Showing 6001 words to 9000 words out of 86122 words
Chapter 3 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt
dan yamasa qarin bayani
Daddy yace kwarai sabida Fauziyyah bata dace da miji irin papa ba, aurensu bawani abu sai tauye mata rayuwa da zaiyi, tana yarinya qarama
Cikin rashin fahimta Abba yace kafahimtar dani Alhaji
Daddy yace Alamin yacanza daga Alamin d'in daka sani, Alamin yadauko wasu halaye nadaban yamaidasu abokan rayuwarsa nan ya zayyanema Abba halin papa tas sannan yace kaga fitan da yayi yanzun toh shida yadawo sai 12am ko 1am
Shiyasa nace maka sam Fauziyyah bata dace dashiba, sai yaje can ya nemo abokiyar shashancinsa ya aura
Abba kuwa zufa kawai ke tsatstsafo masa ta ko ina
Nisawa yayi sannan yace tabbas wannan alamarine babba kuma abin dubawa.....
βπ»Faty Mmn Faty
[10:39PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
0β£7β£
Amma wannan bazai hana komaiba, Fauziyyah matar Alamin ce
Muyi fatan Allah ubangiji yasa sanadin auren yazama shiriyarsa kuma muci gaba da addua Allahu ya shiryeshi
Wani dadi Daddy yaji, rungume amininsa yayi yace nagode nagode Allah ya bar zumunci
Abba yace da Fauziyyah da Alamin dik 1 sike awajena, kamar yadda barin kyamaci Fauziyyah ba haka barin kyamaci Alamin ba
Daddy yace babu abinda zan cemaka kagama mun Komai arayuwa
Abba yace bakomai inaga kawai nan da watanni 4 masu zuwa sai ayi bikin ko kuwa
Daddy yace dik yadda ka tsara hakan zaayi, Allah ya kaimu ya nuna mana
Abba ya amsa da amin, Inyaso sai yazo su fahimci juna kafin lokacin biki
Daddy yace insha Allah next week zaizo Allah yasa Fauziyyah ta amince
Abba yace ai Fauziyyah bazataqi dan uwantaba sabida dan bawani saurayima take dashiba dan nahana babu wani wanda ke zuwa wajenta fatanmu Allah ya daidaita su
Washegari da safe Abba ya koma
Bayan tafiyar Abba Daddy yasamu momcy yamata bayanin yadda sukayi da Abba
Momcy taji farin ciki sosai, nan taji wani sabon son Fauziyyah har cikin zuciyarta
*********
Abba da mama suna zaune Bayan sun tattauna maganar biki, sai dai sam bai fada mata halayen papa ba
Mama tayi naam da hukuncin da suka yanke
Abba yace ta kira masa Fauziyyah
Tare suka shigo dakin Abba, durqusawa tayi gani Abba
Zauna da kyau mamana, gyara zamanta tayi
Fatima Abba ya kira sunanta
Dam zuciyarta ya buga dan Abba bai taba kiran sunanta haka direct ba sai yau
Naam ta amsa asanyaye
Abinda yasa na kiraki munyanke shawarin hada ki aure da dan uwanki Alamin dan gidan baffanki na bauchi
Dasauri ta dago kanta, dan jin maganar tayi kamar amafarki
Sannan ba shawarinki nake nemaba umarni nabaki, ina fata zaki amince masa dan kitayani cika alqawarin dana dauka shekara da shekaru
Kuma ina fatan yau kin fahimci dalilin dayasa, na haneki tsayawa da samari sabida gudun fadawa soyayyar wani bayan akwai mijin da muka tanada maki
Daga kanta kawai ta iyayi dan intace zatayi magana to tabbas kukane zai kubce mata
Abba yace Allah ya maki albarka, tashi kije
Tana fitowa da gudu ta nufi dakin ta, tana shiga ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, dan bata taba tunanin haka zai kasance ba arayuwarta, fatanta Allahu yasa mafarki take kozata farka taga hakan bai faruba
*********
Ranan friday da daddare, Daddy da momcy da papa suna zaune afalon Daddy
Papa yace Daddy gani
Daddy ya gyara zama da kyau sannan ya dubi papa fiska ba walwala
Alamin inason ka bude kunnenka da kyau, kuma kasaurari abinda zan fada maka umarni ne ba shawaraba dafatan kanajina
Papa yayi shiru yace eh inaji
