Showing 57001 words to 60000 words out of 86122 words

Chapter 20 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

04 Jan 2025

8860

yace Alhamdulillah dabaki fada masaba amma kisaurareni kiji abinda zanfada maki


Dafarko nahadaki aure da dan uwanki baason rankiba wadda zan iyacewa dole namaki


Toh yanzun lokaci yayi daya kamata ace kina da aure tunda dik abinda ake nema na rayuwar duniya kinsamu daidai gwargwado


Toh wannan karon bazance ga miji na zaba mikiba amma amatsayina na mahaifinki zanbaki shawara idan har ta miki


Batun maganar Alamin ason raina shine ki amince ki koma dakinki


Cikim sauri ta dago kanta tana kallon Abba


Abba yace bafa nace lallai bane aa shawarace kiduba kiga yanda iyayensa suka daukeki tamkar su suka haifeki


Sannan dik yadda suke tayaki kin Alamin kisani bayadda suka iyane tunda kema kin nuna bakyaso amma suna son dansu kuma sunason farin cikinsa


Kuma nima har zuciyata inasonki da alamin sabida haka kije kiyi tunani da kyau akan maganata


Kuma tunda mutum ya maka laifi ya kuna nemi gafara aisaika yafemasa


Fauziyyah dai nan take tafara hawaye


Abba yace aa nifa banace tilas bane inhar kinfison wancan din shikenan amma ni shawara nake baki kuma kije kiyi tunani mai zurfi


Tsabar kuka gagara magana tayi har Abba ya miqe yace zaitafi shikam


Dakyar ta iya cemasa Allah ya kiyaye hanya


Ranan kasa runtsawa tayi lalle maganar Abba gaskiyane kodan su daddy yakamata ta amince da ya Alamin saidai kuma bata sonsa


Wata zuciyar tace shima Brr. Aiba wani sonsa kikeba


Tunani kawai take taya zata koma zaman aure da ya Alamin tayi kuka har idanunta ya kumbura


Kwana biyu da zuwan Abba abubuwa sun dameta gashi Brr koya kirata awaya bata dauka dan batasan mezata cemasa ba


Shikuma yadauka bata huce bane tun abinda ya faru


Kwanan Abba hudu da zuwa tayanke shawaran amincewa da Alamin amma badan tana sonsa ba saidan farin cikin Abba dan tafahimci yanasonta da Alamin ya boyene sabida kawaici


Haka su daddy ma tasan kawaici kawai suke mata


Ranan tayi kukan rabuwa da Brr hartaji ba dadi


Waya ta kira Abba ta sanar masa ta amince ta zabi ya Alamin


Abba ya ringa samata albarka da mata adduoi sannan yace toh tasanar ma daddynsu shiba ruwansa kada daddy yace shiya tursasata




Suna zaune afalo da daddare tasamu momcy tace tafasa auren Brr. Ita ya alamin zata aura


Momcy tace aa fauziyyah kada kitauyema kanki haqqifa


Tace aa ta amince har zuciyarta


Tashi momcy tayi taje tasamu daddy da maganar


Yace ta kira masa fauziyyah tana fita papa ya shigo bada jimawba suka dawo tare


Bayan ta gaida daddy daddy yace yanzu mom dinku tazomun da wata magana inasonjinta daga bakin


Qasa tayi da kanta sannan tace haa daddy me tayyarki shaadi ya Alamin(hakane daddy na amince da auren ya Alamin)


Wani lamarine mai sanyi papa yaji yana shigarsa tindaga qafarsa kamar anjiqashi da ruwan qanqara


Idanu kawai ya zubawa fauziyyah yanajin wani sabon sonta har cikin ransa....




✍🏻Faty Mmn Faty






🌾🌾🌾🌾🌾?🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾






Budurwar QauyeπŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017




*Wannan shafin nakune kudanku masoya Budurwar Qauye, Mmn Faty tana godia kuma tana qaunarku adik inda kuke,wadanda banisamun damar mayar masu da reply na messages nasu suyi haquri banmanta dasu ba abinne dayawa amma nagode sosai Allahu ya bar qauna 😍😘*




5⃣5⃣
Wani farin cikine ya ziyarci daddy jin abinda fauziyyah tafada da bakinta


Murmushi yayi mai cike da annushuwa yace zonan yar gidan daddy matso kusa dani


Babu musu ta tashi tamatso kusa da qafafunsa ta zauna ta sunkuyar da kanta


Cikin murya mai taushi daddy yace daugther na kifadamun gaskiya dakanki kika amince zaki auri Alamin ko kuma Abbane ya tursasaki


