Showing 30001 words to 33000 words out of 86229 words
Chapter 11 - GIDAN MISBAHU COMPLETE BY SIDIYA SIDI .txt
,saboda bata son duk wani abunda ze tab'arb'are albarkar auren ta ,riya da bidi'a kuma na d'aya daga cikin rukuni na farko dake hana albarkan aure. Badan Hajiya Gwaggo taso ba amma haka ta hak'ura Dan Dole ,Dan gaba d'aya se ma fara jin haushin Lubabatun tayi, a haka dai biki keta k'aratowa ,babu wani alama daga b'angarorin guda biyu da zaka gane cewa hidimar aure ake yi ,aure ne dai gashi nan yadda kasan ma auren na dole ne ,Dan komai a kaffa-kaffa da nuk'u-nuk'u ake yin shi ,ba kowa ne yasan da zancen sha'anin ba ,se na jikin su..._
*______________________*
Ranar asabar ,ya kamata daddy na gida yinin ranar be lek'a koda k'ofar gida ba ,tun bayan daya dawo sallar asuba ,Dan kusan yanzu jam'i baya wucewa shi ,saboda akwai agogo me tunatar dashi koda ya shafa'a wato Haajar.
Bayan ya dawo sallar azahar ,Gaba d'aya dashi dasu Haajar suka d'unguma zuwa gidan gonar shi ,dake ta bayan gidan shi ,Wanda akwai gate da za'a iya shiga kai tsaye ta cikin gidan shi ,tsabar tsafta da kula da wurin ke samu ba dare ba rana yasa idan ba ance maka da akwai gidan gona a wajen ba ,Abu ne me matuqar wuya ga iya ganewa sab'anin sauran gidan gonakin ,sedai d'an abunda ba'a rasa ba na yanayin dabbobi.
Tun daga bakin gate Ma'aikatan wurin keta murna da zuwan daddy, duk Wanda ya gansu da sauri yake k'arasowa yana kwasar gaisuwa da mamakin ganin daddy a wannan lokacin ,bayan lokaci me tsawo daya d'auka baya kawowa wurin ziyara ,yau kuma se gashi.
Sannu a hankali suka shiga zaga wajen suna d'an tab'a hirar yadda abubuwa suka k'ara bunk'asa a wajen , nau'i-nau'i na dabbobi indai naci ne a gida gasu nan barkatai ,kusan cikin wurin ma gaba d'aya ya yiwa wasu dabbobin kad'an dole seda aka killace wasu daga waje.
A cikin hirar da suke yi ne jifa-jifa ,Haajar ke cewa " Ni kuwa Daddy wai kana fitar da zakkah kuwa?"
Dariya maganar taba wa daddy, maimaitawa yayi "wai ma ina fitar da zakkah? To amma me kika gani?"
Itama dariya taba kanta tace "Ah to eh mana, naga gidan gonar nan cike yake da albarkatun dabbobi ,amma banga alamar ana fitar da d'aya daga ciki ba ,Banga kuma alamar ana saida wa ba. Sannan ni a ganina iya wannan ma zaka iya fitar da zakka dashi ba ,ba Dole saka d'iba wani b'angare daga cikin dukiyar kaba".
Daddy rage fara'ar dake fuskar ki yayi ,tare da cewa " A gaskiya Antyn Auta(haka yake kiran ta tun had'uwar su a gidan Hajj Jamil) bazan iya ce miki wani Abu dangane da gidan gonar nan ba, ke ni hasalima bansan komai dake gudana a gidan ba, maganar zakka ko makamancin wannan gaskiya bana yi ,ba kuma bana son yi bane ,duk lokacin dana k'udurci yin wani abun alkhairin wallahil azim se inji na kasa ,ban kuma San dalili ba ,kinga naman miya ma na gida siyan shi nake yi ,ina da me nama dake kawo mun duk wata."
Tsabar mamaki ne ya hana Haajar magana ,tace "to idan ba zaka damu ba ,inaso inyi wani Abu akai ,Amma kafin nan muje mu gana da manajan dake kula da komai na wajen".
