Showing 48001 words to 51000 words out of 86229 words
Chapter 17 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
duniya ya sa ta manta da komai da kuma kowa na ta ,ba ta sauraren kowa ,ba kuma ta da lokacin komai sai sha'anin gaban ta sharholiya. Sai a yanzu take da nasanin duk wasu abubuwan da suka faru a baya... Daga k'arshe ta yanke shawarar ta je asibiti wajen k'wararren likita ,ko zata cire shakkun dake zuciyar ta. Domin ta fi kowa sanin wacece kubra da kuma shu'umancin ta ,ta San kubra tantiriyar gaske ce matakin farko babu abunda baza ta iya aikata wa ba Dan ta cimma burin ta... Da wannan shawarar Khaltum ta yanke cewa za ta je asibiti ,duk da ba wai ta yadda da kalaman Kubra bane ,ta San da ran ta da lafiyar ta ba yadda za'a yi ace an cire mata mahaifa ba tare da sanin ta ba...
Washe gari da safe Khaltum ta shirya ta je asibiti. Kusan asibiti uku tana zuwa amma sakamakon iri d'aya ne shine ba zata tab'a haihuwa ba ,saboda babu mahaifar da d'a ze iya kwanciya a cikin ta balle har ta haife sa. Daga baya ma suka gano cewa ta tab'a samun ciki ta cire ,wannan Abu yayi matuqar d'aure wa Khaltum kai. Duk da irin jawaban da ta samu daga wurin likitoci daban-daban ,hakan be sa ta gama gamsuwa ba ,haka tayi ta yawo duk wani asibitin da ta ji ance sun k'ware wurin duba mata se Khaltum ta je ,amma maganar d'aya ce bata canza ba. Wannan al-amari ba k'aramin tayarwa Khaltum yayi da hankali ba...
Ta ci kuka kamar ba gobe ,idanuwan ta kamar za su fad'o k'asa Dan tsabar kukan da ta darza. Tana dawo gida sashen ta ta wuce ,ta fara watsi da duk wani abun da ya zo gaban ta. Tana kuka tana fad'in "Me nayi miki haka Kubra??? Wani irin laifi na miki da zaki mun wannan sakayyar??? Kubra kin cuce ni ,kin cuce ni,,, bazan tab'a ya fe miki ba,,, ko da zan tafi da zani d'aya se naga bayan ki ,,,,sai na d'au fansa akan ki,,, idan kuwa Kika ga ban zama ajalin ki ba ,to lallai ni ba 'yar halak bace..." Haka Khaltum ta yi ta sambatu iri-iri. Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta fita a hayyacin ta ,idan ka ganta jiya ka ganta a yanzu ba zaka tab'a cewa Khaltum d'in daka sani bane.
Wayar ta ta d'auko ta kira mahaifiyar ta ko zata ji dad'i a ranta. Sai da kiran ya kusa yanke wa sannan Hajiya khairi ta d'auka. Wani matsananci Kuka Khaltum ta fashe da shi tana fad'in "Hajiya kubra ta cuce ni,,, kubra ta min kisan zaune,,, ta gama da rayuwa ta"...
Hajiya khairi tace " wai me kubran ta yi miki?"
Khaltum na kuka ta zayyanawa Mahaifiyar ta duk abunda ya faru....
A mamakin Khaltum sai jin tayi Hajiya khairi ta fashe da dariya tare da cewa "ba kiga komai ba khaltum. Wallahi so nayi ace kubran ta kashe ki gaba d'aya kowa ma ya huta. Mutuniyar banza kawai""" Hajiya khairi na gama fad'ar haka taja wani dogon tsaki tare da yanke kiran...
Wani irin ihu khaltum tayi ,Cike da tashin hankali ta yi jifa da wayar hannun ta ,se da wayar ta fashe ,a lokaci d'aya ta sake fashe wa da wani marayan kuka. Haka ta kwana a zaune tana aikin Abu d'aya.
