Showing 84001 words to 87000 words out of 114314 words

Chapter 29 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5289

"Ameen" kafin ya fita, bayan minti goma da fitarsa Mami taga jikin nata har yay sauqi, ta koma baccinta kuma babu zazzaɓi a jikinta, Mami ta kashe musu fitila kafin ta bar room din, washe gari kam jikin Hajar saidai nace alhmdllh cause kamar ba ita bace ta cikin dare jiya, har ɗaki aka kawo mata breakfast, daga wayewar gari zuwa yanxu da ake maganar 10 na safe Mami ta shigo dubata sau uku, Noor kuma ta wuce school tinda ranar Monday ne.


★Hakima Ruqayyah ta ajiye wayarta a kan mirror bayan ta gama tura text message, ta gyara wuyan rigar kayan baccin jikinta wando da riga kafin ta fita daga ɗakin nata, kitchen ta shiga ta fara preparing breakfast, omelette roll da toasted bread saita tafasa black tea mai kayan ƙamshi, tana gama haɗa breakfast din ta ɗakko Oat meal ta damawa kanta, ta zuba isasshen powdered milk da sugar kaɗan, ta zuba 4pieces na omelette roll ta ɗauki oat meal din ta fita, a palour ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta kai plate da cup en kitchen ta wanke, ta koma room enta ta shiga wanka, ta fito ta tsaya gaban mirror ta gama shafe shafenta tana humming song da tayi setting enta matsayin ringtone na dearest, well ironed uniform ɗinta ta ɗakko ta saka, as usual ta ɗora black Abaya saman uniform en, tsaf ta shirya snn ta ɗauki wayarta ta zura a jaka ta fita ta rufo ɗakin, room din Momy ta shiga don ta sanar da ita ta fita, Momy ta amsa gaisuwar da ta mata tace "kuma kika ce yau night ne dake?", Ruqayyah tace "Eh, exchanging nayi da wata collegue dita ita tanada abinda za tay da safe", Momy tace "ohk, toh sai kin dawo", Ruqayyah tace "uhmm, nayi breakfast na ajiye muku a kitchen", Momy tace "Okay", Ruqayyah ta miƙe zata fita, har ta kai ƙofa Momy ta kirata, dawowa tayi ta zauna, Momy tace "kinsan dai lokacin da Daddy ya ɗebar miki ya kusa ƙarewa ko, ya maganar Dr tinda kince kun sasanta idan ya dawo daga tafiyar komai zai daidaita, ya ake ciki ya dawo en ko bai dawo ba, don na gaji da kareki a wajen Daddy zanyi shiru na zuba idanu ya aura miki Daudan tinda dai bashi da wata matsala...", Ruqayyah ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tace "Momy, har yanzu bai dawo bane, daga ya dawo shknn, dan Allah ki cigaba da bawa Daddy haƙuri, wllh bana son Dauda bayan mata biyu da yake dasu gashi gajere kamar a kife da kwando, kuma fa ɗingishi yake wllh sai a zata gurgune..", tini idonta ya kawo ruwa, Momy ta taɓe baki tace "Au lallai Ruqayyah har kinada bakin kushe wani ko, toh ke da kike ba nakasasshiya ba ai ba finsa kikai wajen Allah ba, toh kwa ki san inda dare yayi miki wllh, haba kin bi kin nace sai Dr, Doctorn da kika tozarta kika gudu kika barsa ranar ɗaurin aure, daman ni jinki kawai nake da kike cewa ai kun sasanta, ai ba zuciyar kare ne dashi ba da zai yarda dake bayan cin amanar da kikai masa, wani chance en sau ɗaya yke zuwa a rayuwa, ki tsaida hankalinki ki fuskanci reality, ki na dai da manema ba babu ba...", Ruqayyah dai gaba ɗaya guiwarta ta saki, ta goge kwallar da ta zubo mata, Momy tace "you may leave na gama dake", Ruqayyah ta tashi tana goge idonta tace "zan biya gidan ya Kulsoom", Momy