Showing 30001 words to 33000 words out of 86122 words

Chapter 11 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt

04 Jan 2025

8877

ba sai dayasa qafarsa ya fincike sai yaga jini ajiki.....






โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
[3:51PM, 8/19/2017] โ€ช+234 803 341 6395โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017






3โƒฃ1โƒฃ
Bashi ya tashiba sai wajen 12


wanka yayi ya shirya cikin wasu qananun kaya masu kyau da tsada ash colour sun matuqar karbarsa




gashin kansa ma kawai abin kallo ne,ya dakko glass nasa ya manna a idanunsa


wasu takalma masu tsadar gaske yasaka aqafarsa,sannan yazo wajen car keys nasa ya tunanin wacce zai fita da ita




key na mercides ya dauka,har yakai qofa ya juyo,wata drawer ya bude ya dauko kudi wadda shima baisan adadinsuba yasa aljihunsa




sannan ya dau wayoyinsa yayi hanyar fita




cikin isah da taqama yake tafiya


๏ผˆniko mmn faty nace ko sarautar ce yau ta motsa๏ผ‰


ahankali ya sauko matakalar benen kamar wadda baiso haka yake tafiya




tsayawa yayi ganin ta akwance afalo tana bacci,tawani duqunqune kamar mai tsoron kar wani abu ya kamata


wata,doguwar tsaki yaja kansa daya ya wuce kitchen




nan ya bude fridge, ya kuma bude freezer,sannan ya wuce store, nanma ya duba komai sannan ya dawo falo


tsayawa yayi akanta,hannunsa yasaka ya jawo yatsar kafanta ya murde hadi da danna mata wata uwar tsawa keh tashi nace




afirgice ta miqe sabida tsawar da ya daka mata,ga zogi da taji ajikin yatsar kafanta




tashi zaune tayi sai jikinta dake rawa dan tsoron batasan mai zai mata ba




cikin daurewar fuska yace keh dan uwarki nan wajen baccine ,kinwani zo kin kwanta ma mutane akan hanya




cikin girgiza kanta tace aa


yace toh kada ki kuma zuwa ki zauna anan baran ki kwanta, idan kuma kinqi ya karkada mata yatsun hannunsa biyu


murya na rawa tace barin sakeba, yace kima sake saikinyi nadamar ranan da aka haifeki




sannan yace kinajina,bai saurari mai zata ceba yace daga yau kada ki kuma dafa abinci da kowa agidannan kiyi naki kekadai




tace toh,sai kuma tayi shiru dama tanason tafada masa akwai abubuwan da babu a kitcthen amma tana tsoro




gashi yanzun ma bataga fiska ba




bai kuma saurarontaba yayi waje abinsa,wajen motocinsa ya nufa ko wacce an wanke sai kyalli take dan dokarsace kullum sai an wankesu duka inya fito ya zabi wacce dai fita da ita




cikin girmamawa dik sukazo suka gaidashi,amma haka dik ya amsa masu adaqile




motarsa ya shiga,mai gadi ya bude masa gate ya fice,direct EATRY ya nufa yayi breakfast


daganan wajen hutawa ya wuce,qarqashin wasu bishiyoyi masu sanyi ya zauna akan daya daga cikin kujerun dake wajen




wayarsa ya ciro ya shiga contact, dialling wata no naga yafara


leqowa nayi dan naga waye yake kira,akan screen din naga MY JUHAINA




wayar tajima tana ringing sannan aka dauka cikin wata murya mai jan hankali akace hello




sai daya wani lumshe idanu ya bude sannan yace hello yan mata




cikin yanga tace barka da rana DR




wani murmushi mai tsada yayi sannan yace au kingane mai magana




ayangance tace haba dai aiko bana da no naka ,voice naka bazai bacemunba


cikin jin dadi yace thanks dana samu wannan matsayi




tace ai kawuce haka ,dftn kasauqa gida lfy




yace lfy lau n u, tace same




yace thats gud so ya mutanen gida


tace wlh all ar fine




yace am glad to hear that,dama nace barin kira queen naji ta sauqa lfy n idan badamuwa zan ringa kira time to time muna gaisawa




