Showing 78001 words to 81000 words out of 86122 words
Chapter 27 - BUDURWAR QAUYE Complete-by miss Deejarh-.txt
zakiji dadin zama acan shikenan zanyi qoqarin danne zuciyata
Ahankali ta rungumesa ajikinta tana cewa dabadan daddyne yace inkomaba niba inda zani
Nasani babyna nasani kinajin tausayina fatana Allah ya baki lfy
Amin ta amsa tana narkewa ajikinsa har bacci yasake daukanta
Bayan ta tashi ya mata wanka ya shiryata sannan yakai kayanta mota yadawo ya riqeta suka fita
*****
Kwance take akan makeken gadonta na gidan momcy
Papa yana zaune agefenta hannunsa cikin nata yariqe gagam
Momcy ce ta shigo tana cewa oh papa dagazangar ka tambayeta mezataci adafa mata shikenan sai najika shiru
Dago kansa yayi yace momcy tun dazun lallaminta nakeyi taqi tace wai bazataci komaiba
Momcy tace aa aikuwa ciwo da yunwa ai saisu nakasa mutum
Sassauta murya tayi tace daugther na fadamun me zakici kinji
Nifa momcy banason komai
Cikin lallami tace haba daugther kifada dai amaki ko kadannce kici aiyafi hakan ko
Toh zanci wainar fulawa amma kada asaka kwai kuma na manja da yaji mai tafarnuwa nakeso
Momcy tace to shikenan barinje yanzun zaa maki ko kefa
Papa ya dubi momcy yace yace mene ne kuma wainar fulawa
Momcy ta dubesa tace oh ahakan kake cewa zaka iya jinyarta baicin dan abubuwanda takeso bakama sansuba baran dafasu shiyada take zaune da yunwa tana fadin haka ta fice
Bada jimawa sosaiba momcy ta kawo mata aifa nan ta tashi tafaraci babu laifi taci mai dan dama kuma bataji tashin zuciya ba
Yaune gobene papa shiru yaqi ya fito ya tafi yana zaune wai sai tayi bacci ya tafi
Har wajen 11 sannan ya fito lokacin tayi bacci, afalo ya tarar dasu daddy ko ajikinsa ya masu saida safe ya wuce abinsa
Dikkansu bayansa sukabi da kallo
Momcy tace oh lalle papa baya da kunya sam shikam
Daddy yayi murmushi yace aikam abinnasa sai kallo yadda yakeji da Fauziyyah Allah ya bata lfy su koma gidansu
Momcy tace shine fata kawai
******
Washegari sassafe kafin ya tafi office saida yazo ya ganta hakannan daya dawo anan ya yada zango sai pass 10 sannan ya tafi
Haka kullum dasafe zaizo da yamma ma zaizo kuma ba kunya abinsa haka zai namiqe mata sai dai wadda yake dakin ya fita ya barsu danshi ko ajikinsa
Satinta biyu tafara sun sauqi domin dama hadda yunwa suka hadu mata
Yanzun kuma dik da dai batacin abinci amma kayan kwalama kam tanaci kuma momcy na kula da ita sosai
Kullum papa yazo qorafi yake mata yafa gaji wlh yanzunkam tunda taji sauqi zasu tafi
Itadai batace masa komaiba amma batason tafiya dan tanajin dadin zaman gidan momcy
Haka dai addaddafe yabarta tayi wata 1
Ranan kuwa yasamu daddy yace zasu tafi tunda taji sauqi
Momcy tace sam bai isaba yabarta tawarware sosai yadda komai zata iyaci amma banda yadauketa akoma gidan jiya to bazai yiyuba
