Showing 81001 words to 84000 words out of 114314 words

Chapter 28 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5287

sauƙi", Hajar na idar da sallah ta koma ta jingina da wall, Mami ta dubeta da sakakkiyar fuska tace "ya jikin naki?", Hajar tace "da sauƙi" tana kallon hannunta da ta ɗane sa, Mami tace "toh koma kan bed ki kwanta", ba musu ta miƙe ta koma kan gadon ta zauna, Anty Zulaiha ta ɗakko robar grilled fish ta bata, da rubber fork Hajar ta ringa cakar dankalin tana ci, kaɗan taci kifin tace ta ƙoshi, tasha ruwa da already shima Anty Zulaiha ta ajiye mata, Mami ta buɗe ledar drug dinta ta duba dose kafin ta ɓalla ta bata, wani irin yamutsa fuska Hajar tayi don idan akwai abinda ta tsana bayan allura to magani ne, da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya ta haɗiye three tablets din. da misalin uku da minti hamsin Umma ta iso asibitin ita da Anty Jamilah, wata staff ce mai shara ta rakosu room din da suka gaya mata sunansa da Anty Zulaiha ta sanar musu ta waya, Hajar na ganin Ummanta ta sakko daga kan gadon tabi bango taje ta rumgumeta hawaye na zuba idonta, Umma tayi yaƙe ta shafa bayanta, Anty Jamilah ta zauna sukay exchanging gaisuwa dasu Mami, Anty Zulaiha ce ta sanar da Mami wace ce Anty Jamilah, Umma kan ba sai an gaya mata ba cause Hajar ta sanar da ita, Umma ta janyeta daga jikinta ta ƙarasa kusa da Anty Jamilah ta zauna, suka gaisa da su Mami, Hajar ta rakuɓe nan gafe guda hannu a ɗane tama faman riritasa, Anty Zulaiha tace "dan dai ta damu da sai an kira mata Ummanta ai da sai mun koma gida za a gaya muku, tinda da yammar nan za a sallameta", Anty Jamilah tayi murmushi tace "gashi dai kam ai lafiya ta samu, ai ƴar uwarta ma taje gidan tanata tsaye a waje ashe ba kowa ana asibiti", Anty Zulaiha tace "Allah sarki, ai tin safe muke nan da yake ciwon da safe ya tasar mata..", Umma ta ɗan tattare fuska, ciwon ya tasar mata, idan fa akace ciwo ya tashi to ana nufin daman tin tini mutum na ɗauke dashi, toh me yake damun ƴarta don ita dai tasan batada wani ciwo. Dr ne ya shigo wanda yayi taking over tinda wanda ta gani da safe ya tafi, kallon gado yayi ganin wayam yace "where is the patient", Hajar ta turo baki ta tashi tana layi kaɗan ta koma kan gadon, few questions yayi mata kafin ya fita yace zai dawo nan da 1 hour, su Umma basu wani jima ba suka tashi tafiya, nan hankalin Hajar ya kuma ɗagawa, Anty Jamilah na kallon fuskarta da hawaye ya cika tam a idonta tasan kuka za tay, ta isa gefen gadon ta zauna kusa da ita ta fara mata magana a hankali, Hajar ta gyaɗa kai tana controlling kukan da yke shirin kwace mata, da kyar tace "tom, na dena wllh kuma zan kwantar da hankalina", Anty tace "good, to sai nazo" da haka ta miƙe ta sake yiwa su Mami sallama, Umma ta dubi Hajar da take daf da rushewa da kuka tayi mata murmushi snn ta buɗe ƙofa ta fita Anty Zulaiha tabi bayanta. Hajar tayi sauri ta kwanta ta tsiyayar da ruwan hawayen da ya cika mata idanu, After 1 hour din kam Doctorn ya dawo a lokacin biyar saura, kai tsaye sallama ya basu daman sunyi magana da waccan Drn. ƙofa akay knocking kafin aka shigo, Nurain ne, ido huɗu sukay da Hajar, yay saurin ɗauke kansa ya hade gira, Mami na kallon Dr tace "A cire mata canular", with a repartee Nurain yace "No, kar a cire", Mami ta dubesa ba tace komai ba, Dr yay musu sallama kafin ya fita. Anty Zulaiha na riƙe da hannun Hajar suka fita harabar Hospital en, Farooq dake zaune a under tree ya taso, Nurain ya shiga front seat ya bawa Farooq key din Mota don haka ya shiga driver seat, Mami Anty Zulaiha da Hajar kuma suka shiga baya, Farooq ya kunna motar ya fara driving suka fita daga asibitin, direct daman hanyar gidan Abba ya ɗauka.


