Showing 9001 words to 12000 words out of 114314 words
Chapter 4 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
tace "Adda nagani", Sabra ta zaro ido tace "lalala chaɓ", Hajar ta sauke rigarta ta kalli umma tace "Umma ki bani kuɗi na siyo brush nawa ya faɗi a gefen kwata", Umma tace "kije wajen babanku ki karɓa", Hajar tace "tom, daman yanzu zanje na gaishesa" ta fita waje, a ƙofar ɗakin Baba ta tsaya tayi sallama sannan ta yaye labule ta shiga, ta durƙusa tace "Baba barka da safiya, an tashi lafiya??", Baba yace "lafiya ƙalou Hajara Allah yayi albarka", tace "Ameen Baba", yace "yaushe zaku fara jarabawar??", tace "banda wannan satin wani mai zuwa zamu fara", yace "toh Allah yasa a fara a sa'a, saiki dage da karatu", tace "Tom Baba" sai kuma ta fara murza hannunta tace "Baba dan Allah ka tahomin da brush idan ka fita aiki nawa ya lalace", ya karkace ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa yace "gashi ki sayi brush ɗin, ragowar canjin kuma kiyi kuɗin makaranta dasu na gobe", tasa hannu biyu ta karɓa tace "nagode" ta miƙe zata fita daga ɗakin, Naseer ne ya yaye labule ya shigo fuskarsa duk kumburin bacci, Maama ce ta kunno kai ta wani rirriƙo Sa'adatu, Hajar dai ta koma gefe tana kallon ikon Allah sai kuma tace "yaya ina kwana??", Naseer yana murje fuskarsa yace "lafiya" ya samu guri ya zauna, Maama ce ta tattagosa wai tana buƙatar ganinsa a ɗakin Baba, ita dai Hajar ta kama gabanta ta samfe a ɗakin, Maama ta zaunar da Sa'adatu itama ta zauna tana kallon Baba tace "barka da safiya mal, yaudai ga ɗanka nan na kawo maka shi kayi masa katangar ƙarfe da dukar min ƴaƴa, ni nayi masa magana yaƙi ji, kalli kaga yadda ya sauyawa Sa'adatu kamanni, Maimuna ma tana ɗaki ya kwaile mata baya, toh gashi nan dai kayi masa magana wataƙila kai yaji maganarka, nidai nan gaba idan ya sake dukar min ƴaƴa kamar haka to wllh saina kwashe masa albarka kaf ehee", Baba ya kalli Sa'adatu ya juya ya kalli Naseer yace "kai ka daketa ??", Maama ta ɗaga murya tace "yo ƙarya zan masa kake tambayarsa, kayi masa gargaɗi kawai mal", Baba yace "dakata Rabi ki bari na gama magana, Naseer ina jinka me ya faru", Naseer ya gyara zama yace "Baba yarinyar nan kullum akan hanyar fita take daga gidan nan da shigar da bata dace ba, da dare sai kaga an ajiyeta a wata ƙatuwar mota, kuma motar da take kawota daban-daban ce, nayi mata kashedi amma taƙi ji shine jiya na zaneta", Sa'adatu ta fashe da kuka tace "Baba wllh ƙarya yake min, ai Maama tasan inda nake zuwa wajen ƙawata kuma ni ba a taɓa sauke ni a mota ba a napep nake dawowa", Naseer yace "ni nake miki ƙarya?", Maama tace "yo yarinya da bakinta kana ƙoƙarin yi mata sharri ai dole ta ƙaryata ka, mal nidae daga yau sai yau kar Nasiru ya sake taɓa min ƴaƴa, tashi muje", Maama ta miƙar da Sa'adatu suka fice daga ɗakin, Naseer yace "Baba, Maama tana sakaci da tarbiyyar yaran nan, wllh yarinyar nan a mota ake ajiyeta kuma namiji ne ba mace ba, ai ko macen ce a zargeta duniya ta lalace", Baba yace "na yarda da kai Naseer, abinda nake so da kai duk wani hukunci da za kai ka fara sanar dani kafin ka wanzar dashi, tashi kayi tafiyarka Allah ya shiryesu".
