Showing 66001 words to 69000 words out of 86229 words

Chapter 23 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt

27 Dec 2024

3948

kaico da irin halin da ta sanya mijin ta a ciki ,ta yadda duk wani abun da zai je ya dawo laifin ta ne. Ta San bata kyauta wa mijin ta, d'anta da rayuwar auren ta ba ,kai hadda rayuwar ta kacokam. Ta yi matuqar tausaya wa mijin na ta da ita kanta. Gafarar ubangiji ta shiga nema ba dare ba rana ,Dan tasan matuqar ta mutu a haka ta shakka babu aljannah ko a gidan ubanta ake raba ta sai dai a raba babu ita. Da yake tana da rabo, watsar da duk wani rud'in duniya ta yi ,aikin ma tace ta aje ,ta dawo ta rumgumi auren da mijin ta hannu bibbiyu. Ta fara basa kulawar da a da can bata basa makamancin sa ba. Ta je ta cire tsarin iyalin da ta yi, a cewar ta bata son haihuwa da yawa ,Dan idan ta tara 'ya'ya za su hana ta aiki.. Ita dai aiki... Sosai ta ke iya bakin k'ok'arin ta na ganin ta kula da mijin ta. Hajj jamil ya ji dad'i sosai yadda Hajiya zaliha ta sauya lokaci d'aya, sai dai fa a gefe wutar son Haajar ne kawai ke dad'a ruruwa a zuciyar shi.






Ranar hutun k'arshen mako wato weekend Hajj jamil da Matar shi Hajiya zaliha tare da d'an su suka je gidan daddy. Fad'a sosai tare da nasihohi mai shiga jiki Hajiyar daddy ta dinga yi ma ta. Hajiya zaliha hadda hawayen ta. Ta yi wa Hajiya alqawarin insha Allahu za ta gyara. Yadda Haajar ke tafiyar da rayuwar ta yayi matuqar burge Hajiya zaliha ,wannan ya sa Hajiya zaliha ta so su had'a k'awance duk da cewar za ta girmi Haajar d'in. Kuma Haajar 'yar yayan mijin ta ne. Sai dai da yake babu wata shaquwa mai qarfi tsakanin su. Amma ta tabbata girman huhun goro ba shi bane. Saboda haka suka sha hirar yaushe rabo da Haajar. Har dare su Hajiya zaliha su na gidan daddy kafin su ka tafi. Tun daga ranar Hajiya zaliha ta samu wurin zuwa dan ta maida Haajar tamkar qawarta. Bayan sati d'aya sati biyu haka takan zo su sha hira sosai da Haajar. Shakka babu Hajj jamil ya ga amfanin zaman Matar shi da Haajar. Dan ba iya rayuwar su komai ya canza ba ,hatta a shimfid'a ya ji bambamcin na daban.
Bayan wata tara Haajar ta haifo santala santalan 'ya'yan ta mace da namiji. Namijin kama yake da daddy sak macen kuma kama ta ke da marigayiya Haseena. Murna a wurin wannan ahali abun Sai Wanda ya gani. Tun randa aka haihun Hajiya zaliha kullum ta na gidan ta na yiwa Haajar d'awainiya. Saura kwana biyu biki ,dangi na kusa da na nisa suka halatto ,da ma ga shi an dad'e ba'a yi sha'ani a gidan daddy ba. Musamman dangin Haajar d'in da wasu daga ciki sai dai suka ji labarin d'aurin auren. Yayyin ta da k'annen ta rankatakaf babu Wanda aka baro ,tare da Matar mahaifin su da ta zamo tamkar uwa a gare su. Kai! Haajar ranar ina ruwa ta tsoma kan ta Dan murna. Daga b'angaren daddy ma anga gayyar mutanen kano da kewaye. Hajiya zaliha ma ba'a barta a baya ba wurin yo tata gayyata. Ranar suna namijin yaci sunan Hajj jamil ana masa laqani da Hassan d'in shi, macen kuma taci sunan marigayiya Haseena ana kiran ta da hussaina. Taro ya yi taro anci ansha ,mai jego da 'ya'yan ta sun yi shiga daban-daban gwanin ban sha'awa. Duk Wanda ya zo taron suna da abun azziki yake tafiya. Banda kyaututtuka da zunzurutun kud'i da jariran suka samu daga wurin abokan su daddy. Hajj jamil kuwa kamar shi aka yi wa haihuwa ,Dan kusan komai shi ya yi. Barr Kabir ma sai da ya yiwa yaran kyautar naira dubu d'ari tare da akwatin kayan jarirai biyu. Hajiya ma ba'a barta a baya ba ,Dan kyauta ta yi Haajar d'in na musamman. Hatta Dr. Imam mahaifin Haajar sai da ya yo aike. Kai lissafa tarin alkhairan da Haajar da yaran ta suka sa mu b'ata lokaci na. Dan idan za mu kwana mu wuni ba zamu gama lissafe adadin abubuwan azzikin ba. Bayan su na mutane na ta watsewa. Ranar da 'yan uwan Haajar za su tafi ,kyauta daddy ya musu ba ni da kyauta ba. Sun ji dad'i matuqa sun kuma yaba da irin mijin ta Haajar ta samu. Bayan kowa ya gama tafiya. Haajar Sai da ta nemi inda za ta ajiye kayan yaran ,dan tsabar sun mata yawa. Uban gayyar kuwa wato daddy ,kyutar gidan gonar shi sukutum ya yiwa yaran shi. Haajar ba ta so ba Dan gani take abun ya yi yawa. Ga wa'yancan ga kuma wannan. Hadda k'wallan ta Dan farin ciki. Account Daddy ya bud'ewa yaran ya zuba musu duk kud'ad'en da suka samu. Haajar ta tambaye sa akan ya za'ayi da su yace ta yi amfani da su idan ta na da buqata Dan shi dai idan bai qara musu ba bazai karb'a sisi ba. Shawartar shi Haajar ta yi akan to ko ta bud'e gidauniya na taimakawa gajiyayyu da nakasassu. Daddy yace wannan shawara ce mai kyau. Hakan kuwa aka yi. Kafin kace me sunan Haajar da tallafin ta ya zaga sakkwato da kewaye.






