Showing 42001 words to 45000 words out of 86229 words
Chapter 15 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
a kan stairs taci karo da kubran tana sauko wa. Kubra ganin data yi ran Khaltum a b'ace yasa ta tambaye ta "Yaya?" Nan Khaltum ke sheda mata duk yadda suka yi da Lubabatu a k'arshe ta k'ara da cewa "Har cewa tayi ba ni ba ko ke baki isa ba"...
Wani d'an tak'aitaccen murmushin gefen baki kubra tayi ,tare da cewa " Ina ba dai ni ba. Ta dai yi dake Dan inaga kun fi zama kai d'aya "
Da mamaki Khaltum tace "Ban gane me kike nufi ba?".
Kubra tace " zaki gane a gaba".
Wasa-wasa kusan kwana ukku daddy be koma gida ba ,yana asibiti tare da yaran shi yana kula dasu. Babu yadda Haj Jamil beyi akan ya koma gida ba amma yak'i.
Ganin har kusan rana na hud'u daddy be dawo ba yasa kubra ta kira shi a waya, amma be d'aga ba, Khaltum ma ta kira shi yafi sau nawa amma yak'i d'auka...
A washe gari ne Haajar ta farfad'o ,dan seda aka mata d'inki tsabar k'aruwan data yi. Amma Haseena kam se abunda Allah yayi...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/10, 8:13 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA TALATIN DA HUD'U_
*___________________________*
_Alhamdulillahi Haajar ta samu sauqi sosai ,dan kusan Yanzu ita ke kula da Haseena. Tun bayan abunda ya faru Haajar ta d'auke wa Daddy ,bata wani yi masa magana sosai se can baka rasa Ba, shima se idan maganar ta kama na dole ne kawai take yi masa. Ba kad'an ba hakan ya damu daddy ,gashi Hajj Jamil ma kwana biyu be zo asibitin ba balle daddy ya samu damar sanar dashi halin da ake ciki. Wasa wasa har kusan sati biyu Hajj Jamil be shigo ba ,tun abun baya damun daddy har ya soma hasashen abubuwa da dama. Dan Yanzu ya gano dalilin daya sa Haajar take share shi da kuma rashin zuwan Hajj Jamil, tabbas akan abunda ya faru ne ,yasan abun da d'aci ,amma ya kamata su gane ba yada lefi a ciki, shima ba'a son ranshi hakan ya faru ba, Dan shi da anbi ta tashi tun a wancan lokacin sedai idan b'arayin kashe shi zasu yi su kashe shi ,amma baze tab'a yiwa 'yar mutane fyad'e ba._
Sosai daddy ya shiga damuwa ,Dan ko kiran Hajj Jamil yayi a waya baya d'auka. Idan ma ya matsa masa da kira se dai ya turo masa message akan cewa 'yana aiki daga baya ze kira shi' kuma baze kira d'in ba. Daddy yayi ta k'ok'arin zuwa gida Neman sa a gida amma baya samun sa ,duk zuwan daze yi sedai Tukur me gadi yace masa yanzu ya fita ko ya dad'e da fita. Haka dai daddy yaci gaba da bibiyar Hajj Jamil. Gashi a Yanzu ba yada wani buri daya wuce yaga ya auri Haajar ,kuma hajj Jamil shine kad'ai Wanda ze taimaka masa ya samu auren Haajar cikin sauqi ,sedai baya tunanin hakan ze yiwu musamman da wannan abun ya faru tsakanin shi da Haajar...
Sau da dama daddy na k'ok'arin ganin ya tambayi Haajar ko tana waya da hajj Jamil amma babu dama Dan baya samun fuskar hakan. Kawo yanzu zuciyar daddy kamar zata tarwatse da tsabagen tunani daya masa yawa. Ga dai tunanin Haajar daya hana shi sukuni ,ga rashin jin Hajj Jamil da baya yi ,a gefe d'aya kuma ga rashin lafiyar haseena, abubuwa sun taru sun tsaya masa a rai Wanda abinci ma dak'yar yake samun nutsuwar cin sa. Saboda wannan matsalar yasa ko gidan shi ya kasa koma wa ,gaba d'aya sedai ya tattara ya koma hotel da zama ba tare da sanin kowa ba. Kullum hakan siyo abinci ya kawo musu asibiti amma rashin sake masa da Haajar bata yi yasa gaba d'aya baya samun walwalar sake wa a asibitin ,duk wani abunda suke buqata yana k'ok'arin yi musu.
