Showing 27001 words to 30000 words out of 86229 words

Chapter 10 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt

27 Dec 2024

3930

masa yayi ba. Sun kusa minti talatin a toilet d'in kafin suka fito ,Jikin Daddy har wani karkarwan sanyi yake yi ,gado ya koma ya kwanta ,Hajj Jamil yaja masa abun rufa ,tare da rage k'arfin Sanyin A/C, saboda yadda yaga jikin shi na wani cira. Kusan dai daddy ranar a kwance ya wuni da zazzab'i, Dr.Zaidu kuma na iya bakin k'ok'arin shi ,dukda be San wainar da ake toyawa ba.


Ranar Haajar bata wani jima ba sosai a asibitin ta koma gida. Kwana ukku ,duk tayiwa Daddy abinci da MA'UL WARDI se yayi irin wannan aman daya yi kwana biyu da suka wuce ,se dai ba kamar ranar daya fara yi ba. A hankali sauk'i na samuwa. Satin shi d'aya Haajar na iya bakin k'ok'arin ta ,Alhamdulillahi daddy ya samu sauqi tangaram, shi da kanshi ya lura da akwai abunda Haajar ke sako masa a abinci da idan yaci yake saka shi wannan aman ,amma shi kan shi yasan ba aman lafiya bane yake yi ,ga kuma wasu sababbin canji daya ke ji a jikin shi, har wani raman wahala yayi ,yayi bak'i...


Bayan sati d'aya Daddy ya samu kanshi ,aka sallame shi daga asibiti, Tare da Haajar gaba d'aya suka wuce gidan Hajj Jamil. Bayan sun zauna Hajj Jamil ke cewa


"Nifa inaganin idan zaka koma gida tare dasu Auta zaka tafi saboda suna kewar ka sosai ,se dai wannan karon tare da Haajar zaku tafi ,taje tad'an kwana biyu tunda dama anan d'in ba kowa Zaliha bata dawo ba har yanzu ,daga ita ne se 'yan aiki ,itama idan taje can d'in zata fi sake wa ,kuma kaga zata kula dasu Auta"..


Daddy ya dad'e yana jinjina lamarin ,har k'asan zuciyar shi yaji dad'i ,amma be San yadda Haajar zata d'auki lamarin ba. Ganin yayi shiru yasa Hajj Jamil cewa


" ko hakan be maka bane?"


Ajiyan zuciya Daddy ya sauke ,kafin yace "ba wai be mun bane. Ni inaga ita Haajar d'in zata amince kuwa? Karfa mu cika zak'e mata da yawa ,d'an Abun azzikin ma da take yi mana tazo ta dena". Daddy ya fad'a iya gaskiyar sh.


Dariya maganan yaba Hajj Jamil yace " Haajar fa 'ya tace ,kuma kaima 'yar ka ce"


Wani kallo daddy ya masa alamar ta ina?


Hajj Jamil daya gane cewa yana son k'arin bayani yasa yace "Kaddai kace mun baka San Haajar ba? Ko da yake ba lallai kasanta ba ,Dan ba'anan take zaune ba ,tana can tare da Asadussunnah a Sudan ,da wani aiki yakai shi can shine ya tafi da ita ,acan tayi karatun ta, kwatakwata bata shekara biyu da dawowa Nigeria ba"


Zaro ido daddy ya shiga yi tare da cewa "kaddai kace mun 'yar Asadussunnah ce Haajar? Lallai kuma idan hakane nayi b'atan kai, mutum da 'yar shi sukutum"


Hajj Jamil yace "Aikuwa dai"


Mahaifin Haajar Dr. Imam Ali Asadussunnah ,shahararren malamin addini ne daya shahara ba a iya jahar shi ta jigawa kad'ai ba ,Nigeria da kewaye babu inda sunan shi da alkhairan sa na fad'akarwa be zaga ba, a b'angare d'aya kuma k'wararre ne kuma likita ne wajen had'a magungunan Islamic... Wannan kad'an kenan...











