Showing 24001 words to 27000 words out of 114314 words
Chapter 9 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
fita za kay?, yaran nan fa har yanzu ba a buɗesu ba", Baba ya gyara wuyan rigarsa yace "sai aka yi yaya da ba a buɗesu ba?", tace "daman naga ko sallar asuba basu yi ba gashi rana ta fito", yace "Au daman kina damuwa idan basuyi sallah ba?", ta fara ƙinƙina tace "dan girman Allah mal kayi haƙuri, a yi musu afuwa", Baba ya gyaɗa kai yace "za a yi musu, amma in tambayeki mana?", tace "toh mal", yace "waye uban Sa'adatu da Maimuna?", ta saki baki sai kuma tace "kaine mana mal", yace "ni mijinki ne ko A'a?", tace "kai mijina ne mana", yace "idan kina so igiyar aurenki ta cigaba da rayuwa to ki gyara tarbiyyar ƴaƴanki, idan kina son ƴaƴanki to ki gyara tarbiyyarsu, kar Sa'adatu ta sake barin gidan nan, Maimuna karta sake fita da daddare, Nabilah ta fito da miji na aurar da ita", Maama ta gyaɗa kai tamkar tsohuwar ƙadangaruwa tace "tom", ya ciro muƙulli daga aljihunsa ya bata yace "ki buɗesu idan na dawo ina son ganinsu", Maama ta karɓi muƙullin tana harararsa ƙasa-ƙasa tace "toh" ta fita a ɗakin, ruɓaɓɓen kichen ɗin ta buɗe Sa'adatu da Maimuna suka fito wujiga-wujiga, zafi ya dakasa ga kuma jikinsu da yayi tsami.
★Nurain ya fita masallaci sallar la'asar, bayan ya dawo ya tsaya suna gaisawa da Garba da yake bawa flowers ruwa, Nurain yace "wace motar ka wanke min?", Garba yace "farar na wanke maka", Nurain yace "Ohk, ka amso min takalmana daga wajen polish", Garba ya dukar da kai yace "toh alhaji ƙarami", Nurain ya wuce ciki, har zai zauna a balcony sai ya fasa dai ya shiga main palour ya zauna a kujera, remote ya ɗauka ya canza channel, bayan few minutes ya miƙe ya shiga kitchen ya buɗe fridge ya ɗauki Apple guda uku ya ɗora akan plate ya dawo palour ya zauna yana ci, Noor ta shigo palourn tace "Yaya Mami is calling", yace "Ohk", ya miƙe ya ɗauki plate ɗin Apple ɗinsa ya shiga part ɗin Mami, Mami ta ringa kallonsa har ya zauna a kujerar kusa da ita, ya ɗan rame kaɗan amma kuma fuskarsa babu wata damuwa, Mami tace "where is your phone?", ya shafa kansa yace "Ta fashe ne", tace "Ohk, toh dan ta fashe shine ba za ai amfani da ita ba, saika zauna haka ba waya", yace "zan siyo wata ne", tace "good do that fast", yace "yeah" tace "when are you resuming work?", yace "next week, daman na ɗauki leave na two weeks", ta gyaɗa kai tace "Son, why not go towards Khausar", yace "Khausar?", tace "yess Khausar"..........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{14...}
Nurain ya ajiye Apple ɗin hannunsa yace "Mami i don't get you", Mami ta ɗauki remote ta danna mute tace "Nurain, ga Khausar nan ƴar uwarka, me zai hana ka nemi aurenta, kasan yarinyar nan kuma kasan iyayenta, duk wani qualities da ake so a wajen mace Khausar na dashi, asali, ilimi, home training and what majority of men are after to, beauty right?, she's beautiful..", ya sauke ajiyar zuciya yace "but Mami I don't have such feeling for her, i only see her as my lil sister", tace "Alright, tinda kace haka shknn, you may leave", ta ɗauki remote ta canza channel snn ta buɗe volume, Nurain dai bai sake cewa komai ba yana nan zaune ya cigaba da cin Apple ɗinsa, bayan 20minutes ya miƙe yana jan shirt ɗinsa ya nufi door, har ya murɗa handle Mami ta kira sunansa, ya juyo yace "Na'am", ta nuna masa plate ɗin da ya shigo dashi, ga apple nan guda daya da bai cinyeba akai, ya shafa kansa ya dawo ya ɗauki plate ɗin ya fita, Mami ta bisa da kallon gefen ido. room ɗinsa ya wuce yayi abinda zai yi snn ya sakko down stairs hannunsa riƙe da car key, compound ya fita ya wuce parking space, farar motarsa ya buɗe ya shiga, saida yayi warming snn ya gangara ya fita daga compound ɗin bayan mai gadi ya buɗe masa gate, a daidai wani katafaren wajen siyar da waya yayi parking, ya kashe motar ya buɗe door ya fita, ya shiga building din da akay molding ɗinsa da kirar waya, few minutes ya fito hannunsa riƙe da ƴar leda, yana komawa gida aka kira sallar magrib, yayi using tap din compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo daga masallaci ya bude car ya ɗauki ledar ya wuce ciki, direct a room ɗinsa yayi branching, ya ɗauki wayarsa da ta tashi daga aiki akan mirror, sim cards dinsa ya cire snn ya farke sabuwar wayar da ya siyo, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayar tana booting bayan ya danne switch dinta, bai ɗaukesa wani lokaci ba ya gama setting wayar, kira ne ya shigo wayar, Nurain yayi murmushi ganin me kiran nasa video call ya ɗauka, Farooq ne cousin dinsa da yake Russia, Nurain yace "why the call dude?", daga ɗayen ɓangaren Farooq da ya sha wata jibgegiyar sweater yace "I can't reach you since last week, what was the problem?", Nurain ya jingina da allon gado yace "look, wnn wintern ta garin ku ai bazata bari kayi reaching mutane ba", Farooq ya ɗaga gira yace "decline, look for another way", Nurain yace "Ohk", Farooq yace "ya Mutan 9ja?, ya su Mami?", Nurain yace "All lafiya", Farooq yace "looks like you lost some weight Dr, ko dai Ruqayyah bata iya girki ba, i forgot to asked about her, how is she?", Nurain yace "she is great", Farooq yace "good", Nurain yace "when are you coming?", Farooq yace "nanda 2weeks insha Allah, kuma a gidanka zan fara sauka naci girkin Amarya Ruqayyah", calmly Nurain yace "Ruqayyah is not my wife and she will never be, i don't think ma zaka tarar dani a Nigeria", yadda yayi maganar without joke yasa Farooq fahimtar something has happened, Farooq yace "bro what...", Nurain ya katsesa yace "don't ask me, zan gaya maka later, after my heart healed", Farooq yace "Ohk, amma ina zaka da kace bazan sameka a Nigeria ba?", Nurain yace "India", Farooq yace "Ohk, ynxu ka yarda zaka koma ka ƙaro karatun kenen", Nurain yace "yeah", Farooq yace "Ohk, i understand, i gotta go, good night", Nurain yace "Ohk, good night" ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya.
★Da daddare Baba yana zaune a ɗakinsa Maama tayi sallama ta shigo, tana daga bakin ƙofa tace "mal kace kana son ganin yaran nan?, toh su shigo yanzu ko sai anjima?", Baba yace "ki kirasu yanzu nan, kema kizo", Maama tace "tom" ta juya ta fita, ɗakinta ta shiga tana kallon ƴaƴan nata tace "kuzo inji Babanku", Maimuna ta tashi daga kan kayan wanki tace "na shiga uku na, Maama dan girman Allah kice nayi bacci, wllh har yanzu harbin kunamar nan bai bar jikina ba", Maama tace "A'a dole ki taso, ko baccin ma ki kai tashinki zanyi", ta kalli Sa'adatu da Nabilah tace "kunji dai me nace ko?, ku taso", Sa'adatu ta miƙe tana gunguni ta fita tsakar gida, Maama tabi bayanta, ɗakin Baba suka shiga suka zauna, suna zama