★Nurain ya sakko down stairs yana gyara zaman rantsatten agogon hannunsa, bai samu kowa a main palour ba don haka ya wuce part din Mami, da sallama ya murɗa handle ɗin palourn Mami ya tarar bata nan sai ya nufi ƙofar bedroom ɗinta, a hankali yayi knocking, daga ciki Mami tace "come in", ya buɗe door ya shiga, Mami na zaune bisa prayer mat ta idar da sallar walha, ta kallesa tace "A'a fita za kai, yau ai ba aiki ko??", yace "yeah, wajen Anty Zulaiha zani, tace tana son gani na, and i have another appointment", tace "ohk, anjima Abba da su Salisu zasu je gidansu Ruqayyah aii", ya jinjina kai yace "ammm Mami kin yiwa Anty Zulaiha maganar ne??", tace "eh na sanar da ita jiya da daddare", yace "ohk i think that was the reason take nema na, Noor fa?", tace "ta fita Grocery shopping wai girki zata ma friends ɗinta zasu zo", yace "ohk, na wuce", Mami tace "wait" ta miƙe ta buɗe huge press ɗinta ta ɗakko wata paper bag ta miƙa masa tace "ka kaiwa zuhaiha", ya karɓa ya fice daga part ɗin, katafaren compound din gidan ya fito mai ɗauke da shuke-shuke masu kyau da parking lots na motoci ƴan ubansu, Garba ne ya taho da sauri ya russuna yace "barka da fitowa alhj ƙarami", Nurain yace "yawwa, an gama wanke motar", Garba na washe haƙora yace "Eh an gama alhj" ya ciro key daga aljihun rigarsa ya miƙa masa, Nurain ya karɓi key ɗin ya zura hannu a trouser pocket dinsa ya ciro wallet ya buɗe ya fello dubu goma ya miƙa masa, hannu bibbiyu Garba ya amsa yana washe haƙora yace "Alhj harda hidima haka, to nagode Allah ya saka da alkhairy yasa afi haka", Nurain ya nufi wajen wata dunƙulalliyar mota a parking lot ya buɗe ya shiga, yayi warming sannan ya mirgina ya fita daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa damfareren gate. Slowly yake driving yana waya da Ruqayyah, wani murmushi ya sake speaking calmly yace "why are you doing this babe?, mesa bazan zo yau ba?", from the other side Ruqayyah tace "haba dearest nidae kunya nakeji, ka bari sai gobe kazo", yace "naji cewa sai gobe amma mesa zakiji kunya bayan da kanki kika kaini gidanku kikace kina sona kuma zaki aureni...", ƙit yaji ta katse kiran yayi murmushi ya sake dialing amma taƙi picking, a hankali yace "shy girl". A daidai gate din wani gida Bungalow ya danna horn, Gate man ya buɗe masa ya shiga da Motar yayi parking ya buɗe ya ɗauki paper bag din da ya ajiye a kujerar mai zaman banza ya fito, direct Main building din gidan ya dosa, ya tsaya a ƙofar shiga ya ciro wayarsa daga pocket ya kira Antyn nasa, tana yin picking yace "I'm here Aunt", Anty Zulaiha tace "toh me kake jira come in mana", Nurain ya shiga palourn da ya ƙawatu ba ƙarya bayan yayi sallama ya zauna akan kujera ya ajiye bag din hannunsa a gefe, wata ƴar budurwa ce da bazata wuce 20yrs ba ta fito daga kitchen hannunta riƙe da serving spoon, zaro ido tayi ta ƙaraso cikin palourn tace "yaya Nurain sannu da zuwa", yace "yawwa Khausar, ina Anty?", tace "bari nayi mata magana" tabi wani corridor, tare suka fito da Anty Zulaiha, Khausar ta koma kitchen Anty Zulaiha ta zauna kan kujerar dake kusa da nashi tace "na taso Dr da sassafe", ya shafa sumar kansa yace "ai mun saba da fitar safe, ya gida Anty?", tace "lafiya, ya Noor ta dai ƙi zaman gidan nan", yace "ai Noor Mami's tail ce" ya ɗauki paper bag din ya miƙa mata yace "inji Mami", tace "toh me na samu haka wajen yayata haka" ta buɗe taga perfumes ne kala uku, Khausar ta fito daga kitchen da trayn mai ɗauke da drink da kuma snacks ta ajiye masa, ta buɗe lemon ta tsiyaya masa a glass cup sannan ta koma kitchen, ya ɗauki lemon yayi one sip ya ajiye, Anty Zulaiha tace "jiya Mami take gayamin abin arziƙi, ashe yau za a kai kuɗi da sa rana, toh Allah ya tabbatar da Alkhairy, Ruqayyahn ce dai koh??", yace "yeah", tace "tom, maganar lefe na gaya maka balance dai koh??", yace "yea, yanzu zan miki transfer ba 2m ba??", tace "Eh haka yake, Insha Allah zasu isa a gama harhaɗo abubuwan da suka rage..", yace "idan ma basu isa ba just Ping me". Khausar da take rakuɓe a ƙofar kitchen kaf hirarsu a kunnenta ta lumshe ido a hankali tace "what kuɗin Auren yaya Nurain za a kai".............✍️
