Showing 39001 words to 42000 words out of 86229 words
Chapter 14 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
bindiga itama iyalinka ce?"
Shiru daddy be amsa suba. Wani irin shed'anin dariya ya sake fashewa dashi kafin yace "Zan kuwa so ka tabbatar mun da haka. Ka kawo yarinya me kyau irin wannan ka aje a gidan ka da sunan holewa kana yaudaran mutane. Gata kyaky-kyawar gaske kuwa" ya k'arasa maganan tare da zuk'unna wa daidai setin fuskar Haajar yana kwashe gashin daya rufe mata ido...
Wani d'aci da takaici ne ya daki k'irjin daddy ,Wanda ya haifar masa da wani irin kishi dashi kanshi be San yana dashi ba, a hasale ya sake maimaita tambayar shi "Nace Ku gayamun me kuke so in Baku Ku fita Ku bar mun gida na"
"Kwantar da hankalin ka ,fita mubar maka gidan ka ai ya zama dole ,kar manta mu bak'i ne amma bana zana ba na tafiya ,ziyara mukan kawo saboda a gana a kuma sada zumunta. Abunda muke so d'aya ne be kai biyu ba. Da kuma zaka bamu had'in kai cikin mintuna da basu Gaza sha biyar ba zamu yi komai mu gama cikin lokaci, kaga ka taimaki kan ka ka kuma yi mana saving time ,Dan lokaci da kake gani Abu ne me matuqar amfani a rayuwar mu." Dake wa tare da sake fuska d'an ta'addan yayi kafin yaci gaba da cewa "kaga wannan kyaky-kyawar budurwan bake so kawai inga ka angon ce da ita nad'an wani lokaci ,idan kayi mun wannan ka gama mun komai ,idan kuma kak'i labari ze sauya"...
Wani irin zaro ido Haajar tayi ,tsantsar firgici da tsoro yasa bugun zuciyar ta tsananta kamar ana harba ganga ,daddy ko jin maganar yayi kamar saukar arado.
" ina baze yu ba ,idan ma turo Ku akayi to kuje Ku sanar da me shi yayi a banza ,Dan wallahil azim sedai Ku d'auki raina dadai in aikata abunda kuke so in aikata" daddy ya fad'a rai a matuqar b'ace...
Ogan 'yan fashin yace "lallai kuwa daka tafka kuskuren dahar kabar duniya ba zaka tab'a manta wa dashi ba. Kaga wa'yancan yaran naka ,ya nuna masa k'ofa ,a gaban ka zan kwanta dasu d'aya bayan d'aya kuma in saka yarana suyi kamar yadda nayi ,bayan mun gama kuma zan kashe su a gaban ba ba'a bayan kaba. Ina tunanin wannan shine Abu mafi d'aci da koda ban kashe kaba ze iya zama sanadiyyar bugawar zuciyar ka cikin sakan talatin. Saboda haka wanne ka zab'a??? Ban kuma cire maka ko wacce a cikin suba hatta 'yar k'aramar cikin su (da cewa auta) Dan k'ananan yaran ma kusan sun fi manya gishiri, kai wannan d'in ma ya nuna Haajar itama bazamu bar maka mutuncin taba warwas zamu maka haihuwar mayya akace ina d'a tace ta cinye"....
Shiru daddy yayi Dan gaba ki d'aya yanzu kam ya sare, babu abunda yake ambata a k'asan zuciyar shi se sunan Allah da Neman taimako a wajen shi. Ganin yayi shiru yasa ogan 'yan fashin cewa
" karka manta na gaya maka lokaci Abu ne mai tsada a wajen mu, saboda haka kai idan tsabar ya gagare ka ni na tsabar maka.... Ku rufe min su"... Ogan ya k'arasa fad'a tare da nufar hanyar waje alamar wajen su suxee ya nufa...
Kuka Haajar take yi tana shurin daddy akan yayi wani Abu ,amma.....