Girgiza kanta tayi cikin natsuwa tace aa bashibane ba baima da masaniya akan hakan


Alhamdulillah Allahu ya hada kanku ya kuma kauda fitina
ALLAH ya maki albarka ya baki yara masu biyayya kamar yadda kika mana


Momcy tace amin ya Allah dan itama wani farin ciki takeji marar misaltuwa tana kuma jin son fauziyyah har ranta


Daddy yace tashi kije abinki Allah ya maki albarka


Asanyaye tace amin sannan ta miqe ta fice dakinta tana shiga tafada kan gado ta bude sabon shafin kuka


Daddy kuwa tana fita ya maida hankalinsa kan papa wadda shikuma yabada full attention nasa akan hanyar waje inda ta fice ya bita da kallo ya kuma gagara dauke idanunsa


Daddy yace toh nadawo kanka yafada yana kallonsa


Jin muryar daddy yasa ya juyo yana kallon daddy


Kasaurareni da kyau kaji abinda zanfada maka


Nafarko kagodewa Allah da mahaifin fauziyyah mutumin kirkine sannan itakuma yarinyace mai biyayya


Toh kagama bin kafa har kasamu burinka ya cika


Amma kasani bazan lamunci kwatankwacin abinda ya faru abaya ba


Matuqar kanason zama inuwa daya da ita saika sake halayenka tass


Cikin ladabi papa yace insha Allahu zankiyaye daddy


Daddy yace Allah yasa sannan tunda burinka ya cika saika tattara kakoma gidanka gobe dan bazaka zauna karinga takura mata ba


Ko ajikinsa yace shikenan daddy Allah ya kaimu


Daga haka ya musu saida safe ya fice zuciyarsa fari qal qal


Yana fitowa ya nufi dakin fauziyyah cikin saa kuwa qofar abude take


Falon shiru sai qaran AC gami da wani sansanyan qamshi wucewa yayi har cikin bedroom nata


Da sallama ya shiga kwance ya hangota tayi rubda ciki akan bed kuma bata amsashiba


Wani kasalane yaji ya sauqo masa ta dalilin abubuwa uku


Nafarko sanyi da qamshin daya doki hancinsa na biyu tsaftan dake tattare da dakin kamar kada ya fita haka yakeji
Na uku yanayin kwanciyar da tayi saiyaji kamar ya qarsa ya kwanta ajikinta dan saiyaji dik hankalinsa ya tashi


Gashi dama wata yaloluwar doguwar rigace ajikinta dazataje wajen daddyne ta daura hijab akai tana shigowa kuwa ta cire
Dik tabi jikinta ta manne sannan ta bayyana illahirin suran jikinta


Wani yawu ya hadiya yana godema Allah daya sanya fauziyyah zata zama mallakinsa


Itakuma tanajin motsin bude qofa da sautin muryarsa taji wani baqin ciki yasake kamata


Banza tayi dashi kamar batasan da shigowarsa ba


Ahankali ya tako har bakin gadon leqa fuskanta yayi nan yagane idanunta biyu kuma kuka mq takeyi dan ganan hawaye shabeshabe akan fiskanta


Nan take yaji ya damu gashi baisan dalilin kukan nata ba


Cikin murya mai tattare da natsuwa da kulawa ya kira sunanta My Fauzy


Wani dam taji zuciyarta ta buga sakamakon tuno mata da yasir da yayi dan shine kadai ke kiranta da wannan


Anatse yasake kiranta My Fauzy sunotoo(kinajina)


Nanma banza tayi dashi kamar da dutse yake magana


Zama yayi agefenta ya riqo hannunta dake gefensa ya sake qasa da murya cikin sanyi yace My Fauzy pls jababdo(ki amsamun)


Bata kulasaba sai yunqurin kwatan hannunta daya riqe takeyi


Saqe riqe hannunta yayi gagam ganin baya da niyyar sakinta saita rabu dashi kawai


Tambayarkifa nake why ar u crying n baki amsaniba yafada atausashe
Ganin batada niyyar yimasa magana yasa ya cigaba da fadin


Koma meke daminki pls kiyi haquri kibar kuka banson kanki yayi ciwo ko idanunki yayi ja


Nazo namaki godia ne akan amincewa da kiyayi zaki aureni
Inkuma qara baki haquri akan abinda namaki abaya


My fauzy inaroqonki kibani dama na nuna maki irin sonda nake maki
Nayi nadamar abinda na aikatamaki abaya
U don't know how much i regret everything that i have done to u


