Showing 3001 words to 6000 words out of 114314 words
Chapter 2 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
ce ta turani na amso mata wani saƙo shine nabi wrong way, har car na ya samu matsala, you know yesterday anyi ruwa toh wani ruwa na faɗa a street ɗin, i wasted my time there looking for a solution", tace "ohk, Allah ya kiyaye", yace "Ameen, har yanzun ma coffee mai sanyi zan sha?", juya idanunta tayi ta miƙe ta duba wrist watch ɗinta tace "Byee, zan shiga surgery da Doctor Mansoor, see you later after the surgery.." ta fita ta rufe ƙofa. wasa ya farayi da yatsun hannunsa yana juyi a kan kujera idonsa a lumshe yana tunanin the girl he encounter with this morning, her face look so innocent but she's stubborn, ƴar gidan gini.........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{3...}
Ƙarfe sha biyu na rana Dr Uthman ya shiga surgery with his well trained team, shi ƙwararren likita ne da ya karanci ɓangaren thorax da duk wani abu that is located in the chest region, alhmdllh surgeryn da Dr Uthman yayi was successful, yana dressing room yana cire kayan da yayi surgery dasu Dr Marwan ya shigo wanda shine yayi masa first assistance, Dr Marwan ya buɗe lockern kayansa yace "gaskiya Dr surgery nan yayi kyau, gashi patient ɗin ya daɗe da ciwon amma kuma komai yayi kyau", Dr Uthman yace "everything goes well saboda aikinku mai kyau my team members, idan babu ku ai komai bazai yi daɗi ba", Dr Marwan yayi murmushi yace "still dai kaine 70 percent na success ragowar percent ɗin aka raba mana", Dr Uthman yace "Marwan next week inada surgery amma bazan samu damar zuwa ba, kaine za kayi heading sai Khaleel yayi first assistance", Dr Marwan yace "sure Allah ya kaimu", Dr Uthman ya mayar da lab coat ɗinsa ya wuce office, Halima tace "welcome Dr akwai patient da yake jiranka, zan iya shigo dashi??", tsadadden wrist watch ɗinsa ya kalle yace "am off amma ki shigo dashi tinda ya riga yazo", tace "yes sir" ta ɗauki landline ta kira reception tace "hello patient ɗin da yake jiran Dr Uthman ya shigo yanzu" ta katse kiran. babu jimawa patient ɗin ya shigo office ɗin, Dr Uthman ya kallesa yace "referral ne??", patient din yace "Eh" ya miƙa masa wata takarda cikin envelope, glasses dinsa ya ɗauka ya kwamawa idanunsa kana ya karanta takardar tas yace "mal shu'aibu jeka ka kwanta a wancan gadon" yayi masa nuni da gadon da yake a can edge of the office, mal shu'aibu ya kwanta a gadon, Dr Uthman ya ɗauki stethoscope ya isa bakin gadon ya fara dubasa, bugun zuciyarsa ya fara ji sannan yace "mal shu'aibu kaja dogon numfashi", mal shu'aibu yayi yadda aka umarce sa, bayan Dr ya gama duk wani gwaje-gwaje ya koma mazauninsa yayi rubutu ya basa yace "tests ne guda biyu, ayi su kafin nan da sati mai zuwa sai a kawomin", mal shu'aibu yace "nagode likita" ya karɓi takardar ya fita. Dr Uthman ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern Nurse Ruqayyah wacca yayi saving da Love, ya jingina da kujera ya kara wayar a kunne. Nurse Ruqayyah tana zaune a nurse station taji wayarta na vibrating cikin aljihun rigarta, da sauri ta zarota ganin mai kiran tayi murmushi ta kara a kunne tace "my Dr badai harka fito ba??", daga ɗayan side din Dr Uthman yace "yeh na fito, yanzu ma zan wuce, yaushe zaki wuce gida?", tace "ohk, zan yiwa wata da za'a yiwa CS Anesthesia ne kafin na wuce gida", yace "ohk, byee Love", tayi murmushi tace "byee" ta katse kiran, Nurse Jidda da take kallonta tace "gaskiya Ruqayyah kin afka, yanzu fa shekara biyu kenan kuna tare da Dr Uthman, wai yaushe za muga cigaban wannan soyayyar ne??", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta taɓe baki tace "kwana nan zamu girbi soyayyarmu inshallah, kinsan dai cewa iyayena sun san dashi tinda ya tura magabatansa sunje nema masa izinin zance, toh tin lokacin suka so su bada kuɗin aure, amma Daddy yaƙi amincewa yace sai mun fahimci juna tukun, toh dai tin daga lokacin ba a sake maganar kai kuɗi ba, daman bai gama shiryawa ba yana so ya ƙarasa gidansa kuma ya zama rigid a business ɗinsa, to alhmdllh komai dai ya zama settle gida ma har an saka masa padlock ya gama komai, and his business shima alhmdllh, last week yake gayamin cewa zai turo magabatansa a kawo kuɗi sannan asaka rana, though shi baya so asaka sama da three months, amma nasan Daddy bazai amince ba saboda he is not ready, toh kinji yadda muke ciki", Jidda ta jinjina kai tace "ohk mashallah, Allah ya tabbatar da Alkhairy", Ruqayyah tayi murmushi tace "Ameen".