*__________________________*




Garin kano... Hajiya Gwaggo ta dage se shirye-shiryen bikin suke yi ita da dangin amarya ,Amarya lubabatu kuwa ta gama shirin ta tsab na amarcewa a gidan daddy, koda yaushe tana sashen Hajiya Gwaggo ,daga su kitsa wannan se su kwance wancan. Ko da bansan me suke kitsewa ba ,amma daga gani kai kasan ba alkhairi bane...






















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/28, 9:41 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ASHIRIN DA HUD'U_


*___________________________*
























_A Ranar da suka dawo gidan ,a ranar Suxee da Haseena suka zazzaga da Haajar ko ina na gidan ,tare da nunnuna mata wasu abubuwan ,a sashen kubra sukayi branch har ita ,saboda su suxee ,bata son duk wani Abu daze sa tayi nisa dasu._


_Duk da basu da masaniyar ko tasan komai game da gidan su ,amma shak'uwar su da ita yasa suka kasa b'oye mata komai, duk wani Abu na rayuwar gidan a wuni d'aya ta San shi ,hakan kuma ba k'aramin taimaka mata ze yi ba ta fannin zamantakewar ta a gida. Auta kuma kamar an tsoma ya a aljannah ,Dan kuwa murna take sosai da suka taho tare da Haajar gidan su._


_A ranar base gobe ba ,Haajar tasa aka fitar da duk wani na'urar jin sauti a gidan ba tare da wani shakku ko tsoron me ze je ya dawo ba. Haka ma duk wani hoton bango ,se dai na iya sashen Daddy kawai tasa aka kwashe aka k'ona su. Ita dasu Suxee suka shiga sashen ,suka gyara masa shi ,gyara Wanda tun da yake be tab'a samun irin sa ba ,Dan seda ta sauya wa komai mazauni ,idan ba ka lura dakyau ba ,kana shiga sashen zaka zata ko wasu kayayyakin aka sauya, Hatta kayan daddy na cikin Sip seda ta fito dasu duka ,wani abun mamaki data bi kayan d'aya bayan seta ga akwai killatattun kayan da akawa alama da farin zari ta wuya ,mamakin duniya ne ya hana ta magana ,kwatakwata jikin ta be bata daidai ba ,Dan haka tabi kayan d'aya bayan d'aya, duk Wanda ta gani da wannan alamar seda ta tsame shi, sannan ta maida masa sauran ta Jere su tsaf ,komai ta nema masa mazaunin sa na musamman, hatta filon kwanciya da Khaltum ta kawo guda d'aya na mugun abun ta seda Haajar ta sauya wani,,,, seda ta fara turara 'ya'yan Habbatussauda ,sannan ta bishi da turaren wuta me masifar k'amshi, kan kace me wuri ya zagaye da wani daddad'an k'amshi, Wanda kafin ka iya gano ainahin wani irin turare ne ,sedai idan dama ka sama tu'ammali da kayan k'amshi ne kad'ai. Ko ina k'amshi ke tashi ,tun daga dosowa farkon shiva sashen ,parlou ne ,duka d'akuna ukun dake zagaye da parloun da ban d'akin su ,hatta kayan Daddy idan ka bud'e sip din k'amshin turaren kaga na maza ne zaka ji yana bugar k'ofofin hancin ka. Seda ta tabbata an gyara komai ,sannan ta ciro m-card d'in wayar ta ,tayi placing a manyan na'aurar sautin dake parloun, cikin sakan talatin tayi setting d'in komai ,se ga k'ira'ar AHAMD SULEIMAN na tashi a karo na farko a sashen Daddy._


_Gaba d'aya yaran jin su suke kamar a wata sabuwar duniyar daban sab'anin Wanda suke ciki a yanzu. Da daddare tare suka shiga kitchen ,girke-girke sukayi sosai ,sedai babu na Daddy a ciki ,daban Haajar tayi masa nasa saboda rashin lafiyar hawan jinin shi._


_A karo na farko da masu aikin gidan suka ci abincin gidan ,Dan gaba d'aya Haajar seda ta aika musu da abincin data girka had'i da abun sha me sanyi. Ranar kowa ya tabbatar da Haajar tazo GIDAN MISBAHU, Dan alama na sauyin nayi daya kai wa ahalin gidan ziyara._


