Showing 63001 words to 66000 words out of 86229 words

Chapter 22 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt

27 Dec 2024

3949

ba". Ba Dan daddy ya so ba haka ya hak'ura aka maida Haajar d'in gida. Kwanan su biyu da komawa gida sai ga Abu na Nema ya fi na da. Dan Haajar matuqar aka bar ta ba kowa a kusa da ita to fa ta fara cin na kare kenan tana nema ta fita. Abun da ya sake K'ullewa ahalin gidan kai. Kowa abun da yake kawowa a ran shi Haajar ta had'u da shafar aljannu ne. Hajj jamil ya sake kiran Dr Imam mahaifin Haajar ya shaida masa halin da ake ciki. Ba Dan ya kammala abunda ya je yi a qasar da yaje ba ,haka yabar komai ya kamo hanyar dawowa gida Nigeria saboda yadda Hajj jamil ya zayyana masa ciwon babu sauqi sai a wurin Allah. Kwanan shi biyu kafin ya iso Nigeria ,sai da ya kwana a jigawa ya d'auko duk wani maganin da zai buqata, sannan ya hawo jirgi safe zuwa sakkwato.




Hajj jamil ne ya je ya d'auko shi ya kawo shi gidan daddy. A mutunce su ka gaggaisa. Babu Wanda bai yaba da dattakon Dr. Imam ba. Mutum ne mai matuqar karamci. Sai a yanzu Hajiya ta gane inda Haajar ta yi gadon mutunci. Sai da ya huta sannan aka kai shi sashen Haajar d'in. Ba qaramin tausaya mata ya yi ba. Ba dan ya na da qarfin hali ba, babu abunda zai hana bai yi mata kuka ba ,musamman yadda soyayyar Haajar take a cikin ran shi. Kaf a 'ya'yan shi babu Wanda yafi so sama da Haajar.


Hajiya ,hajj jamil ,Anty zuwaira ne a zazaune sun zuba wa sarautar Allah ido.


Daddy da ke gefe kamar a jikin shi ciwon yake Dr. Yace a d'aure masa ita da igiya. Kowa ya shiga zaro ido. Hajj jamil yace "Abbu Yusuf mai yasa ba za'a rik'e ta ba sai an d'aure ta?" Murmushi Dr. Iman ya yi tare da cewa "wannan aikin ba na mutum bane Jamilu. Kai dai Ku d'aure ta. Daddy ko motsi bai yi daga inda yake ba ,saboda tsabar tausayin Matar shi da yake ji. Ba Dan ma mahaifin ta bane shakka babu bazai bari a maida masa da mata kamar mahaukaciya ba. Da taimkon Dr. Imam hajj jamil ya samu nasarar d'aure Haajar d'in ,shi ma sai da ya zuba mata wani ruwan magani akai sannan. Sai wani zaro ido take yi tana fad'in " Kai kuma waye? Ka sake ni nace. Ba zaka sake ni ba? Sai na kashe ka mutumin banza". Sai kuma ta fashe da kuka tace "Me nayi miki? Kar ki kashe ni" can sai ka ji ta fashe da wani irin ihu Mara dad'in sauti...