Sannu a hankali Haseena ta fara samun sauqi cikin iyawar ubangiji. Bayan sati uku jikin ta yayi sauqi sosai Dan ba abunda bata yi ,sedai lafiyar ba kamar da ba. Bayan sati d'aya aka sallami Haseena. Dr. Zaidu ya buqaci Haajar akan ta kira daddy yazo yana so yayi magana dashi.
"Ba nida kati a waya Dr. Amma idan ba damuwa me ze hana kai ka kira shi!" Haajar ta bashi amsa
Dr. Zaidu yace "to ba damuwa zan yi k'ok'ari in neme shi. Muje office d'ina inaso inyi magana dake".
Ba musu tace masa " toh"
Bayan sunje office d'in sun zauna Dr. Zaidu ya kira daddy a waya ya sheda masa yana Neman sa. Ya kuwa yi sa'a daddy na kusa da asibitin ,ba b'ata lokaci se gashi ya k'araso.
"To ya jikin naki yanzu?" Dr. Zaidu ya tambayi Haajar
Fuske a sake ta amsa masa da "Alhamdulillahi naji sauqi sosai ni ai yanzu"
Dr. Zaidu yace "masha Allah. Haka nake son ji ai. Ciwon a jikin ki yake amma ni ke jin rad'ad'in".
Murmushi me qayatarwa Haajar ta saki tare da cewa "Ka dai ji Dr.da wani dad'in baki. Ta iya Wanda ke ciwo daban ,me jin zafin ciwon daban? Ai Abu ne Wanda baze yu ba".
Shima Dr.zaidun dariya yake yi a lokaci d'aya yana fad'in " Ai dama baki sani ba? To idan baki tab'a ji ko gani ba ,to ai yau kinji ko"...
"Aikam naji wannan tatsuniyar" Haajar ta bashi amsa tana da fara'a a fuskar ta
Dr. Zaidu yace "Ina ba kiji tatsuniya ba ,za dai kiji. Dan har gida zan zo in baki tatsuniya me dad'in saurare Wanda kunnuwan ki basu tab'a jin irin suba"...
Dariya maganar yaba Haajar ,tace " To Allah ya kaimu"
Cikin raha suke ta tattaba hira. A haka daddy yayi sallama ya shigo office d'in. Wani irin takaici ne ya tokare masa mak'oshi lokacin daya ga Haajar a office d'in Dr. Zaidu se faman murmushi take masa ,wato shine ba zata iya yi wa murmushi ba ,amma ta zo ta zauna tana wani washe wa wani k'ato baki se kace mijin ta. Nan take yaji hausin su ya kama shi, a lokaci d'aya kuma yanayin shi ya sauya, idanuwan shi suka canza launi.
Daga Haajar d'in har Dr. Zaidu idanu suka zuba masa. Takaicin kallon da suke masa ne ya sake kama shi. Dr. Zaidu fad'ad'a fara'ar dake fuskar shi yayi tare da cewa
"Hajj Misbahu barka da k'arasowa. Bismillah".
Kamar daddy baze tanka shi ba ,se kuma ya dake ya k'arasa ya zauna. Dr. Zaidu yace
" Ka ganni da mutuniyar ko muna d'an tab'a hira? Ai wato ita d'in ce akwai iya zantuttuka masu dad'i " Dr.Zaidu ya fad'a zuciyar shi d'aya, Dan shi har cikin ran shi son Haajar yake yi.
Murmushi Haajar d'in tayi tare da cewa "Nagode Dr."