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/8, 7:20 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA TALATIN DA BIYU_
*___________________________*
_Har ogan 'yan fashin ya kusa fita ,Haajar ta sance d'aurin dake bakin ta tare da dakatar dashi cikin disash-shen muryar ta da baya fita sosai. Dawo wa baya yayi cikin isa da k'asaita tare da d'aga kai alamar ya akayi?_
_Haajar dake shash-shekan kuka tace "Dan Allah kuyi hak'uri Ku k'yale su kar Ku musu komai ,ze yi duk abunda kuke so yayi indai baza Ku tab'a wa'yancan yaran ba"...
Da mamaki daddy ya kafe ta da ido tare da cewa " Haajar ba kida hankali ne? Ba kiji abunda yake so na aikata miki bane? Fyad'e fa yace ko bakiji bane?"
Wasu hawayen bak'in ciki ne da takaici ya shiga reto a fuskar Haajar wani na bin wani ,k'ok'arin share hawayen ta tayi tace "Daddy naji sosai ,naji abunda suke so ka aikata mun. Amma kai ma baka ji abunda suka fad'a bane akan cewa lallai idan bakayi hakan ba zasu lalata rayuwar su Haseena? Me wa'yannan yaran suka sani? Me suka yi dahar suka cancanci irin wannan d'anyen aika-aikar? Saboda haka bazan iya jure kallon su a irin wani yanayi me kama da wannan ba balle kwatankwacin sa ,na yadda na bada kaina fansa akan su."
Wani irin rufe ido Daddy yayi yana jin wani d'aci a ranshi, a lokaci guda kuma son Haajar ya k'ara ratsa kowani sassa da jijiyoyi na jikin shi. Kafin yayi magana yaji ogan 'yan fashin nan na tafi, tare da cewa
"Good! Kin kyauta sosai. Saboda haka na Baku minti goma. Idan mintuna goman nan suka cika ba kuyi kamar yadda nace ba ,to lallai Ku shirya haihuwar wasu 'ya'yan amma ba wa'yancan na waje ba..." K'ofa yasa aka bud'e, yace "Ku kalla Ku gani"
Waigawar da zasuyi suka ga mutum uku akan su suxee kowanne ya d'ora musu bindiga akai, alamar a shirye yake yayi harbi matuqar an bashi umurni,,,sannan yasa aka rufe masa k'ofar...
Hankalin haajar ne ya sake tashi. Ganin da tayi na daddy baze iya tunkaro taba yasa ta kai masa kanta.
Tana ji tana gani daddy ya rabata ta da 'yan matancin ta. Duk da irin rad'ad'i da azaba dake k'ok'arin ratsa ta a wannan lokacin bakin ta be kasa furta addu'ar saduwa ba. Shigan da daddy ya mata wani irin shiga ne dashi kanshi be San yayi shi ba ,shiga ne irin Wanda ya saba yi da matan shi ,a tunanin shi duk hakan take.
Wani abun da na lura dashi shine kamar duk a cikin matan daddy be tab'a auren ainahin abunda ake cewa cikakkiyar budurwa ba ,Dan yanayin yadda yake shigar Haajar ya tabbatar da hakan...
Wani irin k'ara Haajar ta saki lokacin da daddy yayi nasarar yaga mata rigar budurcin ta, saboda wani irin azaba daya ratsa ta Wanda bata tab'a sanin akwai shi a duniya ba. A hankali take sauke numfashin ta Dan gaba ki d'aya iskan duniyar nan ji tayi ya mata kad'an wajen shak'a...
Wani irin son ta da tausayin tane ya kama daddy ,be San lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba, musamman daya ke ganin wacce tafiye masa komai a rayuwa a cikin wannan halin....
Wani dariyar ta'addanci ogan 'yan fashin nan yayi, had'ida wani irin tafi me k'ara, tare da cewa "Job done! Good of u!" Yana gama fad'ar hakan yayi pito ,gaba d'aya yaran shi suka zagaye shi. Hannu ya Sara wa daddy tare da cewa "Good bye"... Yana gama fad'ar hakan suka bar wajen da alama tafiya suka yi gaba d'aya...
