Showing 18001 words to 21000 words out of 86229 words
Chapter 7 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
ijabar ,to ina ji a jiki bada jimawa ba ,Allah ze musanya maka da mafi alkhairi insha Allahu."""
A ranar dai daddy da Hajiya kwana suka yi suna tattauna matsalolin gidan shi, da daddare yaso ya tafi sashen bak'i ya kwana ,ko ya samu yaji rad'ad'in da zuciyar sa ke masa ya ragu ,amma tsakanin d'a da mahaifi se Allah ,tunda Hajiya ta karanto akwai damuwa a tattare dashi ,hana shi fita tayi ,se dai suka kwana a sashen ta. Ko parlour bata bari ya tako ba ,gadon ta ta sauka ta bashi ,ita kuma tayi shimfid'a a k'asa, ranar kwana yi masa nasihohi tayi ,tare da lallashin zuciyar shi ,a haka Daddy be ma San bacci yayi awon gaba dashi ba...
_washe gari tunda sassafe Hajiya sakina (kishiyar Hajiya Gwaggo), ta auko wa daddy da abun karin kumallo..._
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/23, 2:19 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA SHA SHIDA_
*_________________________*
_Tun bayan tafiyan Daddy kano ,su suxee ke cikin walwala da kwanciyar hankali. Sosai Haajar ke saka su nishad'i ,musamman data gane kamar akwai damuwa a tattare dasu, ba kuma wai sun gaya mata bane , a'a hasalima wani magana ta b'angaren rayuwar junan su be shiga tsakanin su ba ,saboda Haajar ba mace bace me yawan magana musamman akan abunda be shafe ta ba ko ba'a saka ta a ciki ba ,amma tana da Abu d'aya Wanda zamu iya cewa yana daga cikin baiwar da Allah ya mata ,duk yadda mutum yake cikin damuwa kuma yake k'ok'arin b'oye ta ,to hakan a wurin Haajar kamar ma k'ok'arin bayyana mata kake yi ,ba dai zata ga abun bane saboda batasan gaibu ba ,amma tana da hasashe nad'an Adam, da ace zata nazarci matsalar ka sosai ,to idan da zata furta cewa ga abunda ke damun ka ,kuma seka ga insha Allahu kamar ta sara akan gab'a ,ko kuma k'anin hakan. Sosai take kutse cikin rawar su haseena Dan ganin ta kwatanta wargatsa abunda zata iya na damuwar su ,seda tayi duk yadda tayi suka sake da ita ,Auta kam ta samu sabuwar Anty Dan ko abinci idan dai ba Haajar ce zata bata ba ,to bafa zata ci bane ,idan ma aka matsa mata se ta tsiri k'ananan kukan ta ,haka dai Haajar ke biye ta ,Ashe dama Auta fili take nema ta b'arje gumin ta ,samun wuri yasa har ta fara wani shagwab'an iyayi da bata yi da a gidan su. Sautari idan Suxee tana ganin yadda Auta ta samu kyaky-kyawar kulawa a wurin Haajar, har k'wallan tausayin kan su take yi, saboda a rayuwa su basu tab'a sanin menene soyayyar uwa ba, se dai ta uba ,shima ba wani kyaky-kyawar kulawa ba saboda d'an kasuwa ne ,ba zama yake yi ba. Ba Auta kad'ai ba ,hatta su d'in da suke manya Haajar bata saka musu ido ba. Bata tab'a barin su cikin kad'ai ci ,ko wani lokaci takan nemi abunda zasu yi me amfani Dan karta barsu zaman tunani._