I luv u my fauzy i luv u with all my hrt


Magana yake yana murza dan yatsun hannunta masu laushi da taushi kamar na jarirai


Maimakon taji sanyi aranta sai tasakejin wani zafi aranta nan tasake fashewa da wani sabon kuka mai sauti ahankali


Nam yayita lallami da maganganu masu dadi amma abanza harya fahimci maganarsane batasonji akan dole ya miqe ya fita yanajin kukanta har cikin zuciyarsa


Adaren ya kira TJ ya shafa masa halin da ake ciki


TJ yayi murna sosai ya kuma sake bashi shawara mai kyau akan kada gaba ya kuma gangancin kwatanta abinda ya faru abaya


*******
Washegari daddy ya tafi dambam nan suka zartar da maganar biki sai nan da watanni biyar masu zuwa
Kafinnan angama ginin sabon gidan da zaa kai fauziyyah


Yan uwa kowa yayi murna da samun labarin komawar fauziyyah musamman saida aunty mabarukha tazo bh takuma dauki nauyin gyaran amarya idan lokaci yayi


Haka maman fauziyyah da farko taqi yadda saida Abba yamata nasiha sannan ta amince takuma sanya Albarka


Da aka sanarda papa lokacin auren sai cewa yayi shifa lokacin yamasa tsayi gaskiya


Momcy harta qulu tace tosaika rage tunda ka isa da hakan


Cikin sati daya magana tagama kankama har daddy yabada contract na ginin gidan sabon gidan papa amma wanna karon a kusa dasu nan *Gida Dubu*


Wani filin daddy dake kusa da gidan Aunty naja dambam sukayi shawaran gina masa


Momcy tace gara kusa da auntynsa tunda koba komai yafi shiri da ita kuma zatana leqasu akaiakai taga inda yayi ba daidaiba tasashi ahanya


Dan abinda ya faru abayama harda rashin wani babba akusa wanda yake leqasu


Daddy ya amince da shawarin momcy


Daddy ganin har sati guda papa baida niyar komawa gidansa yasa ya kirasa yace ayau dinnan yayi parking inba so yake ya saba masa ba


Babu musu ya hada kayansa ya loda a mota sai abinda baa rasaba ya bari saidaga baya zaizo ya dauka nan ya




nufi gidansa dake sokoto road wadda rabonsa da gidan tun rabuwarsa da j
uhaina....




*Wai ina labarin juhaina kam[truncated by WhatsApp]




🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾






Budurwar QauyeπŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017




*This page goes to Aunty Faty G Dambam, Nagode da qaunar da kike nunama littafina, Insha Allah 2019 Bauchi sai Proffessor, Mmn Faty Luvs u 😍😘*
5⃣6⃣
Hankali kwance yake driving har ya qaraso


Amma yana isowa gate sai yaji ransa ya baci cos nan take kwakwalwarsa tafara recalling masa abinsa yafaru lokacin rayuwar da yayi da ex wife nasa juhaina


Horn yafara mai gadi ya bude masa gate dan yasan da zuwan ogan nasa cos ya kirasa awaya kan cewar agyara gidan before ya yazo


Qarasa shiga yayi har parking space yayi parking motarsa


Qarema gidan kallo yake saiyaga ya canza masa kodan ya jima rabonsa da gidanne oho


Koda kudin buqatar maigadi da sauransu saidai suyi waya yazo ya karba


Wani iska mai zafi ya furzar kafin ya bude qofar motan yana tattara wayoyinsa


Yana fitowa daidai da isowar maigadi kenan


Sannu da zuwa yallabai ya fada yana risinawa


Cikin kulawa yace yawwa ya gidan dai hope babu wata damuwa


Aa babu konai yallabai ankuma gyara ko ina kamar yadda ka umarta sai dai daki daya wadda yake akullene da baa gyara ba sabida acikin keys da suke wajena babu nasa aciki


Ok babu damuwa i think key din yana wajena barin qarasa ciki zan fito saika shigar mun da kayana idan kuma Abdu ya iso shikenan


Toh yallabai afito lfy


Wucewa yayi ciki inda yabar maigadi da mamakin canzawar ogan nasu


Tun bayauba ya lura da sauyin idan yaje wajensa but nayau dabanne lura da yadda ya bada time nasa sukayi magana ta fahimta


Falo ya bude ko ina tsaf sai qamshin room freshner da sanyin AC


Ba komai acikin falon sai carpet dake tsakiyar falon


Wucewa yayi falonsa nanma komai agyare yadda yake ba kuma abinda aka taba


Kallon dakin juhaina yayi kamar ya wuce amma sai ya qarasa ya bude nanma bakomai ciki da sauri ya jawo qofar ya rife hadida rintse idanu sabida tuno da abinda ya faru da yayi