Nabilah ma ta shigo, Maimuna ce ta shigo a ƙarshe, tana ƙoƙarin zama Baba yace "karki zauna Shiga wajen Umma ki kiramin ita da kuma Hajara", Maimuna ta kalli Maama, Maama ta ɗauke kanta, haka Maimuna ta fita ta tsaya a ƙofar ɗakin Umma tace "Baba yace kizo keda Hajara", bata jira cewarsu ba ta koma ɗakin Baba ta zauna kusa da Nabilah tace "na kirasu", Maama ta haɗe rai tace "mal naji kace a kira waccar matar da ƴarta, to mene dalili?, mene haɗinsu da zamanka da ƴaƴanka?", Baba yace "Toh haka dai nace a kirasu", Maama bata sake cewa komai ba, Umma ce tayi sallama ta shigo Hajar biye da ita, suka haɗa ido da Maama wacca take harararta ƙasa-ƙasa, Umma ta zauna tace "mal gani", Hajar ta zauna kusa da Umma, Baba ya ƙare musu kallo duka yace "Nabilah!!", Nabilah tace "Na'am", Baba yace "acikin samarinki ki fitar da wanda yayi miki kice masa ya fito, aurar dake zanyi, idan kuma baki da wanda kike so toh zaɓi yana wajena, na baki nanda sati biyu..", Nabilah ta marairaice fuska tace "Baba aure fa..", ya katseta yace "Ba cewa nayi kiyi magana ba, tashi ki ban waje", Nabilah ta miƙe ta fita zuciyarta na zafi, Baba ya juya kan Sa'adatu yace "Sa'adatu!!, Sa'adatu!!, Sa'adatu!!", Sa'adatu ta haɗe gira tace "Na'am", Baba yace "sau nawa na kiraki?", tace "Uku", ya gyaɗa kai yace "gargaɗi na ƙarshe kenan da zan miki, zunubin ki mai kauri ne, wllh wllh wllh tsattsauran mataki zan ɗauka akanki, tashi ki bani waje", Sa'adatu ta miƙe ta fita zuciyarta na tafarfasa, Baba yana gamawa da Sa'adatu ya juya kan Maimuna yace "ke kuma duk abinda Sa'adatu tayi shi kike yi ko?, kin ƙi makaranta kin zaɓi yawon dare ko?, toh ranar Litinin Mu'azzam zai mayar dake makaranta, ɓacemin daga gani", Maimuna ta miƙe ta fita ranta na soyewa, wai makaranta za'a mayar da ita. Baba ya dubi Hajar da take zaune kusa da Umma yace "saura ke Hajara, uwar rashin haƙuri, Nabilah, Sa'adatu duk yayyenki ne, Maimuna ce sakuwarki kuma itama ɗin gaba take dake, karki sake yi musu rashin kunya", Hajar tace "toh Baba", yace "toh tashi ki tafi, Allah yayi miki albarka". Maama ta hura tukubar hancinta tace "suma Allah yayi musu Albarka su da ba ƴaƴan so ba", ɗakin ya rage daga Baba sai Maama sai kuma Umma, Baba yace "Rabii", Maama ta miƙe tace "Allah ya tashemu lfy, ba sai kace komai ba mal, ai naji abinda kace da safe" ta fice a ɗakin tamkar zata tashi sama. Rayuwar gidan ce ta canza zuwa wani fannin daban, babu ruwan kowa da kowa, yau sati guda kenan ba ai hargitsi ba, sosai Maama tayi ladaf ta hana ƴaƴanta fita, daman suma sun tsorata da Baba shiyasa ko ƙoƙarin fitar ma basuyi ba. Sa'adatu ta leƙa kwanon ɗumamen tuwon da Maimuna ta shigo musu dashi matsayin breakfast tace "chab wllh bazan ci tuwo ba", Maimuna tace "ga koko nan", Sa'adatu ta zabga tsaki ta ɗauki jakarta ta ciro kuɗi ta saka hijab ta fita tsakar gida, Maama da take riƙe da kofin koko tace "ina zaki Sa'adatu", Sa'adatu tace "ba nisa zanyi ba, wajen mai shayi zanje na siyo biredi da shayi, ni bazan ci tuwo ba", Maama ta zaro ido tace "kin san dai Babanku ya hanaki fita ko?", Sa'adatu tace "ai ba ko wace fitar yake nufi ba, nifa nan nan wajen mai shayi zani ba wata uwa duniyar ba", Maama ta girgiza kai tace "A'a, kawo kuɗin na leƙa waje idan na samu yaro sai ya siyo miki", Sa'adatu ta miƙawa Maama duba ɗayar data rage mata, Maama ta