★Umma na zaune akan kujera tana zuba ƙullun kulele cikin fafaffun gwangwanayen da aka shafesu da Manja, Sa'adatu ce ta fito daga ɗakin Maama taci kwalliya, wata riga da skirt ta saka na material mai rawa, kayan sun ɗameta sosai da kyar take tafiya ga takalmi mai uban tsini a ƙafarta, mayafin da ta saka dashi gara babu, fuskar nan ɗaɗau tasha hoda da mai, Baba ya fito daga ɗakinsa ya kalleta sama da ƙasa yace "ina za kije Sa'adatu?", Sa'adatu ta zumɓuri baki tace "Baba daman bikin wata ƙawarmu ake, yau ne ɗaurin aure", yace "toh wa kika tambaya da zaki fita a haka?", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "na gayawa Maama ai", Baba ya sake kallon shigar jikinta yace "koma ɗaki babu inda zaki", ta tsaya tana ƙunkuni da murguɗe-murguɗe, ya zabga mata carbin hannunsa a baya, ya sake ɗaga hannu zai zabga mata ta ruga da gudu tana gurɗewa ta afka ɗakin Maama, Nabilah da take laɓe a jikin labule ta tuntsure da dariya tace "Baba ya matsa lamba", Maama ta miƙe ta fita waje daman kaf tana jin abinda ya faru, Baba ya juya zai koma ɗaki Maama tace "haba mal ya za ai ka daddage ka daki yarinya budurwa haka, inaji dai ta gaya maka na bata izinin fita shine kake mata wannan dukan", ya juya ya kalleta yace "indai ni na haifi Sa'adatu to ban amince ta fita a haka ba", Maama ta ɗaga murya tace "Toh ai ba kai kaɗai ka haifeta ba malam, nice nan uwar Sa'adatu kuma ta samu amincewa ta", da karfi Maama tace "ke Sa'adatu maza fito ki kama gabanki, Allah ya tsare", Sa'adatu daga ƙuryar ɗaki tace "Tom Maama gani nan fitowa", Baba yace "Rabi ki cigaba da ɓata tarbiyyar ƴaƴanki, yaran nan ko makaranta sunƙi zuwa, ba arabi ba boko, wallahi muddun baki canza ba wataran zakiyi kuka da idanunki", Maama ta zabga uban salati tana tafa hannaye tace "Malam da sanyin safiyar nan kake ƙoƙarin yimin baki, kana kiramin kalmar kuka da idanuna, na shiga uku ni Rabi yau na gamu da jafa'i", Baba ya girgiza kai yace "ƴaƴanki bazasu taɓa koyi da ƴar uwarsu Hajara ba, yarinya mai son karatu", da gudu Nabilah ta antayo daga ɗaki tace "Baba Allah ya tsaremu muyi koyi da wannan tabbatacciyar shegiyar yarinyar", sai a lokacin Umma ta tanka tace "ke karki sake kiran ƴata tabbatacciyar shegiya na gaya miki", Maama ta rangaɗa wata shegiyar guɗa tace "ahayye, da Mu'azzam da Hajara duk shegu ne, da tsohon cikin Hajara da Mu'azzam yayayye kika zo gidan nan", Umma tace "ga ubansu nan, kuma shi yasan ƴaƴansa ne", Maama ta tafa hannaye tace "laha'ila ha illallahu, kuji fa wai Adamu ne uban Hajara da Mu'azzam, yau naga inda ake liƙawa mutum ɗan shege ta ƙarfin tsiya, wallahi ƙarya kike faɗima Sabra ce kaɗai ƴar Malam amma wallahi Hajara da Mu'azzam saidai ki nemo musu uba", Baba ya nuna Umma yace "faɗima karki sake cewa komai, koma ɗakinki", Umma ta rufe ƙullun kulelenta ta shiga ɗakinta, Sa'adatu kam tunda taji tsakar gida ya fara ɗaukar harami ta rungume cogen takalminta ta fita sum-sum tamkar munafuka tayi soro, Baba ya kalli Maama yace "Allah ya shiryeki Rabi idan kinada rabo" ya koma ɗakinsa, ai Maama saida ta gama kumfar bala'i ita kaɗai sannan ta koma ɗaki, Nabilah tace "Maama kinga har yanzu Maimuna bata dawo ba sai kace wacca aka aika wata duniyar", Maama ta zabga tsaki tace "inajin ta tafi sabgar gabanta".
