kuka harta gode Allah kuma tarasa dalilin kukanta


TJ ne ya kirasa dan yaji yadda suka qare cikin damuwa ya zayyanema sa yadda sukayi yace TJ i dont know what to do nayi iyaka qoqarina amma ko saurarana batayi pls TJ help me out


TJ yayi shiru yace shikenan zansan abinyi amma kaci gaba da addua dakuma lallaminta harta amince


Suna gama waya TJ yasamu khairy ya fada mata halin da ake ciki ya roqeta taje gidan momcy gobe ta taushi fauziyyah


Da yamma washegari bayan fauziyyah ta taso aiki sukayi waya da khairy TJ ya kawota


Saida suka shiga daki bayan sun gaisa da momcy nan khairy tafara bawa fauziyyah baki akan ta haura tayafewa papa


Fauziyyah tace dake bake akaciwa mutunciba ko dole mijinki ya dauko yakawo mana saboda abokinsa




Khairy tace wlh ko kadan nibadan haka bane kefa musulmace kuma kada kimanta Allah ma muna masa laifi kuma muroqi yafiyarsa ya yafe mana


Kiyi haquri komai ya wuce wlh Dr yayi danasanin abinda yamaki kuma tunda harya baki haquri saiki hakura kodan albarkacin su daddy


Shiru tayi tana tuna irin walaqancin daya mata sai hawaye




Nan khairy taita lallashinta tace kimanta abinda yafaru abaya matuqar kina tunawa to bazaki taba haquraba


Tabbas kowa yasan abinda papa yamaki bai kyautaba amma ai yaga sakayyah nishawara nabakk ba doleba amma kiyi tunani akai


Fauziyyah tace nagode khairy Allah ya bar zumunci kuma insha Allahu komai ya wuce amma nance kifadama mijinki ba














Khairy tace oh miye laifin Abban mubeen wlh har kullum shi yana bayanki fa


Ya tsina fiska tayi tace tunda abokin ya Alamin ne shiyasa baruwana daku ai




Khairy ta sheqe da dariya tace toh amana afuwa






Dariya sukayi gaba dayansu sai bayan magriba sannan tamata sallama ta tafi.....




โœ๐ŸปFaty Mmn Faty








๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ



๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




5โƒฃ0โƒฃ
Aranan bayan tafiyan khairy taita tunani takuma gamsu da shawarin da khairy ta bata kodansu daddy ma ya cancanci ta yafe masa kuma kodan tasamu yarabu da ita zata furta masa kalmar yafiya




Tindaga ranan suka shiga wasan boye, dik hanyar datasan zai hada ta da papa ta kaurace masa


Papa kuwa dik yadda yasan zai hadu da ita yanayi amma abin ya faskara


Har sati biyu rabonda su hadu, a hospital kuwa baiyi gigin zuwa wajenta ba dan kada ta yankwanasa acikin mutane gashi kowa yana ganin girmansa


Amma ya qudiri aniyar kota halin qaqa sai yayi magana da ita sabida haka yau da wuri ya shirya saida ya daidaici lokacin fitanta sannan ya fito


Cikin saa kuwa yasamu momcy da daddy ma dik suna break fast sabida daddy zaifita shima


Assalamu alaikum ya masu sallama yana ajiye jakar system nasa akan kujera a falo


Dik tsayawa kallonsa sukayi


Fauziyyah data debo abinci zata kai bakinta sai ta daga idanunta ta kalloshi itama abin mamaki ya bata


Yau sanye yake da wata dakakkiyar shadda army green tasha aiki mai tsadar gaske


Hularsa kalan kayansa ga wani agogon azurfa dagani ba tambaya kasan kudinsa dayawa


Abinka da farin mutum sai yafito kwarjininsa ya qaru akanna nada dan kayan baqaramun karbansa sukayiba


Abinda ya basu mamaki shine rabonsa da saka manyan kaya haka tun bikinsa da juhaina wadda shine na biyu daya taba saka jumper arayuwarsa