Karatun qurni Dr. Imam ya fara yi na Neman yaddar Allah kan aikin da ze yi. Haajar sai wani dariya ta ke yi tana zage-zage. Wani kundi Dr. Imam ya d'auko ya bud'e. Haajar na ganin shi ta fara ihu tana kururuwa. Duk Wanda ke wurin sai da ya zubar mata da hawaye. Wani magani Dr. Imam ya je ya bud'e bakin ta ya zuba mata. Sannan ya doki tsakiyar kan ta da qarfi tare da take qafar ta na hagu. Shak'e mata wuya ya yi a lokaci d'aya yana ci gaba da karanto alqur'ani. Shak'ar da Ya yiwa Haajar kowa sai da ya d'auka mutuwa za ta yi a yadda take kakari. Zuwa can sai ga shi tayi wani irin amai baqiqirin na sare saren zare. Kundin nan Dr. Imam ya ajiye a gaban ta ,ya danna yatsanta a ciki. Nan da nan hannun ya kama da wuta. Wani haske ne ya mamaye inda Haajar d'in ke tsaye. Can sai ga Haajar ta fad'i a gefe ga kuma wata siffa mai kama da Kubra sak an fitar a gefe. Duk Wanda ke wurin sai da ya girgiza. Nan Dr. Imam ya shiga yi wa wannan sifa tambayoyi ita kuma tana bashi amsa cikin wani yare Mara dad'in saurare da ba Wanda ke iya gane mai take cewa sai shi kad'ai. Hannun ta d'aya ya dad'a dannawa a cikin kundin, tana ihu tana qarawa a haka dai da jikin ta ya k'one gaba d'aya, daga k'arshe sai ga wani haske na bartsi. Daga nan ta watse. Dr. Imam ya yi hamdala tare da komawa ya zauna. Wani magani ya had'a San nan ya dawo kan Haajar da ke kwance kamar gawa. Tsakiyar kanta ya bud'e ya zuba wani magani na gari sannan ya fara yi mata yayyafi da wani ruwan magani da ke cikin kwalba fari. Ya dad'e a zaune kusa da ita yana karanto mata ayoyin waraka daga ubangiji. Kusan mintuna ashirin sai ga Haajar ta mik'e kamar ba ita ba tare da yin salati. Mamaki tayi yadda taga an tattaru akan ta. Ga mahaifin ta zaune kusa da ita. Tace "Me ke faruwa ne? Dan Allah Ku gaya mun"




Ruwan zamzam da aka yi wa addu'o'in shifa mahaifin ta ya d'auka ya bata. Da ido ta ni shi alamar mai zata yi da shi yace "ki karb'a ki sha" ba musu ta karb'a ta shanye tas.. Sannan yace a bata d'ankwali ta d'aura a kanta.




Wani zufa ne ya shiga tsatsafo wa Haajar ta ko ina ,sharkaf ta yi kamar wacce aka tsamo da teku. Nan Dr. Imam ya ce a kunna mata na'urar sanyi Wanda kafin ya fara aiki ya ce a kashe. Hajiya da kanta ta tashi ta kunna panka da kuma na'urar sanyi ,nan da nan iska da sanyi ya karad'e ko ina a parlourn. Sai wani ajiyar zuciya Haajar d'in ke saukewa kamar wacce tayi gudun tsere. Shima Dr. Imam ajiyar zuciyar ya sauke tare da zaro k'yallen goge zufa ya goge zufan fuskar shi ,sannan ya soma da hamdala tare da yiwa annabi salati, kafin ya d'ora da cewa "Dukkan godia ya tabbata ga Allah. Na San dikkan Ku kun ga abunda ya faru a yanzu ,za kuma kuyi mamakin wani irin nau'in al-amara ne wannan?" Hajiya tace "wannan gaskiya ne" Dr. Imam yaci gaba da cewa "Ciwon nan da Haajar d'in ake ta sanya mata jini alal haqiqa ba ita ake sanya wa jinin ba ,saboda masu shanye shi daban. Idan kuma da za'a yi shekarun annabi Nuhu A.S ana sanya mata jini ko makamancin wannan ba za Ku tab'a ganin ci gaba ba, sai dai ma daga k'arshe Ku rasata ma'ana ta mutu ,saboda jinin jikin ta da ake zuqa daga wani wurin daban. Wannan siffar da na fiddo daga jikin ta nasan kunsan ta?" Hajiya tace "shakka babu wannan Abokiyar zaman Haajar ce data mutu a gobarar da akayi a gidan ba da jimawa ba". Dr. Imam yace " to ta mutu ne amma kuruwar ta na nan na yawo. Ta kuma lashi takobin hana wannan ahali zaman lafiya. To amma da yake Allah ke yi ba wanin shi ba. Wannan kundi da kuka gani ,kundi ne na k'ona rauhanai. Saboda haka na nayi nasarar k'ona kuruwar wannan baiwar Allah da ke cikin jikin Haajar. Ba'anan matsalar take ba. Wannan ba ita bace asalin ruhin. Kuma muddin ba'a Nema ta asalin an k'ona ta ba ,to fa akwai gagaruwar matsala. Saboda haka na yi mata tambayoyi tun kafin na qona ta. Ta kuma gayamin inda za'a samu wannan babban kundin ,da an d'auko shi aka k'ona komai zai zama tarihi da izinin Allah." Wani irin ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da cewa "To yanzu a ina za'a samu wannan kundi malam?" Sunan wani daji Dr. Imam ya fad'a mai matuqar hatsarin gaske. Wanda ba lallai ka shiga wannan dajin ka dawo ba ,idan kuwa ka dawo to ba shakka zaka iya tab'uwar hankali. Ya kuma shaida musu akan lallai lallai Haajar d'in ake buqatar da ta je da kanta. "Kai ina!" Inji daddy "bazan tab'a barin Haajar ta je wannan wurin ba". Dr. Imam yace " Wannan itace mafitar mu ta k'arshe ,idan ba haka kuruwar zata dawo ,kuma idan ta dawo to dawowar bazai wa kowa kyau ba". Shiru kowa ya yi yana jimanta al-amarin. Kafin Dr. Imam yaci gaba da cewa "Zan shirya komai a Daren yau insha Allahu rabbi." Daga haka yace a rufe sashen Haajar d'in kowa da kowa ya koma sashen Hajiya. Haka kuwa aka yi.