💛 HAJAR💛
by Feenerh_feeche
{7...}
A wannan rana aka kai kuɗin auren Nurain da Ruqayyah, tsakanin ɓangaren ango da na amarya aka taƙaice sa rana wata huɗu cif, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Nurain ba cause he is eager to have her as his wife, on Monday Ruqayyah na zaune a Nurse station, Nurse Jidda tace "an yiwa shuka bar ruwa tasha taki ranar girbi ya kusan ƙaratowa nanda 4months", Ruqayyah tayi murmushi a taƙaice tace "ni kam abin yayi min wuri, i thought Daddy zai saka 1year haka amma wai da suka ce wata uku shine ya ƙara wata ɗaya", Jidda tace "A'a shi Daddy da zai aurar dake ɗin ai ya shirya, toh ke mene dalilin ki da zaki ce yayi wuri??", keenly Ruqayyah tace "my own schedule, anyway nothing is going to change, i can deal with it", Jidda tace "hey i don't get you me kike cewa ne??", Ruqayyah tayi murmushi tace "zaki gane ne", Jidda ta ringa kallonta sai tace "think wise kafin kice za kiyi wani abun", Ruqayyah har ta buɗe baki sai kuma tayi shiru sakamakon wayarta da ta fara ringing, the ringing tone yasa tayi murmushi ta ciro wayar daga handbag ɗinta, ta haskawa Jiddah screen ɗin wayar tace "kin gani my Dr ne yake kira, he loves me so much duk abinda zanyi zai min uziri", har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa sannan Ruqayyah tayi picking ta kara a kunne tace "slm dearest, ka ƙaraso ne??", daga ɗayan ɓangaren Nurain yace "yeah", tace "ohk yanzu zan kawo maka coffeen nasan sai kasha zaka shiga surgery", wayar kare a kunnenta ta miƙe ta dubi Jidda tace "plxx ki kulamin da ward A kafin na dawo", Jidda ta galla mata harara tace "A nawa??", Ruqayyah tace "zan taya ki Night" ta wuce gaba. Nurain yana zaune a office ɗinsa yana duba tsirarun patients ɗin da zasu gansa a yau, Dr Marwan da Khaleel ne suka shigo a tare, Nurain ya ɗago ya kallesu ganin yanayin fuskokinsu yace "what??", Khaleel yace "Allah ya sanya Alkhairy Boss", Dr Marwan saida ya zauna kan kujera yace "fatan alkhairy", Nurain ya taɓe baki ya jingina da chair yana wasa da yatsunsa ya kallesu duka yace "tnx, ƙarfe 11am zamu shiga surgery, get ready", Khaleel yace "yes bari nayi gathering team ɗin", Nurain yace "good", Khaleel ya fita daga Office ɗin, Dr Marwan yace "who will anesthesetice the patient, our anesthesetic is absent", Nurain yace "that is not a problem i have one", Dr Marwan yace "ohk then", Ruqayyah ce ta shigo hannunta riƙe da Mug, Dr Marwan ya miƙe daga kujera yace "tom Dr sai mun haɗu a surgery room", saida yazo fita ya kalli Ruqayyah da take gefe yace "toh Allah ya sanya alkhairy A Nurse, naga tin yanzu ma ana kula mana da Dr ballanta an samu full license", Ruqayyah tayi murmushi tace "ya Amarya??", Dr Marwan yace "tana nan lafiya" ya buɗe door ya fita, ta taka a hankali ta zauna kan chair tana facing Nurain, gani tay ya wani haɗe rai yana latsa wayarsa, Mug ɗin da ta shigo dashi ta tura masa tace "dearest ga coffeen fa", ba tare da ya kalleta ba yace "take it with you", ajiyar zuciya ta sauke tace "sorry ai a faɗan laifina dai ko?", wayar ya ajiye ya zuba mata idanunsa da suke tamkar madara yace "daman kin iya murmushi haka??", dariya ce ta kusan kufce mata tace "jealousy sorry bazan sake ba", keenly yace "good". tace "happy tinda an saka lokaci kaɗan yadda kake so", yace "kefa ba kya farin ciki ne??", shiru tayi ta fara wasa da hannunta, yayi ajiyar zuciya yace "help me", ta ɗago da kanta tace "how?", yayi mata wani narkakken murmushi yace "zanyi surgery anjima zaki min anesthesia", ta juya idonta tace "sure my Dr".