cikin jin dadin kalamansa tace badamuwa ur always wlcm




yace ok, nagode barin barki haka later




tace its my pleassure


nan sukayi sallama kowa zuciyarsa cikin jin dadi




WACE CE JUHAINA


Asalin sunanta JUHAINA MUKHTAR, mahaifinta shine deputy governor na kaduna state amma wannan zaben da akayi sun sauqa dan suncinye tenure nasu, asau biyu suna cin zabe


su hudu ne awajen iyayensu, amma ita kadaice mace awajen iyayenta, tana da yayu maza biyu sai ita sannan autansu wadda shima namijine


suntaso cikin gata da kula musamman juhaina wacce ita kadaice mace,bayan ta qare secondary school nata shine ta tafi singapore tayi degree nata acan yanzun tagama tadawo gida inda anan suka hadu da Dr Alamin




juhaina wayayyar mace ce ajin qarshe,ga kwalliya da iya gayu,sannan yar duniya ce dan tsabar gata yamata yawa harta sangarce yahadu da zaman waje




dan ita atsarinta ma batun aure yanzun, amma ganin Dr Alamin yasa lokaci guda taji kwadayin aurensa dan yadace da mijin datake burin aure idan ta tashi




wannan kenan....




Ranan haka fauziyyah ta yini cikin ciwo ga yunwa dan ta gagara cin abincin sam, sai black tea data dan hada tadan sha




washe gari da safe tadan tashi da dan sauqi,sakkowa tayi ta nufi kitchen sai ta tuna ashefa yace kada tasake girki da wani




tunanin mezataci ta fara dan wata masifaffiyar yunwace ke damunta,gashi daga shinkafa sai taliya da macaroni ,indomie ma baifi guda hudu ba ya rage




bandasu ba komai sai mangyada dasu maggi




indomie tadauko guda biyu ta dafa bako albasa dan bata dashi




da kyar tadanci kadan dan bai mata dadi ba




tana cikin wanke plate din taji muryar papa yanacewa keh keh ,cikin sauri ta dauraye hannunta tayi waje dan tasan da ita yake




tana fitowa ta tsaya agefe tace gani




yace au kinajina dama ashe inata kiranki dan iskanci bazaki amsa ba




wata katuwar leda mai kamar jaka tagani ahannunsa, dangwala mata yayi agabanta yace oya kafin naje nayi wanka na fito ki tabbatar kin wanke jakar nan sannan kin mun folish na takalmana,idan kuma har na fito baki gama ba hmmm sorrynki




bai sauraretaba ya wuce,zazzage takalman tayi tun tana qirgawa harta daina dan yawansu




haka taje ta wanke jakar ta dawo tafara goge takalman,ga ba dadi takejiba ga yunwa ga aiki sai zufa takeyi ahaka har ta kammala tsaf






yana fitowa yasamu tana shiryasu acikin jakan dan kamar leda take tana kadeta ta bushe




cikin shirin fita ya sauqo ashe tsabar walaqanci bama sakawa zaiba kawai yabata wahala yasa yayi hakan




tace gashi nagama,yace toh sai yaya kidauka kikaimun qofar falona ki ajiye yana fadin haka ya fice abinsa






Cikin sati biyu fauziyyah wahala da damuwa ga bata iya cin abinci kota girka hakan yasa ta rame ta lalace




papa kuwa izuwa yanzu soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsa da juhaina,yini suke suna waya da charting




dayake sai next week zai resuming office,kuma aqsrshen sati yaima juhaina alqawatin zuwa kd dan yaganta.....






โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
[3:52PM, 8/19/2017] โ€ช+234 803 341 6395โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017






3โƒฃ2โƒฃ
Ranar Friday yaje gida ya yima su momcy sallama akan zashi kd




Momcy tace son mezakaje yi a kd kuma?


Yace daurin auren abokinsa zashi


Nan suka masa fatan alkairi da sauqa lfy




Washegari early morning ya wuce,Inda ko takan fauziyyah baibiba




Kafin azahar yajima da shiga kd, sai daya huta a hotel din daya sauqa


Bayan asr prayer yasake kwalliya ya caka ado sannan ya nufi unguwar su juhaina


Da waya maqale akunnensa tana masa kwantance har ya isoh


Gidane qato na gani na fada, dagani masu gidan suna cikin daula


Horn yayi maigadi ya bude masa kamar yadda tace ansan da zuwansa


Yana shiga yayi parking sannan ya kira wayarta


Bada jimawaba ya hango ta tafito cikin shiga ta alfarma


Wata doguwar rigace ajikinta, dark purple, ya matuqar yimata kyau,saman rigar ya kamata qirjinnan ya fito afili,gyalen kayan ta yane kanta dashi


Tana isowa ya bude mota ya fito, tana isowa da murmushi afiskanta tace wlcm my king


Shima murmushin yayi yace aha my queen


Muqarasa tace dashi


Wani qaton falo wadda aka qawatashi da kayan ado na zamani ta kaishi




Nan ta cikashi da kayan chi dana sha,spring rolls yadauka yana ci


Guda biyu yaci sannan yasha juice yace Alhamdulillah


Dubansa tayi cikin shagwaba tace haba my king bakafa ciba


Yadda tai maganar ya burgeshi sosai haryasanya shi wani murmushi na musamman yace eyyer my gueen nafa qoshi ne cos banjin yunwa


Tace dik da haka sai ka qara


Yace do not worry my queen as u wish, but not now


Tace OK so ya hanya


Yace well um hanya normal fa




Tace wonderful haka akeso,yasu momcy, daddy n others


Yace all ar fine my darling, ya nasameku hop kowa lfy


Absolutely fine ,ta amsa masa


Yace masha Allah


Shiru suka danyi cikin soft voice nasa yakira sunanta juhaina


Naam my king ta amsa tana kallonsa


Yace nazo kd sabida ke,kuma nibanazo dawasa ba dagaske nake aurenki zanyi ammafa idan kin amince


Cikin murya mai Jan hankali tace na amince my king


Yace naji dadi ammafa akwai abinda banfada maki ba


Tace uhum go on am all ears


Yace inada mata


Daram taji gabanta ya Fadi Dan abazata taji maganar




Yaci gaba da fadin sai dainibani sonta auren hadi aka mana,kuma bazan hadaku gida 1ba


Gidanki daban zan maki ,kuma kece wacce nakeso kece zabina so kada tadameki Dan nima bata gabana




Sai anan taji hankalinta ya kwanta amma ta qudiri aniyar saita koreta kota halin qaqa




cikin kissa da kisisina tace kada kadamu aini kaina keso kuma dakai zan zauna bada itaba


cikin jin dadi ya dada tabbatar lalle juhaina tana sonsa sannan ita wayayyar mace ce ba irin haukan kishin nan akanta




Sunsha hira sosai da zai tafi yashiga suka gaisa da dad da mom din juhaina


Sai data rakoshi har bakin Mota sannan ya bata tsarabarta da yayi mata


Nan sukayi sallama akan washegari zai shigo su gaisa kafin ya wuce


Washegari kuwa kamar yadda yayi alqawari sai daya shigo kafin ya wuce


Haka suka rabu cikin shauqin so




*****
Watan papa 1 da dawowa daga Singapore amma kamar ya shekara awajen fauziyyah sabida uquban dayake gana mata




Yau yakama saturday tinsafe ta gagara cin komai, harwani zazzabi takeji Dan yunwa


