Showing 18001 words to 21000 words out of 114314 words
Chapter 7 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
ya zauna yace "Maama barka da safiya", ta kawar da kanta kamar bazata amsa ba tace "lafiya, ai da yake shi kaɗai ya haifeka dole ka fara zuwa wajensa", tin lokacin da ya shigo ta hangosa ta shatin labule, ya shafa kansa yace "ya gida Maama?", ta galla masa harara tace "saika tambayi gidan kaji ya yake, ni ka tambayeni wani gida, nice nan uwarka Nasiru, wato duk abinda ka shigo dashi saika nufi ɗakin mahaifinka ko, ni banida mutuncin da zaka fara zuwa wajena ko, kaida Huzaifa saidai nayi muku addu'ar Allah ya dawo muku da hankalinku da tunani, an riga an shanyemin ku wllh, ƴaƴana mata kam sai san barka ta ko'ina alheri nake samu dasu", shi dai ya sunkuyar da kai yace "ayi hakuri Maama", Maimuna kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da jin waƙarta tana sabgar gabanta, tashi yayi zai fita suka haɗa ido da Maimuna ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, yana fita ta daka tsaki tace "masifa, jaraba ya dawo, Allah yasa dai yau zai koma", Maama ta kalleta tace "leƙa kiga akwai doya a tsakar gida", Maimuna ta leƙa ta dawo tace "Eh naga Baba yana rabawa", Maama ta miƙe ta gyara haɓar zaninta tace "rabawa kuma?" ta fita tsakar gida, Baba har ya gama kasafta doyar gida biyu dai-dai, ya ɗauki guda uku cikin kaso ɗaya ya ƙara a ɗaya, Maama dai ta bishi da kallo tana jiran taga abinda zai yi, ya dubi Maama ya nuna mata kason da yafi yawa yace "ɗauki wannan, Nasiru ne ya kawo mana", Maama ta harari kason doyar bata ce komai ba, Baba ya kira Umma ta fito daga ɗakinta itama ya nuna mata ƙaramin kason yace ta ɗauka Naseer ne ya kawo, Umma tace "toh masha Allah, Allah yayi albarka an gode", ta sunkuya ta fara ɗiban doyar, Maama ta daka wata tsawa tace "wllh ba a isa ba, idan na yadda kwarankwatsa dubu ta waɗo a kaina", Baba ya tsaya yana mata kallon mahaukaciya, Maama ta buga ƙafa har zaninta yana ƙoƙarin kuncewa ta nuna Umma tace "kaji matsiyaciya kwaɗayayyiya, yanzu ke baki ji kunyar ɗaukar doyar nan ba, ɗanki ne ya kawo ko ubanki, keda haihuwa ba tay miki rana ba shine zaki raɓo kice zakici arziƙina, wllh ki ajiye doyar nan tin kafin ranki yayi mugun ɓaci", Umma ta mayar da doyar da ta fara ɗiba ta ajiye ta juya zata koma ɗakinta, Baba ya dakatar da ita yace "Faɗima dawo ki ɗebi doyarki, ai ni Nasiru ya kawowa kuma inada iko akan wanda zan bawa", Maama ta rangaɗa Shewa tace "toh banda nan mal, iko ko?, to baka dashi anan, wllh wannan shegiyar da shegun ƴaƴanta bazasu ci doyar nan ba, haramiya ce a garesu", tana gama bambaminta ta kwalawa Maimuna kira, Maimuna bata ji ba sbd earpiece dake kunnenta, Maama ta leƙa ɗakin ta window ta ɗauki warin slipers ta jefa mata, Maimuna ta fizge earpiece ɗin kunnenta a hasale tace "wane ɗan iskan ne ya wurgomin takalmi", Maama tayi mata daƙuwa tace "fito", kafin Maama ta ankara har Umma ta shiga da wata doyar ɗaki tinda Baba ya umarceta da ta ɗauka dole, Maama ta barƙa ashar tace "wllh saikin fito dasu" ta kalli Maimuna tace "shiga ɗakinta ki ɗakko min doyar da ɗana ya siyo, ni bazan shiga na ɗebo bala'i ba", Maimuna tace "chab kenan ni bala'in ya shafeni", Maama tace "tofe jikinki da addu'a ki shiga ki ɗakko min gumin ɗana", Baba ya nuna Maimuna da yatsa yace "karki kuskura ki shiga ɗakin nan", Maimuna tace "yo Baba kanafa gani Maama ce ta sakani" ta doshi ƙofar ɗakin, Hajar daman tana laɓe a jikin labule zuciyarta na tafasa, ai kam ta ɗauki doyar da Umma ta zube a bakin ƙofa, Maimuna tana kunno kai ta wurga mata ita a fuska, daman doyar guda huɗu ce kuma saida ta jefe Maimuna dasu tas a ƴan sakanni, Maimuna ta riƙe hancinta da doyar ƙarshe ta sauka akai tana jin kamar zai gutsire sbd azaba, Hajar tace "ga tsiyarku nan" ta banke ƙofa ta saka sakata, hannu biyu tasa ta rufe duka kunnuwanta tana bubbugasu sbd karma taji muryar Umma ko Baba.