Daddy ma yace nikam lfyrka kuwa toh ba inda zataje inhar dik zuwan da kake kagama rashin kunyarka bamai kulaka bai ishekaba saina hanaka zuwama gaba daya
Nan suka masa fatafata ya tashi rai bace yayi dakinta
Yana shiga ya dannama qofar key
Tana kwance akan bed tadago tana masa murmushi
Fiskansa ahade ya qaraso ya zauna abakin gadon
Tashi zaune tayi tace my one n only yadai naga kamar ranka abace
Dan gajeren tsaki yayi yace wlh nagaji haqurina ya qarefa yanzunkam
Matsowa tayi jikinsa ta kwantar da kanta abayansa tace da akayime hooney
Sauqe murya yayi dan yadda ta rungumesa ta baya saiyaji kasala ya sauqo masa yace haba baby kinsanfa ina haquri da rashinki amma sam su daddy basa ganewa wlh a buqace nake daurewa kawai nake sabida bakyada lfy but now Alhamdulillah kinsami lfy daidai gwargwado amma sunqi subarmin matata haba why yaqarashe maganar kamar zaiyi kuka
Wani tausayinsa ne yakamata tasake qanqamesa da murya mai kwantar da zuciya tace nasani kana haquri amma ka qara akan wanda kakeda komin daren dadewa zsmu koma gidanmu ai
so kada ka tada hankalinka
Bazaki ganeba kema yafada
Tace niko nagane toya kakeso nace
Yace shikenan amma dai tunda kinji sauqi sai kibani haqqina ko
Zaro idanu tayi tamatsa baya kadan tace wlh kafaye wasa dayawa
Hawowa yayi ya kwanto jikinta yace au wasa kikace wlh am serious
Tace tab so kake azo asamemu ince me kenan
Kai baby babu wanda zaishigo na kulle qofarfa kai toma saime idan ansamemun zina mukayi ko haramne nida matata ta haka zasu gane abinda suka kasa ganewa su barmin matata
Tace tab tobadaniba gaskiya tafada ashagwabe
Kansa ya dan dora akan cikinta yace kinji little babyna yana fadama daddynsa wai yayi missing nasa shima
Tace ah lalle kam toyani banjiba
Yace aidani yake magana ba dakeba so yaukam zan gaisa da little babyna naji lfyrsa
Batayi auneba tajisa yawani rungumeta yana wani shafata
Zip din rigarta ya zuge yana qoqarin balle mata bra ta riqe hannunsa da sauri tace haba ya Alamin meye haka bafa agida mukeba
So what idan ba agida mukeba pls sakemun hannuna kiga yafada yana zame hannunsa daga nata
Ganin dagaske yakeyifa yasa ta turesa ta matsa gefe tace gaskiya kayi haquri wlh nikam kunya nakeji bazan iyaba
Ransa ne yaji ya baci cikin bacin rai
Yace oh kema kinabin bayansu kenan ko bakya tausayina ko good ya maki kyau dan kinga ina binki yadda kikeso shiyasa zaki walaqantani ko
Rai bace ya miqe zaune yana hada bottons nasa daya cire
Ganin yadda ransa ya baci lokaci guda fiskansa ta koma fiskan shanu sai taji kamar bata kyautamasa ba lokaci guda zuciyarta ta karye amma batajin zata iya biyesa suyi wannan rashin kunyan kam gara ta basa haquri ta lallamesa yafi kawai
Sauqa yayi daga kan gadon zai fice cikin sauri tace tafiya zakayi kuma kamar zatayi kuka
Afusace ya juyo yace ina ruwanki toh dani
Dan Allah....
