Showing 21001 words to 24000 words out of 86229 words
Chapter 8 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
kowa ba ,yasa yayi hanzarin d'aukan mukullan motar shi ,ba tare da ya ga yawa kowa inda zashi ba. Cikin mintunan da basu gaza sha biyar zuwa ashirin ba Hajj Jamil yakai gidan Daddy ,a bakin gate yayi parking motar shi ,Dan ba yada kuzarin dahar ze iya shiga da mota ,da sauri yayi parking motar ya shiga gidan. Masu gadi se gaida shi suke amma ina ,shi ko jin su ma bayayi ,hankalin shi ya wurin yaje yaga halin da aminin shi ya shiga. Sauri yake yi hadda d'an had'a wa da gudu ,a haka har ya k'arasa sashen Daddy
Be tsaya wata wata ba kawai ya bud'e k'ofar tare da sa kai cikin parloun ,da sallama d'auke a bakin shi. Waige waige ya shiga yi yana baza ido ,yaga ta inda ze hango mutum amma be hango kowa ba. Sallama ya sake yi ta yadda idan ma akwai mutum yasan ze iya jiyo shi amma shiru. Ganin ba alamar kowa yasa ya nufi bedroom d'in. Se da ya fara knocking tukunna ,Nan ma shiru.
Tunani ya fara yi ,to ina Daddy ze shiga ,bayan ya gaya masa yana gida ba yada lafiya ,k'ofar fita ya nufa ,da niyyar yaje ya tambayi koda d'aya daga cikin masu aikin gidan. Har yakai bakin k'ofa ,se kuma wata zuciyar tace masa 'kai koma dai ka duba ciki ,Daddy na nan ba inda ze je' ,fasa fita yayi ,maida k'ofar yayi ya rufe ,sannan ya nufi bedroom d'in, wannan karon yana zuwa bud'e wa yayi tare da shiga ciki.
Taku d'aya yayi ,be kai na biyu ba ,ya hango Daddy tsube a tsakar d'aki warwass. Ba shiri ya k'araso da gudu a lokaci d'aya yana furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
"MISBAHU!!! MISBAHU!!!" Hajj Jamil ya shiga girgiza shi yana kiran sunan shi ,cike da tashin hankali da fargaba. Juyo shin da zeyi ,se yaga ko numfashi baya yi ,se wasu siririn hawayen dake saukowa daga gefen idon shi na hagu...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/25, 2:43 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA GOMA SHA TARA_
*_________________________*
_Gaba d'aya hankalin Hajj Jamil idan yayi dubu ya tashi. Tunanin meze yi meze yi ya fara yi ,tunowa da yayi yana da numbern babangida me gadi ,yasa yayi saurin Ciro wayar shi ,ya kira shi ,bugu d'aya ya d'auka tare da gaishe shi "Ka same ni yanzu a sashen daddy ,kayi sauri ina jiran ka". Shine kawai abunda Hajj Jamil ya iya cewa tare da yanke kiran. Cikin mintuna da basu gaza biyar zuwa goma ba se ga babangida ya shigo ,ganin ba kowa a parloun kuma k'ofar bedroom d'in a bud'e yake yasa ya shiga kai tsaye ,Dan yasan koma menene to ba lafiya ba._
_Ganin daddy da babangida yayi a kwance a k'asa kamar matacce yasa shima hankalin shi ya tashi ,kafin yace komai ,Hajj Jamil yace " yanzu ba lokacin magana bane ,kama shi mu saka shi a mota",,,, da taimakon babangida aka saka Daddy a mota, Ba b'ata lokaci Hajj Jamil yaja motar ,be yi tunanin kai Daddy babban asitin garin sakkwato ba ,Dan yasan daddy sanannen mutum ne, a take abun ze baza duniya ,Dan haka se ya yanke shawaran kiran wani abokin su dake aiki a asibitin UDUTH ,ya sheda masa abunda ke faruwa ,ya kuma fad'a masa dalilin sa na rashin son kai daddy babban asibiti. Kasancewar manyan likitocin nan se ka same su da asibitin kan su a waje ,wato private hospital, nan Dr Zaidu yawa hajj Jamil kwatancen asibitin shi, tun basu gama wayar ba Hajj Jamil ya karyar dakan motar shi zuwa asibitin da Dr Zaidu ya kwatanta masa._
_Dr Zaidu k'wararren likita ne daya samu yabo da k'warewa akan aikin shi. Hajj Jamil na isa ba b'ata lokaci Dr yasa aka shiga dashi ciki._
_Tambayar Hajj Jamil Dr. Zaidu yake yi akan me ya samu daddy? Hajj Jamil yace "wallahi Dr. Bansani ba ,nidai nasan yana fama da zazzab'i, to kuma yau muna tare ,bayan ya koma gida ne na samu labarin ciwon ya masa tsanani ,kafin in kaima shine na taradda shi a haka yadda kagan shi"._
_"OK to ,zanyi iya bakin k'ok'ari na insha Allah!"_
Shine kawai abun da Dr.Zaidu ya samu damar fad'a, kafin ya nufi d'akin da aka kai daddy ,Wanda yake zagaye da kayan aiki.