★Da safiyar ranar ɗaurin aure, Meema friend ɗin Ruqayyah kuma cousin ɗinta ce ta fita palour neman amarya, gidansu Ruqayyah acike yake da ƴan uwa da abokan arziki, Kulsum ta hango akan kujera tana breakfast, Meema ta matsa kusa da ita tace "amm yaya ko kinga Ruqayyah", Kulsum ta ajiye mug ɗin hannunta a gefen kujera tace "A'a bata wajenku ne?, nima tin ɗazu nake nemanta ta ɗauki kayan da zata saka yanzu", Meema tace "Ohk, nima tinda na tashi ban ganta a room ɗin mu ba, to i thought tana wajen Momy ne", Kulsum tace "ping her on phone", Meema tace "switched off, tin ɗazu nake kira amma bari na sake kiran", Meema ta kunna wayarta dake hannunta tayi dialing numbern Ruqayyah ta saka a handsfree, switched off suka ji, Kulsum ta amshe wayar daga hannun Meema ta sake kira, same thing dai aka ce mata wato switched off, keenly Kulsum tace "where could she be?", ta miƙawa Meema mug ɗin hannunta da bata gama shan shayin ciki ba, direct ɗakin Momy ta wuce, ai kam dai tayi sa'a ba kowa a ɗakin sai Momy, kayanta tagani wargaje akan carpet a nannaɗe gefe ɗaya, ta kalli Momy tace "Momy wane ya fitomin da kaya daga cikin jaka??", Momy ta juya hannu tace "ni kam bansani ba, ai saida nace kisa a wardrobe", Kulsum ta fara mita ta tsugunna ta fara kwashe kayan sai kuma tace "to ina jakar kuma??", Momy tace "toh kodai ɓarawo ne ya shigo ɗakin nan, kinga yanzu ma naga box ɗin kayan Ruqayyah a buɗe", Kulsum tace "yawwa Ruqayyah ta gaya miki zata fita ne??", Momy ta buɗe wardrobe tace "A'a, me zai kaita fita yau", Kulsum tace "toh ina ta shiga, Meema ma tace bata wajensu", Momy ta dakata da abinda take cikin wardrobe ta juya tace "An kira wayarta", Kulsum tace "yess", Aisha ce ta shigo babbar ƴa agidan, ta wuce hanyar toilet tace "gwara nayi wankana da wuri kafin na shiga sabga, a matsayina na second mother", Kulsum tace "yaya ko kinga Ruqayyah", Aisha ta riƙe handle ɗin ƙofar toilet tace "A'a rabona da ita tin jiya wajen mother's Eve, me ya faru?", Kulsum tace "yo nemanta fa ake tazo ta shirya", Aisha tace "ko wajen make-up ta tafi?", Momy ta sauke ajiyar zuciya domin har hankalinta ya fara tashi, Kulsum tace "Eh kam haka ne, wajen make-up ta tafi, amma da wuri haka kuma bata gayawa kowa ba", Aisha tayi slight hiss tace "yaran yanzu rawar kaine dasu akan aure" ta shige toilet. Kulsum dai bataga jakar kayanta ba kawai ta saka kayan a press din Momy ta koma palour don ta ƙarasa shan shayinta, ta zauna a position ɗin data tashi ɗazu ta amshi shayin daga hannun Meema tace "toh ai Ruqayyahn wajen make-up ta tafi", Meema tace "wajen make-up, mai kwalliyar fa har gida zatazo tayi mata, kuma mafa kawai gyara mata fuska za tay da ɗauri ba wata kwalliya ta azo mugani za ay mata ba, kinsan Ruqayyah da maintaining natural beauty, aikam bari na kira makeup artist din". Meema ta takune gira bayan ta gama waya da mai kwalliya ta tabbatar mata Ruqayyah bata zo wajenta ba. secretly Meema da Kulsum suka fara neman Ruqayyah a gidan, ko ina saida suka duba kuma suka tambayi waɗanda suka dace, daga ƙarshe Kulsum ta koma ɗakin Momy, this time ƙannen Momy su biyu suna nan da ita kanta Momyn, Aisha kuma tana gefe tana rubbing lotion, Momy