Wani irin kallo daddy ya bita dashi ,daya sa ta had'e girar sama Dana k'asa tare da kauda kan ta gefe d'aya. Zuciyar Daddy ne ya dad'a k'una cike da b'acin rai yace
"Daddy kace inzo ,kuma nazo kayi shiru baka ce komai ba? Ina da ayukka a gaba na"
Yanayin yadda daddy yayi magana ba k'aramin basu mamaki yayi ba, musamman Dr. Zaidu dabe tab'a ganin sa a irin wannan yanayin ba. Ganin haka yasa ya kauda wasa gefe tare da zare gilashin dake manne a idon shi yace
"Hakane! Da ma akan ciwon Haseena ne!" Nan dai Dr.zaidu ya fad'a musu qa'idodi da dokoki had'id'a hanyoyin da zasu bi Dan gudun kar haseena ta shiga wani matsalar. A yadda ya shada musu kuma ,rayuwar ta na tsakanin rayuwa da mutuwa matuqar basu iya kiyaye wannan dokokin ba. Wasu magunguna masu tsadar gaske ya bada yace "wannan suna maganin da zata dinga amfani dasu ,akwai nasha k'arfe shida na safe ,akwai na sha biyu na rana ,akwai na shida na yamma sannan akwai na sha biyu na dare. Ko wanne kuma ana buqatar a kiyaye lokacin shan shi. Rashin kiyaye hakan kuma bazan iya cewa ga abunda ze faru ba ,Dan se abunda Allah yayi amma hakan ba k'aramin barazana ne ga rayuwar taba."
Godia sosai Haajar tayi wa Dr. Zaidu ,tare da karb'an magungunan. Daddy yace "mun gode" ya fad'a a tak'aice tare da mik'ewa ya fita daga office d'in...
Kai tsaye mota ya wuce ,yana jiran fitowar su. Haajar kuwa da Dr. Zaidu tare suka shiga d'akin da Haseena dasu suxee ke ciki ya taya su kwashe kaya. Auta se murna take zasu tafi gida ,Dan ta gaji da zaman asibitin ,haseena ma murna tayi sosai Dan har ga Allah ta jinyatu.
Had'a komai da komai suxee tayi a jaka. Dr. Zaidu ya rik'o musu wasu daga cikin kayayyakin har mota sune tafe suna hira. Dr. Na cewa ze yi kewar su ,Dan zaman su a asibitin ba kad'an ba ya saba dasu sosai...
Seda suka saka komai a mota. Dr. Zaidu dubi Haajar yace "A gaskiya zanyi kewa sosai Haajar. Da ma zaki taimaka mun koda da numbern waya ne kinga ai se mu dinga gaisawa kuma in dinga jin ya jikin Haseena"...
Murmushi Haajar tayi tare da cewa "to ba damuwa. Ai se in baka lambar!" Nan ta karanto masa lambar ya saka ,tare da cewa ze kira ta idan sun isa gida. Allah ya kiyaye ya yi musu sannan ya koma ciki.
Suxee da Auta ne suka shiga gidan gaba ,a inda Haajar da Haseena kuma suka shiga gidan baya...
Wani irin fizgar motar daddy yayi ,Wanda seda yasa Haajar buga kai da kujerar direba dake gaban ta ,ba Dan ta rik'e haseena ba ita ma da se kan ta ya bugi kujerar. Wanda har seda auta tace "A'aaah Daddy" ,suxee ko bin daddy tayi da kallo da bema San tana yi ba.
Fanfala gudu ya shiga yi a hanya kamar Wanda ze tashi sama, be taka burki ko inaba se k'ofar gidan shi, Wanda shima se a yau ya dawo gidan tun bayan faruwar abun.