Bayan sun yi arba'in. Suka shirya Dan zuwa gano Hajiya Gwaggo da ta dad'e a kwance ba tada lafiya. Gaba d'ayan su suka tafi. Yadda su ka samu Hajiya gwaggo kam rai hannun Allah. Washe garin zuwan su wata tsohuwa mai suna TANI ta zo gidan. Hannun ta d'aya a shanye. Aka tambaye ta wa take nema? Tace Hajiya Gwaggo. Nan aka kaita taga yadda jikin Hajiya gwaggon ya yi. Matar nan ta fashe da kuka. Nan ta soma basu labarin abunda ya wuce shekaru aru-aru. Ga Hajiya sakina a zaune kishiyar Hajiya Gwaggo ,ga hajiyar daddy da daddyn kan shi ,ga wasu daga cikin 'ya'yan Hajiya sakina. Haajar ma na daga gefe a zaune. Matar mai suna TANI tace "Tun suna 'yan mata sun gina rayuwar su akan Neman duniya da son zuciya ita da Hajiya Gwaggo. Ba su da aiki sai shiga malamai. A haka har suka yi aure. Ko da mijin Hajiya Gwaggo zai auro Hajiya sakina babu inda ba su shiga ba Dan su hana wannan auren ,amma duk inda suka shiga sai a ce musu wannan aure ba fa shi. A haka aka zo aka yi auren har Hajiya sakina ta fara haihuwa. Duk lokacin da Hajiya sakina ta samu ciki sai sun je an yi musu duba. Har lokacin da ta samu cikin mahaifin daddy aka fad'a musu cewa namiji za'a haifa, kuma mai arziki. Nan fa muka dinga k'ulla tuggu akan yadda za mu zubar da cikin amma Allah ya yi sai abunda ke cikin nan ya ta ka doran k'asa. To dama a lokacin Hajiya Gwaggon itama tana da ciki. Allah kuma yasa lokacin haihuwar su yazo rana d'aya. Mu ka yi amfani da wannan damar muka canza 'ya'yan. A inda muka d'auke d'an Hajiya sakina wato mahaifin daddy mu ka sauya shi da 'yar Hajiya Gwaggon Dan ace ita ta haifa. Ashe da ma 'yar da muka sauya wa muka ba Hajiya sakina ba mai zama bace, Dan tun kafin a yi suna Allah ya yi Mata rasuwa. Hajiya Gwaggo kuma ta ci gaba da rik'e d'an Hajiya sakina a matsayin na ta." Tsohuwar nan ta sake fashewa da kuka. Tace "Na ga jarabawar rayuwa da mugayen qaddarori da bazan so ace na mutu a ciki ba. Duk Wanda muka zalunta na yi ta k'ok'arin ganin na nema inda yake na ba shi hakuri. Nan ma kusan sama da shekaru goma ina Neman gidan amma Allah bai sa na gane gidan ba Sai yau." Tsohuwar na kuka tana Neman gafarar su. Hajiya sakina tace ta yafe mata ta ta shi ta tafi. Hajiya Gwaggo ko hawaye ne ya shiga wanke mata fuska ,tana so ta nemi yafiyar su amma ba dama ciwo ya ci qarfin ta. Hajiya sakina na hawaye tace wallahi ta yafe mata har ga Allah ta kuma gargad'e su akan ba ta yadda a fitar da zancen ba. Tun da har Wanda ake yi Dan shi ya mutu. Ranar kowa da abun ya kwana a rai. Abu sai kace wasan kwaikwayo. Washe gari kiran sallar farko na asubahi Hajiya Gwaggo ta amsa kiran ubangiji. Hajiya sakina ta yi kuka kamar ba gobe ,Dan ita har ga ba ta tab'a rik'e Hajiya Gwaggo a ran ta ba. Tana kuma matuqar qaunar ta har cikin zuciyar ta ,musamman jiya da ta ji ance ta riqe d'an da ta haifa. Abunda ta yadda da shi shine ,babu Wanda zai so naka har ya rik'e face masoyin ka...


























