Showing 63001 words to 66000 words out of 86122 words
Chapter 22 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt
kiran sallan laasar sunayin sallah suka fara shiri daya daga cikin abokansa guda uku da sukazo daga india yace shikam yau jumper zaisa dan yana shaawar kayan shiyasa yasaka aka dinka masa dan yayi shigar hausawa
Ango ne nagani ya dau wanka cikin wani coppee brown yard mai kyau da sheqi
Kyansa shiya bayyana tsadarsa
Sum matuqar karban fatan jikinsa abinka da farin mutum
Ya kafa wata tsadaddiyar huwa
Brown covvers yasaka aqafarsa sai agogon azurfa dake daure ahannunsa
Ga wani uban qamshi dayake xubawa na musamman
Tabbas ya fito a Ango sakππ»
Nan fa su Dr khalid suka fara tsokalansa anata barkwanci
TJ ne ya kirasa awaya yana dauka yace yane kuna inane
Papa yace muna gida amma yanzun zamu wuce
TJ yace shine ka azalzalemu ashema baku fitoba to gashinan yanzun haka muna hanya mun dakko amarya
Papa yace to sarkin mita naga dai munfiku kusa dawajen ko kafin ku qaraso mun iso muma
Ok toh saimun hadu
Nan suka fito suka shishshiga motocinsu suka wuce wajen da zaayi KAMUN
Su papa suna isowa su TJ ma suka iso
Sunsamu angama taruwa amarya kawi da ango ake jira
TJ yace basai kunfitoba barin su qaraso naga suna tahowa sannan shima ya fice
Ta cikin glass take hangosa shida abokansa suna tahowa sunkuyarda kanta kawai tayi wadda ita kadai tasan yanayin datake ciki
Suna qarasowa yasa hannu ya bude motar datake ciki
Ya salam shine abinda ya furta ahankali ganin irin kyan datayi
Sanye take cikin wani less pich colour mai toches na coppee brown
Dinkin riqa a siket wadda yamatuqar qarbanta kaman ba gobe
Fiskantannan yasha makeup
Dan qaramin bakinnan anlailayesa da pinks jambaki
Kyaukam baa magana gashin kantannan sai sheqi da qamshi yake andaureshi waje guda da pich ribbon
Sai head na kanta shima coppee brown jeweries natama wasu passion ne dik suma coppee brown masu adon duwarwatsu pich n white
Takalminta da purse nata dik coppee brown
Ahankali yake sakin wani murmushi wadda shikadai yasan maanarsa
Daurewa yayi ya daidaita muryarsa ya kira sunanta cikin wani tattausan murya yace my princess
Dago daradaran idanuwanta masu yarwar lashes tayi ta amsa da muryarta mai dadin gaske naam
Wani lumshe idanu yayi sannan ya bude yana kallon kwayar idonta wadda yasha kajol da maskara tare da siririn line eye liner
Sannan yace meet my friends yana kirga mata sunansu
Dik saida suka gaisa kuma sun yaba da zaben abokin nasu
Daga qarshe ya introducing mata abokansa uku da sukazo daga india yace yeh he Himesh(wannan shine Himesh), Salman aur Imran(da)
Cikin sakin fuska suka gaisa nan TJ ya qaraso yace man kukadai ake jirafa
Papa yace ok muje toh duban Fauziyyah yayi yace my princess muje ko
Cikin natsuwa ta sako qafarta nan yasake shagala wajen kallon lallen da aka qawata qafarta dashi na zallan jan rani
Jerawa sukayi cikin takun qasaita dan jin kansa yake asama qasaisatar ta motsa jinin sarautar ya tsinke
Fauziyyah kuwa dik saita jita atakure dake ita bawasu qawaye ke gareta ba kwakwata su shidane sai
Suna shiga cikin hall din waje ya kaure da tattausan waqa mai dadin gaske
Wajenda aka qawatashi da ado sosai kuma kalan kayansu hatta ballons da aka decourating wajen pich n coppee brown ne
Wasu kujeru ne guda biyu iri daya masu kyan gaske suka qarasa suka zauna sai kuma na abokanai da qawaye da aka ajiye daga bayansu
Kowa ya shashe ranan angwangwaje naira tayi kuka ko motsi tayi saiyace yadai baby kingaji ne sabida yadda yakeji kamar ya maida ciki dan so
Fans na Mmn Faty Novel ma baa bassu abayaba dan sun nuna murnansu sunkuma nunama ma fauziyyah gata
Kodagakan irin liki da sukaringa mata shima abin ajinjina masu ne
Baa tashi ba sai gabda magriba sannan taro ya watse
Ahanyar su ta komawa gidane papa yaga canji yayi juyin duniya fauziyyah tayi magana amma taqi sam shikuma harga Allah baison shirunta shifa ko zaginsane garatayi yasan tayi magana dan baimanta lokacin data kullaci abu aranta tadaina masa magana