_Da daddare bayan daddy ya dawo yaga abubuwan ban mamaki ,gaba d'aya gidan se yake gani kamar ba gidan daya Sani ba ,Dan tun daga gate masu gadi suka fara cewa Daddy sun ga abun alkhairi ,a taya su yiwa Hajiya Godia, duk da be San wata Hajiya suke nufi ba da kuma alkhairin da suke magana tayi musu ,tunani ya fara yi ,ko su kubra sun dawo ne? Wata zuciyar tace masa "Alkhairi daga wajen su kubra anya Abu ne me matuqar wahalar gaske"... Da wannan tunani-tunanin daddy ya k'arasa ciki...






Shi dai daddy da ido ya dinga bin su ,be kashe k'wark'watan idon shiba ,se da ya doshi sashen shi ,wani irin masihircin k'amshi me sanya nutsuwa ya daki madaidaitan k'ofar hancin shi ,bin ko ina yake da kallo kamar yau ne rana ta farko daya fara shigowa sashen nashi. Zama yayi kan kujera mazaunin mutum d'aya, tare da jinginar da kanshi had'ida lumshe matsakaitan idanuwan shi ,a lokaci d'aya kuma yana k'ara shak'ar daddad'an k'amshin dake ambiya a parloun, ya jima a haka ,kafin ya shiga d'aki Dan rage kayan jikin shi ,nan ma kusan idanuwan shi zazzago ne basu yi ,Dan ganin abun mamaki. Daya shiga toilet Dan watsa ruwa kusan mintunan shi sama da talatin ya kasa fitowa ,ji yake kamar ya kwana a ciki, Hamdala ya sake yiwa ubangiji daya kawo masa sauyi a rayuwar shi cikin d'an k'ank'anin lokaci, ji yake ina ma ace Haajar matar shice ,gaskiya da se yafi kowa sa'ar mata, amma ta ina ma hakan ze yiwu? Wata zuciyar kuma tace masa ,ka fiye zak'ewa MISBAHU, daga ganin sarkin fawa se miya tayi zak'i?,,,,da sauri ya kauda wannan tunanin ,seda yayi sallah kafin ya fito parlour.


A zazzaune ya tarar dasu Haajar kan kujeran dinning da alama shi suke jira suci abinci,,,, dikkan su sannu da zuwa suka masa fuskokin su d'auke da farin ciki ,shima ya amsa fuske a sake ,bayan ya zauna ya ke tuna rabon da yaga yaran shi cikin irin wannan farin cikin har ya manta. Amma se gashi rana d'aya, kusan har k'ok'arin manta wa da duk wani damuwar su suke yi ,ina ma ace farin ciki da walwala ze d'ore mana kamar haka,,, Daddy ya furta cikin ran shi... Dramar da ake yi wajen cin abincin ne ya dawo masa da hankalin sa.


Cike da shagwab'a da samun wuri Auta tace "Ni fa Anty Haajar ni zaki fara zuba mawa"


Wani siririn tsaki Haseena taja ,tare da cewa "kinga Anty Haajar Dan Allah ni ki fara zuba mun ,wallahi baki ji wani irin azababben yunwa da nake ji ba yau ,wannan irin aikin da muka tik'a da biyana za'ayi ai nasan kud'in da za'a bani yaci ya siya mun gida da mota har da 'yan chicken change"...


Gaba d'aya wajen kowa dariya yake yi har Daddy, Haajar tace " Ayyo! To dama an gaya miki komai a banza ake samun shi? Ai komai na rayuwa da kike ganin shi dole seka wahala tukunna kake samun abunda kake so Haseena ,wannan kad'ai ma ya ishe ki darasi"


"Aikam dai" Haseena ta fad'a tana jinjina kai.


Auta aka fara zuba wa ,tana fad'in "yeeh Yaya haseena ni aka fara zuba mawa" ta k'arasa maganan tana mata gwalo. Kowa se dariya yake mata ,banda Haseena data cika tayi fam Dan kwatakwata ita ba tada hak'uri ne.