bata kofin hannunta tace "shigarmin dashi ciki, bari na aika yaron", Sa'adatu ta amshi kofin ta koma ɗaki, Maama tayi hanyar soro kamar da gaske, tana zuwa soro ta laɓe a bayan ƙofa ta ɗaure kuɗin a haɓar zaninta ta koma ciki, Sa'adatu tace "Maama har an samu yaron", Maama tace "Eh yanzu zai kawo miki, ɗan gidan Munkaila ne", Sa'adatu tace "yawwa, ga kokon ki". Maama ta zauna tana kurɓar kokonta tana kallon Maimuna da Nabilah da suke kwarfa lomar tuwo. Shiru-shiru yaro zai kawo Shayi da biredi amma maƙatau ba labari, yunwa sai kartar ƴar hanjin Sa'adatu take, Sa'adatu ta leƙa soro a karo na bakwai ta dawo ciki tana gunguni ta kalli Maama dake bakin murhu tace "har yanzu fa yaron bai kawo ba, yunwa nake ji", Maama ta tura mata kwanon tuwon data rage tace "ki rage hanya da wnn kafin ya dawo", Sa'adatu tace "tuwon ne fa bazan ci ba", Maama ta gyaɗa kai tace "yo ba yunwar kike ji ba, shknn saiki jira shayin". ƙarfe sha biyu da rabi Sa'adatu ta fito ta wafci kwanon tuwon da Maama ta bata ɗazu tace bazata ci ba, loma huɗu tayi masa ta tashi dashi, ta ringa suɗe hannu tana muzurai don ko tsarga mata beyi ba.
★Momy ta Shiga palourn Daddy hannunta riƙe da tray, sallama tayi, Daddy dake zaune kan kujera shallow in thoughts ya amsa mata, ta ajiye trayn akan center table kana ta shiga making tea, thick tea ta haɗa cikin Mug ta dire a gaban Daddy, ta buɗe warmer da ta shigo da ita mai ɗauke da chips, plate ta ɗauka ta zuba chips ɗin with omelette egg a gefe, ta matsa ketchup a wani ƙaramin bowl, ta jera in front of Daddy kana ta koma kusa dashi ta zauna, a hankali ya fara cakar chips din da fork yana dangwalar ketchup yana ci, kaɗan yaci ya ajiye fork ya ɗauki tean ya fara sipping, keenly yace "have you eaten?", tace "I'm not hungry", yace "Tom", calmly tace "Alhaji yarinyar nanfa bamu san inda take ba har yanzu, yaufa kwana sha biyu babu ita babu dalilinta..", yace "so", tace "do something", yace "something like what?", Momy was speechless kawai kallonsa take, ya ajiye Mug din hannunsa yace "lokacin da Ruqayyah ta saka ƙafa ta fita na sani ne?, ajikin lettern da ta ajiye ma tace kar mu nemeta zata dawo, to kinga kuwa me zai sa na ɓata golden time ɗina wajen nemanta..", Momy tayi ajiyar zuciya tace "har yanzu fa ba a samun wayarta, ai dole hankalina ya tashi", yace "toh maza ki ɗauki haramar saka damuwa a ranki, wai yarinya nan ba da kanta ta fita ba, dan ba a sameta a waya ba ai ba wata matsalar bace, tana sane ta kashe wayar, what Ruqayyah did really hurts me, idan tanada wata damuwar why not ta sameki ta gaya miki, and she can talk to me if there was any problem, am i not a free Father?, plxx don't ruin my mood this morning akan maganar Ruqayyah", da haka Daddy ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, Momy tabi bayansa da kallo sai kuma ta tashi ta fita a palourn, bedroom ɗinta ta shiga ta ɗauki wayarta tayi dialing numbern Kulsoom, saida ta kusan yankewa snn tayi picking, Momy tace "saiki ringa nesa da wayarki", Kulsoom tace "Momy ina kitchen ne", Momy tace "toh kina jina Daddy yaƙi saurarata, anjima da yamma sai muje police station mu shigar da report", Kulsoom tace "toh Momy, har yanzu babu wanda ta kira", Momy tace "Eh", Kulsoom tace "toh ina gama abinda nake zan shirya na taho", Momy tace "toh shknn saikin zo" ta datse kiran.