Murmushi daddy yayi ,Dan shi harga Allah yana son Haajar a cikin al-amurran shi ,Dan hakan ba k'aramin ci gaba dake kawo masa ba. Ce mata yayi " Karki damu Antyn Auta ,na riga na miki izini da komai nawa tun ba yau ba"
"Nagode sosai" Haajar ta fad'a cike dajin dad'i
"Kar ki damu ,cancantar kice tasa hakan ,ai kinfi k'arfin hakan a waje na ,kana da kamar Wanda yaso naka ne?"
Murmushi Haajar tayi tare da cewa "Babu"
Yace "to kin gani ,Wanda yaso naka ,tamkar kai d'in yaso kacokam ,koba haka bane?" Daddy ya fad'a cike da raha
Ita dai Haajar se faman murmushi take yi tace "Hakane kam"
A haka dai suka suka k'arasa ciki wajen manager ,suna d'an tab'a hirar su na MAKAHON SO DA LINZAMI... Yayin da su suxee kuma suka tafi nasu yin a cikin gidan gonar...
Da fara'a sosai maganer ya tarbe su ,wurin zama ya basu tare da d'auko musu abun sha ,Godia Haajar tayi masa dukda basu sha ba ,kafin ta fara masa tambayoyi akan yadda suke gudanar da aikin gidan gonar. A yadda manager ya sheda mata ,Komai na tafiya yadda ya kamata daga b'angaren su ,ana kuma samun ci gaba sosai ,ribar da ake samu kuma yana tafiya ne kai tsaye ta asusun bankin Kubra uwar gidan daddy. Mamaki ne sosai ya narkar da zuciyar Haajar lokacin da manager ya ambato adadin kimanin kud'ad'en dake shiga asusun bankin kubra a matsayin riba ,Wanda ya tabbatar musu da cewar, ba a cikin wa'yannan kud'in suke biyan ma'aikatan wajen ba ,ba kuma a ciki suke siyan duk wani abun da dabbobin ke buk'ata ba. Shidai Daddy nashi ido ne ,dukda shima ba kad'an ba ya shiga mamaki ,sedai ba yada wani abun da ze iyayi akai, a karo ba farko daya fara jin Kubra ba k'aramin yaudarar shi take ba ,Wanda ya k'ara tabbatar masa da cewar bata qaunar ci gaban shi a rayuwa. Haajar ce ta katse masa tunani data fara cewa
"Duk naji bayanan ka manager na kuma fahimta, sedai za'a kawo wasu 'yan sauye-sauye Wanda ina fatar zamu samu had'in kan ka"
"Insha Allahu ranki ya dad'e" cewar Manager
Murmushi Haajar tayi tare da cewa "ze fi kyau ka kirani da Haajar shine sunana"
Shima manager murmushi yayi tare da cewa "Ayi mun afuwa Hajiya Haajar"
Ita ma dai murmushin ta sake yi masa ,sedai bata k'ara bi takan wannan jayayyar ba ,ta fara masa bayani kai tsaye akan hasashen zuciyar ta.
"Amma kafin kaji sababbin tsare-tsaren da zamu kawo ,zan so sanin nawa ne albashin ma'aikatan gidan gonar nan Gaba d'aya" Haajar ta fad'a tare da maida hankalin ta kacokam wurin manager Dan jin bayanin sa dalla-dalla.
A nutse manager ya fara mata bayani "Eh to, ma'aikatan namu dai sun kasu kashi uku ne: akwai k'ananan ma'aikata masu share share ,akwai masu kula da b'angaren abincin dabbobi akwai kuma masu kula da fannen cinikayya nayau da kullum. kamar dai k'ananan ma'aikatan mu nuna biyan su naira dubu ashirin da uku duk wata ,,, kashi na biyu kuma muna biyan su naira dubu talatin ,se mu kuma kamar ni misali ina d'aukar naira dubu Hamsin da biyu a wata... Kinji yadda lissafin yake"
Wani siririn ajiyan zuciya Haajar ta sauke tare da cewa "Naji naka, nima kuma ina son ka saurari nawa kaji dakyau ,bana so a samu wani tangard'a. Abu na farko ,inaso a datse ribar da ake samu daga shiga asusun madam ,kai tsaye kud'in su dinga shiga asusun ajiyar Alhaji MISBAHU... Na biyu; zaku samu k'arin albashi bisa ga la'akari Dana yi na cewa aikin Ku yafi kud'in da ake biyan Ku ,wannan Abu ne me kyau kuma,,, daga yau ma'aikatan mu kashi na d'aya ,zan fara taKu kenan, albashin Ku ya tashi daga hamsin da biyu ,ya koma saba'in da biyu,,, kashi na biyu kuma daga naira dubu talatin zasu dawo suna d'aukar naira dubu Arba'in da biyar,,,, se kashi na uku masu d'aukar naira dubu ashirin da ukku zasu dinga d'aukan naira dubu talatin da biyar insha Allahu zamu fara daga watannan me kamawa"
Wani irin wage baki manager keyi kamar Wanda akayi wa albishiri da aljannah, zama ya gyara sosai Dan jin sauran bayanan.