Hannu ya daga mata yace nabarki kiyi yadda kikeso kuma indai nine bazan kuma zuwa neman wani abuba inkuma haka tafaru call me what u want yafada cikin masifa sannan ya fice afusace
Shiru tayi tana tunanin rabon dataga fushinsa haka harta manta amma tasan zai huce inyazo saita basa haquri
Papa kuwa baibi takan kowaba ya fice, gida ya wuce ransa amatuqar bace amma zaiyi maganinta ya fada aransa
Washegari tunsafe har dare ba papa ba labarinsa
Tun abin bai damunta harya fara damunta
Haka aka kwana aka sake yini baizoba bai kuma kirata awayaba itakuma ta kira wayarsa amma busy take gani batasan yayi diverting line nata ba
Wasa wasa har tsawon sati guda bata kuma ganin saba hakan ya tabbatar mata lalle yayi fushi bana wasaba bakuma yadda zatayi
Damuwa sosai ta shiga gashi cikin ikon Allah tasamu sauqi sosai
Ahaka har akayi sati biyu nankanfa bata iya boye damuwarta dan dan abincin data fara cima yanzun gagaranta yake
Afannin papa kuwa da kyar ya daure zuciyarsa yake haqurin rashin jin da ganin babynsa
Yayi hakane dan yasata adamuwa ko hakan zaisa su momcy su maido masa da matarsa amma fushin dayake da ita ya jima da hucewa
Matsanancin kewanta ke daminsa, gidan yamasa fadi shikadai haka yake rayuwa cikin kadaici har abin tausayi ya koma .......
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
7โฃ2โฃ
Momcy ta dubi daddy tace daddy inagafa abinda yafi da yamma zan maida fauziyyah gidanta
Meyasa kikayi wannan tunanin kodan fushin da Alamin yayi?
Aa kokadan badanshibane, ita kanta Fauziyyah yanzun tashiga damuwar rashinsa akusa da ita
Ina lura da ita tacanza kwana biyunnan kuma dik bai wuce rashin mijinta bane
Hatta abincin bata iyaci koda kadan din datakeci, tunda tayi sauqi inaga kawai ta tattara ta koma Allah ya bata lfy kawai
Daddy yace shikenan ba damuwa Allah ya kaimu yamman, amma wazai namata dan ayyukan gida kuma?
Momcy tace wannan bamai damuwa bane nayi magana da talatu akwai qanwarta wadda aurenta ya mutu to dama tamin magana akan idan ansamu aiki ataimaka wa qanwar tata
Toh shine nace taje ta taho da ita sai su tafi tare take mata ayyukan ko me kagani
Daddy yayi murmushi yace momyn yara kenan ashe dik kin tsara komai abinki
Toh hakan yayi bamatsalan komai nan suka cigaba da hiransu
Sai bayan azahar tasaka talatu ta hada kayan fauziyyah lokacin sundawo
Bayan laasar takira papa ta tambayesa yana gidane
Yace eh yana gida tace shikenan sai anjima ta kashe wayarta
Papa kuwa dayaga wayan momcy yadauka zatace yazo yadauki matarsa amma sai take wani tambayarsa wai yana gida ne nan haushi yasake kamasa ya kuma rasa tudun dafawa
*****
Momcy datagama wayar dama tana dakin fauziyyah ne tace toh tashi kisa mayafinki mutafi
Fauziyyah tace ina kuma momcy
Momcy tace gidanki mana kafin mijinki yakawo mana sammaci kuma da alama kina bayansa tun wuri gara namaidaki
Wani dadi fauziyyah taji amma sai ta sunne kanta qasa ganin yadda momcy ke kallonta sai kunya ta kamata
Momcy tace ganan hannatu qanwar talatuce tare zamu tafi zata ke maki ayyukan gida
Itadai fauziyyah qala bataceba sai hijab nata ta dauko tasaka tabi bayan momcy dan ita tafice
Afalo ta samesu sai tace momcy barinje nayima daddy sallama
Momcy tace aiko ya fita tun dazu, dawowa tayi suka fice