Misalin k'arfe sha biyu na dare babu Wanda ya iya runtsawa banda suxee da auta da basu San wainar da ake toya wa ba. Wata farar mata ce ta shigo su Dr. Na zaune. Dr.imam yace ta zauna. Bayan ta zauna suka tattauna da shi cikin harshen larabci. Suna gama magana daddy yace wa Haajar "ki yi wa baquwa ta rakiya". Ba musu Haajar ta bi bayan wannan farar mata ,ita kuma Matar ta rik'e hannun Haajar suka fita.






Bayan sun fita daddy ya dubi Dr. Imam tare da cewa "Wannan wacece da suka fita da Haajar?" Gyara zama Dr. Imam ya yi tare da cewa "Wannan da kuke gani ba mutum bace aljana ce, Sunan ta maimunatu. Maimunata aljanar zuri'a ta ce ta amana." Cike da tashin hankali daddy yace "ina kuma zata kai Haajar?" Dr. Imam yace "dajin da fad'a muku za'a d'auko wannan kundin. Da taimakon Allah da taimakon maimunatu Haajar zata kai ga wannan kundi". A gigice daddy ya fita da gudu yana kiran suna Haajar! Dr. Imam yace " da'ace zaka dawo ka kwantar da hankalin ka da ya fiye maka kwanciyar hankali. Dan babu Haajar take so a wurin mu yanzu sama da addu'a." Kuka daddy ya fashe da shi ya na mai ci gaba da kiran sunan Haajar d'in babu qaqqautawa Sai da ya bawa kowa tausayi. Aiki Dr. Imam ya shiga yi tuk'uru. Dan kusan saida ya yi saukar alqur'ani. Su Hajiya kuwa alwala suka yi suka duqufa sallah har garin Allah ya waye. Banda daddy dake zaune cunkus kamar wani Mara lakka ,tun yana kukan mai sauti har ya koma sai dai hawaye kawai ke yi masa zuba.






















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/24, 12:09 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA SHIDA_