_Hajj Jamil ma ba'a barshi a baya ba wajen basu kulawar data dace ,haka yake jan su a jiki tamkar 'ya'yan daya Haifa na cikin su ,Dan tsakanin shi da Daddy fad'in alaqar b'ata lokaci ne , 'yan uwa ma na jini sunyi kad'an su nuna musu so da qaunar junan su. Shi gaba d'aya ma yaran tausayi suke bashi ,kusan da abun yake kwana arai dashi kuma yake tashi ,koda yaushe tunanin shi shine ina mafita ,haka dai ya fawwala allah al-amarin ,be kuma yi k'asa a guiwa ba wajen ci gaba da gayawa ubangiji matsalar da suke ciki. Wannan yasa idan ya dawo da daddare se ya tafi can sashen nasu ,yayi ta Jan su da hiran ban dariya ,a haka se sukai k'arfe goma na dare, kawo lokacin wani shak'uwa me k'arfi ne ya sake shiga tsakanin shi dasu suxee Wanda ada babu._
_Kwanan su suxee uku ne kawai a gidan Hajj Jamil ,Amma idan ka gansu kai kace sun shekara ne. Sosai suka sake suka gudanar da al-amarin su ,tamkar suna gidan Daddy, kai wani abun ma da suke anan basa yin shi acan ,saboda sun San a gida ko sunyi ba duba musu za'ayi ba. Rayuwar se ta koma musu sabuwa fil ,se dai idan suxee ta tuna cewa ,idan fa Daddy ya dawo zasu koma gida ,duk se wani bargon tsoro ya lullub'e ta ,Dan ta riga ta gama tsorata da gidan zuwa yanzu._
_Se da daddy ya kwana uku ,yana shan nono wajen Hajiya ,Dan gaba d'aya kulawar da Hajiya ke bashi a kwana ukun nan yasa ya fara mantawa da wasu matsalolin. Zallar soyayya da qauna ,so irin na d'a da mahaifi ,shi Hajiya ke nuna wa daddy ,ji take kamar ta hana shi komawa ,amma hakan baze samu ba. Daze tafi Hajiya harda 'yar k'wallan ta ,ba tada dai matsalar komai na buqatun rayuwa Dan gaskiya Daddy na k'ok'ari ta wannan fannin ,ba ma ita ba ,na tare da ita ma na cin albarkacin ta. Be yiwa Hajiya Gwaggo sallama ba ,Dan ita a tunanin ta tun ranar ya koma, sashen Hajiya sakina kawai ya shiga ,Fura ta bashi manya-manya da aka saka a cikin bakko guda uku tace "ga wannan akaiwa iyalin ,nasan Hajiya k'arama dason fura". Godia sosai Daddy ya mata ,kafin ya kama hanya ,a ransa yake raya cewa ina ma Hajiya sakina ce kakar shi ba Hajiya Gwaggo ba ,Dan kwatakwata rayuwar su ta banbanta._
_tun bayan fitowar daddy gaban shi ke fad'i ,har zuwa lokacin daya kira Hajj Jamil ya sheda masa yau ze dawo ,gaban sa be dena fad'uwa ba. Be kawo komai a ranshi ba ,Se da ya shigo garin sakkwato ,nan fa zuciyar shi ta fara wani irin tsalle kamar zata fad'o k'asa. Yanayin yadda yake ji kamar wani al-amari ne ke shirin faruwa dashi, se kuma tunanin shi ya rabu gida uku ,Hajiyar shi ya fara tunowa ,musamman daya San yadda suka rabu bata so ba ,wata zuciyar tace masa kai ba ita ba ,se kuma ya fara tunanin su suxee ,nan ma dai zuciyar shi ta k'aryata shi ,Gidan shi ya tuno ,Sam zuciyar shi ma ta kasa bari ya tuno su ,A haka dai ya kama hangar gidan Hajj Jamil, sosai bugun zuciyar shi ya tsananta ,hankalin shi se ya k'ara tashi ,Allah Allah yake yaje yaga 'ya'yan shi, Dan gaba d'aya ya kasa samun natsuwa..._
_A bakin gate yaci karo da Hajj Jamil ,da alama shima dawowar shi kenan. Da fara'a sosai a fuskokin su ,suka yi musaba. Se a lokacin Daddy ya fara jin sauqin abunda yake ji ,Dan ganin Hajj Jamil da yayi cikin walwala da annashuwa a yanzu ya tabbatar masa daba wata matsala. A tare suka k'arasa cikin gida. Se hiran yaushe rabo suke yi ,se kace wa'yanda suka dad'e basu ga juna ba.