★Washe gari da misalin ƙarfe biyu da Rabi na rana, Hajar ce ta fito tsakar gida sanye da uniform ɗinta na islamiyya, daga bakin rariya ta hango Naseer yana goge kaushi tace "yaya ina wuni", yace "lafiya Hajar makaranta za'a tafi", tace "Eh, Sabra nake jira", yace "toh Allah ya bada sa'a", sai kuma ya miƙe ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin Maama ya kwalawa Maimuna kira, saida ya sake kiranta sau biyu sannan ta fito tace "yaya gani", yace "ke bazaki fito ki tafi makarantar ba", tace "yaya wace makaranta kuma??", ya daka mata tsawa har saida ta firgita yace "islamiyya mana", ta fara inda-inda tana mutsuttsuka hannaye tace "daman yau bazan je ba, Maama bata nan, Nabilah da Sa'adatu suma duk sun fita, wa zan barwa ɗakin Maaman??", yace "shiga ki sako kayan makaranta ki wuce ki tafi", tace "toh yaya wai wa zan barwa ɗakin..", kwalla mata mari yayi har saida ta bugu da bango yace "duk abinda kuke agidan nan kawai kallonku nake, yaushe rabon da kije makaranta, zaki wuce ko saina tattaka ki", a guje Maimuna ta afka ɗakin Maama tana gursheƙen kuka, ta buɗe Ghana most go ta ɗakko zumbulelen hijab ɗin islamiyya wanda rabonta dashi wajen wata huɗu, yaci uban squeezing yana warin ajiya, ta lalubi inda Maama take ajiye padlock ta ɗauka ta fito, Naseer yana tsaye a bakin ƙofar bai tafi ba ya kalleta ganin squeezing ɗin da hijab ɗinta yayi yace "ƙazama", Maimuna ta kulle ɗakin ta rufe fuskarta da hijab ta cigaba da kuka, Naseer yasa ƙafa ya kwarfeta ta baje a ƙasa yace "miƙe munafuka, ai Maama ce ta kyaleku kuke yin abinda kukaga dama, wallahi daga yau kika sake fashin makaranta saina tattaka ki mara kunya", da gudu tayi waje tana kuka, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana tiƙar dariya a zuciyarta tace (Allah shi ƙara), Sabra ta fito suka kama hanyar islamiyya. Hajar tana zuwa ajinsu Abubakar Siddiq wanda shine ajin sauka ta tarar har an fara bitar Al'qurani tinda sunyi sauka, saida aka gama bitar sannan Zainab ta taɓo Hajar tace "me yasa jiya bakizo ba?", Hajar tace "kinsan shirye-shiryen NECO muke, to jiya akai mana online registration", Zainab tace "nima ai naje registration ɗin kuma nazo islamiyya", Hajar tace "nida na kusa samun matsala, ai ina gaya miki saura ƙiris ayi NECOn bana ba ni", Zainab tace "A saboda me??", Hajar ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Zainab ta zabga mata harara tace "dalla malama gafara can, wai da kika ƙi haƙura kika shafa masa kwatamin mene ribarka?", Hajar tace "zuciyata tayi sanyi aii", Zainab tace "ki ringa haƙuri ƙawata dan Allah", Hajar tace "uhmm nidai akai min saina rama wallahi", Zainab tayi murmushi tace "mutuminki fa ya shigo ajin nan yafi sau ashirin jiya", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa kenan??", Zainab tace "wa kika sani bayan ya sayyadi Nura..", Hajar ta juyar da fuskarta tana murmushi..........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{4...}