*____________________________*


















Har wuraren shida na safe babu Haajar babu alamar ta. Gaba d'aya ahalin gidan sun shiga damuwa ainun. Shida da rabi, Dr. Imam ya fito wajen sashen da suke ciki. A bakin k'ofa ya ga Haajar d'in a yashe ta yi wani irin baqi ta sauya kala kamar ba ita ba. Koma wa ciki ya yi ya yiwa daddy magana akan yazo ya d'auko matar shi. Da sauri daddy ya miqe yana fad'in "Ina take?" Ganin kwance a qasa a k'ofar shiga ya sa yayo saurin yowa kanta ba shiri ,ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan ta. Dr. Imam yace "ka shigo da ita ciki". Daga haka ya yi shigewar shi. Ba shiri daddy ya sunkuci Haajar d'in ya bi bayan Dr. Imam. A tsakar d'aki Dr. Imam yace ya ajiye ta. D'ankwalin dake k'ulle a jikin zanin ta ya kwanto tare da warware k'ullin ya furta " Alhamdulillahi! Wannan shi ne kundin da ake da buqata". K'ok'arin k'ona kundin ya shige yi da ayoyin Allah. Nan take wannan kundin ya ka ma da wuta ,wani bak'in hayak'i na tashi. Sai da ya cinye tas sannan ya yiwa Haajar d'in yayyafin ruwan magani. A zabure ta tashi zata ruga a guje ,ya rik'o ta, Tare da ci gaba da karanto mata ayoyin waraka daga ubangiji. Sambatu Haajar d'in ta shiga yi kamar wata zararriya. Addu'o'i sosai Dr. Imam ya dinga yi mata, daga haka wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Ya sake furta "Alhamdulillahi! Sauqi ya samu daga Allah! Yanzu ta samu bacci. Sannan wannan baccin idan zata kai sati d'aya tana yin sa kar a tashe ta ,sai lokacin da ta farka da kanta. Kar kuma Ku damu, babu abunda zai sake faruwa da izinin Allah. Za kuma Ku iya ci gaba da sabgogin ku". Hajiya tace " Insha Allahu za mu yi k'ok'arin kiyaye wa. Sannu da aiki malam, Allah ya saka maka da alkhairi. Da ba Dan kazo ba bansan yadda za mu yi da wannan rikitaccen al-amarin ba mai kama da al-mara. Duk da cewar Haajar 'yar ka ce ,amma mu ka yi wa wannan taimakon, Dan Haajar wata jigo ce daga cikin wannan ahali da ba zamu tab'a qaunatar abunda zai same ta na rashin dad'i ba. Mun gode sosai". Dr. Imam yace "Allah ya tsare gaba".




D'akin Hajiya aka maida Haajar d'in. Sai a lokacin kowa ya samu kwanciyar hankali. Hajj jamil jan Daddy ya yi suka tafi gidan shi ,a can suka yi bacci , ba su suka farka ba sai wuraren sha biyu na rana. Anty zuwaira ma zuwa tayi ta kwanta. Dr. Imam kuwa labari ya shiga baiwa Hajiya, kan abunda ya faru da kuma dalilin faruwar abun ,ya tabbatar mata cewa asalin tushen gurb'acewar rayuwar Kubra akwai sanya hannun mahaifiyar ta ,Wanda tun farko aka gina rayukkan akan b'ata da sagba ta miyagun jinnu, Wanda shi ne dalilin da yasa ko bayan ta mutu ta dawo a matsayin kuruwa. Wannan kundin kuma da aka k'ona shi ne asalin rayuwar Kubra... Ya faffad'awa Hajiya maganganu da dama na firgi ,al-ajabi da kuma ban tsoro. Hajiya ta yi ta mamakin dama hakan na faruwa a wannan duniyar ta mu? Dr. Imam ya tabbatar mata da akwai abunda ma ya fi wannan d'aure kai idan ta ji shi... Kusan kwanan Haajar uku ,ko k'wak'k'waran motsi ba ta yi ba. Wanda kowa ya damu da hakan. A gefe d'aya kuma mahaifin ta na ci gaba da yi mata addu'o'i da taimakon magungunan musulunci da yake da k'warewa akan su. Sai a rana ta biyar sannan Allah ya yi mata farkawa. Farin ciki ya dawo sabo. Kar ma daddy ka ji labari, Dan har rumgume ta ya yi Dan murna, ya ma manta cewar akwai mahaifiyar shi da mahaifin Haajar d'in a wurin. Nasihohi sosai Dr. Imam ya yi musu. Ya kuma ba da magungunan da Haajar d'in za ta ci gaba da amfani da su. Washe gari Dr. Imam ya yi musu sallama ya tafi. Haajar hadda kukan ta ,Dan sosai take kewar mahaifin na ta. Ya sha gaya mata a baya cewa duk soyayyar nan da yake mata ,za'a yi wani lokacin da wani ko wasu sun fi shi buqatar ta'. Shakka ba bu wannan lokacin ne. Bai tafi ba sai da ya yi mata nasihohi sosai itama, ya kuma k'ara gaya mata yadda mijin ta da ahalin shi ke matuqar Kaunar ta. Gargad'i Dr.Imam ya yi mata akan komai wuya wannan ahali sune abokan rayuwar tana duniya...