★Maama ta rantse ta kuma rantsewa ta buga cinya tace "billahillazi la'ilaha illa huwa sai malamin tsamiya ya biyani kudina dubu arba'in, tinda aikinsa bai ci ba wllh sai ya biyani kuɗina", Balaraba da ke kallonta baki a hangame tace "ai kwa kya yi kya gama Rabii, wane cin kike magana a kai, naga dai auren da ba kya so a ɗaura naga dai ba a ɗaura ba, bata auri malamin makarantar ba ehee, kinga kwa malamin tsamiya yaci kuɗinsa wllh", Maama ta fige ɗan kwalin kanta da ya rufawa kanta asiri, don wani irin tsohon kitso ne a kanta wanda zai kai wata huɗu, ta sosa kan wanda nasan babu shakka kwarkwata ce ta mintsileta, tace "Balaraba malamin nan dan abu kaza kaza ne, me yasa bai hango wanda zata aura ba iyee, wllh da nasan haka zata faru wllh tllh bazan yi asarar kudina ba, ai gwara ta auri malamin makarantar....", Balaraba tace "Wai a sbd me kike faɗin haka?", Maama ta dafe goshinta mai lemon tsami tace "dana sanin da nayi yafi cikin kwando Balaraba, wato ina gaya miki, malamin makarantar nan ba komai bane akan wanda Hajara ta aura...", Balaraba ta kuma hangame baki har ƙudaje suka fara shawagi, Maama ta sharce zufar dake keto mata tace "ke kinga gidan da aka kaita kuwa gari guda, lefen da aka bata kam ya linka na malamin makaranta sau shida..", Balaraba ta kore ƙudajen da suke shawagi kusa da bakinta tace "an shiga ƙuryar ɗaka ba'a tsira ba, Rabi kimin bayani yadda zan gane..", nan Maama ta gyara zama ta shiga fesawa Balaraba zance, ta ƙarashe tana sharce zufa tace "kinga lukutar masifar dana jibgowa kaina", Balaraba ta gyaɗa kai cike mamaki ta kasa cewa komai, Maama ta hauta da masifa tace "dalla malama ya zaki min shiru na zo ki bani hanyar ɓullewa, kin wani hangame baki wari duk ya cikamin hanci ciki ya kumbura, kiyi magana na shaƙi warin da hujja tinda dai na rage zafi amma kinyi shiru inata shaƙar ɗoyi a banza", Balaraba tace "Au haka fa, kinsan gwano baya jin warin kansa, ni da kika buɗe wnn tsumman kan naki sai kace hammatar ɗan iskan sabon gari mai ɗoyin tsiya bance komai ba sai ke, toh kafin cikin ki ya kumbura nawa ya gama cika dammm da samamin kanki..", Maama tayi kwafa tace "haka kika ce ko?", Balaraba tayi tsaki tace "Ahap ai kinji mai nace", Maama ta ɗaura ɗan kwalinta tace "biyani dubu biyar ɗita..", Baraba tace "wace dubu biyar?", Maama ta miƙe tsaye a fusace tace "wacca kika ce sai na baki zaki rakani wajen malami..", Balaraba ta miƙe itama tace "bazan biya ba, akan me zan biya bayan na miki aiki kin samu", Maama ta yayibi duƙunnanen hijab dinta mai warin dauɗa ta saka ta fice fuuu daga gidan kamar zata tashi sama, Balaraba ta buga cinya tace "Allah raka taki gona, ni nan da kike ganina ɗuwaiwai ce ko dan zama a nemeni". daf da magrib Maama ta koma gida a fusace, Baba da ke alwala nan bakin rariya ya ringa kallonta kafin yace "daga ina kike?", ta hura hanci tace "nan nan maƙota na shiga an yiwa ɗan gidan shayi", Baba bai sake ce mata komai ba ya cigaba da alwalarsa, Umma ta fito daga ɗakinta itama za tay alwalar, ta ɗau buta ta buɗe tukunya ta ɗebi ruwa, Baba da ke wanke ƙafa yace "ya jikin Hajaran?", Umma tace "Ahh da sauƙi sosai..", Maama