Showing 51001 words to 54000 words out of 86229 words

Chapter 18 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt

27 Dec 2024

3939

,alamar kayan cikin mutum ya fashe. Duk Wanda ke wurin sai da ya razana ,wasu daga ciki har zubarda k'walla suke yi dan tsabar tausayi. Ba jima wa suka sake jiyo irin wannan sautin alamar kayan cikin wani ya sake fashewa. Cike da gigita daddy yayi kukan kura yana so ya fad'a ciki ,yana fad'in "rayukan 'ya'yana!! Allah ka taimake ni!!! Ku ban ni in shiga in ciro yarana! Kuna kallo wuta na cin iyalina!!!" Haka daddy ya dinga sambatu iri daban-daban. Kusan duk wanda ke wurin sai da ya tausaya mass. K'arar sautin fashewar kayan cikin mutum suka sake jiyo wa a karo na uku. A wannan karon daddy yanke jiki yayi ya fad'i, sai da aka kwashe shi a k'asa sumamme se asibiti...






Wannan al-amari ba kad'an ba yayi masifar tayar wa mutane da hankali. Har kusan yamma kafin aka samu nasarar kashe wutar da ke ciki. Dak'yar aka yi nasarar zaqulo gawawwakin su ,dan kusan sun k'one qurmusus. A irin qonewar da su ka yi ,ba na tunanin ko rayuwa suka yi za su yi wani amfani a duniya ,mutuwar dai itace Hutu a gare su...




Gawar mutum uku aka fitar ,Wanda ba'a iya tantance su waye da waye ba. Nan da nan gari ya d'auka. Hajj jamil shine Wanda yayi ruwa yayi tsaki akan mamatan. Washe gari da safe aka sallata gawawwakin aka kai su gidan su na gaskiya. A nan sai dai muce Allah ya jiqan wa'ayanda suka Riga mu gidan gaskiya...




Kwanan daddy uku a asibiti be San Inda kan shi yake ba. Hajj jamil ne ya kira hajiyar daddy ya sanar mata. Ba shiri hajiya ta taho sakkwato hijab a baibai...


Hajj jamil ne ke kula da daddy yayin da Hajiyar daddy ke kula da sauran majiyatan ,da basu qone ba ,sai dai jikata da suka yi had'ida qananan raunuka...






A rana ta hud'u daddy ya farfad'o. Kuka sosai ya ke na rashin 'ya'yan shi. Dan shi duk a tunanin shi gaba ki d'aya ba'a fidda kowa ba. Dan idon shi ya riga ya rufe ,ba ze iya tantance lokacin da aka fito da wasu ba balle har ya iya Sanin ko su waye daga cikin su...




Hak'uri Hajj jamil ya shiga ba shi tare da yi masa nasihohi akan qaddara, ya d'ora da cewa "wannan itace taka qaddarar MISBAHU,,, ba kuma dan Allah baya son ka bane yayi maka haka. Kar kayi mamakin wani tanadi ya maka Wanda yafi Wanda ya karb'a daga wajen ka"...haka hajj jamil ya dinga rarrashin daddy.


Daddy na kuka yace " ka banni inyi kuka jamilu. Na rasa komai da kowa nawa. Ba ni da kowa ba nida kowa. Wannan wani irin musiba ce??? Wani kalar baqar qaddara ce ke bibiyata haka??? Me na aikata Dana cancani irin wannan tashin hankalin??? Gidana ya dawo tamkar kushewa"


Hajj jamil na hawaye yace "Ka dena fad'ar haka MISBAHU. Baka rasa komai da kowa ba tunda ka na da Allah. Ya kuma San dakai. Shine kuma ze Isar maka ga dukkan al-amurran ka...MISBAHU kar ka manta Allah s.w.t Idan ka ga kayi dariya ni na saka ka ,idan kuma kaga kayi kuka to ni ne na saka ka shi ma...idan allah ya saka ka dariya ba wanda ya isa ya sa ka kuka ,idan kuma ya saka ka kuka to wallahi ba wanda ya isa ya saka ka dariya. Wannan shine karantarwa ta aqida... Allah dakan shi yace a cikin littafin shi mai girma "WA ANNAHU HUWA ADHAKA WA ABKA" Wato Allah shine me dariyantarwa, kuma shine me kukantarwa. Saboda haka ka yi tawakkali da Allah sai ya kaga ya Isar maka ga dukkan al-amurran ka..."