Dr.Zaidu yayi iya bakin k'ok'arin shi ,Dan kusan wuni yayi zungur akan Daddy ,kafin Allah ya bashi damar gano kan matsalar ,bashi ya fito ba se wuraren Bayan magirb.
Bayan ya kammala aikin shi ,ya umurci wasu daga cikin nurses din shi dasu kai Daddy d'akin Hutu.
Hajj Jamil na zaune a wajen ,ya had'a cikin hannun shi da fuska ,aka fito da daddy ,Wanda har a lokacin akwak oxygen (wato na'urar k'ara numfashi) sanye a hancin shi. Ciwon wuni d'aya duk Daddy yabi ya k'are ,Hajj Jamil ya furta a k'asan ran shi. Da ido yabi gadon har aka wuce daddy ,be San lokacin da wasu hawayen tausayin Daddy ya fara gangaro mishi ba. Ganin Dr Zaidu na zuwa ,yasa yayi saurin goge hawayen shi ,kafin ya k'araso yayi saurin mik'e wa ,tare da bashi hannu ,se a lokacin suka samu damar gaisawa.
Dr Zaidu yace "muje office d'ina akwai bayanin Dane ke so in maka".
Kai kawai Hajj Jamil ya gyad'a ba tare da ya amsa ba ,sannan yabi bayan Dr.
Bayan Dr ya zauna ,ya umurci Hajj Jamil akan shima ya zauna. Shidai gaba d'aya jikin shi a sanyaye yake. Zama yayi tare da zuba wa Dr Zaidu jajayen idanuwan shi.
Dr zare gilashin dake manne a idon shi yayi ,sannan ya fara yiwa Hajj Jamil bayanin ciwon Daddy
" wato a gaskiya Hajj MISBAHU na cikin wani hali ,badan ma kayi saurin kawo shi asibiti ba ,Allah ya tsare da ba'asan me ze faru ba. A iya gwaje-gwajen Dana masa ,na gane cewa yana d'auke da ciwon kasawar zuciya wato (Heart failure) Wanda idan yayi wa mutum yawa yakan iya leading to Heart attack wato (bugawar zuciya) ,wannan ciwo ba k'aramin ciwo bane da k'alubale ga Wanda yake d'auke dashi ,musamman ga magidanci irin wannan. Ba komai be kawo wannan ciwon ba illa matsanancin damuwa da k'alubalen rayuwa Wanda mutum ya kasa maganin shi ,sannan iya abunda na gano ciwon ya dad'e yana cin shi ,alama ta nuna nuna kuma baya tsare shan magani. Hajj Jamil wannan ciwon ba ciwon da za'ayi wasa dashan magani bane ,wallahi idan aka bari ,kaga yadda aka kawo shi yau ,idan aka Bari ya sake fad'uwa da kanshi har so ukku ,to ina me tabbatar maka idan kowanne yana tashi to ana ukkun sedai wani bashi ba , 'ka'idar wannan ciwon kenan. Kar kuma kayi zaton magani kawai ze iya warkar dashi ,ko alama. Wannan ciwon na buk'atar mataimaka ,musamman ma na MISBAHU daya masa mugun kamu. Dole ne se an kiyaye wasu abubuwan. Duk wani abunda baya so ya zama wajibi a Nisan ta shi da ganin shi ,a kuma yi k'ok'ari wajen faranta masa ta hanyar abunda yake so ko yafi so ,kar a barshi ya kad'aita shi