Cikin sanyin jiki ya wuce dakinsa key yasa ya bude qofar


Qurakam baa magana ko ina yayi qura kallon dakin yake sosai fridge ya bude nanma da sauri ya kulle ganin kwalaben wine iri da ban daban


Ga wasu kwalabe a zube aqasa ga kuma kwalayen sigari da dai sauran kayan shaye shayensa


Lokaci guda yaji kyaman dakin ya kamasa fitowa yayi ya shiga kiran layin Abdu bada jimawaba ya daga hello oga sir am sorry pls na kusa isowa


Ok am ka tsaya ahanya kasamomin kwalaye manya mana ammafa empty


Ok badamuwa ya fada


Bada jimawaba ya qaraso da manyan kwalaye kamar yadda aka sashi


Karba yayi ya shiga loda tarkacen aciki saida ya kwashe su tas sannan ya manne su tass ya kira Abdu yace yayi waje dasu ya loda su a boot


Falo ya dawo ya zauna ya jira Abdu ya gyara masa dakin nan ko ina ya tsaftatu kamar bashiba


Kayansa suka shigo masa dasu daganan ya wuce toilet ya watsa ruwa hadi da alwala


Agurguje ya shirya ya nufi masallaci


Sai da yayi ishai sannan ya dawo


Yabawa Abdu kudi ya samo masu abinci


Bayan yayi dinner ya jawo system nasa ya kunna ya duba wasu abubuwa sai dai ya gagara samun natsuwa


Jingina yayi da jikin kujera ya lumshe idanunsa ya tuno fiskar luv of his lyf


Jiyake inama yana da no wayarta daya kira yaji muryarta ko zaisami sukuni


Gashi ya na zaune shiru shikadansa dik kadaici ya damesa


Wayarsa ya jawo ya kira TJ


Amma baidaukaba harta katse sake kira yayi akaro na biyu sannan ya dauka


Hello man how far


Papa yace cool ya khairy n mubeen


All ar fine ya amarya


Wani murmushi yayi mai natsuwa kafin yace tana gida amma dai lfyrta lau


Kaikuma kana ina kenan at this tym


Ina sokoto road daxu nayi parking wlh daddy ya matsamun wai sai dai na qaura




Hhh Tj ya sheqe da dariya yace aikam daddy ya birgeni dan wlh nasan takurin fauziyyah zakanayi


Tsaki ya danyi yace aikaiba nasan iya abinda zakace kenan tokoma mene ne dai nikasamun no wayarta now now


TJ yace toh nikuma a ina zansamomaka kuma yanzu adaren nan


Tsuke fuska yayi kamar yana kallonsa yace banason iskancifa kawai inajira tinda komai saika maida shi wasa


Toh naji naji barin karba awajen madam saina turo maka shikenan


Eh shikenan thanks


Nyt saika ganito


Ok nyt yafada yana sauqe wayar amma bai ajiyeba jira kawai yake yaga message ya shigo


Aiko bada jimawaba saiga message cikin sauri ya bude ya dauko dayar wayarsa ya shigarda no din


Dialling no yafara saidai yaji user busy


Sake kira yayi nanma yaji user busy


Nanfa ransa ya fara baci todawa take waya awannan daren haka


Itakuwa fauziyyah Brr nabil ne ya kirata awaya harda kukansa akan maiyasa ta yaudaresa tasan ba aurensa datayiba gidan mijinta data koma


Daddy ya kirasa ya masa bayani akan yayi haquri shinefa ya shiga cikin damuwa zuciyarsa take ganin yaudaransa kawai fauziyyah take shiyasa bata daukar wayarsa


Dik iya bayani da rantsuwa data masa yaqi ya yarda sabida kishi ya rife masa idanu kawai gani yake dagangan tamasa haka


Shinefa suka dauki time suna magana har ya kira yaji busy


Ya kira yafi sau ashirin cikin saa yaji wayar ta shiga


Harta kusa katsewa sannan yaji ta dauka cikin sanyin murya tace pls ka amince dani wlh wannan auren sabida iyayena zanyi badan so ko wani abuba nifa kaine araina kuma kaina keso bayadda na iyane kawai na amince da auren ya Alamin


Itakuma tadauka Brr ne ya sake kiranta dake da wata no ya kirata shiyasa dataga no ne yanzuma saikawai tadauka shine tafara magana