Amma kuwa saiya karbeshi sosai ya fito masa da kamalarsa na cikakken mutum


Qarasowa dinning din yayi yana cewa mornimg daddy morning momcy


Momcy tayi murmushi ganin sauyin da take gani awajen danta tace morning son har anfito yau da wuri haka


Umm inada wani aiki shiyasa na fito da wuri


Daddy yace Dr yaukuma aure zakaje daurowane ba katin gayyata


Murmushi yayi yana sosa keyarsa yace haba daddy kawai dan nasaka saiya zama aure zanyi


Daddy yace ah toh nasani tunda baswa kakeyiba saida dalili


Murmushi yayi yace aa kam kawai nayi shaawar sawane


Daddy yace ko kaifa amma mutum kullum cikin qananun kaya dik jiki atakure amma nasan yau kafi jinka very compotable haina(koba haka ba)


Hakane daddy ya fada yana daukan fork dan shima abincin zaici


Fauziyyah kuwa da tunda ta kallesa sau daya bata qara bin takansa ba bata kuma cemasa kala ba saima ajiye cokalinta tayi ta miqe zata bar wajen


Momcy tace badai kin qoshiba


Cikin shagwaba tace naqoshi momcy zan wuce office


Daddy natafi saina dawo


Momcy tace toh Allah ya tsare hanya daddy ma yamata addua adawo lfy sannan ta fice


Papa kuwa harta fice kallonta yake sabida komai nata birgesa yake baran ya kwan biyu baiganta ba


Haka muryarta baqaramun dadi take masa ba koda masifa take muryarta dadi takeyi baran yanzu dayaji yadda tayi magana ashagwabe sai yaji taqara birgesa


Zama yayi ya break nasa hankali kwance koba komai ganinta da yayi yasami natsuwa


Yau aiki ya riqe masa wuta sosai gashi ranan saturday mai zuwa zaayi bikin sabon asibitin da suka bude mai suna *NAMSA MEDICAL CENTER*


Tinda ya dawo suna tare da daddy har suka fita masallaci tare


Ranan saturday aka bude sabon asibiti hadi da walima


Manyan mutane sun hallarta sosai sannan abin ya qayatar abin birgewa


Da yamma momcy ta shirya walimanta acikin gida inda itama ta gayyaci yan uwa da abokan arziqi


Fauziyyah kuwa tinda aunty mabarukha tazo suna tare har aunty niima tana mata tsiya


Papa kuwa tinda ya dawo yana kwance adakinsa dan yagaji sosai tashi yayi ya wanka ya shirya cikin wani danyan boyel ash colour wanda yamatuqar amsan fatar jikinsa ya kafa hulan nan kamar wani ango


Har ya juya zai fita sai yaje jikin window ya daga curtain dan yagani kozai samu ya fice dan tun daxu yakejin hayaniyar mutane


Kamar wasa ya hangi fauziyyah tasha ado da kwalliyah cikin wani matetial maroon colur dinkin doguwar riga


Ta kafa dauri tayi kyau sosai


Tana tahowa kallonta yake yaga inda ta nufa saiyaga ta shige lambu ta qofar baya inda ake shiga bayin fulawa aiko cikin sauri ya fito ya nufi lambu shikuma ya shiga tacikin falo


Can ya hango ta zaune akan kujera da waya akunnenta


Itakuma wayarta da aka kira yasata shigowa lambun


Qarasowa yayi inda take zaune yaja kujeran gefenta ya zauna


Dagowa tayi ta kallesa sai tayi kamar bata gansaba taci gaba da wayanta ita da Barr.Nabeel


Daure zuciyarsa kawai yayi yanajin yadda take fadan kalaman soyayyah dikda baisan itada wayeba amma yana tunani itada wanda yataba ganinsu tarennan ne