Can cikin dare ta fara jiyo hayaniya sama-sama. Kamar dai ba zata fito ba ,Dan abunda ya ishe ta ya ishe ta ,sai kuma ta ji hayaniyar yayi yawa Dan haka ta leqo ta ga meke faruwa...
Wuta ne ke tashi daga sashen daddy. Dukkan ma'aikatan gidan sun taru a wajen suna ta aikin kashe wutar ,amma wutar kamar dad'a hura ta suke yi. Lubabatu se ihu take tana kururuwa ,wannan ne ya k'ara janyo hankalin mutane da dama zuwa wurin. Daddy baya nan d'aya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya kira shi a waya ya sanar mishi da abunda ke faruwa, cikin mintunan da basu Gaza biyar zuwa goma ba sai gashi. Kubra ma bata nan ,sai su Haajar ne da basu San wainar da ake toya wa ba.
K'arar motar ruwa ta kashe wuta ne ya sa suka leko su ga abunda ke faruwa. Cikin tsananin tashin hankali suka k'arasa wajen. Mutane sai rirrik'e daddy suke yi dake ihun
"Dukiya ta!!! Jama'a Ku taimake ni!!! Duk Wani abunda na mallaka yana ciki!!! Ku taimake ni!!!""
Haka aka yi ta rik'e shi ,a cikin masu rik'o shi hadda Haajar dake ta aikin kuka.
Duk rashin imanin ka idan ka ga daddy a wannan ranar Dole ka tausaya masa. A haka yana ji yana gani komai da komai ya k'one k'urmumus ,sai wuraren asuba aka yi nasarar kashe wutar ,lokacin komai da komai na sashen daddy ya koma gawayi....
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/13, 8:58 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN...ALLAH YA YI WA MAHAIFIYAR AUFANA RASUWA. D'AYA DAGA CIKIN MARUBUTAN QUNGIYAR MU TA INTELLIGENT. HAQIQA RASHIN MAHAIFIYA BABBAN RASHI NE DA YA FI KO WANI RASHI D'ACI A WANNAN DUNIYA. ALLAH YA JIQANTA DA RAHAMA YA KUMA KYAUTATA MAKWANCIN TA. AMEEN.πππ*
_BABI NA TALATIN DA TAKWAS_
*____________________________*
_Haqiqa wannan al-amari na gobara ba k'aramin rikita daddy da duk wani masoyin shi ya yi ba fiye da yadda mai karatu ke tunani. Wannan na nufin duk wani wahala da daddy ya sha sama shekaru aru-aru ya tafi a banza. Dukiyar daya dad'e ya na tarawa yau rana d'aya ta qone qurmumus. Ka ma daga takaddun manyan gidajen shi ,takaddun manyan filayen shi ,takaddun kamfanonin shi ,kai hadda na kwantiragin shi komai ya qone. Lallai dole daddy ya shiga rud'ani da tashin hankali Mara misaltuwa. Domin kuwa kariyar azziki babban masifa ne ,Wanda ya zo mana a hadisi ingantacce cewa Annabi s.a.w yace "A TAUSAYA WA DUK WANDA KARIYAR AZZIKI YA SA MA"..._
Tun a washe garin ranar da abun ya faru Hajj Jamil ya samu labari. Dan haka be yi qasa a guiwa ba wajen zuwa yi wa daddy Jaje. Nan da nan gari ya d'auka, kasancewar daddy babban mutum ne. Nan fa k'ananan maganganu suka dinga tashi ,wasu suce " ije aka yi wa daddy saboda d'aukaka shi da Allah ya yi...wasu kuma suce da sa hannun abokan kasuwancin shi...kai wasu ma cewa suke da sa hannun uwar gidan shi wato Kubra... Haka dai maganganu suka yi ta yawo lungu da sako ,sakkwato da kewaye...
Har tsawon sati biyu da faruwar abun mutane kai kawo suke a gidan daddy wajen yi masa jaje. Yayin da matakan tsaro suka ba da k'aimi wajen tuhumar duk wani Wanda aka San abokin hammayar daddy ne. Daga k'arshe daddy yace ya fawwala wa Allah komai na shi, saboda haka a dakatar da binciken da ake yi Dan kar a d'au haqqin mutane da da ma.