MUJE ZUWA💃




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/26, 7:29 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI_


*____________________________*
















Misalin k'arfe Tara da safe aka yi jana'izar Hajiya Gwaggo aka kai ta makwancin ta. Kusan duk Wanda ya bud'e baki Allah wadai yake da halayyar Hajiya Gwaggo. Banda Hajiya sakina da ke ta faman kuka tana fad'in ta yafewa Hajiya Gwaggo duk abunda ta yi mata duniya da lahira. A gefe d'aya kuma ahalin gidan sai k'ara jimanta lamarin suke yi wai Hajiya Gwaggo ba ita ce ta haifi Baba Alhaji ba mahaifin Daddy,,, kai wannan Abu da d'aure kai yake. Ran da aka yi addu'an uku jama'a suka fara watsewa, yayinda wasu daga cikin ahalin wannan gida ke jin dad'in mutuwar Hajiya Gwaggo, a cewar wasu daga ciki ,ta gallaza musu ta addaba musu, su da gidan mahaifin su amma ba su da saqat. 'Ya'yan Hajiya sakina sai murna suke yi na kasancewar daddy d'an d'an uwan su ne. Suka zauna suka tattauna akan yadda za su k'arfafa zumuncin su, a ka saida magana cewa za'a dinga had'uwa anan gida duk bayan wata uku lokacin 'ya'yan su dake makaranta sun samu hutu, ya ka ma zama hud'u kenan a shekara. Wannan batu ya yi wa kowa dad'i. Daga su Haajar ba su baro ba sai da aka sanya ranar auren Suxee da Barr Kabir nan da wata uku me kamawa. Aka sanya na wasu 'yan matan wa'yan da 'ya'yar daddy wata biyu bayan bikin Suxee. Ba'a tashi daga taron ba saida Hajiya sakina ta yi musu wasu 'yan nasihohi masu ratsa jiki. Kusan dikkanin su da farin ciki suka watse cike da d'aukin junan su. Daga haka kowa ya watse, ciki yadda su daddy. Rayuwa ta dawo musu sabuwa.