Tana cikin wanan yanayin har bayan laasar,kamar daya sama taji shigowar mota


Jin ana nocking yasa taje ta bude,aiko wazata gani momcy da Dady


Cikin murna ta taresu, saida suka zauna momcy da tun shigowarsu take kallon fauziyyah


Tace daughter na bakida lfy ne


Cikin sanyin murya fauziyyah tace eh momcy banida lfy




daddy yace ayyah amma Alamin bai fada manaba,yaya jikinnaki


tace dasauqi




Wani dadi ne ya lullube momcy atunaninta ciki fauziyyah take dashi


Daddy ne yace Alamin bainan ne


Ahankali tace yana nan




Daddy yace jekice masa munzo ko


Miqewa tayi jik ba kwari ta haura dakinsa


Tsayawa tayi abakin falon tana tinanin Mezai mata idan tashigar masa daki




Shahada tayi ta murda handle din aiko cikin saa abude qofar take


Ahankali ta tura ta shiga,nan wani sanyi da qamshi suka welcoming nata


Qarema wajen kallo take yadda ya hadu iya haduwa tace lalle ya Alamin dan gayene tundatake bata taba shiga waje mai kyau da tsaruwa irin nanba




Ganin bainan yasa ta wuce cikin dakin, fitowarsa daga wanka kenan yaganta kamar dagasamma




Daure fuska yayi cikin masifa yace keh meya kawoki dakina




Adiririce tace su Daddy ne suka zo,shine sukace namaka magana




Toh naji wuce kifita banza qazama kafin kibatamun daki




Cikin Sauri tafice,sai data tsaya ta goge hawayenta sannan ta saqqo


Tazo daidai step na qarshe kawai sai su momcy sukaji Tim Abu ya Fadi


Aiko wazasu gani fauziyce tayanki jiki ta Fadi,cikin sauri suka nufota hankali tashe


Daidaida papa yake qoqarin saqqowa


Ganin su abirkice ga Kuma fauziyyah akwance a qasa, yasa shima ya saqqo da sauri.....




โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
[3:53PM, 8/19/2017] โ€ช+234 803 341 6395โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




3โƒฃ3โƒฃ
Fauziyyah, Fauziyyah shine abinda momcy take fada cikin tashin hankali


Daddy yace Alamin dagota mutafi hospital


Cikin sauri ya dagota ba bata lokaci suka tafi asibitin daddy


Direct emergency suka wuce da ita, daddy dakansa ya shiga dubata inda papa yarasa meke masa daddy Dan baisan amsan da zai bawa daddy ba idn yatambayesa


Momcy kuwa ta gagara zama sai sintiri takeyi awajen


Cikin mintuna 35
daddy ya fito amma fuskarsa a daure da alamu ransa abace take


Da sauri momcy ta nufoshi,daddy meyasa meta shine tambayar data fara masa


Sauqe ajiyar zuciya yayi yace muje office,papa da yarasa ta cewa shima ya biyo bayansu


Sai da momcy ta shiga ,papa yazo zai shiga cikin sauri daddy ya daga masa hannun da kakkausan murya yace tairo(dakata)


Afusace ya rufo qofar,momcy dake tsaye tace Ya jikin nata ?


Daddy yace relax momcy ,munshawo kan matsalar,yanzun numfashinta ya dawo normal, ansamata ruwa zaa maidata dakin hutawa


Momcy tace to meyasa meta haka wlh hankalina ya matuqar tashi


Daddy cikin takaici yace YUNWA


Yunwa? Wacce irin yunwa kuma


Yace to a iya bincikena Nagano lfyrta qalau sai yunwa da damuwa wadda sanadin haka ta yanki jiki tafadi




Momcy tace to batacin abincine kenan,daddy yace wayasani niban yarda da Alamin ba,yanzu kije driver ya kaiki gidan nasu kidauko mata kayanda zata saka idan ta tashi saiki bincikamun gidannasu akwai abinci ko kuwa