Wannan nasiha ba kad'an ba ya shigi Daddy. Hajiya da ke gefe ita ma ta karb'e shi ,sai abunda Allah be bata ikon fad'a wa daddy ba na Kalmar nasiha da rarrashi. Daga k'arshe tace "MISBAHU baka tab'a baqanta mun ba ,ban tab'a rik'e ka a raina koda na sakan d'aya ba. A koda yaushe Addu'a ta da albarka ta na tare da kai. Ba zaka tab'a ganin ba daidai ba ,insha Allahu lafiya zaka gama..." Wannan Kalma ba kad'an ba ya sake kwantar wa da Daddy hankali.




Satin daddy biyu aka sallame shi daga asibiti. Ranar da aka sallame shi ,Hajj Jamil yace yazo ya raka shi yana so ze dubo wani a cikin asibitin. Ba musu daddy yabi bayan shi.


Sallama suka yi tare da shiga d'akin majinyatan. Haajar ce akan gado daya ,daya gadon kuma dake gefe Suxee. Ga hajiya a zaune akan kujera tare da auta. Da mamaki daddy ke bin su da kallo ,murza yayi yana so ya tabbatar da abunda yake gani. Ganin kamar yana shakku yasa Hajj Jamil ya janyo hannun shi suka zauna daga gefe kan gadon da Suxee ke kwance.


Cike da al'ajabi daddy yace "Haajar,,, Hajiya k'arama da ma Baku mutu ba?""... Murmushi Haajar tayi tare da cewa " Allah ya raya mu Daddy ". Dariya maganar ta ya bama kowa. Suxee tace " Daddy ya jikin ka?" Tsabar farin ciki yasa daddy ya ma kasa amsa ta. Se bin su yake da ido kamar yau ya fara ganin su. Hannu ya d'aga sama tare da godewa Allah, ya kuma sake gasgata maganganun Hajj Jamil ,ga shi yanzu Allah ya dawo masa da wasu daga cikin ahalin shi a lokacin daya fi buqatar su...


Hajiya tace "ka gani dai ko? Dama mun Bari ka samu sauqi ne tukunna kazo ka gan su. Amma haqiqanin gaskiya da aka ce maka kowa na ka ya mutu ba gaskiya bane ,Allah ya fitar maka da wasu daga ciki. Ka ga shi Allah ba'a yanke rai da rahmar sa. A koda yaushe kuma Rahma da ni'imar sa kewaye take da bayin shi salihai"...




Jinjina kai daddy yayi cikin zuciyar shi ya sake godewa Allah. A fili ya furta " Lallai Allah ne abun godiya"...




Suna zaune likita ya zo ya kawo takaddar sallama nasu Haajar tare da magungunan su. Had'ida sheda musu cewa Haajar ta dawo sati na sama a sake duba ta. Hajj Jamil ya tambaya ko da wani matsalar ne? Likita ya mik'a mi shi sakamakon gwajin da aka yi wa Haajar. Karb'a Hajj Jamil yayi bayan ya karanta ya saka a aljihu...




Gaba d'aya suka d'unguma a mota zuwa gidan Hajj Jamil. Haajar na ganin an d'au hanyar da ba na gidan daddy ba ,tace wa Hajj Jamil dake toqa motar "Abbu sameer ina kuma za mu je?" Ba tare da ya juyo ba yace "Gida na zamu je mana". Girgiza kai tayi tare da cewa " A'ah Dan Allah! Ina so muje gidan daddy akwai abunda nake so in d'auka". Gaban daddy ne ya yanke ya fad'i lokacin daya ji Haajar ta ce aje gidan shi. Ba kad'an ba ya tsani yaji wani labari akan gidan balle har ace wani Abu ya sake kai shi gidan...