Suna fito ba shiri daddy yayo kan Haajar yana jijjiga ta ganin da yayi kamar ko numfashi bata yi ,d'ago ta daze yi se ganin yayi tana zubarda jini. Iya gigicewa daddy ya gigita. Jijjiga ya shiga yi yana kuka kamar wani yaro tare da sako zance iri-iri "Dan Allah ki tashi Haajar. Ki tashi,,,Haajar karki tafi ki barni ,kyace rayuwa ta ,ban tab'a sanin menene dad'in rayuwa ba seda na had'u dake ,kece jin dad'i na dani da yarana,,,,Haajar!!!" Daddy ya dinga maimaitawa kamar wani zazzautacce.
A hankali Haajar ta fara bud'e jajayen idanuwan ta. K'ok'arin d'aga hannun ta take yi a haka har ta samu nasarar cin k'arfin hannun ,tana nuna masa k'ofa.
Cike da zumud'i daddy yace "me kike so?"
Hannun ta ya kalla yaga inda take nuna masa alamar yaje ya dubo su haseena...
Yace "Su Auta?".
Lumshe ida tayi ,se ga wasu siraran hawaye nabin gefen kuncin ta...
Yace " bazan iya nisa dake ba Haajar "
Tattaro duk wani kuzarin ta tayi ta bud'e baki a hankali tace cikin muryatta da se kayi da gaske kafin ka iya gano me take cewa tace "Kaje ka dubo su daddy"...
Ba shiri daddy ya ajiye ta ,Dan duk dramar nan da ake akan hannun shi take, ya nufi wajen. A d'ad'd'aure yagan su ,da alama tun d'aurin da suka musu na farko ne ,sun galabaita ,gaba d'aya k'arfin su ya k'are. K'ok'arin kwance su ya fara yi.
Auta har bacci ya d'auke ta daga nan inda take a d'aure, Suxee kuwa tun tana kukan ,har ya koma sedai hawaye na ke zuba daga idanuwan ta. Tsoro daddy yaji lokacin daya ga ya kwance haseena ta fad'o a jikin shi warwas ,ya d'ago ta ,se jin yayi ya canb'ala hannun shi cikin jini, dubawar daze yi se ganin yayi ta dafe gefen cikin ta ,ga wani jini me guda-guda dake b'ul'bulowa...
Murya a rud'e daddy yace " meya same ta? Haseena!!!Haseena!!! "
Cikin muryar kuka suxee tace "Harbin ta sukayi da bindiga daddy saboda ta musu taurin kai. Sun zo suci zarafin mune ita kuma ta nuna bata yadda ba ,shine suka harbe ta a ciki...."
Wani irin tashin hankali ne ya bayyana k'arara a tattare da Daddy. Kuka yake yana fad'in "me yasa zasu mun haka? Me na musu? Me iyali na suka musu da suka cancanci wannan wulaqancin haka???"...
Ganin baze samu amsar tambayoyin shi a wajen kowa ba yasa ya tashi a daburce ya suri Haseena yakai ta mota ,sannan ya dawo ya d'auko Haajar a k'irjin shi kamar wata 'yar tsana yakai ta mota itama ,suxee ta d'auki auta ,suka bar gidan ,basu taka burki ko inaba se asibitin Dr. Zaidu...
A can suka kwana gaba d'ayan su... Seda safe ya kira Hajj Jamil yake sheda masa akan ya same sa asibitin Dr. Zaidu ,amma be sanar dashi komai ba.
Hankalin Hajj Jamil ya tashi sosai Dan a tunanin shi ko ciwon Daddy ne ya sake tashi. Barin abunda yake yi yayi ya taka mota se asibitin...
_Washe gari su Hajiya Kubra suka duro Nigeria_....