fuskar Kulsum kawai ta kalla tasan akwai damuwa don haka tace "mene ne??", Kulsum tace "Momy bafa a ga Ruqayyah ba?", Aisha ta dakata da shafa man da take tace "bata wajen make-up din", Kulsum tace "yess, mun duba ko ina a gidan nan, kuma mun tambayi waɗanda muke tunanin tana tare dasu amma bata nan, and her phone is switched off", hankalin kowa yayi kan Kulsum da ta gama magana, Momy ta zauna a kan bedside thinking of another thing, haj Safiyya tace "Kulsum ku nutsu dai ku dubata sosai, yo ina zata?", Kulsum tace "Aunt wllh bata nan, baki ga duban da mukai nida Meema ba", Momy tayi wani tunani tace "kun duba part din Daddy", Kulsum tace "nan ne kawai bamu shiga ba", Momy zata miƙe hook ɗin zip ɗin rigarta ya riƙo wani ɗan siririn plastic dake kewaye da bedside lamp, tana miƙewa lamp ɗin ta biyota, saura ƙiris ta faɗi, Momy ta mayar da ita sai kuma ta tsaya tana kallon papern data faɗi a kan tiles maimakon fitilar, bata san dalili ba amma tana kallon papern zuciyarta ta buga, ta sunkuya ta ɗauka a zatonta zata ga electricity bill da tayi misplacing jiya, saɓanin electricity bill sai taga rubutun ƴarta Ruqayyah wanda kalaman ciki suka sa ta koma ta zauna a kan bedside babu shiri, Sosai hankalin mutanen ɗakin yayo kanta, Aisha ce ta fara yo kanta tace "Momy lafiya" sai kuma ta zare takardar hannunta wacca ta lura itace ta jefata a wannan hali, Aisha ta zabga salati bayan ta gama karance takardar itama tace "jama'a Ruqayyah ta gudu". iya su da suke cikin ɗakin ne suka san abinda yake faruwa sai Meema wacca bata san cewa Ruqayyah gudawa tayi ba amma tasan ba a ganta ba. Kulsum ta sakawa ɗaki lock gudun kar wani ya shigo, bayan ƙura ta lafa na firgici da tsantsanin mamakin abinda Ruqayyah ta aikata ɗakin yayi tsit, Momy ta zabga uban tagumi tana kallon takardar, haj Safiyya tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, ya kamata ki sanar da Daddy", Aisha tace "chab wannan wane irin abin kunya ne?", Momy ta sauke ajiyar zuciya, wato jiya da taga Ruqayyah da daddare wato ƙoƙarin guduwa take. ta ɗauki papern ta fita daga ɗakin, ƴan biki na gidan sai hada-hada suke wasu ma har sun fesa wanka sbd baifi saura awa ɗaya lokacin ɗaura aure yayi ba, haka Momy ta ringa ƙetaresu tana yaƙe harta wuce part ɗin Daddy, tin daga palour taji ƙamshin turarensa na tashi, Momy ta haɗiyi yawu tana son ƙwallon da ya tsaya mata a maƙoshi ya wuce, a hankali ta shiga bedroom ɗin Daddy da sallama, ta tarar dashi har ya shirya yana waya, ji tayi yace "Eh yau ne ɗaurin auren, ana idar da sallar Juma'a za a ɗaura Inshallah", ta koma gefen gado ta zauna tana jiran ya gama wayar, bai jima ba ya kammala ya juyo ya kalleta yace "me ya faru?" yana gyara hular kansa, bata basa amsa ba kawai ta miƙa masa takarda, karɓa yayi ya saka glasses a idonsa, ya buɗe takardar ya karanta yana ƙanƙance ido yace "meye wannan", Momy tace "Ruqayyah ce ta ajiye", ya cire hular kansa zanna bukar ya ajiye akan mirror, malum-malum ɗin jikinsa da ta sha ado na ɗinkin hannu da zare mai tsada itama ya cireta yayi hanging yace "Shikenan ta yiwa kanta". Daddy ya kira ƴan uwansa maza su huɗu ya sanar dasu abinda ake ciki kuma yace suje su