A haraban gidan suka ci karo da Auta ta rugo da gudu ,Nan fa hankalin Daddy ya tashi ,a tunanin shi ko wata matsalar ce. Haseena ce ta fito itama a guje da alama ita auta ke wa guje-guje ,kamo ta tayi ,tana wani tsalle-tsalle tare da fad'in "Ni bana so, ni bakya zaki mun ba Anty Haajar ce",,,, wannan yayi daidai da fitowar Haajar ,aiko Auta na ganin ta ,k'wace hannun ta tayi daga na haseena ,ta ruga a guje tare da fad'a wa jikin Haajar. Da gudu Haajar d'in ta d'auke ta cas, suka shige ciki. Gwalo Auta ta dinga yiwa haseena. K'wacci haseena tayi tana fad'in " Zan kama ki ne yarinya ,se kinyi bayani"...
Wani irin sanyin Dad'i ne ya mamaye zuciyar Daddy Wanda ya assasa k'wacewar wani siririn dariya a bakin shi...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/23, 10:25 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA SHA BAKWAI_
*__________________________*
_Sashen Hajj Jamil suka nufa ,dama Hajj Jamil ya sanar da Haajar dawowan daddy ,Dan haka ta shirya masa abinci da abun sha gwargwadon k'warewar ta. Bayan yaci abinci ya huta ,gaba d'aya suka je masa sannu da zuwa ,sosai yaji dad'in yadda yaga yaran shi cikin walwala, godia yawa Haajar sosai akan k'ok'arin da take yi wajen kula da yaran. Auta na wajen shi yana mata wasa ,tana ganin su Haajar zasu fita da gudu ta biyo musu ,tare da rik'e hannun Haajar_
_Bayan sun fice ne ,daddy ya maida duban shi ga Hajj Jamil. Yake cewa "Gaskiya yarinyar nada natsuwa ,A yadda na fahimce ta kuma tana da ilimin addini dan naga komai nata kamar a k'a'idan ce take yin sa, gata dai daga gani bata wasu shekaru sosai ,amma tasan komai na zamantakewa. Murmushi Hajj jamil yayi tare da cewa " Ai indai haajar ce haka take Abokina ,bata da matsalar rayuwa". "Ta huta" shine abunda daddy ya fad'a a tak'aice kafin ya soma Gaya wa Hajj Jamil duk yadda yayi da Hajiya Gwaggo ,be rage masa komai ba. Sosai Hajj Jamil ya jinjina lamarin. Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci kafin Hajj Jamil ya sauke wani gajeren numfashi tare da cewa_
"Yanzu zuwa yaushe tace maka za'ayi bikin?"
"Kamar yadda tace dai ,ta Riga ta gama magana da iyayen yarinyar nan da wata biyu masu zuwa, amma kuma ai kasan lokaci na hannun Allah ne!" Daddy yaba Hajj Jamil amsa ,fuskar nan tashi d'auke da damuwa, yaci gaba da cewa "Yanzu menene abun yi kenan?"
Hannu biyu Hajj Jamil yasa rik'e da hab'a, alamar yana wani tunani daban. D'agowa yayi yana duban daddy na wasu 'yan mintuna ,kafin yace
"Ni ina ganin a yadda nasan Hajiya Gwaggo ,ba wani hanya da zamu b'ullo mata Dan tsaida wannan auren ,kamar dai yadda ta gaya maka inda tana da rai ba fa shi ,to fa haka zancen yake. Abu d'aya nake tunanin shine mafita ,Wanda kuma idan akayi dace shine jigon rayuwar ka dama na gidan ka gaba d'aya..."
