Showing 45001 words to 48000 words out of 86229 words

Chapter 16 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt

27 Dec 2024

3934

daga nan bana son ganin ta" Haseena ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani marayan kuka ,a lokaci d'aya ta fad'a jikin Suxee tana ci gaba da rera kukan ta me ban tausayi. Suxee ita ma nan da nan hawaye suka fara sauko mata na tausayin kan su...




Rai a matuqar b'ace Kubra ta juyo tare da cewa "Kin fita a hankalin ki ne? Me..."


"Ya isa haka Dan Allah." Suxee ta katse Kubra ,sannan taci gaba da cewa " Ya isa! Wasan kwaikwayon ya isa haka. Dan Allah ki tafi. Kin zo ganin mu ko ? To mun gode da ziyara Allah ya ba da lada. Ki tafi pls ki bar mu da abunda muke ji ,tun kafin ki janyo mana wata masifar bayan wacce muka shiga"... Suxee ta fad'a hawaye na sauko mata.


Zuciyar Kubra ta shiga k'una ,iya b'acin rai ran ta ya b'aci. A fusace ta fita hawaye na sauko wa daga idanuwan ta. Da gudu ta haura sama ,ba ta ko lura da Khaltum dake lab'e a wurin ba ,da alama taji duk abun da ya wakana tsakanin Kubra da 'ya'yan ta...




Wani irin dariya Khaltum ta yi na makirci. Tare da d'aukar alwashin gano bakin zaren...
























MUJE ZUWA๐Ÿ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...โœ๏ธ
[8/11, 9:14 PM] SIDIYA...โœ๏ธ: ๐Ÿ ๐Ÿ  *GIDAN MISBAHU*๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ 
*_๐Ÿ (base on true life story)_*๐Ÿ 


*_๐Ÿ INTELLIGENT WRITERS ASSO๐Ÿ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)โœ๏ธ*









_BABI NA TALATIN DA SHIDA_


*_____________________________*




















_Kubra kai tsaye d'akin ta nufa ,tana zuwa ta fa d'a kan gano tare da fashewa da wani sabon kuka me tattare da takaici da bak'in ciki. A rayuwa bata tab'a tunanin rana me kama da wannan za ta zo mata ba. Ace yau 'ya'yan ta na cikin ta ne suke furta mata Kalmar tsana da k'iyayya har suna furta k'ila su ne ajalin ta. Wannan Abu ba k'aramin tab'a kubra ya yi ba. Dan yinin ranar ko ina ba ta iya zuwa ba ,a d'aki ta wuni..._


Ganin haka yasa Khaltum ta zo sashen ,a kan gado ta samu kubra tayi rufda ciki ,da alama wani gajeren bacci ne ma ya kwashe ta ba tare da ta sani ba. D'an bubbuga gadon Khaltum tayi. Firgigit Kubra ta farka.


Daga gefen gado Khaltum ta samu ta zauna tare da tambayar Kubra abun da ke damun ta


"Ya na gan ki haka ne hajj Kubra? Ba ki da lafiya ne? Tun d'azu ina ta jiran ki har na gaji da jira na koma ciki. Yanzu ma gani nayi shirun yayi yawa nace bari in leqo inji ko lafiya. A karo na farko da kika fa sa zuwa chasu ,nasan ko menene lallai babban dalili"... Khaltum ta fad'a kamar ba ta ji komai ba.


Wani nannauyan ajiyan zuciya Kubra ta sauke tare da cewa " Khaltum ina so in gyara tsakani na da 'ya'ya na!!! Ina so in ba su kula wa na tsakanin uwa da 'ya'ya... Khaltum ina son yara na ,bazan iya jure ganin su cikin wani hali ba... Ba zan tab'a yafe wa kaina ba idan wani abun ya same su ta sanadiyya ta ,balle ace wani na da hannu a cikin b'ata musu..."


Wani kallon mamaki Khaltum ta bi Kubra da shi kafin tace "Me hakan ke nufi kenan? Ya na nufin zamu da ne shaqatawa da shar holiya? Kin San hakan ba k'aramin asara bane gare mu. Ki manta da wannan ,mu mori rayuwar mu. Naga cewar yaran lafiyar su qalau, kuma mahaifin su na kula da su ,me yasa zaki damu kan ki?"...