Momcy tace to bari naje nadawo amma kuwa matuqar Alamin yana da hannu aciwon yarinnan sai ya raina kansa, tana fadin haka tai waje




Tana fitowa papa ya biyo bayanta, yana mata magana ko kulasa bataiba ta wuce abinta


Direct dakin fauziyyah ta shiga ta dauko mata kaya acikin sannan ta duba kitchen din falonta,wayam ba komai,sakowa downstairs tayi ta shiga kitchen da store ,rai bace ta fito suka nufi asibiti


Office din daddy ta shiga nan ta labarta masa komai cikin takaici tace Alamin yaci amanar yarinyannan ,bakomai banda shinkafa da mai da maggi kuma INA zaton tun garan bikinsu nema




Daddy yayi shiru yace balaifi ya kyauta muje wajenta kada ta farka ba kowa


Dakinda aka kaita suka shiga,basufi minti goma ba tafarka ,tana bude idanunta sai kuma ta fashe da kuka




Momcy tamatso kusa da ita tana shafa kanta,cikin lallashi tace kiyi shiru daughter gani nan kusa dake ba abinda zai sameki


Asabe mai aikin momcy ce tashigo,da basket na abinci da flask ahannunta, ajiyewa tayi tana tambayar ya mai jikin


Momcy tace dasauqi ,kikoma gida saimun dawo kawai inaga nan zamu kwana


Tace toh Allah ya sauwaqa sannan ta tafi


Tea mai kauri momcy ta hada sannan tace daughter muje kiyi brush kiyi wanka saiki sha ko


Ba musu ta tashi,saida ta kaita har toilet sannan ta a fito ta barta


Tana fitowa ta bata kaya taje tacanza, bayan tacanza kayan tafito zama tayi a bakin gado tayi shiru


Daddy ya ce ya jikin,ahankali tace dasauqi


Miqo mata tea momcy tayi amma maimako takarba sai tafashe da kuka




Rarrashin duniya sunyi amma taqiyin shiru, cikin lallami daddy yace mekikeso daugther nah fadamun amma kibar kuka kinji


Cikin kuka tace nikam wajen Abba da Mama zanje


Daddy yace toh kiyi shiru zan kira maki Abba awaya amma fa sai kinyi shiru kuma kinsha tea kinci abinci kin yarda


Cikin sauri tace na yadda


Daddy yashafa kanta yace good girl


Momcy ta matso tafara bata tea aiko nan da nan tashanye tass dan yamata dad'i, rabon data sha mai dad'i haka ai harta manta


Plate momcy ta dauka ta zuba mata fried rice wadda tasha kayan lambu da papper chicken


Nan tahauci hannu baka hannu kwarya,daddy juyawa kawai yayi dan takaici ace kamar fauziyyah dan tasamu abinci takeci kamar almajira


Momcy ma haka shiru kawai tayi amma baqin ciki ne fal ranta


Tass tacinye ta kora juice mai sanyi, haba sai wani natsuwa yaxo mata,har wani lumshe idanu tayi tanajin wani natsuwa ajikinta




Daddy ne ya kira Abba awaya bayan sungaisa yace masa ga fauziyya zasuyi magana, Abba yace lfy dai ko


Daddy yace lfy ba lfy ba itance bata da lfy amma dasauqima shine take rigima wai sai dai akawota gida shine nakira taji muryarka ko hankalinta zai kwanta


Ok toh bani ita, tana karban wayar tace ina yini Abba


Lfy lau mama na ya jikin dai,


Tace dasauqi,yace to kuma sai rigima kice sai kinzo gida




Cikin shagwaba tace ai inason ganinku ne


Abba yace toh ai basai kinzoba gobe insha Allahu zamuzo mudubaki


Cikin jin dadi tace dagaske Abba


Yace insha Allah ga mama kugaisa


Nanma cikin murna suka gaisa da mama , mama tace harda khairy zamuxo dan tazomun hutu