tace "kar kiyi dare", tace "tom" kafin ta buɗe ƙofa ta fita, slowly take tafiya a street en gidansu tana saƙa da warwara a zuciyarta har ta fita babban titi, ta tsayar da Napep ta gaya masa inda zai kaita, har cikin asibitin ya shigar da ita, ta sauka ta buɗe jaka ta bawa mai napep kuɗinsa, a hankali take tafiya tana kallon parking spaces, wani irin harbawa zuciyarta tayi, hope din da take dashi ya zagwanye gami da tsiyayewa ta guiwarta ganin babu motar Dr Uthman a wajen parking ensa, direct hanyar office ensa ta nufa, tayi zaman jira kan silver chair dake ƙofar office en nasa, nace wasa farin girki hakima Rukky, almost one hour tana jira amma babu alamarsa, ta shiga aikin da ta saba na kiransa da tura masa text message, ta ciro handkerchief ta fara share hawayen dake sauka idonta, ji tayi ance "A Nurse are you okay?", ta ɗago kanta sukay ido huɗu da Khaleel, tayi fake smile tace "Oh Dr am fine..", ya tsuke ido yace "are you sure?", tace "sure", ya kalli ƙofar office en Dr Uthman yace "but what are you doing here all alone?, aren't you suppose to be in nurse station?", ta sake yin wani fake murmushin tace "yeah, yanzu nake shirin tafiya can en", yace "ohk see you later.." da haka ya bar wajen ya barta zaune, ta dafe kanta a hankali tana tunanin what next, ga dukkan alamu dai wanda tazo Hospital en dominsa bazai zo ba, daman yau sai dare take da duty amma sbd shi ta ƙuma uban sammako, gashi kuma bai zo ba, tamkar wacca aka zarewa spine haka ta tashi ta bar bakin office en, wani irin nauyi zuciyarta tayi mata, haka ta sake saɓa ta fito daga asibitin, ta tsari napep zuwa gidan Kulsoom.


★Sosai Hajar ta ware, she really appreciate yadda mutanen gidan suke they were so humble and caring, duk abinda take buƙata an mata shi, lunch ma har ɗaki mai aiki ta kawo mata, ga Mami wacca take dubata akai akai, da daddare Hajar ta idar da sallahr magrib knn tana wrapping prayer mat Noor ta shigo, tace "Alhmdllh jiki yay sauqi, ai zaki iya fitowa ko?..", Hajar ta ajiye darduman kan stool ta girgiza kai a hankali, Noor ta jingina da jikin ƙofa tace "na shi gangaɗe...", da farko kamar Hajar ba zata tambaya ba sai kuma tace "me ya faru?", Noor ta shafa forehead dinta tace "wllh iron lady ce, nace mata kin samu lfy amma duk bayan minti talatin saita ce nazo naga ya kike, wai ƙafarta ke ciwo bazata iya tafiya sosai ba, ta hanani ma kallon stuff ena gashi i hate watching it on phone or computer, i prepare watching it on TV...", Hajar dai ba tace komai ba, Noor tace "dan Allah kizo muje ta ganki in yaso saiki dawo, Allah bazata barni na huta ba", Hajar dai tayi shiru ba ta san me za tace ba, ita kam bata son ma ta ɗara ko ina, kawai dai dagewa take tana so ta zama comfortable which was very hard on her, ta kalli expression en fuskar Noor wacca take kallonta da pleading eyes tana jiran amsa, da kyar ta iya cewa "tomm", Noor tayi clapping hands enta wanda hkan ya bada sound kaɗan tace "thank you, muje ko, tana ganin dai you are fine saiki dawo abinki, rigimar tsufa ne..." da haka ta buɗe ƙofa, Hajar ta gyara wuyan dogon hijab din da ta idar da sallah kafin tabi bayanta, ba kowa a huge palourn Mami, itama Mamin ta shiga bedroom enta daman idan ta shiga sallar magrib bata fitowa sai after