" Khaltum ba zaki tab'a gane abun da nake nufi ba ,ba zaki tab'a gane irin soyayyar dake tsakanin uwa da 'ya'ya bane. Da zaki shiga zuciya ta kiji irin zugin da nake ji a yanzu da baki fad'i cewa in manta da su ba. Ko da yake ta ina ma zaki San me nake ji bayan ba uwa bace ke??? Ta ina zaki san abunda nake ji a yanzu bayan baki san darajar 'ya'ya ba. Da ace kin tab'a d'aukan ciki ko da so d'aya ne ,ko baki haife cikin ba ki kayi b'ari ina ga zaki fi gane d'acin dake rai na a yanzu. Ban ma ga amfanin zama ina gaya miki wannan ba Dan be shafe ki ba ,kuma ba ki da maganin da zaki mun. Uwa ya kamata in fad'a wa wacce tasan darajar 'ya'ya ,wacce ta tab'a d'aukan ciki ta haihuwa amma ba ke ba"...




[8/11, 8:29 PM] SIDIYA...โœ๏ธ: Ba kad'an ba kalaman Kubra ya yi matuqar k'onawa Khaltum rai. Dan ta fahimci akwai suka da habaici a cikin maganganun Kubra. Wato me Kubra ke so tace mata? Tana nufin ita juya ce ko kuwa? Tana nufin ita bata San zafin haihuwa ba shiyasa bata San darajar 'ya'ya ba? Lallai ya kamata ki farka daga dogon baccin da kika yi Khaltum' Khaltum ke ta faman sak'e-sak'e a ran ta. Tab'e baki ta yi tare da cewa


"Wannan haka ne kam. Amma ga wannan ina ga idan kika sha ze rage miki rad'ad'in abunda kike ji a yanzu, nasan zaki ji dad'in shi"... Khaltum ta k'arasa fad'a tare da mik'e wa Kubra wani syrup.


Ba musu kubra ta karb'a kwalban maganin nan ta d'aga ta shanye se dai ta aje kwalba ta shanye tas... Nan kubra ta fara sambatu iri iri akan tana so ta kasance da 'ya'yan ta. Wannan ya k'ara tabbatar wa da Khaltum cewa lallai kubra ta fara damuwa akan yaran ta ,ta San kuma komai ze iya faruwa daga wannan lokacin. Tashi tayi ta koma sashen ta. Ranar bata iya yin bacci ba ,kwana tayi tunanin yadda zata b'ullowa al-amarin, kafin safe ta yanke wa kan ta hukunci....






Kusan sati d'aya Kubra bata lek'o koda k'ofar sashen ta ba. Har wani rama tayi. Amma da yake fitar a jinin ta yake bayan sati d'aya da faruwar abun. Wata rana da la'asar tana zaune taji fitar ta tsikaro ta ,tana tunanin yadda za'ayi ta fita kawai se ga kiran Hajja Fati ta gaya mata akwai chasu. Dan haka kubra ta gama shirin ta tsaf na zuwa wannan chasun.


Bayan ta gama shirya wa ta biya ta sashen Khaltum akan ta sanar da ita fitan ko za ta shirya su je tare. Daga farkon dusan sashen Khaltum d'in ta fara jiyo k'amshin girki. K'arasawa tayi ciki tare da zama kan d'aya daga cikin manyan kushin d'in da ke makeken parloun...




Khaltum ce ta fito rik'e da wasu manyan kuloli a hannun ta ,tana ta aikin jera wa ,taci ado matakin k'arshe, tana ta Ku d'ai-d'aya kamar bata son taka k'asa. Har tazo ta wuce ta gaban kubra ba Dan bata gan ta ba. Kubra bata kawo komai a ranta ba. Da fara shimfid'e akan fuskar tace "Wannan wanka haka yau kuma Khaltum ,ko dai bak'i za muyi ne a gidan ,naji se k'amshin girki ne ke tashi."