kad'ai a guri ,Dan zaman kad'aici ne ke janyo har mutum ya fara tunanin abunda bashi bane. Sannan stress ya masa yawa ,yana buk'atar ya samu Hutu sosai Dan dawo da kuzarin jikin shi. Kaga wa'yannan abubuwan Dana gaya maka a yanzu ,matuqar aka kuskure ayin Abu d'aya gaskiya labarin ze sha banban ,saboda da wannan kad'ai ne zamu iya shawo kan abun cikin sauqi ,karka manta yana da hawan jini, Wanda shima ya taimaka wajen janyo masa wannan ciwon ,jinin shi yahau kuma fiye da tunanin ka. To me kake tunanin rashin kulawa ga mutum me hawan jini da kasawar zuciya? A gaskiya rayuwar MISBAHU na kokuwa ne tsakanin rayuwa da mutuwa. Zan d'ora shi akan magani na biyu ,Wanda muna fatar Allah yasa a dace. Badan ma yana kokari wajen yak'i da zuciyar shi ba ,da abun yafi haka ,da alama abubuwan sun soma fin k'arfin shine shiyasa har ya ciwon ya damk'e shi sosai.
Yanzu an masa duk wani abunda ya kamata ,sannan akwai allurar bacci a cikin drip din da ake saka mishi ,idan ya k'are ze iya farkawa a koda yaushe ,amma yana buqatar isash-shen bacci ,saboda haka idan ma be farka akan lokaci ba kar kayi tunanin ko wata matsala ne ,a bash-shi yayi"...
Tunda Dr Zaidu ya fara bayani Hajj Jamil ya shiga cikin matsanancin tashin hankali da rud'ani "hawan jini da kasawar zuciyar? Kuma ze iya rasa ran sa akoda yaushe?" Shine abunda hajj Jamil keta maimaitawa a k'asan ran shi. Godia sosai yawa Dr Zaidu ,sannan ya tashi ya fice jiki ba k'wari.
D'akin hutun da aka kai Daddy nan ya nufa kai tsaye. Kujeran dake gefen gadon ya samu ya zauna, tare da tsurawa daddy idanu, baccin da yake yi da yanayin yadda yake fitar da numfashi dak'yar kai da ka gani kasan na wahala ne. Nan danan hawaye suka fara bin kuncin Hajj Jamil, kuka yake sosai ,musamman idan ya tuno da Dalilin shigar aminin shi wannan halin iyalan shine. Kwana yayi zubadda k'walla da Allah wadai matan daddy, gefe d'aya kuma idan ya tuna da sharud'od'in da Dr. Ya gindaye se ya fara tunanin taya za'a fara ,bayan _GIDAN MISBAHU_ gida ne daba d'igon kwanciyar hankali a ciki,,,Gida ne daba abunda ke k'unshe a cikin shi se tarin k'unci da takaici. A iya abubuwan da suke faruwa da Daddy ,ba k'aramin namijin k'ok'ari yaga yayi ba ,sama da shekaru yana fama da Abu d'aya, ba wani ci gaba ,a maimakon ma a samu ci Gaba da daidaiton al-amurra a'ah se ma dad'a rugujewa da komai ke yi.
A daren ranar Hajj Jamil kwana yayi kusa da Daddy yana ta tufka da warwaren yadda ze b'ullowa wannan al'amari na _GIDAN MISBAHU_.