Wata d'aya da faruwar wannan iftila'i wani masifar ya sake tunkaro wa. Dan kuwa Khaltum na nan akan bakan ta na ganin ta d'au fansa kan abunda kubra ta yi mata...
Wata rana Haajar, Suxee da Auta sun fita tare da daddy ,an je kai Haajar asibiti kasancewar ba ta jin dad'i. Haseena kuma tana gida tana bacci ko da suka tafi ganin hakan ma yasa basu tashe taba suka tafiyar su Dan ba dad'e wa zasu yi ba...Bayani Haajar tayi wa likitan akan duk abunda take ji. Ya basu gwaji na fitsari dana jini ,bayan an yi ,aka ce su dawo gobe Dan karb'an sakamakon. Da haka suka juyo suka dawo gida.
A garden daddy ya tsaya tare da auta. Haajar tace bari ta k'arasa ciki ta kwanta Dan wani jiri da take ji. Tare da suxee suka k'arasa...
Duk wani motsi na su akan idon Khaltum su ke yin shi. Sai da ta tabbatar ta ga shigar su sannan tabi bayan su. A tunanin ta ko Suxee da Haseena ne ,Dan bata ma San da Haajar a gidan ba.
Khaltum ce ta fito ta nufi sashen kubra. Sai da ta tabbatar ta kulle duk wani k'ofa da window na ciki da na waje, sannan ta haura sama ,inda ta tabbatar za ta samu kubra...
A kwance ta samu kubra ta jingina da kujera ,idanuwan ta a lumshe ,k'arar sauti na tashi a hankali. A gefe kuma ga lemu me sanyi a kofin glass da alama ta gama sha ne ta ajiye...
Jin kamar alamun tsayuwar mutum akan ta yasa ta bud'e idanuwan ta. A hankali ta sauke su akan Khaltum dake tsaye tana qare mata kallo tsaf. Tashi zaune kubra tayi ta zauna daidai kafin tace "Sannu da zuwa! Se kuma kika tsaya a tsaye sai kace wata baquwa? Ki zauna mana" ta fad'a tana nuna mata wurin zama
Khaltum da idanuwan ta ya cika da hawaye tace "Kubra ba zama ya kawo ni ba. Ina so ki gaya mun ta yadda kika saka aka cire mun mahaifa ,da kuma lokacin da aka yi bansani ba ,Dan nasan ba ke ce za ki yi da kan ki ba ,saka wa za ki yi ayi."
Wani irin guntun murmushi kubra ta yi tare da cewa "Na fuskanci kin d'au zafi da yawa. Amma ga wannan kisha ko zaki ji sanyi a ran ki." Ta k'arasa maganan tare da mik'a mata ragowar lemun dake Kofi a kusa da ita.
Kau da kai Khaltum ta yi gefe tare da cewa "Ba na buqata. Ki amsa min tambaya ta kawai".