Haka suka sauqeta suka dawo gida
Washe gari Thursday akayi Family n Friends day
Nanma sunyi kyau ba qarya
Ranan friday akayi Hafla
Sai washe gari Saturday misalin Qarfe sha daya na safe dubban jamaa manyan mutane maaikata yankasuwa hadda sarakuna da sauran Alumma suka shaida daurin Auren Dr Muhammad Alamin Abubakar n Fatima Usman abisa sadaki 100k lakadan ba ajalanba
Papa dai bakinsa bai rufuwa daka ganshi kasan yana yanayin farin ciki lura daga kayan jikinsa komai fari tass
Sai gaisawa yake da jamaa kawai
Makada da maroka kuwa sai wasashi sukeyi abindai abin birgewa sai muce Allah ya kade fitina kawai
Da yamma akazo daukan amarya
Wata goggonsu papa wadda take yace awajensu daddy ita tabada wata Alkyabba ta musamman tace asawa amarya ita
Fauziyyah tai kuka harta gode Allah sabida nasihan da su Abba suka mata mai ratsa zuciya da dikkan gangan jiki
Da mata adduan Allah yasa sai gawanta zaa fitar agidan Alamin
Haka aka wuce da ita fada su anty papa aka samu a side din da zaa sauqi amarya
Nan suka karbi amarya da murna da farin ciki gami da mutunchi
Nan suka shiga hidima da baki dan Aunty naja(Auntyn Papa ) batada rowa kuma batason harkan qaranta
Dik wadda yazo kawo amarya ya yaba da irin kaunar da yan uwan papa kema Fauziyyah sai fatan alheri suke musu
Bangare guda Aunty papa ta sauqi Fauziyyahs' team
Kuma sun yaba sosai dan Aunty papa bata musu qarantaba ta nuna musu cewar biki ake na dan gata
Har wajen magriba fauziyyah taqi yin shiru sai kuka take
Saida Aunties dinta suka shigo suka lallasheta sannan tayi shiru
Anayin sallan ishai Aunty mabarukha ta kawo mai kwalliya akayima Fauziyyah
Wani mterial ne dinkin doguwar riga milk n golding colour tasaka wadda yasha ado sosai yakuma matuqar yimata kyau
Kwalliya sosai aka mata sai dan veil din rigar wadda shima golding colour ne tayane kanta dashi
Wani danqareren saitin gold Aunty Mabatukha takawo mata tasaka hadda bangkes dinsa manya guda biyu
Takalmin hill ne sosai da purse dinsa suma golding colour
Wasu turaruka na musamman tafesa wadda dik aunty Mabarukha ce takawo mata su
Nan tafito a amaryarta ba qarya
Members na Mmn Faty Group sunsha anko dinsu na material
Fauziyyahs's team sunyi ankon material golding colour
Sai papas' team sukuma ankon material milk colour sukayi
Nan aka fara tafiya dinner kowa ya tafi sai Fauziyyah ita kadai akabari dan wannan umarnin Ango ne
Tana zaune abakin bed shiru itakadai sai taji motsin bude qofa
Bata dago kanta ba amma qamshin turarensa daya gauraye dakin shiya tabbatar mata papa ne
Sanye yake da wani dhegen gezna maih danbanzan kyau da tsada Milk colour
Dikin yamatuqar amsansa ga hularsa da ta dace da kayan hafi da takalminsa
Qaremata kallo kawai ya tsaya yi yana yima ubangiji tasbihi acikin zuciyarsa daya mallaka masa ita amatsayin mata
Ahankali ya tako har bakin gadon datake zaune
Maganama ya kasa kawai hannunta ya kamo ya riqe gam acikin nasa
Wani taushi dayaji shiya haifar masa da kasala lis ajikinsa
Dayan hannunsa yasaka yana murza bangles din hannunta
Da wata iriyar murya yace my princess pls na roqeki kimun magana kinji
Kallonsa tadanyi ta kasan idanunta ta dan turo baki tace to mai zance maka pls kasakemun hannuna
Cos yadda yake wasa da hannun nata dik sai taji ta takura
Shikuma gyara zamansa yayi yama manta da yabar mutum awaje nan yafara barbada mata maganganun soyayya
Qarar wayarsa yasashi yin dan qaramin tsaki dan yana tsaka da jin dadin yadda yake manne da ita bata kuma turesaba
Ganin TJ ne yasa yace yane akayi
TJ yace lallema toh kawai kace inje insallami mutane tunda kai kasamu waje bazaka fitoba
Papa yace oh yaushema nashigo to naji gamunan fitowa
Baby nah mujeko kinga wannan dan damuwar da takurin yafara mita
Batace dashi komaiba hannunta ya riqo ta miqe suka tako ahankali suka fito....