Wani daci yaji maqoqoronsa ya masa jin yadda take jadda da bata sonsa kuma mawani take fadama haka


Lallai akwai aiki agabansa dole ya danne zuciyarsa haryasamu gurbi acikin zuciyarta


Jin yayi shiru yasa tace pls talk to me mana ka amince da maganata muyi rabuwar mutunci bakadaukeni mayaudariya ba


Cikin sanyin murya papa yace My Fauzy Alamin ne


Abazata taji maganar hakan yasa tayi shiru ta gagara magana


Sharewa yayi yace My Fauzy kina jina


Nanma shiru ba responde

Yace nasan kinajina meyasa bakiyi bacciba har yanzun while dasafe zaki fita aiki


Dama na kirane naji muryanki mai dadi mai sanyani natsuwa kuma gashi kinqi kimin magana amma da kika picking call nawa i appreciate it so ki kwanta kiyi bacci but do not forget kiyi addua kafin ki kwanta


Allah ya tashemu lfy kiyi bacci mai dadi n swt dreamz


Dik yadda yake maganar cikin wani salo mai matuqar dadin sauraro


Hakan yasa tabar dai wayar akunnenta tanajinsa bata kuma kasheba


Yana fadin haka ya zame wayar akunnensa ya kashe yana tunanin ta yadda zai samo hanyar dazai shawo kan fauziyyah dan tabbas yasan akwai ga garumin aiki agabansa


Itakuma jin ya katse wayar ta sauqe daga kunnenta hadi da jan tsakin dabatasan miye dalilin yinsa ba


Message ta rubutawa Brr ta tura masa sannan ta blocking layukansa kafin ta kwanta amma batayi bacciba tana tunanin abubuwa da dama


********
*Waikam ina juhaina ta bace ne???*


Tunda tasamu ya amince mata akan tashiga tacanza kaya amma kada ya sameta agidansa


Suna fita itama taja jikinta cikin wahala taje tahada abubuwanta masu amfani ta canza kaya kafin ta fito


Motatta ta shiga ta fito tana waigen inda zataga munnir sai tahangoshi kwance aqasa baya ko motsi agefen wani lungu bakowa kasancewar yanayi. Layinnasu da bayawan mutane


Fitowa tayi ta koma cikin gidan ta shiga dakinsa ta dauko jakar kayansa ta dawo da kyar tasamu tasaka masa kaya sannan ta koma ta ringa roqon mai gadi har ya amince yazo yasaka matashi a mota ta nufi asibiti dashi


Wani private hospital ta kaishi amma sukaki karbansa saida ta zube masu kudi masu yawa sannan suka amince suka dubashi


Nan itama ta kwana sai washegari ya farfado


Tana samun ya farfado tace dashi toh yanzu alaqansu ya qare tinda yamata sanadin aure kuma ta kawo shi asibitine dan bayida mai taimakonsa sabida haka ita yau zata tafi gida kada ya kuma tunanin yasanta arayuwa idan yaji sauqi yaje yadauki motarsa acan sannan idan yana buqata ya kwashe kayan dakinta yasayar ya san inda dare yamasa kada ya kuma nemanta


Tana fadin haka ta fice ta barshi yana kukan danasani ga jinya ga karaya ga babu haqora guda biyu




Itakuwa tasha taje tasamu fasinjan daya iya mota yajasu zuwa kaduna




Gida ta nufa tana shiga ta ringa kurma ihu dik su mom dinta suka rude gashi duk jikinta shatin duka ya faffashe


Dakyar tafada masu ai papane ya saketa yamata dan banzan duka


Mom dinta tace tabbas saitayi qaransa dan bai isa ya dakar mata ya abanzaba


Dad ne yace aa anemi iyayensa dai aji kanmagana


Nan juhaina tace ai agaban iyayensa yamata haka da saninsu


Mom tace kajiko saina daureshi dan ubansa ta inda take shiga batanan take fitaba


Dad yace indai hakane baiga amfanin wata sharia ba kawai abarsu da Allah su suka sani


Da kyar ya shawo kan mom ta amince inda juhaina taji dadin hakan dan kada asirinta ya tonu.....




✍🏻Faty Mmn Faty






🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾






Budurwar QauyeπŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


September, 2017




5⃣7⃣
The following morning after ya tashi yayi subh prayer baikoma bacciba


Wajen seven ya shiga bathroom ya taking bath


Shirinsa yayi tsaf cikin wata sky blue half jumfer wadda tasha dinkin zirii


Kansa ba hula sai suman nan tayi lufluf which means tasha gyara sosai


Agogon gucci ya daura as usual then

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login