Sannu a hankali 'ya'yan Haajar sai wayo suke yi. Bayan sun dawo kano ba Dad'e wa ba, Haajar ta fara shirin ta na zuwa gida Jigawa Dan dubo 'yan uwanta. Tare da suxee ta tafi, a yayin daddy ya ba su driver sannan ya cika su da kayan arzuka a cewar shi su yi tsara. Ya kum shaida masa ze biyo bayan su shima ya gaida ahalin ta. Kwanan su Haajar biyu da tafiya Daddy ya shirya shima ya tafi. Babu Wanda bai ji dad'in zuwan su ba. Dan kusan lungu da sak'o na 'yan uwan Haajar babu inda daddy be sa Ankai shi ba ,duk inda yaje kuma sai ya yi musu kyauta ta ban mamaki. Kowa sai San barka yake yi da irin mijin ta Haajar ta samu. A yayin da shima daddy ke jin dad'in irin karrmawa irin na 'yan uwan Haajar. Dr. Imam ma yaji dad'in zuwan su, dukda cewar yana shirye-shiryen barin k'asar ne, zuwan su ne ya d'an dakatar da shi. Satin daddy d'aya ya juya. Haajar kuwa tunda taje Matar mahaifinta ke d'awainiyar gyaranta ciki da waje. A cewar ta bata samu damar yi mata na aure ba ,Dan haka take iya bakin k'ok'arin ta na ganin ta ranka mata. Kusan duk wani had'i da Haajar d'in za ta sha ko tayi amfani da shi tare da Suxee suka sha ,dukda cewa suxeen bata son amfani da wasu daga ciki, daga tace wannan ba dad'i ,,sai tace wannan bauri. Haajar tace "kya dai ji da shi. Wata rana ina zaune zaki zo nema" suxee tace "cabdi. Aiko Anty Haajar ba rana." Dariya kawai Haajar tayi tare da cewa "To Allah ya kaimu". Kusan satin su uku a Jigawa sannan suka dawo dawo gida cike da tsaraba.






A kwana a tashi kwanaki tafiya suke yi. Yanzu saura wata d'aya da kwanaki bikin Suxee. Haajar ta shiga gyaran amarya ba dare ba rana. Dan kusan yanzu sun rage zuwa sashen Hajiya ,aka yi sa'a kuma daddy yayi tafiya. Kullum da irin sabon tsumin da Haajar ke yiwa Suxee. Banda gyaran jiki da ake yi kullum safe. Ita da kanta suxee ta ji canji a jikin ta. Ga wani qiba data k'ara fatar nan kau sai shek'i take yi.


Saura sati uku bikin Suxee. Haajar ta zaunar da ita ta fara shimfid'a mata darussa zamantakewar aure ta yadda zata rik'e mutuncin gidan ta ba boka ba malam. Haajar ta soma da cewa "MIJI ABOKIN RAYUWA MACE ABOKIYAR RAYUWA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukin sarki wanda ya shar'anta aure kuma ya sanyashi ya zama bauta ga bayi,Tsira da amincin Allah su tabbata ga uban dakinmu Annabi muhammad ﷺ da iyalan gidansa da sahabbansa da wadanda suka bisu da kyautatawa har izuwa ranar sakamako. wasu daga cikin fa'idoji da kuma al'fano da yake tattare da yin aure.
KAD'AN DAGA CIKIN FA'IDOJIN AURE
Aure Bautar Allah ne kuma sunnah ne na Annabi ﷺ da sauran Annabawan Allah, Babu wani Annabi daga cikin Annabawan Allah face ya kasance yana da aure. Aure Hanyane na Samun zuri'a ta ýaýa wadanda zasu bautawa Allah sannan kuma Annabi yayi Alfahari dasu a ranar alkiyama. Aure Hanyane na samun nutsuwa da kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa. Aure Hanyane na kiyaye ido daga kallace kallacen haram kuma hanyane na kange Al'aura daga fadawa zinace zinace. Aure Hanyane na kare mutuncin yaron da za'a haifa,domin duk yaron da aka haifeshi ba ta hanyar Aure ba, to yaron zai rayu cikin qunci da tsangwama.


WAI SHIN MENENE NI'IMA A JIKIN MACE?