isha'i, Hajar tayi surveying palourn da idanunta tana biye da Noor, Noor ta buɗe ƙofar fita daga part en kafin suka wuce long corridor suka fita main palour, nan ma dai saida Hajar tayi surveying ensa, wani nervousness ne ya rufe ta, ta fara tambayar kanta to wane ne wnn abokin na Baba ita dai bata sansa ba, tinda take bata taɓa ganin palour mai girma da ƙawatu kamarsa ba, ita bata tsaya ƙarewa gidan kallo ba jiya da aka kawota, ko lokacin sallah da agogon room enda take ciki take amfani cause bata gane dare da rana sbd komai na gidan equal yake, safe rana dare duk akwai wuta, Noor ta wuce hanyar da zai leading zuwa part en Hajiya, Hajar dai was following her like one living statue, buɗe ƙofan part en Hajiya Noor tayi da sallama, Hajiya dake zauna kan lallausan carpet ta miƙe ƙafafuwa ta kalli door tace "waye anan?", Noor ta matsa gefe Hajar ta shigo da sallama, Hajiya ta sake cewa "nace waye anan...", Noor ta tsugunna gabanta ta ɗauki glasses enta ta saka mata tace "da me yasa kika cire glasses dinki..?", Hajiya tace "yo idon ne yake min ƙaiƙaiyi shine na cire zan sosa, ban kai ga sosawar ba naga inuwa akaina", Noor ta dubi Hajar tace "ƙaraso mana", Hajar ta ƙarasa shiga cikin palourn ta zauna can ƙarshen carpet, Hajiya ta bita da ido, Hajar tace "ina yini..", Hajiya tace "wace ce wnn?", Noor tace "Au keda glasses din ma idon naki sai a slow, wacca fa kika takura naje na dubo miki ce fa", Hajiya tace "O oho matar Usuman din ce?", Noor tace "daman nace miki taji sauqi, toh gashi dai yanxu idonki ya gani", Hajiya tace "matso kusa mana ƴar nan saiki raɓe can ƙarshen buzu sai kace wata bare ba ƴar gida ba", Hajar ta matso a hankali ta shigo kan carpet en sosai ta sake tisa gaisuwar da tayi mata, Hajiya ta amsa tana dashare wawulon bakinta tace "tubarkallah masha Allah, yarinya ta saɓe jiki yayi kyau alhmdllh", Noor tace "ai na gaya miki", Hajiya tace "ita ta zaunar dani a gidan nan, yo inba larura ba mai zaisa na baro mijina na zo nan na zauna, hankalina ne yaƙi ya kwanta wllh tin jiya da naga yadda muka kaita asibiti, ace ana kawo mna yarinya sai kawai ta kwanta ciwo sai kace an kawota wajen mayu, kinga kwa gobe in Allah ya kaimu saina kira Umaru yazo ya ɗaukeni na koma gidan tsamiya..", Noor ta haɗe gira tace "nan ma ai gidan tsamiya ne", Hajiya tace "nan fa ɗaya, ba miji a gida ta ina ya zama gidan tsamiya", Noor ta miƙe tana kallon Hajar tace "bari nayi leading enki ki koma ko..?", Hajar ta gyaɗa kai, Hajiya tace "ta koma ina kuma, rabu da ita anan tayi zamanta tinda ba tace ta gaji ba, haka kurum ki ƙugata a ɗaki", Noor ta koma kan kujera two sitter ta zauna, remote ta janyo ta canza channel, tayi murmushi don yanxu ne ake taken next Cdrama da take so, ta fara cin coconut macaroons da ta ajiye nan tare da popcorn, Hajiya ta micincina idanu tana kallon Tvn tace "ji mutane sai kace aljanu, fuska kamar anyi ɓarin filawa, anya ma kwa akwai jini a jikinsu?", Noor dai an riga da an bada amanna ba ta ji ma sosai, a hankali Hajar dake wasa da laushin carpet ta ɗaga kai ta kalli TV, ko minti goma ba ai da fara film en ba ta ji ya ɗan birgeta sbd margic da ake zubawa, Hajiya sai mita take a mayar mata da makka, Noor kam tayi mata shiru tinda ita ta nace saita zauna a