Daddy yace good, so abinda nake so dakai gobe idan Allah ya kaimu kaje dambam gidan baffanku Usman kasami yarsa Fauziyyah ku daidaita dan aurenku nan da watanni 4 masu zuwane
Dftn kufahimci magana ta kuma banson musu ko excuse dan aure babu fashi
Papa dake zaune sai daya miqe dan jin maganar yayi kamar saukan guduma atsakar kansa
Idanunsa nan take suka kada sukayi jajur, no no Daddy shine abinda yake fada yana girgiza kansa
Daddy yace ai nagama magana kuma zamu bata dakai matuqar ka tsallake maganata that's all
Juyawa yayi yana kallon momcy ko zata sa baki
Amma sai yaji tace ga wannan ka kaima Fauziyyah kuma koda wasa kada kace nina bata, kabata amatsayin tsarabarka
Karba yayi ya fice kawai
Dakinsa ya wuce kansa kawai ya dafe dan yarasa mafita
Washegari ba wanda yayi ma sallama ya wuce abinsa dan dik haushinsu yakeji
Bayan azahar ya isa, sai daya huta kafin ya sake wanka, shiryawa yayi cikin farar shirt mai layin baqi da black jins
Baqaqen bufalinos ya saka aqafarsa kallo daya zaka masa kagane akwai naira a hannunsa
Wayoyinsa ya dauka ya fice, danwareriyar motarsa ya shiga itama baqa sannan ya nufi gidan Abba
Fauziyyah ta fito daga wanka kenan tana kwalliya dan zataje gidansu Amina Ibrahim qawarta
Sai taji mama tana gaisawa da mutum, daga yanayin maganar ta fahimci baqon da Abba taji yace zaizone ya iso
Dogon tsaki taja yanzun dik saurina ya tashi a banza kenan, naso na fice kafin yazo ta fada afili
Mama ce ta shigo tace Fauziyyah ga Alamin yazo yana waje sai ki bude masa falon abbanki
Naji shine abinda tace
Takai 15mins kafin ta fito nanma sai da mama ta sake mata magana
Papa yagama quluwa kamarshi ace wata banza har ta ajiyeshi, duba time yayi nan da 5mins idan bata fito ba to zaiyi tafiyarsa
Sai gata ta fito, fiskanta fayau ba kwalliya tana sanye da atampa riga da zani, da farar hijab
Wani wawan tsuka yaja Dan gaba daya haushi ta bashi, ji qirjinta kamar na sauro to ma yaci me da ita
Ganin yayi shiru yasa tazargi kallonta yake ta cikin glass din idonsa
Kallo 1 tamasa ta kauda kanta, ina yini tace dashi
Qalau yar Qauye, Zaro ido tayi
Yace meye kike Zaro ido qaryane, dubeki wai Budurwar Qauye ko
Toh kisani nafarko banson raini dan nasan halinki ne
Sannan wannan auren hadin iyayenmune kada kiyi tinanin inasonki kozan soki, so kitsaya amatsayinki
Kada nakuma zuwa ki bata mun lokaci
Yana fadin haka ya bude mota, wani bag mai kyau ya miqo mata gashi inji momcy
Bata riqe ba yasake, jakar tafadi aqasa
Ko kulawa baiba ya wuce ya shiga mota yayi tafiyarsa
Fauziyyah kuwa rasa ma mai zatayi tayi, lalle wannan inna bashshi abinda zai mun kare bazaiciba
Amma zan gwada masa nafishi qin wannan auren
Sunkuyawa tayi ta dauki jakar tayi cikin gida da tunani kala2 aranta........
*Toh ina jiran raayoyinku shin Fauziyyah da Alamin ta dace koda Yasir*
Idan naga comment dayawa to zaa qara sambadowa
βπ»Faty Mmn Faty
[10:39PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
0β£8β£
Dakin mama ta wuce, dangwarar da jakan tayi zata juya
Mama tace badai har ya tafi ba?
Eh kawai tace
Mama tace to wannan jakar dakika ajemun nayi me da ita
Turo baki tayi nima banaso
Mama ta qare mata kallo tace ni lfynki kuwa? Ba kwalliya nasameki kikeyiba amma yanzu naga fiskanki haka ba ko kwalli sai farin ido kamar na tsohuwar ba amurkiya
Dad'a turo baki tayi kai mama to mene aciki kawai bana raayin fita da kwalliyarne
Toh ya maki kyau, sai ki daga jakar kiwucemun dagani
Nifa mama nace maki banaso kuma mafa ni baimunba gaskiya
Wane ne bai makinba?
