Showing 99001 words to 102000 words out of 114314 words
Chapter 34 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
ɗaya ta fita daga hayyacinta ido ya zuzzurma...", Umma dake tsaye tsakar gidan ta daka mata wata gagarumar tsawa tace "wllh ko kashin ƴan hanjinta take saita ɗanɗana kuɗarta a yau, na gaji da abinda ake min a gidan nan yau an kaini bango, billahillazi la'ilaha illa huwa bazan haƙura ba..", galala Maama take kallon Umma ta hura tukubar hanci tace "toh ai sai kizo kisa ta ɗanɗana kuɗarata ta, ke kin isa ma ki ɗora hannunki akan ƴata", Baba da tari yake ƙoƙarin sarƙe masa numfashi yace "Rabii ki faɗamin inda Maimuna take ko na sake ki..", Maama ta dafe ƙirjinta ta gwalo idanu waje tace "da girmana da gemuna mal kake cewa zaka sakeni a bainan nasi, toh Maimuna dai ƴarka ce kuma gata can kwance tana makyarkyata...", Baba yace "So nake ta fito nan yanzu yanzun nan..", kasaƙe Maama tayi sai kuma ta rausayar da kai ta shiga ɗakinta, Maimuna da ke rakuɓe can ƙarshen gado ta haɗa hannayenta waje guda tace "Maama dan girman Allah ki rufa min asiri, na shiga uku na lalace..", Maama tace "A'a Maimuna a gaskiya tashi za kiyi ki fita, kina jifa sakina yace zaiyi idan ya sakeni ina na dosa..", Nabilah dake ɗakin itama tace "wanda baiji bari ba ai yaji hoho, saida nace ki bari Maimuna amma saida kika biyewa Maama, tinda dai baku rasa ci da sha ba ina ruwanku da garar Hajara, ga dai irin ƙarangiyar da kika jajiɓowa kanki...", Maimuna ta rushe da kuka ga goshi yayi suntumm, tini Maama ta figi ƙafar Maimuna ta fara janta ƙiyyy jin Baba na sake jaddada mata zai saketa, Maimuna ta riƙe gado ta daƙile tana kurma ihu, ta ƙarfi da yaji Maama ta fitar da ita, daga ita har Maimunan haki suka ringa yi, Maama tace "ƴarka ce daii", Anty dai tinda ta jingina da bango tana kallon ikon Allah ba tace komai ba, Baba kawai kallon Maimuna yake da wani irin takaici, shi ba ya mata baki rayuwarta taɓarɓarce ba. Maimuna ta faɗawa ƴan garinsu da shaɗin carbi, daga tazo guduwa Mu'azzam zai tarota ya dawo da ita don ji yake kamar ya taya Baba dukan ƴar banza, Maimuna da taji azaba iya azaba tace "na rantse da Allah Maama ce ta sani, itace tace na zuba wllh" tana soshe soshe, saura ƙiris Baba yayi collapsing Mu'azzam ya riƙosa ya kaisa ɗakinsa, wnn dalilin ne yasa Umma ta fasa fita, maganin Baban dake wajenta ta ɗakko da ruwa ta shiga ta kai masa, Wani irin tari mai ƙarfin gaske Baba yake, idanunsa sun firfito waje, da kyar aka sami kansa, Maimuna dai ta samu ta arce ɗaki tana soshe soshe, Maama ta bita ɗakin tana sababi tace "Shine kika fita bainan nasi kikai yama ɗiɗi dani..", a gigice Maimuna tace "Allah ya isa na bazan taɓa yafewa ba, munafiki azzalumi mugu..", Nabilah tace "kan bala'i Maimuna wa kikewa Allah ya isa...?", Maimuna tace "waccan Shegen Mu'azzam ai shine yazo ya ƙalamin sharri, kuma na rantse da izu sittin sai yasan ni aka daka ta dalilinsa, wllh tllh saina biya ƴan daba kuɗi sun sassara shi, idan yaci buluss shegiya nake, shi ya isa yasa a dakeni kuma ya fasamin goshi a banza, wllh Allah sai nasa ƴan daba sun sassara shi...".