Ni'ima dai wasu sinadarai ne da suke taruwa wajen jiyar da dadin ma'aurata ko basu cikakken gamsuwa lokacin Saduwa. Alamomin cikakken ni'ima sun had'a da:


1- jin ki cikin danshi
2- kasancewa cikin d'umin farji
3- Fitowan ruwa lokacin jima'i
4- Cikowar gaba da jinki a matse
5- Gamsar da miji da rikicewan salo lokacin saduwa koda baya sambatu
6- mace mai cikakken ni'ima takan ji sha'awa lokaci lokaci
1- Mace zata rika jinta cikin danshi ko tafiya kike zaki ji santsi santsi a jikinki sannan in kinje fitsari wajen tsarki zaki ga ruwa mai dan yauki ko yauki sosai a haraban farjin kina wankowa. ko kiga alamun shi a pant dinki ,kuma ruwan zaki gan shi fari kaman ruwa ko ki ganshi ruwan madara ,ya danganta dai. Amman duk ruwan da zaki gani wanda baida yauki wani daban ko kaman koko to na cuta ne
Dan haka mata ku kula ,mu san wani kalan ruwa muke fitar wa daga jikinmu.
Sannan akwai wani ruwa dake fita daga jikin mace wanda ba ni'ima bane kuma ba infection bane.


Nasan zaku ce wani ruwa kenen???
Idan mace suka yi jima'i da mijinta da daddare to washegari zata ga maniyyi yana dan fita kadan kadan, kuma shi baida yauki sosai wasu har sai washegari ma maniyyin ke gama fita, musamman idan mijin ya zubarda maniyyin shi sosai. Kila kuna observing haka idan baki lura ki fara sa ido zaki gani.
2- Mace ta kasance cikin dumi alama ne na ni'ima dumin hq mace na tsimakawa matuka wajen gamsar da maigida yana tickling high arousal wajen sex yana taimakawa wajen sa bananan maigida ya kara kauri da tsawo ba'aso cikin farji ya kasance da sanyi yana tsinka ni'ima kuma yana rage kuzarin namiji wajen saduwa. Ta yanda zaki gane kina da dumin gaba ko hannunki kika dan jingina ta kasan ki zakiji da dumi. idan farjin ki ba ya da dumi ba zakiji ba...


ABUBUWAN DAKE SA D'UMIN FARJI


1-Tsarki da ruwan dumi koda yaushe
2-Sa pant akai akai amma banda dare
3- Yawan had'e kafan ki in kina zaune
4-Tsugunno kan rushi ko baki sa komai ba.
5-Lulluba da ko zanin gado ne lokacin saduwa... Sai kuma nature.


AKWAI ABUBUWA DAKE RAGE DUMIN FARJI


1-tsarki da ruwan sanyi
2-Rashin sanya pant
2-Yawan wawan zama
3-Rashin lulluba
lokacin jima'i ko kuma kunna fanka ko Ac
4-Saka yatsa a farji
5-Yawo ba takalmi a tsakar gida


BA KYAU, QUGU KO MANYAN NONO BANE D'AND'ANO


Mutane da dama sun dauka mace mai kiba ko mai kyau ko mai kugu ko me manyan brs itace mai ni ima to gaskiya abin ba haka bane..


Allah ya halicci mata kala kala kuma kowacce da irin baiwar da yayi mata wata za ka ga bata da kiba amma kullum kamar korama take wata kuma tanada kiba amma kullum tana bushe. Wasu matan idan su na da ni'ima zasu rinka zubarda wani ruwa mai kamshi sannan kullum suna cikin shauki da sha awar jima'i, amma shi wannan ruwan akwai wanda yake fitowa na cuta ,ya danganta da kalarsa to amma mace wanda bata da ni ima bata cika sha awar jima'i ba amma idan namiji kuma ya nemeta tafishi zumudi....


DAN QARIN SHA'AWA INGATACCIYA DA NI'IMA MAI DOREWA


1- ki samu kankana mai kyau kifere samanta kawai seki caccaka cikinta sannan ki samu kwakwa kallo daya ki gurzata ki zuba aciki duk da ruwan saiki saka garin dabino da garin kanumfari saiki rufe kibarshi ya yini saiki zuba madara peak da zuma ki gaurayayshi sosai seki shanyeshi duka in bazaki iya sha atakeba zaki iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login