Baki kubra ta tab'e tare da cewa " Gaggawar me kike yi? Da kin kwantar da hankalin ki ma har d'akin ki zan zo in gaya miki yadda komai ya wakana. Khaltum ban so tsiya ya had'a mu. Ke kika ja wa kan ki. Dan naji lokacin da kike waya da wata qawar ki a qasar Germany cewa idan har kika samu da ma zaki kawar da ni. Ni ko se naga duk zaman amanar da nake dake Ashe ke ba da zuciya d'aya kike zauna dani ba. Daga wannan lokacin na shirya komai da wata qawata da ke aiki a babban asibitin Germany ,na baki wata k'waya me k'arfi kika sha Dan in d'auke miki hankali ,na kuma Nasara k'wayar ta yi miki cikin sauqi ,na d'auke ki cikin mota na kai ki asibitin na kuma fad'a musu yadda nake so ayi ,cikin minti talatin akayi komai aka gama. Satin mu d'aya a asibitin ba tare da kin sani ba sakamakon allurori da ake miki masu qarfin gaske. Kinji yadda na tsara komai. Ni Kubra kuma kowa yaci tuwo dani miya sha ,bana yafe wa duk Wanda na yadda dashi yake k'ok'arin cin Amanata. Idan akwai Wanda na kama ta in d'aga wa k'afa be wuce Hajja Fati ba ,nasan kinsan yadda take a wuri na ,amma taci Amanata yanzu haka na turo wa Mijin ta videon iskancin da tayi da babban aminin shi ,da duk wani shiri da suke yi na ganin sun raba shi da kujerar daya ke kai na sarauta. Na tabbata komai ya dagule mata kawo yanzu. Idan wannan ne ya kawo ki zaki iya tafiya..." Kubra ta fad'a tare da d'aukar kofin lemun nan ta kai bakin ta...
Da sauri ta janye kofin lemun daga bakin ta ,tare da shaqar iska Dan ta tabbatar da k'amshin da take ji.
"Wannan kamar warin gass nake ji?"" Kubra ta fad'a tare da waiga wa..
Khaltum dake shawaye tace "ba wai bane. Warin gas ki ke ji. Idan kinsan me za ki aikata to baki San me za'a aikata miki ba Kubra. Fad'an wasa shi ake yi wa matsaya ,amma fad'ar gaske kuwa kwana ake yi ana yi. Ni Khaltum jinjirar d'an tsako ce me kwarjini a idon d'an angulla. Gonar sama mai wuyar kai taki... Tabbas kin samu Nasara a karo na farko ,amma ina me baki albishir da cewa kin yi na farko kuma kin yi d'an Autan k'arshe. Ni ni kad'ai kika yi wa amma daga ke har 'ya'yan ki da kike magana akan su wannan ita ce ranar Ku ta k'arshe a duniya...
Kubra furzar da lemun dake bakin ta tayi tare da cewa " Me kike shirin aikata mana haka?"
"Kashe Ku Zan yi. Wannan warin gas d'in da kike ji ,tukunyar gas d'in ki ce na bud'e ,nasan zuwa yanzu ya karad'e ko ina dako ina. Na fi son ayi mutuwar kasko wallahi d'a kwance uwa kwance. Kamar yadda na d'au alwashi ,nima nafi son in rasa rai na matuqar buri na ze ciki..."
Cike da tsaro kubra ta mik'e tsaye tana zaro ido tare da cewa "kin kuwa San me kike yi Khaltum? Rai fa zaki kashe? Menene amfanin hakan? Wallahi Allah baze bar ki ba. Wallahi wuta zaki je"
"Dalla malama dakata!!" Khaltum ta katse ta, sannan taci gaba da cewa "ke har kinsan Allah. Nasan ke abunda kika aikata mun aljannah zaki ce tunda a gidan uban ki ake raba ta. Muguwa kawai me zuciyar 'yan wuta. Nafi son tun a duniya wutar Allah ta fara kama ki kafin kije ki taradda babban azabar ki."
Jin haka yasa kubra rugawa ta gudu ta nufe hanyar fita ,tare da ihun a taimake ta. Se dai bata yi sa'a ba ,dan duk k'ofar data je a kulle gam take jin ta. Ganin haka yasa ta saduda ,ta dawo ta zube k'asa kan guiwar ta kusa da Khaltum tana rok'on ta akan tayi hakuri tayi mata rai ,wallahi ba zata sake ba.
Khaltum na kuka tace "Lokacin Neman afuwa ya k'are miki kubra. Yanzu lokacin girbar abunda kika shuka ne. " tana gama fad'in haka ta kunna ashanar dake hannun ta ,kubra na ihu tana Neman taimako haka Khaltum ta cilla wutar ashanan nan.
Nan take wuta ta fara ci ,ko ina da ko ina ya ka ma a lokaci d'aya. Wuta ne yake ce a sashen kubra sosai. Nan danan hankalin mutanen ciki Dana wajen gida ya dawo nan.