Takai tsawon minti goma tana waya sannan tayi sallama tana sauqe wayar akunnenta ta miqe zata bar wajen


Cikin sauri ya riqo hannunta juyowa tayi afusace ta wurgesa da wani matsiyacin kallo


Saketa yayi da sauri wanda abu biyu yasa yayi saurin sakemata hannun


Nafarko wani danbanzan shorck dayaji kamar wadda wuta ta jashi na biyu wani kallo data watsa masa


Fiska atsuke tace malam wayabaka izinin riqemun hannu


Atausashe yace am sorry pls badagangan bane


Juyawa tayi zata wuce yayi saurin cewa pls Fauziyyah kisaurareni mana tunda nazo wajenki kinsan da magana nazo


Ko kulashi batayiba ta wuce abinta


shan gabanta yayi hakan yasa dole ta tsaya


Pls fauziyyah nasan cewa namaki laifi amma mutum idan yagane kuskure ya roqi yafiya aisai ayafe masa


Kifadi abinda kikeso namaki danki yafemun


Shiru tayi tana sauraronsa yadda yake bata haquri kamar zaiyi kuka tabbas ya Alamin ya sauya fiye da tunaninta


Roqo yake magiya yake haka ya durqusa awajen


Wani iri taji aranta tana tunanin yadda mutum ke sabawa Allah yaroqeshi gafara ya kuma gafarta masa asheko inhakne dole ta yafe masa


Cikin sanyin murya tace ya isa haka ya Alamin yawuce har abada Allah ya yafemu gaba daya amma dan Allah na roqeka daga wannan kada ka kuma shiga harkata koda magana bana buqatar yahadamu


Wani zufane ya yanko masa yace ashe ko inhakane baki haquraba kada kimanta kefa yar uwatace nidan uwankine


Tace yau kenan kasan da wannan yafiyakam nayafemaka har zuciyata kawai alaqa dakaine bana buqata tana fadin haka ta wuce abinta


Jiki asanyaye ya tashi ya wuce dakinsa yaji dadin yadda ta yafe masa amma yadda ta furta wai bata qaunar alaqa dashi shiya damesa gashi riqe hannunta da yayi shiya tuno masa wasu lokuta daya samu kansa acikin zamansu nabaya


Fitan dabaiyiba kenan ya kwanta jikinsa amace.....




*Alhamdulillah anan zandakata sai ALLAH ya kaimu ya nuna mana bayan sallah lafiya sannan mucigaba*


*Inayima dikkannin Al'umman musulman duniya fata da addu'ar yin sallah lafiya*


*Allah yasa muyi hidiman sallah lfy cikin kwanciyar hankali Ameen*






โœ๐ŸปFaty Mmn Faty












Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017


*Alhamdulillah Taqabalallahu minna wa minkum, dafatan munyi sallah lfy Allah ya maimaita mana, EID-EL KHABIR MUBARAKH*


5โƒฃ1โƒฃ
Soyayyah mai karfice ta shiga tsakanin Barr. Nabil da Fauziyyah


Soyayyah mai tsafta suke gudanarwa atsakaninsu


Kamar wasa son Brr. Nabil ya shiga zuciyar Fauziyyah sabida kyawawan halayensa da son addininsa da kuma yanda yake nuna mata zallar kauna da baya gajiyawa da dik irin abinda take masa na halin ko inkula


Ayanzu ta amince da aurensa kuma tayi naam dahakan har zuciyarta


Afannin Barr. Nabil shima yayi farin cikin amincewarta
Inda yanzu har gidansu sun san yana nemanta


Ummansa tayi farin ciki sosai sabida bata da burin daya wuce ganin dannata yayi aure


Kusan kullum sai yazo gida sunsha hira abinsu dan momcy da daddy ma sunsan da zamansa haryazo ya gaidasu kuma sun amince dashi dan sun yaba da natsuwarsa