Hajj Jamil be k'i ta tata ba ya karya motar zuwa gidan daddy...




















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/17, 3:30 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN_


*____________________*




















Har sun kai k'ofar gida barrister Kabir ya yi wa Hajj jamil waya akan yana babban asibiti ,Wanda shi ne mai bincike akan case d'in gobarar gidan daddy ,komai na tafiya ne a k'ark'ashin kulawar Hajj Jamil. Hajj jamil yace masa ya same shi a gidan daddy yanzu... Parking ya yi a k'ofar gida tare da kashe motar. Dikkan su suka fito suka shiga gidan a tare. Tunanin wani sashen za su suka fara yi. Hajj yace su nufi sashen bak'i Dan shi ne kad'ai a gyare, kuma anan zauna lokacin da al-amarin nan ya faru saboda zuwan jama'a ,wasu ya sauke su anan wasu kuma ya kai su masauqin bak'i. Gaba d'ayan su can suka nufa kai tsaye banda Haajar ,da ta zagaya ta bayan gidan da alama ma gidan gona ta nufa. Lubabatu na jin zuwan su ,nan da nan ta isa sashen Har ta na fad'uwa. Kuka ta rushe musu da shi tare da jajanta musu kan abunda ya faru. Wani irin kallo kowa ke bin ta da shi Wanda ya sa ta sha jinin jikin ta, da mamaki kowa ke jinjina rashin kunya da ta ido irin na lubabatu...


A ce duk abubuwan nan da suka faru ,duk sintirin nan da aka yi ta tayi na asibiti babu ita ba labarin ta ,ba zuwa ba aike. Ai ko itace hajiya suwaiba uwar Daddy zata rarrashi zuciyar ta tazo idan ma tace duk rad'ad'in abun ne bai gama sakin ta ba...


Haka kowa dai ya share ta idan ta kamo wancan batu ta saki ta kamo wannan duk na borin kunya. Babu Wanda yace mata ci kan ki. Gara ma hajiya har ta iya amsa gaisuwar ta. Mik'ewa tayi tare da cewa "bari in kawo muku ruwa". Tana gama fad'ar haka ta mik'e tabar parlourn. Auta ce tace " Ni hajiya bacci nake ji" hajiya tace "to muje ciki, daga nan ma na yi alwala Dan na ji kamar an fara kiran sallah". Hajj jamil yace " mu ma bari muje mu yi sallan hajiya ,mu na dawo wa yanzu" hajiya tace "to Ku dawo lafiya jameelu" daga nan daddy suka fita zuwa masallacin da ke cikin gidan shi ,a cewar Hajj jamil idan suka fita masallacin waje mutane za su yi ta zuwa mu su jaje ,kuma yanzu ya fi buqatar daddy ya samu Hutu kamar yadda likita ya jaddada masa...








Fitowar su ya yi daidai da isowar Barrister Kabir. A tare suka shiba masallaci bayan sun fito sun jima suna tattaunawa kafin suka k'araso Dan Barr Kabir ya yiwa hajiya jajen abunda ya faru...


Hajiya na d'aki kan sallaye ,suxee ta shigo tace mata "Hajiya kizo anyi bak'o" shafa addu'a hajiya ta yi tare da cewa "To ga ni nan zuwa". Ta fad'a tare da miqe wa ta nufi parlourn.