★Nurain ne zaune main palourn gidansu, plate din abinci da Noor ta zubo masa ne a gabansa yana ci, Mami ta fito daga part dinta, shigowa palourn tayi tana kallonsa sai kuma ta kalli plate din abincin tace "har yanzu baka tafi gida ba Nurain...?", ya ajiye spoon din hannunsa yace "yeah na tsaya yin dinner ne", tace "Ohk hurry up ka gama dare yayi fa 9 ya wuce tin ɗazu..", yace "Ohk", Mami ta zauna kan kujera, kaɗan ya rage abincin ya tashi ya shiga da plate din kitchen, ya fito da bottle water a hannunsa, Mami ta tashi tace "toh good night zan sawa door lock", kallonta ya ringa yi da mamaki sai kuma yace "am spending the night here", with facial expression take kallonsa tace "baka isa ba kuma wnn", ya girgiza kansa don yana sane ya faɗi hakan don yaji view ɗinta, upstairs ya haura zuwa room ɗinsa, bayan few minutes ya sakko da wata medium bag a hannunsa wacca ya zubo kayan sawa, ya yiwa Mami sallama wacca har lokacin bata bar palourn ba ya fita, yana fita Mami ta sakawa door lock, Nurain ya girgiza kansa don yaji lokacin da ta saka lock din, wato dai Mami harda kora, motarsa ya shiga ya bar gidan, yana zuwa gida bayan yayi parking ya fito daga motar, Inuwa mai gadi ya masa sannu da zuwa, Nurain ya wuce hanyar shiga gidan, keys ya ciro ya buɗe ƙofar ya shiga, tsayawa yayi yana kallon palourn da yake tsaf tsaf sai ƙamshi ke tashi, tsaki yayi ya taɓe baki ya haura sama with his bag, bayan yayi wanka ya shirya cikin Pajamas ya ɗauki jakar Laptop dinsa ya sake sakkowa downstairs, ajiye bag din Laptop din yayi kan kujera ya shiga kitchen, shima dai kitchen din tass yake komai a mazauninsa, daga can gefe yaga foodstuffs, still yayi yana kallon foodstuffs din, ga kuma bucket guda huɗu kusa da foodstuffs din, ya buɗe bucket ɗaya wanda yake cike damm da dubulan, ya sake buɗe wani shi kuma yaga Alkaki shima acike damm, bai buɗe ragowar ba sbd ya gane na mene, Coffee maker ya jona jikin socket kafin ya buɗe cupboard da ya ajiye Coffee powder ciki, within few minutes ya gama haɗa black coffee ya bar kitchen din, saida ya kashe dukka fitulun palourn snn ya zauna a kujera ya kunna Laptop dinsa, operating system din yake at same time kuma yana sipping Coffee, ɗago kansa yayi ya kalli stairs jin footsteps, a hankali Hajar take sakkowa daga benen, harta fara bacci wata azababbiyar yunwa ta farkar da ita, tamkar an yashe mata kayan ciki haka take ji tsabar yunwa, tunawa da kayan garar da aka kawo mata ne yasa ta fito domin ta ɗiba taci kar yunwa ta halaka ta, kafin ma ta ƙarasa sakkowa ƙasa ta hango duhun palourn, Allah yaso da wayarta a hannu, tana gama sakkowa ta kunna fitilar wayar, rays ɗin hasken fitilar wayar da ta kunna ya dallare masa ido......✍️
Feenerhfeeche02 @ Arewa book
💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche
{45..}
Da sauri Nurain ya lumshe idonsa tsabar yadda hasken ya kashe masa su, Hajar da tsoro ya sandarar da ita ta kasa wani cikakken motsi, sosai ta razana don ba tayi tunanin akwai mutum a wajen ba, Nurain ya ajiye cup din Coffeen ya kaucewa hasken yace "kee mene haka kuma are you mad...?", da sauri ta janye hasken daga kansa, furiously ya tashi ya kunna bulbs haske ya gauraye palourn, wani irin shan kunu Hajar tayi ta shige kitchen da sigar ko in kula, sarai tasan haske masa ido tayi amma she don't care tinda dai ba intentionally ta aikata hakan