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/9, 4:19 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
_BABI NA TALATIN DA UKU_
*___________________________*
_Da Suxee Hajj Jamil ya fara cin karo ,tsabar tsoro yasa tana ganin shi da gudu taje ta rumgume shi tare da fashewa da wani marayan kuka me ban tausayi. Wannan Abu ba kad'an ba ya sake d'aga hankalin hajj Jamil har ya rasa da wani Kalma ze yi amfani wajen lallashin suxee Dan duk a tunanin shi ko wani abun ne ya samu Daddy. Lallashin ta ya shiga yi da duk wani kalma me taushi daya zo bakin shi. Seda suka samu wuri suka zauna ,sannan yake tambayar ta ina Daddy???_
_Suxee na kuka nan ta gaya masa duk wani abun da ya faru a Daren jiya har kawo zuwan su asibiti. Wani irin imani ne da tsoron Allah ya cika zuciyar Hajj Jamil ,a lokaci d'aya wani tsoro ya dad'a mamaye masa k'irji_
Be iya cewa komai ba se "Yanzu ina daddy yake?"
A tare suka shiga inda wani d'aki na kwanan likitoci da Dr. Zaidu yakai daddy dan ya huta ya kuma samu kwanciyar hankali. Hannu biyu daddy yasa ya rik'e hab'a ,idon shi a lumshe kamar me bacci ,a zahiri kuma kwanto yayi ba bacci ba. Auta ce kan gado daga gefen shi tana rankon baccin wahala.
Wani irin tausayin daddy ne ya k'ara kama Haj Jamil. K'araso yayi har inda daddy ke zaune ya dafa kafad'ar shi ,tare da kiran sunan shi a sanyaye
D'agowa daddy yayi yana duban shi ,ba tare da ya sani ba wasu siraren hawayen suka fara gangaro masa. Zuciyar hajj Jamil ce ta sake karaya. Girgiza masa kai yayi alamar hakan be kamata ba, tare da nuna masa Suxee dake gefe itama tana aikin zubarda k'walla tun Daren jiya
Hannun daddy ya rik'o suka fito waje. Ya dubi suxee yace ki zauna muna zuwa ,kuma ki dena wannan kukan bana so. Kai kawai ta iya gyad'a masa ba tare da ta iya tare hawayen dake ambaliya a fuskar taba.
Mota suka shiga ,Haj Jamil ya data motar. Gidan shi suka nufa. Seda ya tabbata daddy yayi wanka ya kawo masa Abu me sanyi ,dan yasan shine kad'ai abunda daddy ze iya sha a wannan lokacin...
Bayan ya huta sannan Haj Jamil ya fara tausasan daddy da duk wani Kalma na lallashi daya sani a duniya ,tare da k'ara ankarar dashi game da 'yar taqaitaccen nasiha akan qaddara ta alkhairi data sharri. Ya k'arasa maganan tare da cewa "MISBAHU bawai dan kace kayi imani bane kawai yasa Allah ze barka baze jarrabe ka ba. Cewa kayi imani bashi ya nuna Allah baze yi maka gwaji yaga shin lallai imanin nan da kace kayi da gaske ne ko be kai zuciya ba. Saboda haka duk ka d'auki wannan a matsayin jarabawa daga Allah, kowa da tasa kalan qaddarar wani idan kaji nashi zaka ce naka ba komai bane ,saboda duk yadda kam cikin masifa wallahi wani ya fika ,haka duk yadda kake cikin jin dad'i wani ya fika. To Dan haka ka d'auka wannan shine kalar taka qaddarar kuma ka gode wa Allah da abun ya tsaya iya nan"...
Har cikin ran dad'i yaji dad'in maganganun Haj Jamil ya kuma San gaskiya yake gaya masa amma wani b'angare na zuciyar tashi na k'aryata hakan. A hankali ya sauke ajiyan zuciya tare da cewa " Haj Jamil yanzu har kana ganin akwai Wanda ya kaini shiga masifa balle har ya fini??"
Murmushi Haj Jamil yayi tare da cewa "wani tunda aka haife shi a masifa ya fad'a a haka kuma yake ci gaba da rayuwar shi, kai kuwa se da kayi auren farko tukunna kasan menene matsalar rayuwa ,Ashe ma ubangiji nason ka...yanzu kai idan baka Bawa zuciyar ka hak'uri ba ,taya zaka iya rarrashin yaran nan?"