wajenta don haka sai ta gama kallonta kuwa, Hajiya ta saƙa hannunta ƙarƙashin kujerar da ta jingina da ita ta ciro kwalbar man zafi (Aboniki), ta buɗe kwalbar ta shiga lakuta tana laftawa a sangalale, tini Noor ta toshe hanci sbd har yaji ya bulale palourn, saida ta lafce ƙafufuwanta tasss da Aboniki, sai shining suke da sheƙi, can wajen yatsun ƙafar ne kawai bata shafawa ba sbd hannunta bazai kai ba kuma bata iya tankwashe ƙafar, ta lakuto wani lafcece kafin ta dubi Hajar da already idonta ya kawo ruwa sbd yaji tinda tafi kusa da ita tace "shafa min daga nan saman makyangyamar..", ba musu Hajar ta miƙa hannu Hajiya ta lakuce mata uban man Aboniki a tafin hannu, a hankali Hajar tayi rubbing dinsa a palm kafin ta fara shafesa a toes en Hajiya da suke a yamushe kuma a tattare sbd tsufa. juyowar da Noor za tay kenan taga Hajar na aikin da ita da Aysha ke gudu, Noor tayi murmushi ta kuma toshe hancinta ta cigaba da kallonta, door aka buɗe aka shigo, scent ensa ne ya mamaye palourn, yay sallama yana ƙarasa shigowa sai kuma ya tsaya cak, Hajar ta ɗauke hannunta daga legs en Hajiya gami da mayar dashi cikin hijab ta juya ta cigaba da kallonta, and that gave him the full access to saw her face completely, and he realized her, automatically ya juya ya fita a palourn tare da banging door......✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_ feeche


{40..}
Hajiya tabi ƙofar da Nurain yayi banging da kallo tace "ikon mai duka, cewa nayi fa zanyi magana da kai shine zaka zo ka nunamin wata fuskarka da na rasa dalilin sauyawarta ka fita", Hajar ta runtse idonta tana haɗiyar wani kwallo da ya tsaya mata a throat, ta wutsiyar ido ta gansa shine ta maze, gaba ɗaya taji ta tsani zaman nan en so take ta koma inda ta fito, a hankali ta miƙe tana jan fingers, Hajiya ta dena sababin da take ta ɗaga kai tana kallon Hajar tace "lafiya kika miƙe sai kace wacca aka zubawa mugun mintsili?..", Hajar tayi kasa da idonta tace "zanyi sallah ne..", Hajiya ta nuna mata qibla tace "buzun tsaftatacce ne, kiyi sallar ki", Hajar dai tayi shiru don ba haka taso ba, ita so take ta bar nan din kawai, Hajiya tayi kasaƙe tana kallonta ganin bata kalli qiblar ba kuma ba tada niyyar kabbara sallar da tace za tay, Hajiya ta dubi Noor tace "ƴar nan, kee", ina Noor sai blushing take tana tura coconut macaroons a baki, gaba ɗaya mind dinta na kan TV, Hajiya ta ɗauki trow pillow ta wurga mata, sai a snn Noor ta juyo tana wuri wuri da ido tace "mene ne iron lady?", Hajiya ta mata daƙuwa tace "wnn wane irin masifar kallo kike ne, nayi ta miki magana amma kin saki baki da hanci kin zubawa wasu kodaddu idanuwa a talabijin", Noor ta ajiye coconut macaroons da take ci tayi folding hands tace "Allah ya baki haƙuri, banji bane", Hajiya tayi tsaki tace "kinga ƴar nan matar Usuman tace zatay sallah nace tayi anan tinda buzun tsaftatacce ne amma taƙi yi, toh inajin dai tsaftarsa ba tay mata ba, ki tashi ki ɗakko mata wani acikin ɗaka sai ta ɗora akan wnn tayi sallar", Hajar tayi ƙasa da murya kanta a ƙasa tace "A'a zan koma can din ne sai nayi sallar a can", Noor ta tashi tace "alright muje na rakaki..", da haka Noor ta nufi door Hajar tabi bayanta walking slowly, Hajiya ta bisu da kallo tana taɓe baki tace "Au wnn