ba, wani tuƙuƙi ne ma ya mamaye mata zuciya da taga fuskar tasa, plate ta ɗauka ta zuba dubulan da Alkaki sai chin chin, cup ta ɗauka ta buɗe tap din sink ta cika da ruwa, daga haka ta fita daga kitchen din, direct stairs ta dosa, Nurain ya miƙe daga hannun kujerar da ya zauna ya zuba both hands dinsa a pocket fuskarsa a murtuke yace "hey you stay there", tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya a hankali sbd kar cup din da ta ciko da ruwa yayi tambal tambal ya zube, yayi blocking front dinta yana binta da wani kallon tsana yace "wnn shine karo na ƙarshe da zaki sake fitowa palourn nan idan ina zaune, daga ƙarfe shida na yamma bana son ko silhouette naki ya gifta ta palourn nan, ko me za kiyi ki yisa kafin wnn time din that is weekdays knn, a weekend kuma you just have 3 hours daga shida na safe zuwa tara, daga nan kuma sai gobe, am i clear...?", ta juya lulu eyes ɗinta ta yamutsa fuska sbd yadda tayi perceiving pure men scent dinsa, ta taɓe baki tace "sorry you can't tell me what to do...", yace "ko, toh ki jini da kyau as far as you are living in my house you must follow my rules, bad attitudes din kike ji dashi toh ki tattarasa ki ajiye gefe, ba dai a nan ba saiki bari lokacin da kika gaji da zama kika sallami kanki ki ɗauki abinki ki ƙara gaba, this is my last warning...", da haka ya barta tsaye ya ɗauki Laptop dinsa da cup of coffeen zai haura sama, wata nannayar ajiyar zuciya Hajar ta sauke, har wani huci take masifar ta motsa, idonta ya kawo ruwa, tana ganin yayi rabin stairs din tace "ji mana malam, karka tsaya wahalar da kanka, ka damƙa min shaida kaga idan ban ƙara gaban ba", ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo yace "save the time that you are free to roam in my house..." da haka ya juya ya haura stairs, har wajen 50seconds tana tsaye inda ya barta, gyaɗa kai tayi ta numfasa tace "lallai wnn mutumin bai sanni ba, sanin da yayi min na taɓin gishiri ne, mu zuba ni da kai wanda ya fasa bai haifu ba", ɗakinta ta wuce abinta, akan mirror ta ajiye plate da cup din da ta shigo dasu, ta zauna akan stool dake gaban mirror din tana kallon kanta, kwafa tayi ta girgiza kai ta ja plate din gabanta ta fara cin tarkacen da ta ɗeba, tana gama cin iya yadda zai mata ta sha ruwa, tayi kwanciyarta kan carpet kamar yadda tayi jiya, ta lulluɓe da duvet don wani azabar sanyi ɗakin yake mata sbd Ac gashi bata san ta inda zata kashe ba. Nurain ya gama abinda zai yi jikin Laptop kafin ya kashe ya mayar da ita bag, ya fita da cup din daya gama shan Coffee zuwa Kitchen yana dawowa kuma ya kwanta, da Asuba bayan ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita daga room din nasa, a corridor ya tsaya yana kallon ƙofar ɗakinta, after looking at the for few seconds kawai ya sauka downstairs, bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yayi recitation of the holy book, sai wajen 8 na safe ya rufe karatun, daman already yau Monday yake son komawa work, bathroom ya shiga bayan yayi wanka ya fito da towel a hannunsa yana goge cikakkiyar sumarsa, 9 ya gama shirinsa tsaf ya ɗauki briefcase da ya saka Laptop dinsa ya sauko ƙasa bayan ya rufe part din nasa, bai ga dai alamar ta sakko ba har ya shiga kitchen, ya haɗa tea ya dawo palour yana sha, tsaki yayi don ya saba yin full breakfast kafin ya fita aiki, daga karshe dai ya gama shanye