Cike da mamaki daddy yace "menene wannan kuwa Hajj Jamil" Dan shi fa Daddy a nashi bahagon tunanin ,rayuwar shi kamar ta gama nakasa ne ,gani yake ba yada wata mafita daya wuce yaci gaba da hak'uri har Allah yayi ikon shi akan shi.
Cike da kulawa Hajj Jamil ya maida hankalin shi gaba d'aya wajen Daddy. Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci ,kafin Hajj Jamil ya fara magana a nutse
"Ni ina ganin lokaci yayi daya kamata muyi wa toka hanci. A gani na MISBAHU rayuwar Gidan ka na buqatar mace me TAUHIDI,,, ita kad'ai ce zata iya zama dakai da zuciya d'aya ,ta kuma yi yak'i wajen ganin ta dawo maka da martabar kujeran ka na cikakken namiji me inci. Ina ganin lokaci yayi da zaka farka daga dogon suman da kayi ,dan wannan ya wuce a kira shi da nannauyan bacci. MISBAHU ,kwatakwata baka San me ake cewa jin dad'in rayuwar aure ba ,kai ba jin dad'in aure kad'ai ba ,baka ma San me ake cewa soyayya ba ,idan ban manta ba ,daga auren ka na farko har zuwa na ukun nan da ake shirin yi ,ba Wanda kayi Dan ra'ayin kan ka, ko wacce had'a ka akayi da ita. Kubra matar ka ta farko Hajiya Gwaggo ce sanadiyyar auren ,wanda 'ya ce ga Abokin mahaifin ka Allah ya jik'an rai ,ga Khaltum ita kuma wacce zab'in Hajiya ce, ga wannan za ake magana ita duk dai zani ce ta tadda muje. To yaushe zakayi incin kanka ,da har zaka fara bawa zuciyar ka daman ta zab'i abunda take so? Ko kuwa kana nufin haka rayuwar ka zata ci gaba da tafiya a gurgunce?"
Tunda Hajj Jamil ya fara magana ,daddy ya natsu yana sauraren shi ,tabbas yasan duk abunda yake gaya masa gaskiya ne ,Amma shi ta ina ma ya kamata ya fara ,tunda yake a rayuwa be tab'a furta wa wata 'ya mace Kalmar so ba, shi dama baya shiga sabgar mata ,to ta ina kuma ze fara Neman mace har ma me TAUHIDI...
Ajiyan zuciya ya sauke, kafin yace "To yanzu Hajj Jamil ta ina zan fara?"
"Bincika wa zaka yi ,ko kuma kasa a duba maka ,sannan se kaci gaba da Addu'a."
"Shi kenan Allah yasa a dace d'in, zanyi bakin k'ok'ari na" inji daddy
Hajj Jamil yace "gaskiya kam da yafi".
A ranar ma Daddy a gidan hajj Jamil ya kwana. Washe gari da ze koma gidan shi, Hajj Jamil ya buqaci akan yabar su suxee sud'an kwana biyu anan d'in, tunda ga Haajar nan tana tare dasu ,har zuwa lokacin da ze k'ara auren sa na uku ,ita kuma aga kamun ludayin ta. Daddy be musa masa ba ,Dan be tab'a jin akwai wata alfarma da Hajj Jamil ze nema a wajen sa ya kasa yi masa ba.
Koda su suxee suka samu labarin zasu zauna a gidan Hajj Jamil nad'an wani lokaci ,sosai suka yi murna ,Dan haseena har cewa tayi " Allah yasa ma Daddy yabar mu anan gaba d'aya "...