aka aurawa Usuman, da gani bata son mutane, ta zauna a cikin mutane amma taƙi ta gwammace ta ƙursum sa a ɗaki, Allah dai ya kyauta...". har sun kama hanyar part din Mami sai kuma Noor ta dakata, ta juyo tana ƙarewa main palourn kallo, taji scent dinsa amma kuma bata gansa ba, yana zaune a edge of executive two seater yana operating Mac phone, Noor ta buɗewa Hajar ƙofar shiga part en Mami tace "go ahead am coming", Hajar ta shige ciki, Noor ta koma main palourn ta isa kusa dashi ta tsaya daga gefen kujerar tace "Yaya ina yini?", ciki ciki ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba kawai danne dannesa yake jikin Mac phone, tace "Yaya don Allah zan turo maka da project dina ka duba min kafin nayi submitting na gama..", sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta kafin ya mayar da idonsa kan abinda yake yace "Ohk, Allah yasa ba shirme kike rubuta ba, don naga yanzu ba kya karatu sai kallon shirme kika iya, keep this in front of your mind idan shirme kika rubuta am going to punish you", ta sosa forehead dinta tace "shknn ma, yaya Farooq zan turawa ma kar nayi stressing dinka", yace "kafin 9pm naga mail dinki in my inbox Noory", ta gyaɗa kai a hankali tace "Sure Yaya" ta bar wajen ƙirjinta na bugawa, tasan dai bata rubuta shirme ba cause saida tayi research kafin ta rubuta komai, amma dai dole sai an mata gyara, ta shiga part en Mami, a tsaye ta tarar da Hajar a corridor ta jigina da bango, Hajar tayi saurin juyar da kanta gefe tana goge cheeks dinta, Noor taso ta fahimci cewa kuka take amma kuma demon en gabanta shine ya kwashe mata tunani, har ɗaki ta raka Hajar kafin ta fito, direct kuma room dinta ta wuce tayi plugging Lap top dinta a charge. Hajar ta idar da sallah, kwanciya tayi kan carpet ta lulluɓe da babban hijab din da tayi sallar, tara da rabi Mami ta shigo dubata, Mami ta dafa forehead dinta to feel her temperature, Hajar ta buɗe idonta don ba bacci take ba, tunani ne iri iri ya cunkushe mata a brain, Mami tace "ki dena kwanciya kan carpet ga bed nan, ko headache en ne?", Hajar ta tashi zaune tana girgiza kai tace "A'a ya dena ciwo", Mami tace "toh alhmdllh, ya baki ci abincin da aka kawo miki ba, ko ba kya son sa?", Hajar tace "na ƙoshi, naci da yamma", Mami tace "Okay, toh kisha drugs enki sai ki kwanta ko, if you need anything just let me know kinji", Hajar ta gyaɗa kai a hankali, Mami na fita Hajar ta shiga bathroom, tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin da Noor ta bata, like yesterday night wnn ma ba tayi bacci ba, saidai wnn daren lafiyar ta lou kawai dai ta kasa rintsawa.


★Hajiya ce zaune bisa 3 sitter a great room din Abba, tayi shirinta tsaf da shigar asun da asun na atamfa, ga ɗaurin kallabi irin na tsofaffin nan mai santi, ta zubawa Abba dattijon idanunta da suka sha farin kwalli tace "Muntari nidai ban fahimci zaman Usuman a gidan nan ba, ya ɗauki matarsa su koma gidansu tinda ta warke sumul abinta, tinda dai waraka ta sauka to banga amfanin zama a nan ba, su koma gidan su kar aje a ƙuma musu sata, don wnn uwar dukiyar da aka laftawa gidan ɓarayi sai su shigar musu tinda banga alamar mai gadi ba, amma kuma dai naga wayar shokin zagaye da gidan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login