da bata ƙarasa shigewa ɗakinta ba ta juyo tana tafa hannaye tace "za kiga sauƙi, wato har an fara tsotse jininta, wllh duk wanda ya hau motar kwaɗayi babu inda zata ajiyesa sai a tashar wulaƙanci, kuɗi ƙumbar susa sun hanaku amso ƴarku ko, toh wllh ku ka bari aka tsotse mata jini har ta mutu ranar gobe qiyama sai an muku hisabi da ita, wnn ai cin zali ne da tauye haƙƙi, ƙiri ƙiri kuɗi sun ruɗeku kun wurga yarinya a halaka, kun kaita gidan yankan kai za ai layya da ita..." Baba ya tashi yayi ficewarsa cause har an kira sallah, Umma tayi shigewar ta bayi, Maama ta gyaɗa kai tace "hmmm, a banza an yakushi kakkausa, wllh kanku kuka wulaƙanta" da haka ta afka ɗakinta, ta kalli Nabilah tace "Su Sa'adatu basu dawo ba ko?", Nabilah tace "Eh, dan Allah Maama wai ina ruwanki da auren Hajara ne", Maama ta zabga wani uban tsaki tace "shknn, tinda nace kar su kai dare amma saida suka kai wllh ba ruwana idan mal ya gansu, kar ma shegiyar da ta ambaci suna na".


★Wani extra room dake part din Mami aka gyarawa Hajar, Noor ta kawo mata kaya set biyu da kuma sleeping gown, bayan tayi wanka ta ɗauki guda ɗaya ta saka, Hajiya har nan tazo ta dubata tana rafsa salati da godiya, ai gwara da ta warke kar ace a gidan jikanta ne, Hajar ta durƙusa har ƙasa ta gaida Hajiya, bata amsa ba ta tsaya tana kallon hannun Hajar din da take maƙalesa tsabar san jiki, Hajiya tace "meye wnn en kuma ya sandarar mata da hannu?", Noor da itama ke ɗakin tace "Canular ce iron lady, abin ƙarin ruwa..", Hajiya tace "toh me yasa basu cire mata ba a can asibitin suka barta da wahala?", Noor tace "nima ban sani ba", Hajiya ta kalleta ta saman kantamemen glasses dinta tace "tafi kira Usuman yazo ya cire mata, ji fa yadda hannu ya sandare", Noor tace "ya fita masallaci", Hajiya ta danne sandarta ta mike daga gefen gado da ta zauna tace "nima bari naje nayi sallar" da haka ta dogara sandarta ta fita, Noor tayi ajiyar zuciya tace "Ohh, Hajiya iron lady", Hajar tayi murmushi, Noor tace "kiyi sallah, yanxu zan kawo miki abinci", ta fita, Hajar tayi sallah, tana idarwa ba jimawa saiga mai aiki da tray na abinci, ta ajiye kan couch kafin ta fita, Hajar na idar da sallah ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, jiri ne yake ɗan ɗibanta kaɗan, Mami ta shigo, ganinta a haka tace "are you okay dear?, idan akwai inda ke miki ciwo say it out", Hajar tace "bana jin komai", Mami tace "Alhmdllh, ga abinci ki ci sai ki sha drugs ki kwanta ki huta ko", tace "tom nagode", saida tayi sallar isha'i wacca da kyar ta iya yinta a tsaye sbd jiri snn ta buɗe abincin, aroma na abincin ne ya ɗebeta har ta ɗan ci kaɗan, ta sha ruwa, daga haka ta malale kan carpet, (that question goes to you young lady, what are you doing in my house) shine abinda ya amsa a brain dinta, ta lumshe idanunta hawaye na zubowa a cheeks dinta... Nurain ya shigo palourn Mami da leda a hannunsa, Mami na shan fruits Salad while watching news, kujerar da ke facing ɗinta ya samu ya zauna, ya ringa kallonta ganin ko kallon inda yake ba tay ba her eyes fixed on TV, calmly yace "Mami zan dubata", tace "ohk" tana shan fruits Salad dinta, yayi ajiyar