Suna isowa mai gadi ya bude musu gate suka wuce
Atare suka nufi cikin gidan inda hannatu ke jaye da jakar kayan fauziyyah
Yana kwance afalo da system agabansa yana wani aiki saiyaji qarar door bell
Waye kuma ya tambayi kansa lokaci guda ya miqe yayi hanyar qofa
Aifa yana yaye cuttain din yagansu kasancewar glass ne awajen
Cikin sauri ya bude qofar yana kurema babynsa kallo
Momcy tace toh bamu hanya mana mu wuce ko
Dan sosa qeyarsa yayi dan kunyace taka masa dai yawance da runguman momcy yana cewa oyoyo momcy, nan take yaji baqin cikinsa yaye
Momcy tace harka hucene daga fishin dakake damu, haba nina isa nayi fushi daku kawai ayyukane sukamin yawa
Yayi agogo sarkin aiki tafada tana dan turesa gefe
Falo suka zauna bayan sun gaisa tasake musu bayanin hannatu sannan tace zata tafi
Har mota papa ya rakata sannan ya dawo
Amma saiya dawo fiska abace, duban fauziyyah yayi inda yabarta anan take zaune yace madam kinuna mata room nata daga haka ya wuce yana janye dakayanta zuwa dakinta
Wani room dake qasa mai kyau wadda komai na amfani akwai ta kaita tace to ganan dakinki kihuta zan dawo idan nayi wanka
Toh Hajiya tafada cikin girmamawa dan gabadaya ruwan kanta ya qare tinda tashigo gidan take maimaitawa aranta Aljannar duniya
Dakinta tafito ta wuce, papa dake labe yana jiran yaji tahowarta ya fice danya dan wanata sai yaji motsin tahowarta
Bude qofar yayi ya fito baiko kalletaba zai wuce da sauri tariqo hannunta hakan yasanyashi tsayawa amma bai juyoba bai kuma cewa komaiba
Dawowa jikinsa tayi ta rungumesa sosai tafara magana da raunanniyar murya
Haba my one n only fushi kake dani har yanzun kenan, koma menamaka ban cancanci wannan punishment dinba tafada muryarta na rawa
Baby yafa wuce yafada anatse
Tace aa kam yanayinka ya nuna haryanzun baka haquraba
Shikenana naji pls don't cry y wuce yafada yana qoqarin zameta ajikinsa ya wuce
Aifa saita fashe da kuka tana cewa abakine kacemun ya wuce amma azuciyarka baka haquraba tunda gashi wucewa zakayi ko ya jikina baka tambayaba
Ganin dagaske kuka takeyi yasa ya rungumeta tsam ajikinsa yana cewa am really sorry babyna am sorry ki yarda dani bana fushi dake kiyi shiru
Bana qaurace maki dan wani abubane sai dan ina da dalili kuma gashi yanzun andawo mun dake
Nan tafihimci abinda yake nufi itama
Baby kinsan irin wahalan rashinki danake fama kuwa wlh na azabtu sosai bana fatan abinda zai kuma nesantani dake har qarshen rayuwata
Sai anan taji sanyi aranta tasake narkewa ajikinsa
Sunkuyawa yayi dai2 cikinsa yana kissing dinsa yana cewa am sorry my little baby
Daddy yayi laifiko baije ya dubaka bako sowwie ba laifin daddy bane laifin su garrany momcy ne
Dagowa idanunsa yayi yana kallon idanunta yace kinji my little babyma ya fahimci dadynsa so yakamata mom dinsa ma ta fahimta ko yana daga mata giransa daya
Dariya ya bata saita rungume kansa ajikin cikinta tana cewa i miss u my luv i miss u so much
Dagowa yayi yace missing u more n more my princess
Cidak ya daga har bed room nata ya dire ta akan bed
Yafara qoqarin gaisawa da little babynsa cikin shagwaba tace haba baby baxaka bari sai anjimaba
I can't shine abinda yafada murya ashaqe
Ganin haka simisimi na fice nabarsu.....