Seda ta gama serving d'in kowa sannan ,taji da Daddy da ke cewa "Ai na d'auka 'ya'yan ki kad'ai kika sani ,saura kad'an Gidan Abinci yayi bak'o." Dariya dikkan su suka saka, seda daddy ya saki zancen sannan yama fara wai me nace ma? cewa fa nayi 'ya'yan ta ,kar yarinyar nan ta gano wani Abu a tattare dani fa, gaskiya ba k'aramar kwab'a nayi ba. Seda ya kalli kowa yaga hankalin sa baya kan shi ,kamar ma basu ji meya fad'a sosai ba da farko. Wani ajiyan zuciya ya sauke ,tare da furta Alhmdllh' a k'asan zuciyar shi, Dan shi Daddy Gaba d'aya ganin Haajar yake kamar matar shi ,musamman yadda suka zauna haka ,se yake ayyana inama ita kad'ai ce matar shi kuma uwar yaran shi ,lallai da yafi ko wani namiji alfahari da samun nagartacciyar iyali... Murmushi kawai yayi sannan yayi bismillah tare da kai abinci bakin shi.


Duk wani motsin da yake be San a idon Haajar yake yin sa ba ,kawai dai ta share ne tayi kamar hankalin ta bata wajen shi.


Cikin k'ank'anin lokaci daddy ya kauda abincin dake plate d'in shi ,dama ba wani da yawa ta zuba masa ba, ganin yana k'ok'arin bud'e kula ya k'ara ,Haajar tayi saurin taron hanzarin shi da cewa

"Bari in k'ara maka ,murmushin jin dad'i yayi ,tare da cewa


" Nagode? "


Wani kulan daban Haajar ta bud'e ta zuba masa abincin dake ciki. Nan danan Daddy ya fara auna shi ciki,,,, sedai dak'yar ya k'arasa had'iye abincin bakin shi ,wani irin kallon menene wannan? Yake bin Haajar d'in dashi. Gira ta d'aga mai alamar akwai matsala ne?


Daddy yace "Anya wannan abinci na ne kuwa?"


"Me ka gani?" Haajar ta tambaya kamar bata San komai ba


Yace "Naji abincin ne ba kamar irin Wanda na gama ci ba, kamar ma fa ba'asa gishiri ba ,ko me agwagi ne ake kiran sama na kasa ganewa!"


Dariya dikkan su suka fashe dashi, haseena tace "Daddy me zabo ake cewa ,ba me agwagi ba".


" komai dai menene Ku kuka San shi ,nida ba shiga kitchen nake ba ,taya zan wani San sunayen maggi?"


Haajar ajiye cokalin hannun ta tayi ,tare da nad'e hannaye a k'irji tace "Wannan abincin daga yau irin shi zaka dinga ci ,saboda tsaro"


Daddy wani zaro iro ya shiga yi tare da cewa " ni d'in kuma? Wai saboda me?"


Haajar tace "ka manta masu rashin lafiyar hawan jini abincin su daban ne? To abincin ka kenan har se an gwada ka an tabbatar mana da baka tare wannan ciwon kuma, idan ka bani had'in kai ,wata d'aya yayi yawa kaga komai ya wuce ,ka fara cin abinci kamar namu?"


Shiru Daddy yayi ,har cikin zuciyar shi yayi matuqar jin dad'in yadda Haajar take nuna damuwa da ciwon shi ,Dan shi yanzu har manta wa yake wai yana da hawan jini. Murmushin k'asan zuci yayi , a fili kuma ,had'e girar sama Dana k'asa yayi ,tare da cewa

"Ba wani wata d'aya da zanyi ina cin wannan abincin gaskiya ,kuma bari ki gani"


Basarwa Haajar tayi tare da cewa "OK fine".


Auta ce tace " Anty Haajar nima a k'ara mun, amma ba irin na Daddy ba.