Haajar ta d'ora da cewa " bayan wannan kuma ,duk watan Allah ,a dinga ibar kaji na gida Dana turawa ,a raba guda biyar tun daga farkon layin nan har k'arshe bance a cire kowa ba daga gida me gate har Mara gate , a kuma tabbatar da angyara kafin a raba musu ,Dan muradin mu shine sanya nishad'i a zukatan bayin Allah ,,,, sannan kuma ban cire kuba ,duk watan Allan nan idan ya kama ,duk ma'aikatan dake gidan gonar nan ,babba da yaro a basa kaji biyar. Abu na kusa dana k'arshe shine a bud'e gate d'in can na baya ,a kuma buga poster na tallata Nau'ikan dabbobin da muke dasu a gidan gonar nan ,ga duk me buk'ata k'ofa a bud'e take ,ze iya zuwa ya siya ,sannan adadin cinikin da mutum ya muku akwai percentage na bonus da zaku bashi ,Wanda idan na gama tsara komai zan aiko muku ,koma inzo da kaina. Se Abu na k'arshe ,duk bayan sati biyu a dinga aikawa da kaji da kuma naman rago cikin gida. Idan ana da buk'atar wani abun bayan wannan zan yi maka magana... Amma Dan Allah manager ayi k'ok'arin wajen kiyaye wannan yanzu ,idan wani abun ya sake tasowa za'a sanar dakai.."
Godia sosai manager ya dinga yiwa Haajar kamar ze kama k'afar ta Dan tsabar murna ,sama se kusan tunda aka kafa gidan gonar nan dashi aka fara ,amma wannan shine karo na farko daya tab'a samun promotion. Wasu takaddu yaba daddy yasa hannu ,kafin ya musu rakiya ,har waje... Ranar kusan duk ma'aikatan gidan gonar da farin ciki suka kwana na abun alkhairin da Haajar tayi musu... Manager be kawo komai a ransa ba ganin Haajar ta kawo sauyi a gidan gonar lokaci d'aya, musamman daya ganta tare da mamallakin wurin wato daddy, da farko ya d'auka ko lawyer ce saboda yadda take magana da cikakken yak'ini ba tsoro, amma kuma daga bisani yanayin yadda take bada umurni kai tsaye ga Daddy a zaune be hana ba yasa yayi tunanin ko matar Daddy ce, Dan bayan sun fito yake yiwa daddy Allah ya sanya alkhairi, shidai daddy amsa shi kurum yayi ba Dan yasa me yake nufi ba...
Shi karan kanshi Daddy gaba d'aya ya rasa Wani irin farin ciki yake ciki ,Dan babu abunda Haajar tayi guda d'aya Wanda be burge shiba ,kai komai ma tayi burge shi take yi ,musamman yadda cikin d'an k'ank'anin lokaci take ta k'ok'arin kawo wa al-amurran shi canji ,kuma ALHAMDULILLAHI yana ganin nasarori daci gaba...