โ๐ปFaty Mmn Faty
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ๐พ
๐พ๐พ๐พ
Budurwar Qauye๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ๐คท๐ผโโ
Written by Faty Mmn Faty
September, 2017
7โฃ3โฃ
Har akayi sallan magrib suna daki dan atare sukayi sallah ma
Sai alokacin Fauziyyah tace ya salam tana dafe goshinta
Papa yace lfy baby yana riqota
Tace sam bakaine kasa namanta da hannatu ba
Waye kuma hannatu? Ya tambayeta dan sam yama manta dawata agidan
Mai aikin da momcy tabamu mana tafada tana kallonsa
Afalo kika bartane ? Aa nakaita dakinta amma nace mata zandawo
To miye aciki tunda tana dakinta kika wani tada hankalinki
Da shagwababbiyar murya tace bafa nata da hankalina bane ko ruwa ban bata bafa gashin har dare yayi baran abinci
Haba babyna kada kidamu aidai tasan kina tare da mijinkine ko yanzun muje ki kai mata juice da akwai nama a kitchen wanda nasa aka sayomun banciba inyaso saina fita na samo mana abinci
Toh shikenan muje tafada tana tashi daga jikinsa
Riqeta ya kumayi yace me babyna zataci
Shiru tadanyi tace umm QUNDUN Bauchi Club zanci da graves
Dadi yaji sosai jin tafadi abinda zataci ba gardama
Amma kuma tabasa dariya yadda tace wai qundu, dan qaramin bakinta yaja yace oh baby kwadayi kenan
Bata rai tayi tace nikam bana kwadayi kuma tunda kace haka nama fasa barin ciba
Cikin sauri yace am so sorry bafa dake nakeba nida little babynanefa
Cikin sangarta tace aidai nadauka dani kake
Yace waneni nace maki mai kwadayi muje yanzun nakawo maki ko shalelena
Atare suka fito kitchen ya riqo mata abinda zata kawoma hannatu har bakin qofarta sannan ya miqa mata tare da manna mata kiss a forehead nata ya fice
Washe gari da kyar ya fita office sai wani nan nan yake da ita har bata gajiya da kallon yadda yake mata hidima
Bayan yafita ma ajima kadan ya kirata awaya yana tambayar ya suke ita da little babynsa
Ita kuwa tai ta zuba masa shagwaba tana narke masa
Adaddafe yakai 4pm a hospital sannan ya nufo gida
Ita kuwa tana bararraje afalon qasa hannatu ta mata danmalele ta baza mata a plate, yasha manja da yaji ga kuma robar yajin agefenta
Tafaraci kenan ya dawo
Hannatu tana gaishesa ta wuce dakinta
Shikuma zama yayi agefenta aqasan carpet yana cewa babyna nayi missing naki sosai
Ita murmushi tayi tace me too only, munyi kewarka muma
Tana maganar tana kaiwa loma abakinta
Kallon abinda takeci yakeyi da kyau sannan ya dubeta baby mene ne wannan
Itakuwa tsabar dadi har wani lumshe idanu takeyi tace danmalele zakacine
Kai baby a ina kika koyi cin wadannan abubuwan amma dai dafatan bazaima little babyna illah badaiko
Bata fiska tayi tace nifa wato yamun komaima badamuwarka baneba saita babynka kake ko
No bahaka bane baby ke ai babbace amma babynmu baiyi kwaribafa kike wannan ciye ciye
Tace to nidai inzakacine muci inka qoshi kuma shikenan
Tafada tana qara gumbuda yaji
Kutt baby irin wannan cin yajin haka fa yafada yana daukar roban yajin
Marairaice murya tayi tace pls kabani yajina inbakason yajin barin saka maka agabankaba
Yace nikam barinciba kici dadi lfy amma dai yajin nan ya isheki haka nan
Tace nikam kaban kayana tunda baci zakayiba
Yace ko baxan ciba bazan bakiba
Ganin dagaske yakeyi yasa tace toh naji dan qaramun kadan tai maganar tana langabe kai