"Oh no my baby girl! Ai bama zaki ci irin na Daddy ba , bari in k'ara miki kinji"


Dariya sosai Auta ke yi , da gudu ta zagaye ta kujeran da daddy ke zaune ta rad'a masa a kunne "Daddy kaga na sake yiwa Anty Haajar wayo ko? Kamar yadda na mata wayo tazo gidan mu. Kaima ka dinga mata mayo irin nawa"


Kusan dariya maganar Autan yaso yaba Daddy, shima rad'a ya mata kamar yadda tayi masa yace "Kice dama wayo kika mata ta biyo ki? To amma me kika ce mata?"


With full confidence Auta tace "daddy ce mata nayi fa idan bata zo gidan muba ,kuka zan dinga yi kuma bazan sake zuwa makaranta ba, to shine ita kuma bata so inyi kuka kuma bata so in dena zuwa makaranta ,shine fa ta biyo mu"..


Dariyar abun Daddy ya dinga yi ,tare da cewa " give me 5" bashi hannu Auta tayi suka kashe ,yace "Good girl ,u make it,,, maza je kici abincin ki kar Antyn ki ta gano kin gaya mun wayon da kika mata"...


Da sauri Auta ta koma kujeran ta ta zauna tana dariya. Haseena tasowa tayi tazo wuce wa tace " Daddy inji abincin ka" wani irin Harara ya watsa mata ,daya sa tayi saurin rufe bakin ta tabar wurin tana dariya. Kallon Haajar yayi data gimtse dariyar ta yace


"Kinga abunda kika janyo mun ko?" Tashi tayi itama tabar wurin tana masa dariya ,ba tare da ta amsa shiba. Parlour suka dawo suka zauna suna kallo cike da raha ,har kusan sha biyu na dare kafin suka koma sashen Kubra...








*____________________________*








Garin kano,,,, a kwana a tashi bikin Daddy da lubabutu ya rage saura sati biyu currrr! Shi Daddy Sam yama manta da zancen wani biki...




















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/30, 1:42 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ASHIRIN DA BIYAR_


*___________________________*


































_Hajiyar Daddy tayi iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta binciko halayen Lubabatu Dana iyayen ta ,amma duk Wanda tasa binciken amsar guda d'aya ce ,cewar su d'in Mutanen kirki ne ,sedai lubabatun bazawara ce ta tab'a aure ,shekaran su biyu Allah ya yiwa mijin rasuwa. Wannan shine kad'ai abunda ta iya gano wa ,gashi tayi binciken yafi sau a k'irga amma bayan yabon lubabatu da iyayen ta ba abunda ke zuwa kunnen ta. Ita dai Hajiya hankalin ta be kwanta da hakan ba ,amma ba yadda ta iya dole ta koyarwa zuciyar ta natsuwa da kuma son wannan auren ,Dan sau tari ma idan ta zauna se tayi ta tunanin anya badan bata son auren bane yasa take kawo shakku da kokonto, wata zuciyar kuma tace mata ,duk wani abunda ze fito indai ta b'angaren Hajiya Gwaggo ne to babu alkhairi a cikin sa ,daga k'arshe dai wani sashen zuciyar nata yake ayyana mata cewar 'suwaiba ba yadda zaki yi kuma ba kida abun yi ,daya wuce ki mik'awa Allah wannan al-amarin sannan kuma ki dage da Addu'a tare da nema wa MISBAHU zab'in Allah da alkhairi a cikin wannan auren ,ki kuma ci Gaba da saka mishi albarka ,saboda Addu'ar uwa mace tamkar taki ne tsiro take. Wannan shine kad'ai mafita a wajen ki'... Wani ajiyan zuciya Hajiya ta sauke tare da furta "Allah ya maka jagoranchi acikin al-amurran ka MISBAHU... Wani iska ta furzar tare da tashi taci gaba da ayyukan ta nayau da kullum..._


_Hajiya Gwaggo duk yadda taso ayi cakwaikwaiwa a wannan bikin ya faskara ,saboda lubabatu ta hana ,a cewar ta ita batason bidi'a ,bayan walima babu abunda za'ayi shima se idan an d'aure aure ,yinin biki ma bayi zatayi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login