★Maama daga bakin murhu tana kwashe abinci, kwanon Baba ta fara zubawa sai na sauran ƴaƴanta, bayan ta gama ta miƙe tana sharce gumin da ya tsattsafo mata a goshi saboda zafin wuta ta shiga ɗakinta, Sa'adatu tana kwance akan wani ruɓaɓɓen gado daga gani ba a rasa kuɗin cizo a cikinsa ba, Maimuna kuma tana shafa man bleeching ɗinta a fuska da ɗaurin ƙirji ajikinta sakamakon wankan da bata daɗe da fitowa ba, Maama ta kalli Maimuna tace "tin safe nake ce dake kiyi wanke-wanke amma kin ƙi, yanzu ga abinci can na gama amma babu kwanon da zan zuba muku", Sa'adatu tace "Maama mai aka dafa??", Maama tace "wake da shinkafa ne", Sa'adatu tace "dame kuma??", Maama tace "da manja da yaji", Sa'adatu tace "haka tsura ko ɗan salak babu" ta miƙe a hankali ta ɗingisa saboda har yanzu ƙugunta bai gama saki ba, ta ɗakko jakarta ta buɗe ta fello duba ɗaya, Maama ta zaro ido tace "Sa'adatu ina kika samu kuɗi haka", Sa'adatu ta yamutsa fuska ta miƙawa Maimuna kuɗin tace "ki siyo min kifi na ɗari biyar, balangu na ɗari uku saiki siyomin maltina ta gwangwani guda ɗaya", Maimuna tace "chaɓ gaskiya bazanje ba", Sa'adatu tace "ke dalla malama zan sammiki fa", Maimuna tayi gyatsine ta warce kuɗin, Maama tace "Sa'adatu magana fa nake miki", Sa'adatu tace "toh ai kece Maama wllh kin fiya maida hannun agogo baya, na gaya miki ƙawata ce fa take bani", Maama tace "Allah sarki, toh Allah ya biya ta". Maimuna ta zari hijab ta fita. Sa'adatu ta doka wani uban tsaki tace "Maama saida nace fa ki tuna min yau za a siyo piya-piya a yiwa ɗakin nan feshi ko ma samu sauƙin cizon kuɗin cizon nan, wallahi jiya kasa bacci nayi, ina kallon Maimuna da Nabilah ma sunata bige-bige cikin bacci", Maama tace "wai aikam na manta", Sa'adatu tace "shikenan nasan Maimuna ba sake fita za tay ba". Hajar ta fito daga ɗakin Umma da kwandon soso da sabulu a hannunta, bokiti ta ɗauka ta ɗebi ruwa ta shiga wanka, saida ta gama wanka ta fito ta shirya tsaf cikin uniform ɗin islamiyya, Sabra kam tayi gaba tinda ita da wuri ta dawo daga boko, Umma na linke kayan wanki tace "to Allah ya bada sa'a", Hajar ta ɗauki jakarta tace "Ameen".