Alamin d'in tafada kai tsaye
Eh lalle aifa dama kallonki nake nafahimci take2nki, toh nikam baruwana sai kibari idan Abbanki ya dawo kifada masa
Amma ina baki shawarin kada ma kisoma wannan tunanin dan bamai goya maki baya atow
Kuka tafashe dashi ta juya ta nufi dakinta
******
Washegari papa ya dawo bh, direct sokoto road ya wuce
Can suka had'e da TJ sai wajen 11pm yadawo gida
Washegari da safe cikin shirin fita office ya fito, afalo ya sami momcy da Daddy suna break fast
Fiska daure yace morning Daddy morning momcy
Morning my son Daddy yace dashi, momcy tace lfy kake wani had'e fiska
Sake bata fiska yayi haba momcy yanzun ammun adalci kenan, ahadani da wata tarkacen yarinya kawai
Momcy tace au maganar bata wuce bane dama to nidai baruwana amma kanatsu kama kanka fada, jayayya da iyaye ba abine mai kyau ba
Daddy yace ai tarkacekam kaine ba na biyunka, kuma wlh Fauziyyah itace ta rufa maka asiri
Da wad'annan munanan halayen naka data aureka ahaka
Kai da kanada kunya har dakace baka sonta ai kodan hallaccin da mahaifinta yamaka sai ka haqura ka koyawa zuciyarka sonta
Miqewa papa yayi yace shikenan ai tinda kun dage na amince zan aureta dan kunaso Badan ni nakeso ba
Yana fadin haka ya fice
Direct asibiti ya wuce, excuse ya dauka akan baijin dadi
Fitowa yayi ya shiga motarsa a 360 ya figeta sai office din TJ
Sai da yayi parking sannan ya kirashi awaya, ringing biyu ya picking, ya kana office ne ya tambayesa, ok to ganinan zuwa
Yana shiga ya sami waje y zauna
TJ yana ganin yanayin abokinsa yasan ba lfy, rufe file din gabansa yayi
Cikin kulawa yace yadai man ar u alright?
Ahankali ya zare glass din idanunsa, duban TJ yayi Da jajayen idanuwansa am not ya amsa masa
TJ yace mene ne yake faruwa haka man
Rai bace yace wai aure Daddy zasumin in d next 4 months
Hhhhh TJ ya fashe da wata dariya yace kai mutumina ashe zaka kafaso gari
Papa yasake quluwa yace dan ubanka Ina fada maka damuwana kanamun iskanci
TJ yace ah ai nasan Daddy bazasu maka zaben wasa ba, wlh indai akan wannan ne har kake bata ranka gara kasake musha biki kawai malam
Papa dayaji kamar yashaqo TJ yace wai kai baka ganewane tinda abin naka iskancine kaga tafiyata
Dasauri yace yi haquri mutumina wasa nakema toh ina jinka a ina yarinyar take
Papa yace kaidai bari wata *BUDURWAR QAUYE* kawai Daddy ya jonamun
Nan yabawa TJ labari
TJ yace haba su kuwa su Daddy mene yasa zasuyi haka amma wani hukunci kayanke
Na amince zan aureta tinda naga dagaske Daddy fushi yake but sai ta gwammace bata aureniba dan wlh babu abunda zanci da wannan yarinyar
TJ yace hakan dakayi yayi sabida kasan iyaye sai ahankali amma yakamata muje naganta ko
Kai haba bana da ranan komawa amma idan naga zanje sai muje tare
To godia nake ango Allah yasamu adanshimku
Papa yakai masa duka akafad'a yace kai dai baqaramun dan iska bane, sai anan yaji yasamu relief a ransa
Gida ya dawo yayi kwanciyarsa bai sake fita ba sai Washegari ya fice office
********
Fauziyyah kuwa kwana biyu tanawa mama bore kan itafa atafam bata son Alamin
Mama tace toh kinsan Allah idanma amakaranta ake zugaki zugar qawaye yaukam bari Abbanki yadawo insanar masa kuma daga yau kinqare makarantar
Sanin halin Abba sarai yasa taita roqon mama tayi haquri bazata sakeba