Biyar da rabi na yamma ya sayyadi Nura ya shigo ajin yi musu kiran suna, idonsa akan Hajar ya fara sauka wacca ta sunkuyar da kanta tana duba abinda babu a jaka, Addu'a ya fara yi musu kana ya fara kiran suna, duk wanda aka kira sunansa sai ya tashi ya tafi gida idan kuma kasan kayi fashi sai ka jira ai maka hukuncii, ajin ya ɗaɗe ya rage daga Hajar sai ya sayyadi Nura, register ya rufe ya maida hankalinsa gareta, a hankali yace "Hajara mai yasa jiya kika yi fashi", Hajar ta haɗiyi wani yawu ba tare da ta kallesa ba tana wasa da hannunta cikin hijab tace "ya sayyadi online registration naje na NECO kuma ban dawo da wuri ba", ya sauke ajiyar zuciya yace "toh saiki dage da karatu kinji??", tace "Insha Allah", yace "har yanzu dai Nursing ɗin kike son karanta", a karo na farko da ta ɗago fararen idanunta sai kuma tayi sauri ta mayar dasu ƙasa tace "Eh", yace "toh shknn, indai kin ɓaro marks Insha Allah zaki tafi Nursing School", tace "insha Allah zanyi ƙoƙari", ya ringa kallonta sai kuma ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yace "lokaci nake jira na nemi izini wajen Baba na ringa zuwa wajenki a gida, iya ganin da nake miki a makaranta yayimin kaɗan gaskiya, ace kullum idona baya ci ya ƙoshi", ta janyo hijab ɗinta ta rufe fuska murya can ƙasan maƙoshi tace "ni gida zan tafi", yayi murmushi mai sauti yace "toh taso ki tafi", a hankali ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita a ajin ba tare da ta bari ta kalli wajen da yake ba. a gate ta tarar da zainab da take jiranta suka rankaya suka tafi gida. da daddare Hajar na zaune akan tabarma tana cin tuwo, umma ta fito daga ɗaki da mafici a hannunta itama ta samu guri ta zauna tace "kai gaskiya yau akwai zafi inajin hadari ne a garin", Hajar tace "ɗazu ma naga ana walƙiya, ina sabra ita bazata fito tasha iska ba sai sanƙarau ya kamata?", umma tace "tayi bacci kinsan daga anyi sallar isha'i take kwanciya". Maama tana daga can ƙofar ɗakinta tare da Maimuna wacca ta kawo mata ƙorafi akan Naseer. garin zafi ake shiyasa suka firfito tsakar gida shan iska, Hajar ta miƙe ta kai kwanon da ta gama cin abinci wajen wanke-wanke ta ɗebi ruwa tana wanke hannunta, Sallamar Baba ta janyo hankalin kowa garesa, Hajar tace "sannu da zuwa Baba", ya amsa yana miƙa mata ɗaya daga cikin ledar da ya shigo dasu, Maimuna tana ganin ya miƙawa Hajar leda ta miƙe zaune daga kan cinyar Maama tace "Baba sannu da zuwa", yace "yawwa zoki karɓar muku naku", Maimuna ta taso da sauri ya bata leda ɗaya ya wuce ɗakinsa da guda tinda ledojin uku ne. Hajar ta kaiwa umma ledar ta samu guri ta zauna ta tanƙwashe ƙafa, Umma ta buɗe leda, karfashe ne mai zafi ga kuma yaji a gefe, umma tace "kai Allah ya saka da alkhairy ya ƙara buɗi, sako hannu muce Hajara", a hankali Hajar take ƙurmushe karfashen saboda tana sonshi. Maimuna kam tana buɗe ledar ta kalli Maama tace "Chaɓ, daman tinda naji ƙarni nasan wannan abun ne", Maama ta warce ledar tace "idan bazaki ci ba ki barshi" ta ɗauki guda ɗaya ta luƙa a baki ta ƙurmushe, Nabilah ta fito daga ɗaki da fitilar wayarta rakani toilet ta haska kifin hannun Maama tace "me kuke ci ne naji ƙayau ƙayau ana tauna?", Maama tace "karfashe ne idan zaki ci, yanzu babanku ya shigo dashi", Nabilah ta taɓe baki tace "ni kam bazan ci ya