★Kwanci tashi Hajar ta kammala rubuta jarabawar NECO, yanzu result kawai take jira saita fahimci wace alƙibla zata fuskanta, lokacin jarabawar kam tayi karatu ba ƙarya ga kuma wanda take yi tin fil azal, bayan sati biyu da kammala NECO a islamiyya ma aka fara yi musu screening ɗin sauka, daman sun shafe wata takwas da hattamawa suka tsaya ƙarasa littafai, yanzu kam satinsu uku da fara yin screening, A yammacin wannan rana Hajar ce zaune a kan kujera a bakin rariya tana wanke gwangwanayen kulele, Sabra na yi mata ɗauraya, takun takalma ƙwas ƙwas daga soro yana doso cikin gida yasa Hajar kallon ƙofa, Sa'adatu ce ta shigo cikin wata shiga half naked, ga wani uban kitson attachment da ta yarfa har mazaunai, fuskar nan ɗaɗau harda hujen hanci tayi tana taunar chewing gum ƙass ƙass tamkar cikakkiyar ƴar bariki, yanzu karenta take ci babu babbaka iskanci ya linka na da Maama na goya mata baya, dodon nata Naseer yanzu baya zama a gida tinda ya samu aikin direban tirelar Ɗangote dake jigila tsakanin kano da Lagos shikenan yayi wuyar gani, Hajar ta taɓe baki ta cigaba da sha'anin gabanta, sai kuma ta sake ɗagowa ganin wasu mata wanda suka amsa sunan cikakkun ƴan duniya su biyu a tare da Sa'adatun. Maama na rawar jiki ta shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, Sa'adatu ta nuna ɗaya daga ciki matan tace "Maama wannan itace zeenatu amma anfi kiranta da zeen" ta nuna ɗayar tace "wannan kuma mabaruka amma anfi kiranta da mabruk", Maama ta washe baki tace "Allah sarki, sannunku da ƙoƙari ƴaƴan nan, ai Sa'adatu tayi dacen samunku matsayin abokai", zeenatu tana taunar chewing gum tace "muma haka" cike da rashin ɗa'a da tarbiyya, Sa'adatu ta wage murya tace "ke Maimuna kina ji nazo bazaki fito ba", Maama tace "laaa ai bata nan", Sa'adatu tace "Nabilah fa?", Maama tace "tana ɗaki, ke Nabila ki fito ga ƴar uwarki nan tazo kina ji", Nabilah ta yaye labule ta ƙarewa su zeenatu da Mabaruka kallo tace "Sannunku" sai kuma ta kalli Sa'adatu tace "ɗan shigo daga ciki mana mu gaisa", Nabilah ta koma ɗaki Sa'adatu tabi bayanta, sama da ƙasa Nabilah ta ƙare mata kallo tace "kinga Sa'adatu ki dawo gida ki zauna, waɗannan kuma su waye haka kika kawosu marasa kyan ganii", Sa'adatu tace "nasan zaki zarge ni ai amma wllh kinji dai na rantse ko??, wllh bana kula maza bare takai da abinda kike tunani, rayuwa nake agidansu zeenatu da Mabaruka irin ta wayayyun mata masu ji da kansu", Nabilah tace "wayayyun mata??", Sa'adatu tace "Eh mana ko baki gani ba", Nabilah ta zabga uban tsaki tace "ni ban gani ba, kwata-kwata ma baku ɗauki hanyar zama wayayyun mata ba wllh, ai....", muryar Baba ce ta katse maganarta, a tare suka antayo waje, Baba ya kalli Maama yace "waɗannan su waye??", Maama tace "ƙawayen Sa'adatu ne fa", Baba ya nuna hanyar soro yace "ku tashi ku fitar min daga gida", Mabaruka ta kalli Sa'adatu tace "au daman Babanki bashi da mutunci Sa'adat", zeenatu ta figi jakarta tace "waini ake kora cikin wannan kuturun ruɓaɓɓen gidan sai kace kango, gidanda ko kiwon tumaki bazan yi ba, haba dattijo kai baka ji kunyar kiran wannan kangon da gida ba saboda tsiyar zuci". wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya takore maƙoshin Hajar da take zaune bakin rariya, da sauri ta ɗauraye kumfar hannunta ta gyara wuyan rigarta ta miƙe tsaye a fusace, Zeenatu da ta yo hanyar fita cikin sauri ta tsaya tana kallo, saida ta bari tazo gaf da ita zata wuce ta saka mata ƙafa, wani irin hantsilawa Zeenatu tayi ta kifa da ka, fuskarta ta faɗa cikin kwata, jikinta kuma ya afka kan gwangwanaye, warwas tayi a ƙasa cikin cakwalkwalin ruwan wanke-wanke mai datti da maiƙon manja, gaba ɗaya guiwoyinta da hannunta sun kwaile, da kyar zeenatu ta dafe hannunta ta miƙe bakinta da goshinta sun fashe, fuskarta dama-dama da kwata, Hajar ta gyara wuyan rigarta da wani