tean ya kai cup din kitchen, daga haka ya fita compound bayan ya rufe main door ya zuba keys din a pocket, da sauri Inuwa dake zaune kan white plastic chair a bakin gate ya taso, ya russuna da kyau ya gaida Nurain, a takaice ya amsa yace "akwai wanda suka zo jiya ne bayan fita ta..?", Inuwa yace "Eh alhj anyi baƙi sunxo nan da kayan abinci..", Nurain ya gyaɗa kai bai ce komai ba ya buɗe motarsa da Inuwa ya gogeta tass ya wanke wheels ɗin kuma, bayan ya gama warming ya ja motar ya bar parking space din ya fita daga gidan dan already mai gadi ya buɗe gate, after a ride of 20mins ya isa hospital, yayi parking motar, kallon yawarsa dake kan dashboard yayi kafin yasa hannu ya ɗauka ya zurata a pocket, ya fito walking majestically ya nufi hanyar office dinsa, securities da sauran ma'aikata suka ringa gaishesa da welcoming dinsa, briefly yake amsa gaisuwar yana tafiya, yana ƙarasawa office din ya buɗe ya shiga, secretaryn sa Haleema da ya turawa saƙo ta email cewa zai shigo on Monday, shiyasa tin ranar friday tasa aka kyara office din, Haleema ta tashi with respect tace "good morning sir", da sakakkiyar fuska ya amsa mata yace "morning, ykk..", tace "alhmdllh sir an dawo lfy..?", yace "fine alhmdllh" da haka ya shige cikin office din, ƙarewa office din kallo yayi kafin ya ajiye briefcase din hannunsa kan huge table dake office din, after surveying the huge office ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zuciya, ya kalli glass nameplate dake gaban table din mai ɗauke da sunansa (Dr Uthman). wayarsa ya ciro ya kunna, saida ta gama booting uban messages da suke pending suka gama shigowa, call log ya shiga yayi dialing numbern Khaleel, tana fara ringing Khaleel yayi picking, Khaleel yace "ba dai ka dawo ba boss..", Nurain yace "gani ma a office", Khaleel ya katse kiran, after like 5minutes ya shigo office din, Khaleel ya zauna kan ɗaya daga biyun kujeru da suke gaban table din, bayan sunyi exchanging greetings Khaleel yace "An dawo lfy..?", Nurain yace "alhmdllh, Dr Marwan ya shigo..?", Khaleel yace "yeah amma ya shiga surgery not too long ago", Nurain yace "Ohk", Khaleel ya ciro wayarsa da tayi ringing daga pocket din labcoat dinsa, few seconds ya katse kiran ya tashi yace "i have to go now ana kirana a E.R". Khaleel na fita office din Nurain ya kira Haleema ta landline, tayi picking tace "yess sir", yace "Patients zasu iya fara shigowa", tace "Okay sir". Nurain ya fara attending first patient da ya shigo, yana yiwa patient din ƴan tambayoyi aka buɗe ƙofa aka shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya cigaba da attending patient dinsa, jingina Ruqayyah tayi jikin ƙofar tana mayar da numfashi, ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya sai kuma ta buɗe idanun, kamar a yanzu ta fara ganinsa haka ta zuba masa na mujiya, kawai kallonsa take babu ƙiftawa ta jingina da jikin ƙofar, Nurain yayi prescribing patient din with drugs da cewar zai dawo nan da 2weeks follow up, Ruqayyah ta matsa gefe ta bawa patient din hanya ya fita, tamkar wacca kawai ya fashewa acikin haka ta isa gaban table din nasa kanta a ƙasa tana wasa with her fingers, tinda ya mata kallo ɗayan nan bai sake ba, kwata kwata bai nuna yasan ma da shigowarta ba, ya cigaba da rubutu jikin record book, muryarta na rawa kanta a ƙasa tace "Dearest...", next patient ce ta shigo ƴar