βπ»Faty Mmn Faty
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
*Banmanta dakeba takwarata Fatima Muhammad(Miyatti Allah), nagode da kulawarki gareni Allahu ya bar qauna, Mmn Faty ππ*
6β£1β£
Hannunsa riqe acikin anata har bakin mota
TJ dake tsaye yana jiransu shiya bude mata
Da murmushi afiskansa yace bismillah Amaryanmu
Batace komaiba sai murmushi datayi sannan ta shiga tazauna
Ya rufe kafin ya zagaya ya shiga shima
Papama ta gefenta ya zagaya ya zauna
Tafiya suke suke bamai cewa komai itadai ta sunkuyar dakanta tana wasa da ring din yatsanta
Papa kuwa ya wani matso jikinta kamar wadda zai shige cikinta amma baicewa komai cos hakanma he is totaly satisfied
TJ kuwa katse shurun yayi da kunna wani tattausan music mai dadin sauraro
Da haka har suka iso
Batare da bata lokaciba abokai da qawaye suka rufa musu baya zuwa cikin hall din
Lokacin da suka shigo nan aka fara musu ruwan wasu flowers masu kyan gaske da qamshi mai dadi
DJ kuwa waqar da aka masu ta biki ya kunna nan waje ya birge sosai
Cikin takun natsuwa suka qarasa wajen zamansu kafin kowa ya sami waje ya zauna
Baqarya wajen ya qayatu ya kuma matuqar birgewa dan naira tayi kuka
Nan aka fara gudanar da programs iri da ban da ban
Idan ka kalli Amarya da Ango ka rantse kace wasu couples ne masu mutuwar son junansu
Yadda fauziyyah tasake fiskarta kamar bawani abu aqasa
Shikuma uban gayyar dama sai faraa yake kamar gonan auduga yana wani shige mata ganin yadda ta saki jikinta tamkar ba itaba
Kowa ka gani awajen yasha ado da kwalliya gaskiya bikinsu papa ya matuqar tsaruwa sai fatan zaman lfy
Sai wajen 12 aka tashi
Saida kowa ya watse ya rage su papa aka bari kafin suka taho suma
Ahanya papa yacema TJ man kadaukomin saqona daiko
TJ yace waneni namanta yana gaba nan qasan seat
Papa yace ok thanks
Suna isowa gida TJ ya bude mota ya miqo masa ledan take away sannan ya fice
Itama bude qofar motar take qoqarin zata fice
Riqo hannunta yayi
Juyowa tayi ta sauqe daradaran idanuwanta akansa kafin dan qaramin bakinta ya motsa gami furta lfy daiko
Yadda tai maganar ba walwala afiskanta yasa ya marairaice murya yace pls kiban 15mins acikin lokacinki
Pls mana dear badan niba dan Allah
Komawa tayi tazauna
Thanks yafada sannan yasake mata hannu
Take away din ya bude pepper chikchen ne wadda yasha hadi sosai
Kallonta yayi da kyau kafin yace baby pls bawasa nakeba kici abinci kuma kada kice aa dan nasan wunin yau kaf da wuya idan kinci wani abin
Shiru tayi tana tuna tabbas yau bataci wani abinkirkiba
Bude motar yayi ya balle bottle din ruwa ya dauraye hannunsa
Naman ya kutsiro ya miqo mata saitin bakinta
Ba musu ta karba tafara tauna ahankali
Ganin yadda batai gardama yasa yaci gaba da bata abaki tanaci
Matsowa yayi sosai yana lallabata harta ci sosai kafin ta kauda kanta
Ruwa ya bata tasha sannan ya bude mata roban juice sai anan ta kauda kanta tace umum
Murmushi yayi yace thanks a lot wifey nagode muje narakaki ko
Aa kawai tace dashi tafice abinta
*****
Washe gari sunday akayi walimah dasafe daganan wasu suka fara tafiya garuruwansu
Amma su papa sai gobe dasu koma bh
Abdu yasa ya maida su Himesh bh sabida gobe jirgin safe zasubi zuwa lagos dagacan su wuce
Abokanansu dik sun koma TJ ne bai tafiba sai gobe zasu wuce tare da Ango
Itama qawayenta dasukazo daga bh guda biyu sun koma sauran ukun dama yan uwane
Haka ta yini shiru itakadai su aunty mabarukha ma basu zannaba sabida sallamar baqi
Shima haka ya wuni sallama da baqi gashi sunje gidan Abbama sunjima acan
Sai dare aunty mabarukha ta shigo nan tace tana da magana da ita