GIDAN DADDY...tun bayan tafiyar daddy da yaran shi ,su kubra suka bar k'asar zuwa GERMANY...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[7/24, 8:55 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA GOMA SHA TAKWAS_
*_________________________*
_Bayan Daddy ya dawo gida ,bedroom d'in shi ,ya wuce Dan ya aje kayan shi ya watsa ruwa ,be ko lura da drawern kud'in shi dake bud'e ba. Se bayan ya fito wanka ne ,ya nufi Wardrobe Dan d'aukan k'ananan kaya ya sanya wa jikin shi ,sakamakon wani zafi da ake a wunin ranar. Guiwar k'afar shine yaci karo da marfin drawern dake bud'e ta k'asa. D'an guntun tsaki yayi ,tare da rusunawa ze rufe marfin ,amma a mamakin shi wayam drawern bako sisi ,zaro ido ya shiga yi ,gaba d'aya gurfanewa yayi akan guiwowin shi guda biyu ya shiga bin cike drowowin d'akin amma taro ba sisi. Nan take wani zufa ya fara tartso masa ,kud'i ne ba k'ananan kud'i ba ya ajiye ,Wanda shi kanshi baze ce ga adadin su ba. Tunani ya fara yi ,waye ze masa wannan mummunan abun ,to ko dai bayan tafiya na b'arayi sun shigo ne? Daddy ya tambayi kan shi. Dak'yar ya iya mik'e wa ,ya saka k'ananan kayan daya daya Ciro ,fito wa yayi ya nufi wajen me gadi ,jikin shi a mace yake tafiyan, har wani dishi-dishi yake gani ,a haka har ya iso wajen me gadi. Babangida me gadi na ganin shi ,da sauri ya k'araso_
"Barka da fitowa Alhaji!"
kasa bud'e baki daddy yayi ya amsa ,dak'yar ya iya k'arfin halin cewa "Babangida bayan nayi tafiya dawa dawa yazo gidan nan?"
Babangida yace "Eh to gaskiya Alhaji ,kasan yadda gidan namu yake koda yaushe cikin bak'i su Hajiya suke maza da mata. Bayan tafiyar Ku ma dai hakan ne ,sedai awa she gari suma Hajiya uwargida d Hajiya amarya suka yi tafiya ,sun gaya mun cewa ,duk Wanda yazo Neman su ince sun tafi wace k'asa ma??? Am yauwa GERMANY!!!"
"Akwai wa'yanda suka shiga sashen na ne?" Daddy ya sake tambayar shi
Babangida yace "A'ah to gaskiya Alhaji bazan San wannan ba, sedai ko su Hajiya ,Dan su kad'ai nake ganin suke wurgawa ta wajejen".
Wani irin jiri ne ya iba daddy ,saura kad'an yakai k'asa ,badan Babangida yayi saurin taro shi ba. A kid'ime babangida ke fad'in " ba kada lafiya ne Alhaji?? Ko dai akai ka Asibiti ne???" Shidai daddy shi kad'ai yasan me yake ji ,kai ya gyad'a wa babangida alamar a'ah ,sannan ya masa nuni akan ya taimaka masa ya koma ciki. Da taimakon babangida daddy ya k'arasa ciki, suna shiga parlou daddy yace "Banni anan in kwanta ,zaka iya tafiya". Daddy ya fad'a murya can k'asa. Fatar samun sauqi babangida ya yiwa daddy sannan yaja masa k'ofa ya koma bakin aikin shi cike da tausayin me gidan nashi. Bayan fitar babangida ,tashi daddy yayi yana daddafa bango saboda wani irin jiri dake shirin buga shi da k'asa ,wayar shi ya lalubo ya turawa Hajj Jamil text, seda ya tabbatar yaje sannan ya kashe wayar ya ajiye. Kan kace me zazzab'i me zafin gaske ya rufe daddy ,jikin shi har karkarwa yake yi ,idanuwan shi na wani kakkafewa kamar me shirin barin duniya.
_Ina gida ba nida lafiya ,I need ur help_ Hajj Jamil ya furta " Subhanallahi ! Bayan ya gama karanta text d'in daddy. Cikin ran shi yake raya, me kuma ya faru bayan ya koma gida, bayan ni nan mun rabu lafiya qlau dashi?" Ganin baze samu amsa a wajen