Wani irin murmushi Khaltum take yi. Dawowa tayi ta zauna kusa da kujerar da Kubra ke zaune suna kallon juna ,tace "Aikuwa kin ga se aiki nake ta fama da shi. Da wani abun ne?"


"Eh wallahi Hajja Fati ce ta kira ni akan akwai chasu a NANAYE CLUB ,shine nace bari in zo in gaya miki ki shirya mu je" inji kubra


Khaltum tace "Ayyah! Gaskiya zan kuwa so in halarci wannan chasun dan nasan ba makawa ze ba da citta. Se dai kash! Gaskiya ina da wani d'an uzuri da ze katange ni daga fita yau"...


Kubra tace "Haba dai! Ke d'in kuma? Tukunna ma wasu bak'i ne za'a yi haka da har zaki fasa fita saboda su. Ke da bakya son bak'i" Kubra ta fad'a cike da tsokana


Wani irin dariya Khaltum tayi tare da cewa "Kai Anty Kubra"


Hab'a kubra ta rik'e tare da cewa "Yau kuma wani salo ki ka tashi da shi ne? Wai Anty Kubra ,wallahi ko dad'i be yi ba ,dama kin koma yadda kika sa ba ,Dan ya fi dad'i"


Khaltum tace "Ai kuwa da zaki karb'i sabon canjin sunan da ya fi. Dan daga yau sunan ki kenan"


Kubra tace "ko me yasa?"


Khaltum tace "Ko kin manta ke kishiya ta ce? Ke fa uwar gida na ce ,to ai ya zama dole na baki girma. To bari ma in baki labari ,ni ba bak'in da zan yi girki zan karb'a yau. Saboda haka wannan shirin duk na Alhajin Allah ne"...


Wani guntun tsaki Kubra ta ja tare da cewa " Dan Allah malama wasar ya isa haka ,kije ki d'auko mayafin ki ina jiran ki a mota"... Kubra ta fad'a tare da mik'e wa ta juya za ta fita...




"Da ma zaki yadda da abunda na fad'a miki da ya fiye miki. Dan kuwa ni ba wani chasun da zan je gaskiya a yau, ba ma yau kad'ai ba ,daga rana me kamar na yau na dena zuwa wani Abu wai shi chasu"...


Cak kubra ta ja ta tsaya. Juyowa tayi cike da tarin mamaki tace " To wai saboda me?"


"Bakomai!!!" Khaltum ta bata amsa a tak'aice sannan taci gaba da cewa


"Na yanke hukuncin daga rana me kamar ta yau ,na dena duk wani shashanci da nake yi ,na dawo na karb'i matsayi na na cikakkiyar matar aure ,Zan kuma zauna in kula da gida na da mijina ,,ina ga ta nan ne kawai zan iya zama uwa har in iya fahimtar duk wani matsala da damuwa da duk wata uwa take ciki"...


" wai da gaske ki ke ko da wasa?"" Kubra ta tambaye ta


D'aure fuska Khaltum ta yi kafin tace "Kamar ya da wasa? Wallahi da gaske nake miki. Aure na na karb'a hannu bibbiyu. Zan yi rayuwar aure cikin farin ciki da walwala kamar yadda ko wacce matar auren ke yi. Ni ma ina so in ga jini na. 'Ya'ya nake da sha'awar Inga na Haifa. Ni ma ina so in ga masu kira na da mama kamar yadda ke ma kika samu. To da ga wannan lokacin zamu iya ci gaba da duk wani sharholiya da muke yi amma a yanzu gaskiya komai ya dakata in dai dani ne, ke dai ban hana ki ba idan kinji zaki iya ga hanya ,dama a harkar na same ki ,idan yaso ni se in kula mana da gida da kuma mai Gidan..."




Wani irin shu'umin murmushi kubra tayi tare da tafa hannu, tace "Wow!!! Gaskiya kin burge ni" k'arasowa tayi har inda Khaltum ke tsaye tace "Ni dama nasan rana me kamar na yau ze zo ,nasan wannan lokacin ze zo ,shiyasa na yi wa toka hanci,,,nayi maganin abun tun kafin yazo yafi k'arfi na. Bazan hana ki zaman aure ba Khaltum ,ga ki ga gida. Amma ki sani GIDAN MISBAHU gida na ne ,kuma ni kad'ai ce matar da zan Haifa masa 'ya'ya"...