Gyara zamanta tana sauraronta
Aunty mabarukha tace abinda zan fada maki kidauka ni yar uwarkice kuma ciki daya kikuma dauka bansan papa banida alaqa dashi
Taci gaba dacewa inason kidauki wannan auren yana cikin kaddaranki arayuwa wanda baki isa kikaucewaba
Kuma tunda har Allah ya rubuta haka inason ki haqura kidauki qaddara ki rungumi mijinki kimasa biyayyar aure
Dik halin da kuke ciki da papa ina sane amma yanzun tunda andaura maku aure zance ya qare
Kuma bama fata abinda zai kuma rabaku sai dai mutuwa
Jikintane yayi sanyi kuma ko itama tunanin datake aranta kenan tunda Allah ya qaddari haka tafaru gara ta dau haquri suzauna lfy
Aunty mabarukha tace sabida haka kidauka dik abinda yafaru abaya kamar bai faruba kuma bama fatan ya kuma faruwa
Kuma ina da tabbacin hakan bazai faruba sabida yanzun papa yana sonki so mai tsananin gaske kuma zai iya komai akanki
Amma bawai ina nufin dakunkoma bh kibada kai bori ya hauba aa ki nuna masa cewar kema mace ce
Saikin dan wanasa tukun saiki saqqo ku zauna lfy Allah ya albarkaceku
Sannan kada ki kuskura kiyadda kunya ta cuceki dan matuqar zakiji kunyan yin wani abin toko zaki kwari kanki
Gobe akwai kayan dazan kawo maki idan kinkoma bh
Su zaki ringa sawa agida kina kwalliya tareda yin qayataccen girki kuma kada kihanasa
Kibashi dik tarkone yadda zaiji kawai bazai iya rayuwa bakeba kuma komai kikace yamaki zai maki
Amma kada kimanta kina riqe da class naki harsai yagane kuransa yadda koda kudi akabasa bazai tabayin gigin batamaki raiba
Dafatan kinfahimceni
Cikin sanyin murya tace insha Allahu aunty zanyi yadda kikafada
Aunty tace yawwa qanwata Allah ya maku albarka sannan zanyi magana da Aunty naja(Aunty Papa )tace zatana aiko maku da abinci zance tabari kawai sabida musamu tarkon ya kamashi
Tace toh aunty nagode Allah yabar zumunci
Miqewa tayi tace barinje wajen momcy sabida shirin tafiya amma zandawo mukwana tare
Tace toh saikin dawo itakuma ta fice
Shiru tayi tana tuna maganganun da aunty tafada mata tabbas gaskiyane
Da haka har bacci ya kwasheta sabida dama agajiye take batamaji shigowar Aunty ba
Washegari wajen laasar suka iso bh
Direct gidanta aka wuce ta da ita wannan umarnin daddy ne
Shima papa gidan ya taho yayi wanka sannan ya fita amsa kiran daddy baiko leqa taba dan yasan tana tare da mutane
Aunty ma cewa tayi bari taje gida zata aiko hannatu mai aikinta wadda tare sukazo da driver su kawo mata wannan sakon
Nan sukayi sallama akan suma gobe zasu wuce
Su Aunty niima ma cewa sukayi tafiya zasuyi dik suka watse suka barta ita kadai
Suna zolayarta ainty ce tace Allah ya kaimu next year kamar haka muzo musha suna
Aunty niima tace aikin kai da nisa dama cewa kikayi nanda 9months kinaga yadda papa ke rawan kannan ai kinsan basauqi
Itadai batace komaiba dan kunyama suka bata
Bayan sun tafi itama ta fito tafara zagaya gidan
Tana kallon yadda aka barar da dukiya tundaga kan ginin har izuwa kayan cikin gidan
Ta jinjinama daddy takuma gode masa dan baqaramin rawar gani ya takaba
Tsayawa fasalta kyan gidanma bata lokane mai karatu fasalta da kanka kawai
Sai datayi sallan magriba da ishai sannan tashiga qayataccen toilet dinta ta sheqa wanka
Kwalliya tayi sosai cikin atamfa lemon green mai matuqar kyau
Tayi kyau abinta dambun naman da momcy ta aiko mata lokacin da aka kawo mata saqon aunty mabarukha shitaci ta koshi abinta
Lfyr gado tabi tadau wayarta ta hau facebook tana maida saqon fatan alkhairi da aka turo mata na biki
Papa kuwa ahanyarsa ta dawowa gida saida ya tsaya ya sai masu tsaraban irin wadda ango ke kawoma Amarya