zuciya yace "zan sa mata drip ne, na mata injection..", tace "toh..", shiru palourn ya ɗauka sai ƙarar TV, shi bai sake cewa komai ba kuma bai tashi yayi abinda yace zaiyi ɗin ba, Noor ta shigo tana dariya tace "wnn aboniki naki iron lady ina zan kai yajinsa, dole Aysha ta gudu idan kika ce ta shafa miki..", hanyar room din da Hajar take ta wuce, Nurain yace "Noor", ta juyo tana kallonsa tace "Na'am", yace "tana ina?", tace "waa?", ya tsuke piercing eyes ɗinsa, Mami dai ba tace komai ba, Noor tayi tsaye tana jiran yace wani abun, a dan hasale yace "ina patient din?", tace "tana ciki" tayi masa nuni da ƙofar ɗakin da Hajar take, miƙewa yayi da ledar a hannunsa ya shiga ɗakin, Mami ta bisa da kallo, Noor ta shiga ɗakin itama, a bakin door ta gansa ta wucesa ta durƙusa gaban Hajar dake kwance kan carpet, taping dinta tayi a hankali tace "Hajar are you okay?", Hajar ta miƙe a hankali tana kallon ɗakin sbd scent din da tayi perceiving, jajayen idanunta suka faɗa cikin nasa, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana yamutsa fuska, yace "Noor help her to bed", Noor ta tashi ta riƙe hannunta ta temaka mata ta koma kan bed, Nurain ya ajiye ledar hannunsa kan chest of drawers ya fara haɗa ruwan injection, ya fito da ruwan da zai ƙara mata ya ciro empty syringe ya zuƙi ruwan kafin ya isa gefen gadon, koda wasa bai dubeta ba, hannun da take maƙewa yake kallo don tanan zai mata allurar ya sa mata ruwa, Noor ta tashi zata basa waje yace "no, ɗago min hannun", Noor ta dauki pillow ta ɗora hannun Hajar mai canular a kai ta matsa gefe, ya kwance Canularn making sure bai taɓata ba, ruwan da ya zuƙa cikin syringe ya fara ɗura mata sbd yayi flushing vein en kafin ya zuba ainahin ruwan allurar, wani zafi Hajar taji a hannun da take riritawa, a zabure ta janye hannunta ta kwala ihu.....✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{39..}
Still Nurain yayi yana kallon syring en da ta bar masa a hannu, Hajar ta zaro ido tana yarfe hannunta da already jini ya gama wankesa cause Canularn a buɗe take, da sauri Noor ta isa gaban mirror ta dakko kwalin tissue, ta zauna gefen gadon ta kamo hannun Hajar tana goge mata jinin, Mami ce ta shigo da sauri cause taji ihun Hajar tinda door a buɗe take, Mami tana kallon Nurain tace "what is happening here?", Noor tace "amm flushing vein en ake mata za'a mata allura", Mami ta ƙaraso gefen gadon tana kallon Nurain da ke riƙe da syringe tace "ka mata a hankali mna, you know it's hurting...", baice komai ba ya bar wajen ya ajiye syringe en cikin ledar dake kan chest of drawers snn ya nufi door, Mami tace "Nurain...", ya juyo yace "na'am Mami", tace "ina kuma zaka?, ka gama mata injection din ne?", yace "No, kawai tasha drugs.." da haka ya fice mai gaba ɗaya, Mami ta dubi Hajar da hawaye ya ciko idanunta tace "Sorry" sai kuma ta dubi Noor tace "take that thing off her vein kawai" ta fita a ɗakin, a hankali Noor ta zare mata canularn daga hannun, ta bata tissue ta danne wajen, wani sakayau Hajar taji hannun yayi mata, bayan kamar 2minutes Mami ta dawo ɗakin da ledar drugs da bottle water an rufa mata disposable cup, da kyar Hajar