Sauke numfashi daddy yayi kafin yace "Hakane! Amma Haa.." Be k'arasa kiran sunan Haajar ba Hajj Jamil yace "mu bar wannan maganar yanzu ,zamu tattauna akai wani lokacin"...
Da haka dai Hajj Jamil yaci gaba daba daddy baki har ya samu kanshi. Seda ya tabbatar ya samu nutsuwa sannan suka koma asibitin. A hanyar su ta koma wa asibitin suka tsaya suka siyawa suxee da auta abinci, duk da daddy yasan halin suxee sarai da qawa zuci ba lallai ta iya sawa bakin ta wani abun ba saboda har yanzu ba'a hayyacin ta take ba...
A b'angaren su Hajja Kubra kuwa ,an dawo daga Germany ,sun k'ara gogewa sun yi kyau abun su iskanci da rashin mutunci kuwa se abunda ya qaru. Wanda yasan su da idan ya gansu yanzu ze tabbatar da akwai tarin canje-canje.
Da dawowar su ko wacce sashen ta ta nufa, kubra bata lura da sauye-sauyen dake sashen taba ,kai tsaye wanka ta fad'a ta sakarwa kanta ruwa ,ta dad'e a band'aki kafin ta fito ,rigar bacci kawai ta iya saka wa ta kwanta nan da nan bacci ya kwashe ta ,ba ita ta farka ba se yamma...
Bayan ta tashi ne take tunanin ko ina su auta suka je ne ,Dan taji bata jiyo motsin suba. Tab'e baki tayi tare da cewa "k'ila kuma ya kai su kano".. Da haka taci gaba da gudanar da al-amuran ta...
A b'angaren Khaltum kuwa ta kammala duk wani shirin ta tsaf na karb'ar girki a Daren ranar, a yayin da kubra ita ma ta gama shirin ta na zuwa tunkarar daddy duk da cewar ita ba girkin take da niyyar karb'a ba amma kuma tana kewar mijin ta ,tana so ta gan shi...
Da daddare Lubabatu na zaune a parloun daddy tana kallo ,khaltum ta banko k'ofar ta shiga. Lubabatu dake zaune taso wa tayi a tunanin ta ko daddy ne amma se taga akasin hakan.
Da wani irin d'an iskan kallo khaltum tabi Lubabatu ,yayin da itama take maida mata da martanin ke kuma daga ina???
Cike da tsiwa Lubabatu tace " Ke kuma malama daga ina? Kin shigo wa mutane ba sallama ba komai ko an gaya miki nan choci ce?""
Wani irin azababben mari khaltum ta kwasawa Lubabatu tare da cewa "Ni sa'ar kice daza ki dinga gaya mun duk kalamin daya zo bakin ki? Ko kuwa ba'a koya miki tarbiyya da iya magana bane daga gida? Banza shashasha. Ni ba wurin ki nazo ba wajen me gidan nazo, ki bari zan dawo ta kan ki".. Khaltum na gama fad'ar haka taja wani dogon tsaki tare da nufar hanyar bedroom d'in daddy ,shiga tayi ta dudduba seda ta tabbatar lallai baya nan sannan tazo ta wuce Lubabatu dake tsaye tare da banka k'ofar...
Wani irin shu'umin murmushi Lubabatu tayi tare da cewa " lallai kuwa wannan matar baki San wa kika Mara ba ,Ashe kuwa zaki yi Dana sanin mari na da kika yi a yau ,Dan ni Lubabatu kabewar kan dutse ce ban fito ba seda na shirya. Wi k'aramar kura a kashe ki a d'au alhaki ,a barki ki girma ki kar mutum. Wannan duk kirari na ne, Bana barin bashi. Amma muje zuwa da sannu zan sa ki kwashe kashin ki a hannu. Banza sakariya kawai"... Wani gajeran tsaki taja sannan ta koma ta zauna ta had'e k'afa d'aya kan d'aya tana girza kai tare yin k'wafa...
Kai tsaye Khaltum sashen Kubra ta wuce