Wani lokaci yakanzo asibiti ya sameta sabida yanda yake qaunarta dik lokacinda yaji yana son ganinta saiya taho abinsa


Dik abinda kefaruwa papa yana sane kawai ba yadda ya iyane kuma abinna daminsa kawai baya da mafita ne


Dik lokacin dayayi niyyar yimata magana idan ya tuna kalmar datace wai bata buqatar yin alaqa dashi sai yaji zuciyarsa ta masa zafi


Yauma kamar kullum Brr. Yazo sun hira kasancewar saturday ne dik suna gida


Tun zuwansa papa yake tsaye jikin window yana kallonsu yana jin wani zogi acikin zuciyarsa dan ahar kullum son fauziyyah qaruwa yake axuciyarsa


Yakuma yi niyyar dik abinda zai faru saidai ya faru amma yagaji da wannan walaqancin da cin fuskar da take masa sabida zuciyarsa ta aminta kawai dagangan take masa haka


Itakuwa batamasan yana yiba dan baya gabanta baran tamasa abu da gangan


Yana nan tsaye yanajin zuciyarsa kamar tafashe dan baqin cikin yadda yahango su suna ta dariya abinsu basa da matsalar komai


Tinda yahango Brr. Zai tafi ya fito ya tsaya aqofar falo ya harde hannuwansa aqirji yana jiran isowanta


Kamar wadda akace Brr. Ya juyo aiko ya hangi papa fiskannan ba annuri


Duban fauziyyah yayi yace my life nikam wancan yayan nakin haka yake bai magana ma mutane ne


Cikin ko inkula tace me kagani


Yace sau uku muna haduwa ina masa sallama amma ko ya kulani last zuwana hospital wajenkima mun hadu zan fita shikuma zai shigo ina daga masa hannu amma yayi kamar bai ganniba


Tabe baki tayi tace next time kada kasake kulasa ka rabu dashi kawai


Yazakice haka baicin dan uwankine yafada yana kallonta


Tace to halinsa ne haka idan baiga dama ba kozaka kwana kana masa idan baiga dama ba bazai kulaka ba


Jinjina kai yayi azuciyarsa yace amma ko baida hali afili kuma yace Allah ya kyauta nizan wuce sai munyi waya


Tace toh Allah ya kiyayae hanya agaida umma dasu sis raudah


Toh zasuje sannan ya tafi


Aiko tana nufowa cikin gida tinkafin ta qaraso papa ya taho ganin haka yasa ta kauce ta wucesa


Fauziyyah Fauziyyah Fauziyyah yake kiran sunanta amma ko ta amsa baran ta tsaya


Pls kisaurareni mana ya ina maki magana zaki maidani dan iska


Har takai qofar falo tasa hannu zata bude dan bata da niyyar amsashi


Cikin zafin nama yasa hannu ya fincikota baya


Aiko nan tayo baya kamar zata fadi sabida da iyaka qarfinsa ya janyota dan ransa yagama baci


Cikin sauri ya tarota ta fado akan chest nasa


Wani yarr gaba dayansu sukaji lokaci guda wadda hkan yasa papa sauqe wata wahalalliyar ajiyar zuciya hadi da lumshe idanu


Wani kasalane ya sauqo mata jin yadda ya maqale hannunsa ya zagaye waist nata


Kome ta tuna cikin sauri tasa hannu biyu da iyaka qarfinta ta turesa


Amma kuma takasa barin wajen sabida yadda qafafunta suka mata nauyi


Cikin dakewar murya tace meyasa bazaka rabu dani nasha iska ba abaya kace yafiyata kake buqata kuma na yafe maka to yanzu kuma what else kake buqata ta qarashe maganar cikin fada


Shima da fada fada yafara magana dik da irin yanayin dayake ciki amma dake ta tabomasa indake masa kaikayi yace


Nagaji da irin azabtar dani da zuciyata da kike yi nagaji da ganin walanqancin da kike mun agabana kina tsayawa da wani da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login