★Hajar ce zaune a ɗakin Umma tare da Zainab, Zainab tace "kefa ƴar rainin hankali ce wllh, yanzu saida kika tattagoni, ƙiri ƙiri kin ƙi hawa online", Hajar tace "kuma inada data isasshiya wllh, duk sati ya sayyadina sai ya sakomin credit da data", Zainab ta taɓe baki tace "toh ai kin kyauta da kike masa asara, idan baki yi amfani da ita ba ai tayi expire a wofi", Hajar tace "ya mutan gida?", Zainab tace "lfy wllh, kin san kwa me ya kawoni", Hajar tace "inafa zan sani, ai sai kin shaƙamin", Zainab tayi ƙasa da murya tace "kin tuna wnn katafaren gidan da kika rakani?", Hajar tace "katafaren gida?", Zainab tace "Eh mna, wanda muka je har kika yiwa wani mai mota rashin kunya..", Hajar tace "Au, wnn mutumin da bai san darajar ɗan Adam ba, kinsan kwa na sake ganinsa?", Zainab tace "A ina?", Hajar tace "A hospital, likitane", Zainab tace "okay, yanzu dai kina jina?, ɗan gidan ne yace na bashi digits ɗinki, wllh ya takuramin, ni kuma naƙi bashi nace saina sanar dake..", Hajar tace "yawwa gwara da baki basa ba..", Zainab tace "sbd me?", Hajar tace "toh meya haɗana dashi da zaki bashi digits ɗina?", Zainab ta harareta tace "malama karki raina min hankali, kinfa gane me nake nufi", Hajar ta langwaɓar da kai calmly tace "So, kinsan dai akwai wanda muke tare dashi, kuma har yazo gida", Zainab tace "yess nasani, toh ai ba baiko akai muku ba", Hajar ta juyar da kanta tace "kya yi kuma". can dai Zainab ta miƙe tace "toh zan tafi", suka fito tare da Hajar zata rakata ƙofar gida, Zainab ta yiwa Umma sallama suka wuce hanyar soro tare da Hajar, Sa'adatu ta fito daga bayi ta tsaya tana kallon Hajar da Zainab da suka nufo hanyar fita, Sa'adatu ta dire butar hannunta, daman yau ranta a ɓace yake neman wanda zata huce akansa take, Zainab ta marairaice tace "dan Allah Hajar ki sauraresa, zan bashi numbern..", Hajar tace "zanyi tunani.", Hajar ko kallon inda Sa'adatu take ba tay ba, Zainab tana zuwa wucewa Sa'adatu ta saka mata ƙafa. Zainab ta faɗi a ƙasa, Sa'adatu ta nuna Hajar da yatsa tace "kema baki isa ki kawo ƙawayenki gidan nan ba su fita lfy", Hajar da zuciyarta take tafarfasa ta durƙusa ta kamo Zainab ta taimaka mata ta miƙe tsaye, Hajar ta tsugunna kamar zata ɗakko jakar zainab dake ƙasa, ta saka iya ƙarfinta ta kwashi ƙafafuwan Sa'adatu ta nakata da ƙasa, a lokacin Baba yayi sallama ya shigo gidan, ya tsaya yana kallon Hajar.......✍️
💛 HAJAR 💛
by ~Feenerh_feeche~
{15....}
Wani ihu Sa'adatu ta kurma tace "Hajar kashe ni za kiyi?, nifa ƴar uwarki ce", Hajar ta kasa cewa komai sbd kallon da Baba yake mata, Sa'adatu ta miƙe tana dafe bayanta tace "wllh ta karya min ƙashin baya", Baba baice komai ba ya wuce cikin gida, Umma ce tayo hanyar soro sbd ihun da ta jiyo, kaciɓus sukay da Baba tace "sannu da zuwa Malam", Baba yace "yawwa", ya wuce ƙofar ɗakinsa, ya ciro keys a aljihunsa, ya buɗe padlock ɗin ya shiga, Sa'adatu ta cafki wuyar Hajar tana ƙunduma mata ashar, Hajar tace "wllh badai nawa ba, dalla malama sakeni niba jaka bace da zan haɗa ƙashi dake", Sa'adatu tace "keee anƙi a sake kin, kiyi abinda za kiyi", zainab dai sai raba idanu take tana cewa Hajar kyaleta dan Allah, Umma tana zuwa ta tarar da Sa'adatu ta cakumi Hajar, ta fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Sa'adatu dake wuyan Hajar tace "me ya haɗaku?", Sa'adatu ta cakumo Umma sannan ta danna ihu da ƙarfi tace "Maama ku fito, gasu nan sunyi min rubdugu