"K'arye ki ke yi wallahi. Kina zaune zaki ga yadda zan cika GIDAN MISBAHU da 'ya'ya ,Dan idan na fara zazzaga masa yara se na tabbatar na zazzage duk abun da ke mahaifa ta sannan zan tsaya. Oh saboda kin je kin juya mahaifa ba zaki sake haihuwa ba shiyasa ni ma ki ke tunanin nima zan zauna bazan haihu ba? To tun wuri idan ma mafarki ki ke ki farka"...




Wani irin kafirin dariya kubra ta fashe da shi har da su dafe ciki. Da mamaki Khaltum ke bin Kubra da ido, Dan a tunanin ta idan ta gaya wa kubra haka zata had'iye zuciya ta mutu ,amma se ta ga sab'anin hakan... Dariya Kubra ke yi ba qaqqautawa ,har se da Khaltum ta fara tsora ta da dariyar...




Se da Kubra tayi dariyar ta me isar ta sannan ta tsagaita tace " Ke duk a bahagon tunanin ki zaki haihu a GIDAN MISBAHU??? To wallahi kin makara. Dan kuma haihuwa ba ma a GIDAN MISBAHU kad'ai ba ,haihuwa in dai ta d'aukar ciki ne ki haife se dai ki gani a TV ko ki ji a labarai, amma ba dai ke ba. Ke saboda ma ki cire shakku ina so ki je asibiti na tabbata likitan ze gaya miki ni idan juya mahaifa nayi to ke babu ma mahaifar a cikin ki,,, kin kuwa San ana d'aukar ciki da juyayyen mahaifa amma har abada wacce ba ta da mahaifa ba zata tab'a d'aukar ciki ba. Idan kuma kin mu sa zaki iya zuwa duk asibitin da kike ganin sun k'ware za su tabbatar mi ki da hakan. Na kuma San gwaji ba ya k'arya"... Tana gama fad'ar hakan ya fice war ta.




"K'arya ki ke wallahi ,ba ki isa
ba. Haihuwa kuma kamar na yi na gama. Aikin banza kawai"... Ta ja wani dogon tsaki. Haka Khaltum ta yi ta bambami tana masifa...


















MUJE ZUWA๐Ÿ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...โœ๏ธ
[8/12, 8:42 PM] SIDIYA...โœ๏ธ: ๐Ÿ ๐Ÿ  *GIDAN MISBAHU*๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ ๐Ÿ 
๐Ÿ 
*_๐Ÿ (base on true life story)_*๐Ÿ 


*_๐Ÿ INTELLIGENT WRITERS ASSO๐Ÿ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)โœ๏ธ*









_BABI NA TALATIN DA BAKWAI_


*_____________________________*






















_A daren ranar bayan khaltum ta gama da kubra , sai da su ka yi hayaniya da lubabatu a sashen daddy. Duk wani haushin kubra se da khaltum ta sauke shi akan lubabatu, dan ma dai lubabatun ba kanwar lasa bace. Faษ—a su ka yi sosai akan khaltum tace ita zata karษ“a girki a daren ranar ,lubabatu kuma ta nuna sam bata san wannan zancen ba. K'arshe faษ—an har se da ya kai su hadda doke-doke ,ko wacce ta fitar wa 'yar uwar ta jini. Wanda su ke faษ—an akan shi kuma baya ma ta tasu ,dan ko kwana bai yi a gidan ba. Wannan abu ba k'aramin k'ara bak'anta musu rayuwa ya yi ba. Asuban farko ko waccen su ta kwashi tarkacen ta ta koma sashen ta cike da haushin er uwar ta..._




Har tsawon sati ษ—aya daddy be sake waiwayo gidan shi ba ,amma duk wani abun da ke wakana ya na samun labari ta hanyar Suxee. Ranar wata safiyar Asabar asabar Dr. Zaidu ya kira Haajar akan ya na so yazo su gaisa ,ya kuma sa ke duba jikin Haseena. Haajar bata musa masa ba ,tayi masa kwatance dan a tunanin ta ko bai san gidan bane.