Da motar kubra suka ci karo ,ita da Khaltum da alama fita zasu yi ,amma ganin motar daddy yasa suka fasa fitar tare da karya motar suka koma ciki...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/11, 7:09 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA TALATIN DA BIYAR_
*____________________________*
_Wajen da aka ta nada Dan ajiye matoci nan daddy ya yi parking motar shi. Suxee ce ta fara fitowa tare da Auta, ka fin Haajar ta bud'e gidan baya ta fito sannan ta zagayo ta bud'e wa Haseena d'ayan k'ofar ta fito..._
Haajar da Suxee ne suka kwashe kayan zuwa cikin gida. Tun da suka fito daga mota Kubra dake zaune a motar ta ta sauke gilashin mota tana bin su da ido d'aya bayan d'aya.
Tana wurin har lokacin da su Auta suka shige sashen ta ,daddy ya juya ya fita. Gaba d'aya kubra ta kasa gane komai. A yanayin da ta gan su ,ta tabbatar da akwai abunda ya faru ,ga shi duk sun rame sun yi duhu ,musamman ma Haseena dake tafiyar kamar Mara lafiya, ga Haajar da ta gani a tare da su ,duk da bata San ko wacece ba. Ta dad'e a wajen tana tunani iri-iri. "To me ya same su?" Ta tambayi kan ta ,ganin ba zata samu amsar tambayar ta a wurin kowa ba se a wurin yaran yasa ya fasa fitar. Bud'e marfin motar tayi ta fito. Da mamaki Khaltum ta bita da kallo tare da cewa "Hajja kubra ina zuwa haka? Naga cewa fita zamu yi kuma jiran mu ake yi?"
Kubra bata ce mata komai ba ,ta fito tayi tafiyar ta. Wani guntun tsaki Khaltum taja tare da cewa "kya ji da shi". Ganin kubra na nema ta b'ata mata lokaci yasa ita ma ta fito daga motar ta koma ciki...
Suna shiga Haajar ta kunna na'urar ruwan zafi ta band'aki Dan su samu suyi wanka. Kayan jikin ta ta rage ,Auta ta dube ta tare da cewa " Anty Haajar ni zaki fara yiwa"... Haseena dake zaune tace "Dalla ji ki k'atuwa dake se an miki wanka ,ke har yanzu ba zaki koyi wanka dake ba".
Auta tace " to ai ni idan nayi da kaina bana fita ne ,amma idan Anty Haajar tayi mun ina fita sosai".
Haseena tace "see you! U're getting to 9yrs amma har yanzu ke baki San kin girma ba"...
Auta tace " to ai ni har yanzu k'arama ce Yaya haseena ba irin ki ba k'atotuwa"
Ta sowa Haseena tayi zata kamo ta tana fad'in "Nice ma k'atuwa? Wallahi idan na kama ki zaki gane shayi ruwa ne"
Haajar da ke ta faman yi musu dariya. Ganin haseena ta Neman tashi yasa tayi saurin maida ta zaune tare da cewa "Haba Haseena! Lafiyar jikin ki ba fa kamar da bane, Dole se kin kula sosai".
Murmushi haseena tayi tare da koma wa ta zauna. Suxee tace " Ah to dai gara ki tuna mata idan ta manta Anty Haajar. Yanzu kam ke da Auta se gani se hange. Amma fa shigar miki zanyi ,dan bazan bari auta ta k'arasa mana ke ba, muna son ki".
Murmushi Haajar tayi tare da cewa "Auta muje in yi miki wanka kinji. K'yale su zan ga me tab'a ki a gaban ido ne ,se dai ayi idan ba na kusa"...
Tsalle Auta ta shiga yi tana fad'in" yeeeh Anty Haajar! " ta fad'a tare da yi wa su haseena gwalo.
Wani guntun tsaki haseena taja tace "Ji ta fa Dan Allah! Kwatakwata Auta bata San ta fara girma ba. Zallar wauta ne da yarinta ke damun ta. Bansan yaushe za ta yi hankali ba wallahi"
Dariya Suxee dake gyara musu kaya tayi tana fad'in "Ai Auta Autar ce. Allah dai ya raya ta musha biki"
Haka suka ci gaba da tab'a hirar su cikin nuna qauna irin na 'yan uwan taka...