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/25, 8:19 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA ASHIRIN_
*_____________________*
_Har Washe gari Daddy be farfad'o ba. Yadda Hajj Jamil yaga dare haka yaga safiya ,gaba d'aya bacci yayi k'aura daga idanuwan shi, Masallaci ma kasa zuwa yayi ,se dai ya kira Dr.Zaidu ya aiko masa da sallaya. Toilet din cikin d'akin ya shiga yayi alwala , koda ya fito ,wata nurse yaga ni ta ajiye masa sallayar kan kujera ,duba Daddy tayi dahar lokacin yake bacci ,tayi wasu 'yan rubuce-rubuce irin nasu na majinyatar lafiya ,kafin tayi ficewar ta._
_Hajj Jamil har yayi kabbara ze tada sallah ,ya tuno da gaba d'aya jiya ya manta be yi sallar magrib da isha'i ba ,mamaki ne ya kama shi ,a ranshi yake cewa wannan wani irin makuwa ne yayi jiya? Tunda yake be tab'a had'a sallah ba, amma Daya tuno da halin dayaga daddy a Daren jiya duk se jikin shi ya sake yin sanyi._
_Haka dai yayi ta jero salloli ,bayan ya gama ya zauna kan sallaya ,yafi sama da awa biyu yana kai wa Allah k'arar GIDAN MISBAHU. Har rana ta fito sosai ba yada labari ,kasancewar d'akin da suke ko ina a kulle yake ,babu wani kafa dazaka iya hango hasken waje, sedai iya fitullun dake d'akin masu haske ,Ga sanyin A/C daya karad'e d'akin._
_wayar shi ya janyo ,sakamakon hasken daya ga tana fiddawa ,alamar shigowar kira. Sunan Haajar ya gani akan screen d'in. Wani d'an guntun ajiyan Zuciya ya sauke ,shi gaba d'aya ma ya manta dasu ,gashi ya kamata ya sanar dasu ,saboda yasan zasu yi ta jiran shi, amma kuma koda ze kira sedai ko ya sanar da Haajar ita kad'ai, saboda yasan idan su suxee suka Sani dole zasu shiga wani hali ,musamman idan muka duba yadda daddy ya zame musu uwa da uba, a gurin shi kad'ai suke jin sanyi da dad'in rayuwa, inba yanzu da suka koma gidan Hajj Jamil ba ,shine fa abubuwa suka fara daidaituwar musu..._
_Har kiran ya tsinke Hajj Jamil be Sani ba ,saboda d'an gajeren tunanin daya fa d'a. Seda ta sake kiran shi akaro na biyu sannan ya d'auka tare da yin sallama._
_daga b'angaren Haajar ma sallamar tayi ,bayan sun gaisa cike da damuwa take tambayar shi a ina kwana?_
"Abbu sameer Hankalin mu gaba d'aya ya tashi ,musamman ma Hajiya k'arama ,tun jiya ta karb'a numbern ka take ta kira ,ta kira yafi sau a k'irga, amma baka d'auka ba."
A nutse Hajj Jamil ya rufe idanuwan shi ,sannan ya sake bud'e su. Gaba d'aya baya so yaji abunda ze dami yaran daddy a rayuwa, wani d'aci yake ji a k'asan zuciyar shi duk lokacin daze ga ko yaji matsala a tattare dasu.
"Tana ina yanzu?" Hajj Jamil ya tambaya
Haajar tace "ta shiga wanka"
"Ke kad'ai ce a wurin da kike?" Hajj Jamil ya sake tambayar ta
Tace "Eh! Ni kad'ai ce."
Wani siririn ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu ,kafin ya soma bama Haajar labarin dalilin daya hana shi kwana a gida, ya k'arasa zancen da cewa "Amma bana son su Hajiya k'arama su Sani ,hankalin su ze tashi. Ki dafo abinci ki kawo ,nasan idan ya farfad'o ze iya Neman abinci". Nan ya kwanta mata asibitin ,yace tasa drivern gida ya kawo ta.
Iya tashin hankali Haajar ta shiga tashin hankali, bata dad'e da sanin Daddy ba ,amma kuma ta rasa me yasa ta damu da komai nashi. A kid'ime ta amsa da " toh" ,suna cikin wayar ne Suxee ta fito wanka ,tana tsane ruwan jikin ta ,ganin Haajar na waya yasa ta k'araso da sauri tana tambayar ta "Abbu sameer ne?"