sanar da dangin Ango. suma duk sun sha kwalliyar ɗaurin aure suka hau Mota suka nufi gidansu Ango. A Great room ɗin Abba aka saukesu, shima Abba he was ready duk da dai ya bawa ƙaninsa walicci. bayan sun gaisa babban cikinsu ya sanar da Abba komai, Abba ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama saurarensa yace "Allah ka shirya mana zuri'a", daga haka bai sake cewa komai ba. numbern Mami yayi dialing bayan sun tafi, after wayar tayi ringing sau huɗu Mami ta ɗauka, keenly Abba yace mata yana bukatar ganinta yanzu a part ɗinsa, Mami ta shigo palour cikin wani dakakken lace ɗan ubansu wanda yasha stones da samfalwa mai rawa, fuskarta cike da walwala amma tana ganin fuskar Abba zuciyarta ta buga, kusa dashi ta zauna a kujera 2seater, yana kallon fuskarta sai yaga kamarta da Nurain ainun wanda zai samu karayar zuciya nanda wani lokaci mai ƙaratowa, Abba yace "Khadeeja", Mami tace "Na'am", ya ɗaga kansa ya kalli ceiling yana wasa da yatsun hannunsa yace "ki bawa Nurain haƙuri", ya gaya mata kaf abinda ƙannen Daddy suka gaya masa, tabbas Mami ta girgiza amma Nurain shi yafi tsaya mata a rai, ita uwace wacca tasan ciki da waje na ƴaƴanta, ta san ɗanta yana son Ruqayyah sosai ma kuwa, a hankali tace "shikenan, Allah ya basa wacca ta fita", Abba yana kallon ceiling yace "Ameen, kiyi azamar sanar dashi". Mami ta miƙe ta fita duk jikinta yayi sanyi, tana shiga main palour Noor da itama tasha lace irin nata tace "Mami na kai snacks ɗin ɗakinki, Anty Zulaiha kuma tana nemanki", Mami tace "Ohk, Nurain ya sakko?", Sakeena tace "No, ai duk nan shi muke jira ya sakko muga kwalliyar Ango". Mami ta kalli stairs ɗin da zai kaita ɗakin Nurain, a hankali ta fara hawa stairs ɗin harta kai ƙarshe, sau biyu tayi knocking ƙofar ɗakinsa ya buɗe, he was already dressed up, ta tsaya tana kallonsa da shigar da bata taɓa ganin yayi irinta ba, yayi kyau wanda bai taɓa irinsa ba, caramel skin ɗinsa tayi wani luf-luf, ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinsa wanda bata taɓa jin irinsa a tare dashi ba, murmushin da yayi mata shima bata taɓa ganin irinsa ba, calmly tace "Son are you ready?", yace "almost", ta shiga ɗakin tace "i need to talk to you"..........✍️
💛 HAJAR💛
by Feenerh_feeche
{12...}
Nurain ya mayar da ƙofa ya rufe, Mami ta riƙo hannunsa ta zaunar dashi a gefen bed kusa da gogaggiyar malum-malumsa da hula waɗanda yake shirin sakawa, da wani irin expressions yake kallonta, ta zaunar dashi sbd gudun kar ya faɗi idan yaji abinda zata faɗa duk da tasan shi mai tawakkali ne, a hankali tace "Uthman" tana shafa kansa, yace "na'am Mami na", tace "kasan duk wani abu da yake faruwa ko kuma zai faru nufi ne na Allah, kuma nasan cewa ka yadda da ƙaddara", ya lumshe idonsa yana jin yadda take shafa kansa kamar tana rarrashinsa, tinda yaji waɗannan kalaman yasan cewa something was odd, yace "Mami me kike so ki gayamin ne?", kusa dashi ta zauna kana ta fara magana a hankali tace "Ruqayyah yarinyar da zaka aura...", ta wassafa masa kaf abinda ya faru, wata irin aradu ce ta doka a zuciyarsa idonsa ya kaɗa yay jaa, ya kasa cewa komai sbd karayar zuci, ba ƙarya Ruqayyah broke his heart into million