Cikin doki tace Allah ya kawoku lfy


Mama tace amin sannan sukayi sallama


Daddy yayi murmushi yace rigima ta qare ko


Sunkuyar da kanta tayi sai taji kunya kuma


Daddy yace momcy inaga muwuce gida kawai tunda tasami sauqi


Momcy tace to bakomai nan tafara hada kayayyakin su


Daddy ne ya dubi fauziyyah cikin kulawa yace daugther na zaki bimu ko zaki koma gida


Dasauri tace aa zanbiku


Nan yadada tabbstarwa lalle abunda papa yayiwa yarinyan nan bakadanba ne tunda har take gudun gidansa




Driver ya kira yazo ya saka musu kayansu a mota sannan suka wuce gida




Ranan fauziyyah tayi kwanan natsuwa dan kafinta ta kwanta sai da momcy tasa aka dafa mata farfesun zabuwa wadda yaji kayan qamshi nn taci tayi nak dama fauziyyah badai son dadi ba๐Ÿ˜œ




Momcy ce ta shigo dakin daddy cikin shirin bacci nan tasameshi yayi shiru


Zama tayi agefensa ta dafashi tace daddy lfy kuwa kayi shiru tunanin me kake


Saida ya sauqe numfashi sannan yace tunanin wanne irin hukunci zanma Alamin nake tunda baida mutunci har yana neman kashe yar mutane saboda son zuciya


Momcy tace nima tunanin danake kenan amma kabarni dashi fauziyyah kuma baxata koma ba harsai ya gane kurensa


Daddy yace hakan zaayi amma ahankali kitambayeta medame ya ke mata


Momcy tace badamuwa bari ta warware




Washegari su Abba sukaxo murna awajen fauziyya ba magana


Tare sukazo da khairy


Nan suka shiga dakinta inda momcy da su mama suna falon daddy




*****
Papa kuwa ganin sunqi sauraronsa gashi baifito da wayaba da yakira TJ yazo ya maidashi gida


Drivern daddy yasa ya maidashi gida


Washegari bayan yayi wanka yafara tunanin yaje ne ko kar yaje




Sai yace gara yaje kada yasake laifi amma bari ya kira TJ yazo suje


TJ ya kira awaya yace yaxo rakashi wani wajemana


Tj yace badamuwa in d next 30mins yana zuwa


Bada jimawaba sai gashi agidan papa yayi parking motarsa suka shigata ta papa suka fice


Suna tafe ahanya amma papa hankalinsa yana can tunanin ko momcy data saurareshi




Tj ne ya katse masa tunani yana cewa man kadakkoni rakiya bakafadamun inda zamujeba sannan kayi shiru baka ko magana lfy kam


Baibashi amsa ba saima yaga sun dau hanyar asibitin daddy




TJ yace man kamun bayani mana kuma gashi mundau hanyar asibiti




Papa yace kaidai bari wlh waccar yarinyan ce batada lfy kawai shikenan su momcy suka fara fushi dani suna nuna kamar nina saka mata rashin lfyr


TJ yace wai wace badai fauziyyah ba




Papa yace ita mana ni wlh yarinyannan tazamamun liability




TJ yace i know u very well friend anya kuwa ba wani abu kamata ba


Cikin fushi yace toh mezan mata nikuma


Tj yace Allah yasa dagaskene kake kuma indai da hannunka nima ba ruwana


Daidai da shigowarsu cikin asibiti nan ya hango wata nurse kiranta yayi ya tambayeta tace ai tunjiya suka tafi gida




Shiru yayi TJ yace ai saimuje gidan to


Nan suka wuce gida, Falon daddy suka fara shiga nan suka samu su Abba


Cikin girmamawa papa yagaida Abba da mama


Sannan ya gaida daddy da momcy haka dai suka amsa ba yabo ba fallasa sabida gabansu Abba nema yasa suka amsa


Wucewa cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login