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/1, 2:26 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π
π π π π
π π
π
*_π (base on true life story)_*π
*_π INTELLIGENT WRITERS ASSOπ_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)βοΈ*
*ASSALAMU ALAIKUM. INA TAYA MASOYANA DA D'AUKACIN AL-UMMAR MUSULMAI BAKI D'AYA MURNAR ZAGAYOWAR BABBAR SALLAH, DA FATAR MUN YI SALLAH LAFIYA, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN...*
_BABI NA ASHIRIN DA SHIDA_
*___________________________*
_Babu yadda Hajiya Gwaggo bata yi da daddy ba akan yazo d'aurin aure, amma shi Sam wannan auren baya gaban shi ,hasalima baya wani ji a jikin shi wai shi za'a d'aura wa aure. Ana gobe za'a d'aura auren ,suna zaune a parloun shi ,shida su Haajar ,yake sanar dasu zancen auren. Ba Haajar ba hatta su suxee jin Abu sukayi kamar saukar aradu. Had'a baki sukayi wajen cewa "Aure kuma Daddy?"..._
_Daddy yace " ni kaina ba'a son raina za'a yi wannan auren ba ,sedai muna fatar Allah yasa zuwan ta ya zame mana alkhairi. "_
Tab'e baki Haseena tayi tare da cewa " Wallahi daddy ni na gaji da wannan auren da ke nema maka ,kai me ze hana ka nema da kan ka ,toma da kake maganar Allah yasa zuwan ta ya zame mana alkhairi ,ni fa gani nake duk wacce zata zo koda da alkhairin ne baza ta kai mana kamar Anty Haajar ba ,mu Allah ma da ba'a wani tsira yi maka wannan auren ba ,kawai da ka barmu munyi zaman mu a haka"...
Har cikin ran daddy yasan abunda Haseena ta fad'a ba k'arya a ciki ,amma shima ba yadda ya iya ne ,cewa yayi " Banda abun ki haseena ba dole in k'ara aure Ba ,tunda ba nida wacce ke Sona ,kuma da kike wani maganar Anty Haajar, Anty Haajar ai ba matata bace ko?" ,,, da biyu daddy yayi wannan maganan Dan gaba d'aya yi yake yana duban Haajar...
Wani irin fad'uwar gaba Haajar taji ,,, kauda maganar tayi da cewa "to in banda abun ki haseena,, kin tab'a ganin ka auri mutum badan kana son shi ba? Kuma ma har ka yadda ka zauna dashi ,kaji zaka iya ne ai. Sannan da kike wani zance na ,ni ai ba matar daddyn Ku bace ,kuma tafiya zanyi"... Aikuwar maganar se a kunnen Auta dake gefe tana wasa ,da sauri ta k'araso inda suke zazzaune ta dafa kafad'ar Haajar tare da cewa
" Anty Haajar wai tafiya zakiyi?"
Kowa juyowa yayi yana kallon ta. Murmushin dole Haajar ta kakaro tare da Shafa kan Auta tace "Eh mana Shukra "
Auta tace "To amma dai tare zamu tafi ko?"
Haajar tace "A'ah kina gidan Ku ,nima kinga gidan mu zan tafi!"
Nan fa auta ta shiga rero kuka ba girma ba azziki ,kan kace me kukan har ya soma sakar mata zazzab'i. Da sauri Haajar ta janyo ta jikin ta "Na shiga aljannah na kasa fita ,Shukra Dan nace zan tafi shine kike wannan kukan?"
Gyad'a kai Auta tayi ido jawur. Haajar tace "to na fasa tafiya saboda ke ,idan ma zan tafi to tare zamu tafi kinji yarinyar kirki".
Rumgume Haajar Auta tayi tare da sakin wani ihu " Yeeeeeeeeeh! Anty Haajar tace tare zamu tafi" daga nan bata k'ara bi takan wasan ba ,zuwa tayi ta lafe kan cinyar Haajar ,Haajar d'in na bubbaga bayan ta kan kace me bacci ya kwashe ta ,se wani ajiyan zuciya take sauke wa ,kamar wacce akawa dukan tsiya. Mamaki ne ya kama daddy Dan shi be tab'a tsammanin Shak'uwar dake tsakanin Haajar da Auta yakai haka ba...
Tsabar takaici haseena tace "To wai daddy meze hana ka auri Anty Haajar d'in ta zauna damu, kana ganin dai abubuwan da take mana da kulawar da muke samu a wajen ta ,Wanda ko mahaifiyar da ta haife mu bata yi lokacin mu ba balle har mu samu wannan. Shine me kake tunani idan Anty Haajar ta tafi tabar mu? Ya kake tunanin auren da zakayi ze iya maye mana gurbin ta? ,nidai inaga gaskiya daddy ya kamata ka zauna kayi tunani akai. Nifa se nake ganin Anty Haajar d'in ce ma bata dace damu ba"... Haseena ta fad'a cike dajin haushin Daddy, Dan ita akan haajar gaba d'aya yanzu lefin shi take gani.