Amma azuciyarta har yanzun bata yarda akwai abinda zai hanata auren yasirba
Shiyasa tayima mama likimo kafin tasamu mafita, takuma gagara sanarma yasir halin da ake ciki dan batason hankalinsa ya tashi
*3 weeks later*
Awannan week din ranar saturday papa da TJ suka shirya suka taho dambam
Inda Daddy ya kira Abba yasanar masa zuwan papa
Girki mai kyau yasa mama suka shirya, bayan sallan laasar Fauziyyah da qawarta yar qanwar mama mai suna khairy suka fasa wanka suka shirya suna zaman jiran isowar su papa
Mama kuwa ganin Fauziyyah tasake har da kwalliya yasa taji dadi sosai
Fauziyyah kuma tayi hakane sabida akwai wata manufa aranta
4:30pm
Su papa suka iso, tinda yayi parking sai wani ciccin magani yake, fiskannan kamar an aiko masa da saqon mutuwa
TJ ya dubesa haba mutumina kasake fiskan mana, irin wannan bonewa haka
Yamutsa fiska yayi yace banason rainine kawai shiyasa
Sai da suka shigo suka gaida mama sannan suka fice
Mama tace khairy ki masu iso falon Abba, to ta amsa taja mayafinta ta fice
Cikin natsuwa ta fito ajikin mota tasamesu
Sallama ta masu cikin sanyin murya
TJ ne ya amsa yana tasbihi fa Allah, azuciyarsa yace lalle Ameen baida wayo wannan yarinya haka mai kyau yace baiso atinaninsa Fauziyyah ce
Bismillah kushigo ciki tana fadin haka ta wuce
Sai da TJ yaja hannunsa sannan suka bita abaya har falon Abba...
βπ»Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] βͺ+234 703 448 8635β¬: πΎπΎπΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎπΎ
πΎπΎπΎ
Budurwar Qauye π€·πΌββπ€·πΌββπ€·πΌββ
Written by Faty Mmn Faty
July, 2017
1β£0β£
Yana fitowa mota ya shige rai bace, nan ya kuma tarar da wani abin haushin
TJ yagani ya ritsa dambun nama yana ci hankali kwance
Har papa ya shigo yana qoqarin yima mota key bai ko kalleshiba sai ma kada kansa dayake alamun naman yamasa dad'i
Wata doguwar tsuka yaja, yace Allahu ya kawo maka sauqi
Sai anan TJ ya dago yace da akayi mefa?
Nan papa yasake quluwa yace bansaniba
TJ ya ajiye bowl din hannunsa, sai daya kora lacasera tukun ya dubi abokinsa yace uhum inajinka meyafaru sarki fushi
Papa bai kulashi ba sai ma tada motar da yayi, sai daya hau hanya tukun ya dubi TJ
Yace kaikam zuwa dakai waje jama kai rainine, imba neman rainiba harda wani zagewa kana zuba surutu kamar wani parrot
Hakanma bai makaba sai ka karbi abin hannunta, naman taraina mu kawai haba
TJ yace kagama
Eh ya fada afusace
TJ yace kasan Allah, gara ka natsu ka amshi zabin Daddy hannu biyu dan wlh yarinyannan tayi ta ko ina
Kanaganin yarinya yar shila ga kyau ga natsuwa
Oh, haka kagani kai ai dik yadda mace take birgeka take shiyasa amma meye abin birgewa awajen *Budurwar Qauye*
TJ yace kasan Allah, ni ko aure na tashi, bazan auri wacce ta rufa 20, swt 16 zan samo na aure
Kuma idanma kanaga taima qanqantane kabata shekara 1, tasamu kiwo malam
Haushi yasa baima kulashi ba har suka iso fada bai kuma cewa uffanba
**********
Bayan sati biyu, yanzun Fauziyyah, bata samun matsala wajen yin waya da yasir
Tinda ta nuna wayar daya bata amatsayin papa ne ya bata, dik tym daya kira zata daga amatsayin papa ne
Yauma kamar kullum yasir ya kirata awaya tana dakin mama, tsam ta miqe ta nufi dakinta
Assalamu alaikum ta amsa wayar
Waalaikumussalam beauty na
Murmushi tayi, tace naam habiby
Dftn beauty ta yini lfy?