Da yamma bayan sallar la'asariyya sai ga kiran Dr. Zaidu ya sheda mata cewar yazo yana bakin gate. Haajar ta yi mamaki sosai yadda aka yi ya gane gidan duk da unguwar ba ษ“oyayyen unguwa bace a garin sakkwato... Hijabin ta ta saka har k'asa taja hannun Auta ta rakata. Dr.Zaidu na ganin ta ya sakar mata wani irin murmushi mai ษ—auke da ma'anoni iri daban-daban. Ita ma Haajar ษ—in maida masa martani tayi, a haka har ta k'arasa bakin motar shi. Sallama tayi masa cikin muryar ta mai daษ—in sauraro ,shima ya amsa ta cike da shauk'i...


"Sannu da zuwa Dr." Haajar ta faษ—a fuske a sake


Dr. Zaidu k'ara faษ—aษ—a fara'ar dake ษ—auke a fuskar shi yayi tare da amsa mata.


Haajar tace "ya akayi ka gane gidan ,ko dama kasan gidan ne??"


murmushi Dr.zaidu ya yi tare da cewa "A'ah bansan gidan ba. kawai dai kinsan barin masoyi baya nisa ne. Bugun zuciyar ki nabi ya yi min iso har zuwa wajen ki"..


Dariya Haajar tayi tare da cewa "Kai dai ba ka rabo da abun dariya". taci gaba da cewa "ba za ka shiga ciki bane ,ka tsaya a waje?"


"A'ah! ai nan ma yayi. Asibiti zan je an kira ni akwai aiki ,nace bari in biyo mu gaisa". cewar Dr. zaidu


Haajar tace "gaskiya kuwa ka kyauta. Mun gode sosai"


Dr.zaidu yace "Haba sai kace wani abu. ya jikin Haseena ,fatar ta na samun sauqi sosai ,kuma kuna kula da shan maganin ta akan lokaci??"


Haajar tace "Jiki Alhamdulillah. Magani kuma tana sha akan lokaci".


Dr.zaidu yace " masha Allahu. hakan na da kyau. ki gaishe mun ita dakyau"


"za ta ji" haajar ta bashi amsa. Da haka su ka yi sallama ya wuce ita kuma ta koma ciki...


Duk wani motsi na su, daddy da ke gefe cikin wata mota me bak'in gilashi ya na kallon su, Wanda ba'a iya hango Wanda ke ciki sai dai na ciki yaga na waje,,,, zuciyar daddy har wani tafasa take saboda wani irin kishin Haajar da ke fizgar shi ,a gefe d'aya kuma wani irin haushin Dr.Zaidu ne ya kama shi ,musamman lokacin daya ga Haajar na masa murmushi, ji yayi kamar yabi takan su da mota ya taka su ,ko ya rage jin rad'ad'ad'i da zugin da zuciyar sa ke masa. Kan shi ya had'a da sitiyarin motar ,ya dad'e a haka a hankali ya fara samun nutsuwa ,hankalin shi ya dawo jikin shi ,kafin ya k'arasa cikin gidan...



A b'angaren Khaltum kuwa tun lokacin da Kubra ta gaya mata cewar babu mahaifa a jikin ta ta kasa samun natsuwa. Ko rufe ido tayi maganganun Kubra ne kad'ai ke yi mata yawa a k'wak'walwar kai. Gaba ki d'aya ta kasa samun kwanciyar hankali ,gashi ba ta da Wanda zata kira ya ba ta shawara. Sai a lokacin ta tuno da rabon da ta kira mahaifiyar ta har ta manta ,kuma ta sha ganin kiran ta a watannin da suka wuce amma ba ta d'auka, k'arshe ma sai dai ta katse kiran ,ba Dan komai ba sai Dan ganin da take yi kamar ta samu duniya a hannun ta. Jin dad'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login