Barr dake zaune kan kujera mazaunin mutum d'aya ,yana ganin hajiya ta fito ,har k'asa ya zuqunna yana gaishe ta, tare da jajanta mata kan abun da ya faru. Barr Kabir ba tun yau ya san hajiya ba ,da kuma tarin alkhairan da hajiya ta yi masa a rayuwa, Dan karatun da ya je yayo game da shari'a a qasar waje Allah ne sanadi hajiya ce sanadi ,Dan ita ta biya masa komai da komai ba tare ma da daddy ya sa ni ba. Wannan na d'aya daga cikin abunda yasa ba zai taba iya mantawa da hajiya ba. Auren sa na farko ma hajiya ce ta nema masa ta kuma yi masa komai duk a sanadiyyar zaman shi abokin daddy na k'uruciya kuma an yi zaman mutunci da iyayen shi lokacin da suke raye. Wanda Allah ya yiwa matar tashi rasuwa wajen haihuwa ,bayan ta Haifa masa 'ya mace wacce taci sunan hajiyar daddy suna kiran ta da HAJIYEYE. Zaman lafiya da soyayyar da Barr Kabir yayi da marigayiyar matar shi yasa ya kasa k'ara aure sama da shekaru bakwai ,kullum jiya iya yau ,hajiya ta yi masa fad'a amma koda yaushe maganar Barr Kabir shine shi fa a ganin shi ba ze tab'a samun wacce zata maye masa gurbin matar sa ba. Daga k'arshe ma da hajiya ta matsa masa ,sai ya ce ta sake nemo masa ,in dai ita ce zata nemo masa ya yi mata alqawarin ze yi aure Dan ba yada shakku ko haufi akan zab'in hajiya. Tun daga wannan lokacin hajiya ta sarara masa ,Dan a cewar ta ita ma sai ta yi bincike mai tsawo akan wacce zata samo masa ,Dan qaunar da ke yiwa Barr Kabir yasa bata son duk wani abun da ze zo ya kawo wa rayuwar shi cikas. Ta na kuma son shi da qaruwa kamar yadda take son Daddy da abun da ta Haifa da abun alkhairi. Wannan kuma na cikin karamci irin na hajiya ,duk Wanda ze zauna tare da ita to fa lallai ne yasan kirkin ta.




Bayan sun gama gaisawa ,nan suka shiga tattauna abun da ya faru ,da kuma yadda ya shirya case d'in ganin sun samo bakin zaren. Suna zaune Lubabatu tayo sallama kamar wata mutuniyar azziki hannun ta d'auke da tiren lemu. Har gaban hajiya taje ta aje mata ,ta juya zata fita Barr dake bin ta da ido ya dakatar da ita. Gaban lubabatu ne ya yanke ya fad'i ainun. Hannu Barr Kabir ya sa a aljihun gaban rigar shi ya d'auko wayar sa. D'an danne danne yayi a wayar ,wani folder ya shiga da ke d'auke da hotunan lubabatun. Sake duban ta yayi ya kuma mai da kan shi kan wayar ya duba dakyau ya ga lallai itace ba wa ta bace.




Ita dai lubabatu sai kallon shi take yi ta na so ta gane inda tasan wannan fuskar amma ta kasa tunowa.






Tashi Barr Kabir ya yi yazo har inda lubabatu ke tsaye ,ya dinga zagaye ta yana qare mata kallo Sama da qasa ,Wanda ya sa lubabatu tsarguwa. Kowa ya zuba wa sarautar Allah ido yaga me ke shirin faruwa.


Barr Kabir yace "kin yi kama da wata matar marigayi Alh sambo".




Dummm! Gaban lubabatu ya yanke ya fad'i ,tabbas tasan ko waye ya mata farin sani musamman da ya ambato mata sunan Alh sambo. Zufa ne ya shiga tsiyayo mata ,kan kace me jikin lubabatu ya fara karkarwa.


Murmushi Barr Kabir yayi kafin yaci gaba da cewa "ko da yake duniya ta fa d'i ba lallai ya zama ke ba ,ina ga dai kamar Ku ce ta yi yawa.