Hankalinsa dik yana wajen Fauzynsa dan yasan ita kadaice agida
Yana zuwa bakin gate ya danna horn maigadi ya bude masa ya shige
Parking yayi sannan ya dauko ledodin daya saya ahanya ya nufo gida
Kamar zai wuce dakinsa amma saiyaji ina baxai iyaba saiyaga lfyrta tukun
Tana kwance taji anturo qofar anshigo tare da sallama
Dago kanta tayi kallo daya taimasa tasauqe kanta
Cikiciki ta amsa sallamarma
Shikuma wani murmushi yayi ganin yadda kwalliyar tamata kyau saita sake shiga ransa
Takowa yayi ya ajiye ledodin hannunsa ya qarasa bakin gadon ya zauna kusa da ita
Sai anan ta dago kanta fiska atamke take kallon yadda ya wani zauna kamar zai rugumeta
Why have u come here? Tafada tana kallonsa
Murmushi yayi mai qayatarda face nasa yace nazo ne naga yadda kika yini nakuma miki bangajiya konayi laifine yin hakan baby na
Eh,tafada
Cikin sauri ya dubeta yace bakiso kenan na duba lfyrki
Banaso nanma tafada kanta tsaye tareda juya masa baya
Jikinsane yayi sanyi cikin sanyin murya ya fara magana
I really understand why u ar very angry
Juyowa tayi tace ya Alamin i don't want any discussion, it will be better for u to getout of my room, pls go now
Shiru ya danyi kafin yafara magana da muryar nadama yace baby i do not have the courage to look in to ur eyes
N there's no doubt that i had made a mistake n it is true that i regret everything that i have done
Naji naji pls saida safe banason dogon zance tafada tana juyawa
Yace to kifadamun abinda zanmaki wanda zai zama punishment agareni ke kuma ki huce
Tace maganace banason kamun inhar ba nice na nema ba thats all
Shiru yayi yana jinjina maganar amma bayadda ya iya dole ya amince
Cikin murya mai sanyi yace ok naji inhar hakan zaisa kihuce kuma kiyafemun i accept this punishment
Yana fadin haka ya miqe jiki amace tare dace mata ga Abinci kici kada ki kwanta da yunwa kafin yafice zuciyarsa wani iri yana sakejin tsanar kansa dan yasan shiya jama kansa.....
βπ»Faty Mmn Faty
Budurwar Qauyeπ€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
*Wannan shafin nakine PA ta (Ummy Danees), Banmanta dake ba kina raina Allah ya barmu tare da Qaunar juna Mmn Faty luvs u ππ*
6β£2β£
Yana fita ta gyara kwanciyarta abinta taci gaba da abinda takeyi da wayarta
Sai wajen 10 sannan ta kashe data ta sauqa, kayanta ta canja zuwa na bacci tabi lfyr gado abinta
Baccinta tasha hankali kwance ko juyi bataiba har asuba sabida gajiyar hayaniyar biki
Kiran sallan farko alarm na wayarta ya tasheta
Ita kanta tayi mamakin yadda tasha bacci babu ko farkawa
Toilet taje ta dauro Alwala tadawo tafara nafila kamar yadda kullum tasaba
Saida aka kira sallan asuba sannan tayi rakaa tainil fajr
Tayi sallar asuba kafin ta bude Alquraninta tafara karatu har haske ya fito sannan ta rufe tayi adduo inta
******
Papa kuwa yana fita dakinsa ya wuce
Yana shiga ya rage kayan jikinsa ya fice toilet
Ruwa ya watsa ya dauro towel ya fito, dik abinda yake zuciyarsa a jagule yakejinta
Dan cream ya shafa nanma samasama sannan ya saka kayan baccinsa ya kwanta
Tunani kalakala su suka addabi zuciyarsa
Tuno kalaman daddy yayi akan gargadin daya masa kan kada koda wasa yaji wani abu marar dadi wadda yayima fauziyyah
Idan kuma haka tafaru to tabbas zai fiskanci fushinsa kuma fushi mai tsanani
Afili ya furta babu abinda zai faru da yardar Allah
Da tunanin ko yaushe fauziyyah zata saqqo ta daina fushi dashi har bacci ya daukesa amma bada wuriba
Sai asuba ya farka agurguje ya shiga toilet ya watsa ruwa hadi da alwala ya fito
Wata milk