Dummmm! Kake ji kamar ta ya ta fashe. Wannan k'arar ne yasa daddy dake garden ya ankaro. Da sauri ya taso Dan ganin me ke faruwa. Kafin ya k'araso sai mutane ya gani suna shigowa ,ga gate an bud'e motar kashe wuta na shigo wa. Ai da gudu shima ya isa.
A hankali hayaqi ya fara zagaye d'akin qasa da su haajar ke kwance ,tari suka fara ita da haseena ,Suxee dake band'aki da sauri ta fito Dan ganin meke faruwa. Aifa nan taga hayaqi ,ko gaban ta bata gani sosai ,tari ta fara yi sosai. Tana k'ok'arin kiran sunan Haajar Dana suxee...
Da lalube har ta isa bakin gadon, ta lalubo hannun Haajar ,ba tare da tana ganin gaban ta ba saboda hayaqin daya yi yawa a d'akin. K'ok'arin kiran junan su suke yi ,yayin da mutanen waje ke k'ok'arin fasa k'ofar Dan shiga ceton su.
Daddy se fad'in yake " 'ya'yana na ciki Ku taimake ni,,,Ku taimake ni 'ya'ya na. Wannan Wani irin musiba ba ne??? A karo na farko dukiya ta yanzu kuma 'ya'yana... Na shiga uku ni MISBAHU na ga ta kaina...
Ihun Sunan Haajar ya fara yi kafin ya shiga kiran sunayen su suxee...
A wannan karon daddy kusan zautuwa yayi. Dan yana ji yana gani wuta na ci ga 'ya'yan shi a ciki. K'arshe fad'a wa yayi da shi aka yi ta k'ok'arin k'ofar baya. Amma ba alamun k'ofar zata bud'e...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/15, 7:27 AM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA TALATIN DA TARA_
*_________________________________*
_Da k'yar masu k'ok'arin ceton rayuwar iyalin daddy suka yi nasarar fasa k'ofar baya, a lokacin har wutar ta fara ruzga gini. Sama suka nufa 'kofar da suke iya jiyo ihun Kubra. Sun yi iya bakin k'ok'arin su wajen bud'e k'ofar amma ina hakan bai yiwu ba. Dan khaltum ta datse ko ina da ko ina ,bayan makulli sai da ta saka hadda mab'allin kwad'o ,hakan yayi tasiri da kuma wutar dake ci a wannan lokacin. Ganin da suka yi wutar sai dad'a ruruwa take yi ga shi basu iya Ciro ko da mutum d'aya ba ,yasa suka bar wannan k'ofar Dan dole, suka koma ta k'ofar da su Haajar ke ciki._
Sai da suka yi da gaske kafin suka yi nasarar b'alle k'ofar. Da taimakon Allah suka iya Ciro mutum biyu daga ciki da ba iya tantance ko su waye ba ,sakamakon rud'ani da kuma yanayin tashin hankalin da ake ciki...
Ana fito wa dasu daidai lokacin da motar asibiti ta k'arasa. Kai tsaye asibiti aka wuce dasu Dan ba su agajin gaggawa. Sannan suka koma a karo na biyu dan sake ceto sauran mutanen da ke ciki. Sai dai ina ,,,a wannan karon ba hanyar shiga, Dan kuwa wutar ta kama ko ina da ko ina. Wani daga cikin su me suna Auwal ne ya ke k'ok'arin ganin ko ta halin yaya ya kutsa dan ceton rai. A daidai lokacin da ya kai jiki ze shiga ciki ,wata Katanga dake famar ci da wuta ta ruguzo masa sai akan k'afa, da sauri sauran mutanen dake wajen suka k'araso suka d'auke shi. Yayin da masu kashe wuta wato (fire service) ke iya k'ok'arin su na ganin sun kashe wutar...
Su na ji su na gani haka wuta taci gaba da ci. Jim kad'an suka jiyo wani k'ara tussss