ta iya haɗiyar maganin tana yamutsa fuska, Noor ta gyara mata pillow ta kwanta, Mami tace "Noor saiki kwana anan ko?", Noor tace "tom, bari naje room dina na dawo". ko minti biyar ba ai da fitar Mami da Noor ba bacci ya kwashe Hajar, luntsum tayi cikin duvet tana baccin da ba daban rashin lfy ba bazata iya yinsa ba, Noor na gama uzirinta a room ɗinta ta dawo ɗakin da Hajar take ta kwanta. tsakar dare Hajar ta farka sbd kanta da take jin tamkar zai tsage, ga wani azababben jiri da take jin tamkar ana hajijiya da ita daga kwance, sideways take jujjuya kanta ba tare da tasan tana aikata hakan ba, slight movement da take yi ne ya farkar da Noor wacca sam sam ba tada nauyin bacci, Noor ta kunna bedside lamp kafin ta yaye duvet da ta rufa ta miƙe zaune, saida vision dinta ya daidaita ta lura da yadda Hajar take motsi involuntarily, da sauri ta sakko daga gadon ta kunna lights sosai, with compassion Noor ta taɓa forehead dinta, her temperature was very high at that moment, direct Noor ta fita a ɗakin, after like 5minutes ta dawo tare da Mami, sosai hankalin Mami ya tashi, amma kuma da ta fahimci cewa Hajar na cikin hayyacinta sai damuwar ta ragu, complain ɗin da Hajar tay kawai shine kaii sbd shi yafi takura mata, har Mami zata bata panadol sai kuma ta fasa, Noor da idonta ke cike da bacci tace "kamar ma anyi dischaging enta da wuri fa", Mami tayi ajiyar zuciya tace "nima dai haka na gani, what says the time?", Noor ta duba lokaci a wayarta tace "biyu da minti sha uku..", Mami ba tace komai ba ta tashi ta fita, Hajar dai na jingine da allon gado idonta a lumshe. Mami na fita kai tsaye room din Nurain ta wuce, knocking door tayi, ko 1minute ba tay da fara knocking ba ya bude, ya zaro sleepy eyes dinsa yace "Mami..", tace "kazo ka duba Hajar jikin ya tashi", yace "tom ina zuwa" ya koma cikin ɗakin nasa domin ɗaukar wasu abubuwan, definitely yasan haka saita faru tinda taƙi bari yay mata allura, yana gama ɗaukar abinda zai ɗauka ya fito, yabi bayan Mami suka wuce part enta, yana shiga ɗakin ya ɗauki ledar da ya bari kan chest of drawers, ya zuƙi injection dose en da zai mata a syringe, ya isa inda take jingine da gado yana kallon hannunta da yaji zanen ƙunshi, Mami ta ringa kallonsa ganin yayi tsaye bashi da niyyar yi mata allurar, har ya kai hannu zai riƙe hannunta sai kuma ya fasa, ya farke ledar hands gloves da ya shigo da ita ya saka gloves en a hannunsa, Mami da Noor dai suka bisa da ido, ita kam baiwar Allah Hajar ko iya buɗe idonta ba tayi sbd haske linka mata ciwon kan yake, a damtse yayi mata allurar, ta motsa kaɗan lokacin da ya zare empty syringe en daga muscle enta, ya saka mata drip da bai sa mata ɗazu ba, deeply in his mind saida yayi dana sanin da yasa akay dischaging enta, wai shi gudun liability na asibiti yayi, sai gashi bai tsira ba, yana gama mata duk wani abin da ya dace yace "Mami you should get back to sleep, itama bacci za tay", Mami na kallon Hajar tace "gobe da sassafe sai mu koma asibiti gsky", yace "No, insha Allah she'll be fine", Mami tace "toh Allah yasa, Allah yay albarka", yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login