Kallon Suxee daddy yayi ,alamar kina jin abunda haseena ke fad'a? Gyad'a masa kai tayi tare da lumshe fararen idanuwan ta alamar gamsuwa da zantuttukan Haseena.
Kafin daddy yace wani Abu Haajar tayi saurin katse zancen da cewa " Dan Allah ka manta da maganganun su ,kasan har yanzu yara ne. Muna tayaka murnar auren da zakayi Daddy, Allah kuma ya tabbatar da alkhairi." Ta k'arashe maganar tare da mik'ewa tsaye ta ciccib'i Auta ta d'ora ta a kafad'ar ta, sannan tace masa "seda safe". Tana kai aya ,tayi ficewar ta.
Suxee da haseena ma tashi suka yi tare dayi masa seda safe suka bi bayan Haajar.
Kusan daddy sumar zaune yayi ,Dan gaba d'aya ya lura yaran shi sun fi damuwa da Haajar sama dashi ,sannan bawai son Haajar bane baya yi , A'ah kawai yana tunanin yadda ze tunkari Haajar ne da zancen so, zuciyar shi na raya mishi Haajar bazata tab'a son shi. Wani d'an siririn tsuki yayi tare da Furta wa a k'asan zuciyar shi "Suna gani ma har sun fi ni son ta ne ,duk son da suke mata be kai kwantankwacin Wanda nake mata ba ,balle har ya kamo k'afar shi"... Haka dai daddy ya koma kamar wani sabon zararre a wannan Daren ,kasa bacci yayi ,kwana yayi yana sak'e-sak'en yadda ze b'ullowa al-amarin, se wuraren asuba bacci yayi awon gaba dashi...
Washe gari da safe, Su Haajar basu zo breakfast a sashen daddy ba kamar yadda suka saba ,a gefen su sukayi ,sedai suxee ta kai masa nasa ,kuma koda taje ta tarar yana bacci ,bata yi k'ok'arin tashin shi ba ,ajiye masa kulolin abincin kawai tayi ta k'ara gaba. Daya fito, dukkan alamu sun nuna masa ba'a nan suka yi breakfast ba ,alama ta d'aya daya gane kuwa shine rashin jin k'amshi na tashi ,Dan 'ka'ida ne kafin su fara cin abinci se an gyara wurin ,k'amshin turaren wuta na tashi kamar baza'a mutu ba. Alama ta biyu kuma ganin kula biyu daya yi akan dinning yasan nashi ne kawai dan ba haka suka saba jera abincin ba... Ya kusa mintuna goma a tsaye yana k'are wa wurin kallo ,kafin daga bisani yaje ya zauna ya fara cin abincin, se dai kwatakwata baya jin gard'in a bakin sa ,haka yake cin abincin kamar yana tauna magani ,tsabar ba haka ta saba zama yaci abincin ba ,har cikin ranshi yake kewar rashin ganin su a yanzu, amma daya yi wani tunani ,se kawai ya dake ,tare da cewa "dani kuke zancen ,bazan tab'a Neman Ku ba ,Dan kanku zaku dawo"... Yana kammala cin abincin shi ,yayi ficewar shi zuwa sabgogin shi...
A ranar yasa aka gyara d'aya daga cikin sassan dake gidan ,tare da zuba duk wani abun buk'ata ,Dan ya musu waya akan kar su zo masa da komai, sedai sashen be kai girman nasu Kubra ba ,sannan shi iya na k'asa ne flat babu bene...
Da daddare aka kawo Amarya. Tun ranar da aka kawo amarya daddy be sake sa su Haajar a ido ba ,abincin ma da yake tunanin ko zasu aiko masa tun a ranar farko shima shiru babu alama ko samatan hakan.
Wani abun takaicin ma, duk hasashen da daddy ke yi shine za'a kawo masa amarya ya amayar da shak'uwar sa ,amma ina sedai hak'ar shi bata cimma ruwa ba...
_Ku biyo ni Dan jin dramar da daddy da lubabatu a ranar da aka kawo ta_πππ»
MUJE ZUWAπ
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...βοΈ
[8/2, 2:06 PM] SIDIYA...βοΈ: π π *GIDAN MISBAHU*π π
π π π π π π