farfasan baki ba, kina ganin abu sai kace ƙanzo, Sa'adatu nake jira nasan bazata shigo gidan nan hannu rabbana ba", Maimuna tace "wallahi nima ita nake jira", Maimuna tana rufe baki saiga sallamar Sa'adatu, hannunta riƙi-riƙi da ledoji, da sauri Maimuna ta tarota ta amso ledojin, Sa'adatu ta zauna kan tabarma ta fige ɗankwalin kanta tace "wash nagaji, Maama yau kam ai banyi dare ba ko??", Maama ta kawar da ledar karfashen da take ci ta suɗe hannu tace "Eh yau ba kiyi dare ba ƴar albarka", Sa'adatu ta warce ledojin hannun Maimuna tace "cewa nayi ki buɗe, ai kya bari na buɗe da kaina", Sa'adatu ta ciro takardar tsire da ƙatuwar robar ice cream tace "Maama ga naki", ta ciro wata takardar da kuma robar ice cream ta miƙawa Nabilah tace "keda Maimu". ta kwashi ragowar ledojin ta shiga ɗaki. hannu baka hannu kwarya sai kace mayatattu suke cin tsiren nan suna yaɓa ice cream a baki, Maama sai habaici take zubawa faɗi take "haihuwa tayi min rana, ina zaune akawomin tsire da ƙanƙara mai madara na more, wasu kam sunyi asara kullum saidai a kawo musu takarda ace anyi ƙoƙari a jarabawa", Nabilah ta danna tsire a baki tace "yo daman shege yanada wani amfani ne, ai amfanin shege bai wuce baƙin fenti ba". Hajar ta miƙe ta zazzagi omo ta wanke hannunta ta shiga ɗaki, muddin ta zauna a tsakar gidan nan to kwa tabbas za a iya tashin hankali domin kwa ba haƙuri ne da ita ba musamman ma aka taɓo mata uwa. Washe gari da wuri Hajar ta dawo daga school saboda ranar juma'a ce, umma ta tarar tayi shirin fita, Hajar ta ajiye jakarta tace "Umma fita zakiyi ne??", Umma tace "ta dole ce Hajara, gidan Jamila zanje na duba jikin Hafsa, kar abin ya zama shiririta na shiga wata sabgar ban dubata ba", Hajar tace "to bari nayi sauri na shirya saimu tafi tare", Umma ta girgiza kai tace "da ke nayi niyyar zuwa amma hakan bazai yiwu ba, inada ragowar kulele da ban siyar ba wajen ta dubu, daman ranar juma'a sai bayan masallaci akafi ciniki, ga Sabra nan ta tayaki zama bazan daɗe ba Insha Allah", Umma ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "Hajara karki biyewa kowa ayi tashin hankali dake kinji", Hajar ta jinjina kai tace "Allah ya tsare sai kin dawo..". Hajar tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa roba-roba, ta dasa kujera a tsagar gida tana yankewa Sabra farce, Sabra ta zille ƙafa tace "dan Allah Adda karki yanke ni", Hajar ta ɓalla mata harara ta fuzgo ƙafar tace "da can da nake yanke miki na taɓa yankar ki ne??". wani yaro ne yayi sallama siyar kulele, Sabra taje ta amso kuɗin Hajar ta zuba masa a kwanon da ya kawo, Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko canji ta bata ta kai masa tare da kulelen, saida yaron ya tafi ta tina cewa bata zuba masa yaji ba, tasan aiken iliya mai awo ne tinda taga kwanonsa ne, indai shine sai ya dawo yace a zuba masa yaji, ta zauna ta ƙarasawa Sabra yankar farcenta, tana gama mata ta fita wasa ita kuma ta shiga bayi, tana toilet ta jiyo yaron ya dawo yanata ɓurari wai a zuba yaji a kulele. Sa'adatu ta fito tsakar gida da kayanta haɗin bauta, zani jaka a tsaye sai wata tsohuwar riga Tshirt