pieces, sama-sama yaji muryar Mami tana cewa "pray my Son, Addu'a itace maganin duk wata musiba, i know your in agony but plxx don't let it slaughter you", ya ɗago idanunsa da suke farare ƙal-ƙal amma a yanzu sun canja launi, ya buɗe baki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ya miƙe da sauri ya zubar da links ɗin rigarsa da yake dunƙule a hannunsa, wayarsa da take kan mirror ya ɗauka, yayi dialing numbern Ruqayyah ya kara a kunne, bashi da shakku ko ɗigo akan maganar da Maminsa ta gaya masa, yana so ya tuhumi Ruqayyah ne ya tambayeta Why him?.., me yasa sai shi a duk faɗin mazan duniya zata yaudara?, me yasa ta zaɓi ta ragargaza masa zuciya?, wannan shine sakayyar da zata yiwa soyayyarsa agareta, All love dinda take nuna masa was it a pretence all those years, Mami tace "who are you calling?", ya sake dialing for the fifths times, Mami ta sake zaunar dashi a gefen gado tace "Uthman, plxx relax, ban sanka da haka ba", ya sauke ajiyar zuciya yace "Mami, I'm okay" sai ya dafe kansa, knocking door akay Noor ta shigo tace "Mami tin ɗazu Anty Zulaiha take jiranki", Mami tace "Ohk, muje", Noor ta kalli Nurain da ya dafe kansa sannan ta fita a ɗakin, Mami ta miƙe a hankali ta dubi Nurain sai kuma ta sunkuya ta kwashe links din da ya zubar ta ɗora akan mirror tabi bayan Noor, zuciyarsa tafasa take, akwai ciwo sosai ace wanda ka yarda dashi ya yaudareka, yaudarar ma me zafi irin wnn, wayarsa ce ta fara ringing, ko kallonta beyi ba at this time he don't want to talk to anybody, he don't want to see anybody, all what he want is an explanation from Ruqayyah, wayar ya fuzgo da niyyar dannata a jirgi wani kiran ya sake shigowa from Dr Marwan, ya haɗiyi wani abu yayi picking kana ya kara wayar a kunnensa, Dr Marwa yace "wai ina ka saka wayarka ne tin ɗazu nake kira baka picking, ka gama ne muzo mu ɗauke ka, everyone is there Ango kawai muke jira", Nurain yace "Marwan cancel everything", Marwa yace "Dr what do you mean?", da kyar Nurain yace "yeah, plxx cancel the reception, ka bawa kowa haƙuri" ya katse kiran, ya janyo curtain ɗin wayar zai sakata a jirgi message ya shigo, saida ya saka wayar a jirgi sannan ya dawo ya fara karanta message din da ya shigo from Ruqayyah.. ( 😭 Sorry dearest, i want you to know that i madly love and i will be back to be with you, plxx wait for me.), yana gama karantawa yaji soyayyar Ruqayyah tana juyewa zuwa ƙiyayya, yayi wurgi da wayar ta daki bango sannan ta faɗi ƙasa ta tawarwatse. wnn text din babu abinda yayi masa saima ƙara masa raɗaɗi a zuciya, shi Ruqayyah zata yayyankawa zuciya da wuƙa mai kaifi kuma ta dawo ta bayan fage tana barbaɗa mata gishiri, dama bata turo masa wnn text ɗin ba da maybe some percent na son da yake mata zai ragu koda 3 ne, amma yanzu zero, zeron ma behind decimal point, ƙarƙat an yiwa mai dami ɗaya sata soyayyar Ruqayyah ta faɗi a ƙasa warwas, babu abinda yake ji sai tsanarta. Ruqayyah ta rushe da kuka bayan ta gama tura text message din, ta rungume wayar a ƙirjinta tana kuka sosai, few mutanen da suke kusa da ita a waiting chairs suka dubeta, saida taci kukanta ta more ta ciro barimar kunnenta, ta buɗe wajen sim card ta zare sims