Sallama kubra tayi kamar wata mutuniyar azziki ta shigo d'akin su Suxee, lokacin Haajar na band'aki tana wa Auta wanka. Tun da suka amsa mata sallama ko wacce ta d'auke kan ta. Duban su Kubra tayi tare da cewa "Ba Ku gan ni bane?"
"Mun gan ki" Suxee ta bata amsa a tak'aice
Mamaki ne ya kama Kubra, Dan idan akwai Wanda ya kamata ya yi mata hakan be wuce Haseena ba Dan ita ce me fitsarar cikin su ,amma kuma yau se ga Suxee.
Duk da halin ko in kulan da suke nuna mata ya mata ciwo ,amma se ta share tare da zama a gefen gado kusa da inda haseena ke zaune ,shafo gefen fuskar ta tayi tare da cewa "me yake damun kine haseena naga duk kin rame ?" Kayan dake kusa da haseena Suxee tazo ta kwashe ,nan magungunan Haseenan suka fad'o k'asa. Haseena tace "Yaya Suxee magani ne" ta fad'a tare da nuna mata.
Kafin suxee ta d'auka Kubra ta kai hannu ta d'auko tana dudduba magungunan. Kallon haseena ta sake yi tare da dafa kafad'ar ta tace "Haseena ba ki da lafiya ne? Me yake damun ki haka?"
Kwab'e hannun ta haseena tayi daga kafad'ar ta rai a b'ace tace "Menene damuwar ki dani da har zaki damu da lafiya ta?"
Kubra ji tayi ba dad'i a ranta ,amma ta danne tare da sake da fa kafad'ar haseena a karo na biyu tace "Wani irin magana kike yi haka Haseena? Na damu daku mana ,ni fa mahaifiyar Ku ce!"
Wani irin murmushin takaici haseena tayi tare da cewa "Na riga na manta da wannan tuntuni ,ni ba ni da wata uwa. Amma nagode da kika tunanin da hakan ,amma inaso ki sauke hannun ki daga kafad'a ta tun kafin in manta da cewa ke ce kika haife ni. Ina kuma baki shawaran ki manta da cewa kin tab'a zama uwa ko kina da wasu 'ya'ya kamar yadda mu ma tuni muka manta da cewa muna da uwa irin ki a duniya..."
Ba kad'an ba maganganun Haseena ya tab'a Kubra matuqa. A karo na farko da ta fara jin cewa bata kyauta wa rayuwar 'ya'yan ta ba ,amma son zuciyar ta ya hana ta ganin lefin abunda ta ke aikata wa. A sanyaye kubra ta tashi ta zata fita. Haseena tace
"Du be ta Dan Allah! Tana yi kamar ba ta da hannu a duk abubuwan da suke faruwa da mu. Wacece silar tarwatsewar rayuwar mu Dana mahaifin mu idan ba ita ba!" Haseena ta fad'a cikin b'acin rai. Nan take hawaye suka fara sauko mata.
Da sauri Suxee ta ajiye kayan da ta ke gyarawa ta matso ta dafa ta tana share mata hawaye tare da cewa "Relax Haseena! Kinsan ba wata isash-shiyar lafiya kike dashi ba. Yau fa aka sallamo ki daga asibiti. Be kamata ace har kin fara ta da hankalin ki haka ba. Babban burin mu a yanzu be wuce muga kin samu lafiya ba"...
" Bazan tab'a samun lafiya ba matuqar ina ganin waccar matar!!! Matuqar tana ci gaba da kiran kan ta mahaifiya ta!!! Yaya suxee waccan matar da kike gani ba kowa bace silar faruwar abunda ya faru dani fa ce ita ,itace ummul abasin faruwar komai. Na tsane ta bana son ganin ta, wallahi idan aka yi wasa ni ce ajalin ta ,idan kuwa hakan bata faru ba ,to ita zata zama sanadiyyar nawa ajalin. Yaya suxee na tsane ta ,kice ta fita