dattijuwa, ganin haka yasa Ruqayyah ta bata space, sai a lokacin Nurain ya ɗago yayi attending patient dinsa, a haka dai saida yayi attending 5 Patients kuma har lokacin Ruqayyah na tsaye bata fita ba, na biyar din patient na fita, da sauri Ruqayyah taje ta rufe ƙofa, Nurain ya kira landline yace "i need security now", kasaƙe Ruqayyah tayi tana kallonsa sai kuma ta haɗa hannayenta waje ɗaya tace "plxx talk to me, dan Allah kayi haƙuri ka saurareni Dearest...", rubuce rubucen sa ya cigaba da yi, Security man ya buɗe ƙofa ya shigo with respect yace "sir you call", ba tare da ya ɗago kansa ba yace "get her out of my office", security man yace "yess", ya kalli Ruqayyah da Mamaki ya gama daskarar da ita yace "Muje hajiya..", wani kwallo mai uban tauri Ruqayyah ta haɗiya lokaci guda ta fita daga office din with speed hawaye na zuba idonta. Nurse station ta wuce, tana zuwa ta zauna kan kujera ta hade kanta da table din station din ta fashe da kuka, Nurse Jidda da ita kaɗai ce a station din duk sauran sun shiga ward ta ajiye kidney dish din hannunta tace "Ruqayyah lfy...?", Kuka kawai Ruqayyah take taƙi tace komai, da damuwa Jiddah tace "subhanallah dan Allah ki gayamin mene ya faru..?", Ruqayyah ta ɗago kanta tana kallon Jiddah da jajayen idanunta tace "Jiddah ni yanxu ya zanyi, Dr yaƙi saurarata...", Jiddah ta jinjina kai ba tace komai ba, ita ganin ƙarfin halin Ruqayyah take, yo ko itace Dr ai bazata saurareta ba, Ruqayyah ta goge cheeks dinta tace "wai fa security ya kira yace yayi waje dani sai kace wata ɓarauniya..", ta sake fashewa da kuka, Jidda tace "bari na duba patient a ward A" da haka ta saka kidney dish din da ta ajiye a cikin tray ta ɗauka tabar station din.
★Sai goma da rabi Hajar ta farka daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba, bathroom ta shiga tayi brush ta wanke bakinta da mouth wash, tayi wanka, saida ta wanke bathroom din snn ta fito, tsaye tayi bakin mirror tana kallon uban kayan shafe shafen da Hafsah ta jera mata jiya, wani body lotion ta ɗauka tana duba sunansa sbd da shower gel dinsa tayi wanka, ta zauna kan stool ta fara rubbing lotion din, ta ringa kallon gashin kanta da duk kitson ya fara warwarewa da kansa, bai ɗauketa wani minti 20 ba ta gama tsefe ƙananan kitson kanta tass, daga ta kama jelar zugeta kawai take cause gashinta mai laushi da santsi ne na fulani, combing hair din tayi ta shafa masa oil shima da ta gani, tayi parking dinsa a ƙeya ta tufke jelar, daga haka ta tashi daga gaban mirrorn, ta buɗe huge wardrobe tana taɓe baki, ita dama a box Hafsah ta bar mata kayanta, wata doguwar riga ta atamfa ta saka, ta zumbula hijab ta fita a ɗakin ta sauka ƙasa da cup da plate din jiya da taci kayan gara, kayan garar ta sake ɗiba taci a kitchen din tasha ruwanta a famfo kafin ta fito ta koma room dinta, tanata zaune a ɗakin saidai tayi game a wayarta inta gaji ta ajiye har akay sallar Azahar, tana idar da sallah taji wata yunwa ta bijiro mata, kayan garar dai ta kuma ɗurawa cikinta, samm taƙi yin girki sbd gani take knn ma rayuwa mai tsayi zata yi, palour ta fito ta ringa kallon ƙofa kafin ta matsa kusa da ita ta kama handle ta murɗa, a rufe taji ƙofar, ta koma kitchen ta buɗe ƙofar da zata sadaka da backyard din gidan, luckily ta jita a buɗe, ta ringa kallon backyard din tana ɗan zagawa, ta zauna kan wani dakali da ta gani