Lfy lau, habiby ma dafatan ya yini lfy
Nikam ba lfy ba ya amsa mata
Subhanallah, mene yasameka? Baka da lfy ne? Ta jera masa tambayr arude
Lfy na lau sai dai zuciyata tana cikin wasiwasi, nakasa samun natsuwa my fauzy ina tsoron rasaki
Haba habiby ya kake irin wannan tunanin, insha Allah bana da miji sai kai
Kullum haka kike fadamun, amma koda gidanku, baki taba barina nazoba ko sau1
Marairaice murya tayi, tace wlh dokar Abba ne shiyasa amma na amince ranan da nagama rubuta jarabawa ta ka turo magabatanka wajen Abba, sunemi izinin nema da kuma aurena
Alhamdulillah, abinda nakeso naji daga wajen ki kenanan, wlh har nasami natsuwa, I luv u so much
Jin yadda nan take farin ciki ya lillibesa sai jikinta ya mutu, asanyaye tace I luv u too habiby
Barin fita masallaci, sai zuwa jimawa dan kiraki, bye my queen sai kinji ni
Tace bye habiby
Tanasauqe wayar wasu hawaye masu zafi suka zubo mata , addu'a take Allah yasa burinsu ta cika Abba ya amince kodan ganin girman idon mutane
Kwanciya tayi tana tuno, papa lalle indai kyau ne babu hadi da yasir, haka Komai ya fi yasir
Kuma inda dan kyaune to tabbas papa zata dauka, sai dai bata son papa koda da kwayar zarra ne
Afili tace inaa barin iya auren mutumin da baisona, maganan arziqi bai taba hadani dashi ba, Allah ka kawo mun sauqi cikin rayuwata
Sai data sha kukanta ta more sannan tayi shiru
*******
Afannin Daddy kuwa ginin gidan papa yasa agaba, inda ya dauko hayar companyn *Buildsmart*, yabasu contract na gini da dik wani abin cikin gidan, tindaga kayan daki, kitchen da Komai
Sannan ya kira Abba awaya ya sanar masa baya buqatar yasayi Komai dan yai order na Komai
Abba yayi godia sosai, Daddy yace haba ai Fauziyyah yarsace koda wani zata aura shizaiyi Komai
Momcy da aunty mabarukha Daddy ya basu isassun kudi suka tafi dubai hado lefe
Yanzu biki saura wata biyu ina ko wanni fanni suka fara shirye2
Ango da amarya kam ko ajikinsu musamman papa da mantawa yake da batun auren
Halinsa kuwa sai abinda yayi gaba dan ba abinda ya sauya
Momcy dai fatanta Allah ya shiryeshi kada wata rana ya shawu ya lakad'i yar mutane
2weeks later
Su aunty niima ne da wasu yan uwan momcy da Daddy suka kai kayan sa rana, nanma kaya bana wasa ba aka kai
Dik abinda ake Fauziyyah ko da wasa bata taba fadawa yasir batun auren da ake shirin yamata ba
Papa kuwa tun wannan lokacin da yaje dambam sukayi fada da Fauziyyah bai kuma zuwa ba
Ya fake da aiki ysmasa yawa, Daddy ya kirashi yace yakamata yabar dik aikin dayake yaje yasami Fauziyyah su tattauna maganar biki
Ya amsa da toh, amma ba har zuciyarsa ba, dan baida niyyar zuwa
Fauziyyah kuma yanzu batada zama sabida exams da suka fara
Cikin ikon Allah har sun gama lfy
Aranan yasir ya nufi gombe cikin dokin Washegari zasu taho da su dad dinsa domin tambaya masa auren Fauziyyah
Tun last 2 weeks yazo gombe yasanarma dad ya kuma amince masa
Tunda yasir ya tafi gombe Fauziyyah hankalinta atashe yake dan batasan yadda abin zai qareba
Ranan kwana tayi batayi bacciba sabida damuwa
Washegari haka ta tashi sukuku kamar marar lfy har mama ta tambayeta ko bata da lfy ne, tace aa lfyrta qalau
Bata gama shiga damuwaba saida yasir ya kirata yace sun taso
Wajen 12pm aka turo ana sallama da Abba, anyi saa kuwa yana gida
Yana fitowa yaga manyan mutane tareda matashin saurayi kuma bai wayesuba
Iso ya musu zuwa falonsa, nan yasa aka kawo musu ruwa da dan abin motsa baki
Suka gaisa cikin sakin fiska, Abba yace gashi ban wayekuba kuma
Alhaji sadi baffan yasir yace lalle baka wayemuba mu baqine wannan ya nuna dad