Yadda tai maganar yabasa dariya yace shikenan debi kadan to tana diba ya rufe yamayar kitchen
Baby barinje na watsa ruwa kafin kigama ko
Toh afito lfy tafada tana cigaba da cin kayanta
Girgiza kansa yayi kawai yana murmushi yadda tabada hankalinta wajen cin wannan abin
*****
Haka rayuwa yaci gaba tafiya masu cikin kwanciyar hankali da natsuwa
Dan yanzun fauziyyah ta murmure sosai daga laulayin datake ba abinda ke daminta
Sai dai kwadayi kam kamar kullum qara mata akeyi
Hannatu kuwa mutumiyar kirki bata gajiya da yimata wannan da wancan
Hankalin papa ya kwanta tunda tasamu lfy batada matsala yanzun
Rainon cikinsu sukeyi cikin tattali da kulawa
Sannu ahankali cikinta yake girma har yakai yanzu watanni shida
Ya fito yayi mata das dan gaskiya cikin ya qarbeta sosai yaqara mata kyau idan tayi kwalliya sai cikin ya fito yamata gwadas ajikinta
Wani sontane kullum ya ke qaruwa acikin zuciyar papa yadda kullum itama take tattalinsa ta take bashi kulawa dikda cikin dake jikinta bai hanata ta bashi haqqinsa yadda yakamata
Yanzun har girki tana masa hakan yasa hankalinsa ya kwanta sosai yayi wani haske harda wata yar qiba yayi wadda tamasa kyau sosai
Kullum adduar su momcy dasu Abba bai wuce Allah ya sauqeta lfy ba
*****
Yaukuma da shagwaba ta tashi
Kwance tasamesa a bedroom nasa yana nade acikin wani milk blanket mai laushin gaske
Doguwar rigace ajikinta ta atampa mai laushi
Tamata kyau sosai sai qamshi takeyi
Bakin bed din tazauna tana kallon kyakykyawan fiskansa mai matuqar annuri
Wani kyau taga ya sake mata dikda baccinsa yakesha peacefully
Sannu ahankaki takai dan yatsanta kan bakinsa tana shafawa ahankali
Dan motsi kadan yayi alamun yanajin ana tabasa
Jikin kunnensa takai dan qaramin yatsanta tana sosawa
Bude idanunsa yayi ahankali yana kallonta da alamu bai gaji da baccinba
Cikin muryar bacci yace yadai akayi babyna
Ashagwabe tace nidai katashi hakannan
Pls baby kibarni sai anjima kadan ko kema kizo muyi baccin atare
Nidai nidai banjin bacci Allah kuma kaima katashi
Oh baby pls fa nace
, tace umum fa nace tana janye bargon nasa
Toh naji zantashi amma saikin bani .....yaqarashe maganar ahankali
Cikin sauri ta waro idanunta tace aa wasa nake maka yi kwanciyarka
Bude idanunsa yayi yace ai tunda kikasani natashi saifa kinbani
Miqewa tazoyi yayi saurin riqe hannunta ya daura hannunsa akan cikinta yanajin yadda yake motsi
Baby kinji little babyna yanason gaisawa da daddynsa, nima kuma inasonjin ya babyna ya kwana
Kwantawa tayi ajikinsa da murya mai sanyin shagwaba tace ba jiyama kaji lfyrsaba nidai bayanzunba
Aa baby jiya ai good night namasa yanzun kuma zan masa good morning yafada yana shafan cikin nata
Narkewa takumayi ajikinsa tana cewa nidai katashi kayi wanka kayi break
Aa baby wani break kuma bayan kinzo kin tayarmun da hankali jifa yadda kike qara kashemun jiki da salon shagwabarki, kuma kemafa kinaso kina kaiwa kasuwa jibi yadda jikinki yayi...
Bai qarasaba takai hannunta tana dukan qirjinsa cikin wasa nidai kasakeni intashi
Aifa nafada ba inda zakije baiqarasaba tace wash cikina tana riqe cikin
Ai baisan ya akayiba yagansa azaune cikin rudewa yake cewa mai yasameki baby mene ne
Cikina kadagani zaune tafada kamar zatayi kuka
Ok ok yafada yana miqar da ita zaune
Kafin ya zame blanket din jikinsa ta tashi da sauri