Gyad'a mata kai Haajar tayi alamar Eh. Ai Suxee bata jira Haajar ta bata wayar ba ta fizge tare manna wa a d'an madaidaicin kunnen ta na gefen hagu, a lokaci d'aya tana fad'in
"Abbu sameer lafiya kake kuwa ? Meya same ka? Meyasa bakwa kwana a gida ba jiya? Hankalin mu ya tashi sosai ,jiya ban iya yin bacci ba, gashi nata kiran wayar ka baka d'aga ba. Me yake faruwa ne??" Dika a lokaci d'aya ta shiga jero masa tambayoyi ba k'ak'k'autawa.
Wani irin lumshe ido Hajj Jamil yayi ,a lokaci d'aya kuma yadda Suxee ke masa magana yaso ya bashi dariya...
Jin yayi shiru yasa ta fara hawaye, a tunanin ta ko yana cikin matsala ne ,dama gata gwanar kuka ,Hausa wa suka ce _tusa hali balle anci wake_.
Jin da yayi alamar kamar ta fara kuka yasa ,yayi saurin amsa ta da cewa "A'ah Hajiya k'arama lafiya ta qalau ,wata 'yar matsala ce kawai ta hana ni dawo wa jiyan"
Har lokacin bata dena ruwan hawayen ba, cikin muryar kuka tace "kace lafiyar ka qalau ,kuma kace wata 'yar matsala ce ta hana ka dawo wa jiya ,alamaun kenan dai kana cikin matsala" ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani sabon kuka kamar wacce aka daka
Dafe Kai Hajj Jamil yayi tare da cewa "wai ni Allah na ,Hajiya k'arama rigima. To tsaya in miki baya kiji ni dakyau... Wani aboki na ne aka kira ni ba yada lafiya shine dani da Daddy muka zo duba shi ,to ba d'an garin nan bane, ba yada kowa anan ,shiyasa ni nakwana dashi ,daddy kuma an kira shi za'a sauke masa wasu kaya yau a store shiyasa ya tafi aida shi zan bari ya kwana anan ni kuma in dawo wajen Ku."
Se a lokacin daya mata wannan bayanin ne tukunna ta samu kwanciyar hankali. Share hawayen ta tayi ,tare da cewa
"Allah sarki ,Allah ya bashi lafiya! Muna yi masa ya jiki"
Murmushi Hajj Jamil yayi tare da cewa "Ameen Hajiya ta. To kiyi dariya mana, bana son wannan k'ananan kukan".
Wani murmushi ne ya k'wace mata ba tare da tayi niyyan yi ba Wanda ke k'ara fito mata da asirin kyawun ta, daga b'angaren shima ,murmushin yayi kamar yana ganin ta tare da cewa
" Good gurl. Se anjima idan na kira ko?"
Gyad'a masa kai tayi kamar yana ganin ta ,se kuma tace "OK take care". Kafin suka aje wayar. Haajar tuni ta b'ace a wajen ,ta shiga hada-hadar girkin da zata kai. Dan gaba daya hankalin ta baya jikin ta ,burin ta kawai shine taje taga wani hali Daddy ke ciki...
Daga b'angaren Hajj Jamil kuwa ,bayan ya kashe wayar ,murmushi ne d'auke a fuskar shi ,cikin zuciyar shi yake raya stubbornness irin na Suxee, yarinyar na burge shi ,musamman yadda bata iya b'oye damuwar ta, kai tsaye ce ita. A fili kuma ya furta " Suxee rigima ".
Mamaki ne ya kamashi lokacin daya duba agogo yaga sha biyu saura na rana ,duban shi ya maida inda Daddy ke kwance akan gadon asibiti, se ya fara tunanin meya sa Daddy be farka ba har zuwa wannan lokacin??? Nan kuma hankalin shi ya sake tashi...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/26, 2:26 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π