Girgiza kai lubabatu ta shiga yi cike da sarqewar murya tace " umm...ummm ba ni bace". Ta na gama fadin haka ta yi hanyar waje da gudu. Sai dai a rashin sa'a sai jin tayi taci karo da mutum.


'Yan sanda ne sai dai ba'a kayan aiki su ke ba. Saboda kar su ja hankalin mutane, wanda Barr Kabir ne ya tura mu su adireshin unguwan da layin. Cafke ta suka yi ta na ta kokarin ta k'wace ,tare da cewa "Ku sake ni in tafi ,ba ni na kashe shiba wallahi Ku sake ni"


Barr Kabir yace "da ma wa ya ce kin kashe shi ai yana nan da rai ba mutuwa yayi ba.




Hannu lubabatu ta Dora akai tare kurma ihu tana fadin " na shiga uku na lalace"


Barr yace "ba ki shiga ba za dai ki shiga" yana gama fadin haka yace su tafi da ita.














MUJE ZUWAπŸ’ƒπŸ»




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️




[8/17, 3:30 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA D'AYA_


*_______________________________*
























Ba su kai ga fita da ita ba Sai ga Haajar ta shigo ,wacce sun shigowar su ta fice bata San wainar da ake toya wa ba. Hannun ta rik'e da wani buhu duk ya yi datti ,ba kuma Wanda yasan me ke ciki sai ita data shigo da shi. Tace wa 'yan sandan "Ku dakata tukunna". K'arasawa ciki ta yi , sai da ta k'arasa tsakar parlourn in da kowa ze iya hango ta ,sannan ta zuqunna tare da zaro abun da ke cikin wannan buhun. Da sauri daddy ya mik'e tsaye yana bin abun da haajar ta Ciro a buhun.


" wannan ba akwatin takaddu na bane?" Daddy fad'a tare da nuna akwatin.


Haajar tace "ka sake dubawa dakyau dai ka gani. Ta fad'a tare da mik'a masa akwatin. Karb'a ya yi tare da zama a lokaci d'aya ya bud'e akwatin ya shiga duba takaddun da ke ciki...


Da ido daddy ya bi ta, cike da matsuwar son jin k'arin bayanin In da ta samo akwatin bayan a idon shi komai ya k'one na sashen shi.


Haajar ta fara da cewa " daddy nasan za ka yi mamakin yadda aka yi na samu wannan akwatin? To ba abun mamaki bane ,ba kuma tantama wannan akwatin dukiyar ka ne Allah ya dawo maka da shi Wanda babu abunda ya samu matsala. Sai zan so Ku saurare ni Dan jin a inda na samo da kuma yadda aka yi na samu akwatin". Kowa natsuwa ya yi yana sauraron haajar. Wani ajiyan zuciya ta sauke kafin ta shiga ba su labari Tun daga lokacin da lubabatu ta turo musu 'yan fashi da makami akan azo aci zarafin su... Shirin ta akan sace akwatin dukiyar daddy da ta yi sannan ta k'ona d'akin saboda ta kauda hankalin kowa,,, da yadda ita haajar d'in ta wargaza wa lubabatu shiri ta hanyar canza akwatin da wasu takaddun na bugi,,, ta d'ora da cewa "Tun lokacin da marigayiya Haseena ta gaya mun cewa ba ta yadda da wannnan mutumin dake zuwa gidan nan a matsayin k'anin lubabatu ba ,na sanya ido akan su ,na ke kuma kula da shige da fitan su. Na dinga bibiyar ta ,har lokacin da suka shirya sace maka dukiya. A wannan Daren ta d'auki akwatin ta kai gidan gona ,ta yi rami mai zurfi ta saka a ciki ,ba tare da tunanin me ze ya dawo ba. Bayan tabar wurin na b'atar mata da hankali ta hanyar musaya akwatin da irin sa. A washe gari ta kunna wuta a d'akin sannan ta fito tana kururuwar a taimake ta. Wannan ta Ku da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login