Kusan har aka yi sati Haajar bata gama dawowa yadda take ba, gaba d'aya jin ta take kamar ba ita ba. Daddy musamman ya shirya walima Dan yiwa Allah godia. Satin Anty zuwaira biyu ,ta koma gida jigawa a inda daddy da Hajiya suka cika ta da tarin abun alkhairi... Bayan wata d'aya. Komai ya lafa ,rayuwa ta dawo musu sabuwa. Haajar ta sake samun wani cikin. Kowa sai murna ya ke yi. A b'angaren d'aya kuma an so a saka ranar bikin Suxee da Barr Kabir ,duba da yadda soyayyar su tayi k'arfi. Haajar ta nema alfarman da a bari idan Allah ya sauke ta lafiya. Hajiya tace "duk yadda take so hakan za'ayi. Dan itace uwar amarya kuma uwar biki". Wannan batu ya yiwa Haajar d'in dad'i. Sannu da hankali cikin ta sai girma yake yi. Ta k'ara kyau ta yi haske gwanin sha'awa. Kulawa da tarairaya kuwa daga wurin daddy sai Wanda ya manta ,wannan ne ya k'ara bata damar murje gwad'arta take zuba masa zallar shagwab'a tare da nuna masa so da qauna a koda yaushe.




A b'angaren d'aya kuma Matar hajj jamil Hajiya zaliha ta dawo daga wurin aikin ta da take yi a wata qasa, Bayan tafiya na dogon zango da ta yi na tsawon watanni tara zuwa goma. Wanda a Qa'ida duk bayan wata biyar ta ke dagowa gida, tare da d'anta d'aya mai suna SAMEER. Abun ya yi matuqar d'aure Mata kai yadda ta dawo wannan karon Hajj jamil baya d'aukin ta ko kad'an kamar yadda ya saba. Hasalima ko kad'an bai nuna alamun jin dad'in ganin ta ba. A tunanin ta ko dad'ewar da ta yi ne bata dawo ba ya sanya ya ke fushi da ita, bata San abunda ya ishe shi bane ya ishe shi. Shi damuwar shi d'aya ne akan auren Suxee da Barr Kabir. Hajiya zaliha mace ce ta tsara daidai gwargwado da ta San abunda ya kamata ,tana da duk wani kwalitis d'in da namiji ke buqata, amma a zahiri bansan mai yasa ta fifita aikin ta sama da bautar auren ta ba, aikin ma a wata uwa duniya. Ta yi ta k'ok'arin ganin ta tambayi hajj jamil abunda ke damun shi. Hajj jamil mutum ne da baya tab'a iya b'oye damuwar sa idan ka tambaye shi. Ko kalma d'aya bai rage mata ba akan yadda yake matuqar son Suxee ,farin cikin shi shine ya ga ya auro ta tazo gidan shi a matsayin Matar shi ta sunnah. Hajiya zaliha ba ta gane wacce suxeen yake magana akai ba ,sai da ta sake tambayar shi, ya tabbatar ma ta da Suxee 'yar daddy da ta sa ni. Iya tashin hankali Hajiya zaliha ta shiga tashin hankali, Dan bata tab'a tunanin irin rana mai kama wannan zai zo mata ba. Ta yi kuka kamar ba gobe musamman yadda ta ga mijin ta ya susuce akan son 'yar aminin shi. 'Yar da idan da kara yace ya ba da ita ,ta badu kenan. Sosai tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login