Showing 57001 words to 60000 words out of 114314 words

Chapter 20 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5261

aka kawo lefe, manya manyan tabarmi har guda biyu aka baje a tsakar gida da yamma ana jiran ƴan kawo lefe, Maama da ƴaƴanta sai shige da fice suke suna yaɓa baƙaƙen maganganu, tin Anty Jamilah na sharesu har ta fara mayar musu da wacca tafi tasu zafi da ciwo. an zuba bajinta gsky, lefen Hajar san kowa ƙin wanda ya rasa, dangin Ango suna gama sauke kayan lefe suka ce suna buƙatar a ƙara musu wata ɗaya domin ango ya gama shirye-shiryen sa, kai tsaye aka amsa musu dan Anty da Umma suma suna son su gwangwaje ƴarsu, tray tray su Anty da wasila da sauran ƴan uwan Umma suka ringa fitarwa na kayan motsa baki da kaji da kuma steak suka bawa ƴan kawo lefe, ga kuma kuɗin tukuici mai tsoka da aka basu, sunji daɗin karamcin da iyayen Hajar sukay musu, nan fa aka baje kaya ana musu ɗaɗɗai kowa na sanya albarka, maƙwabta da abokar arziƙi kowa shigowa yake yana kashe kwarkwatar idonsa, a duk wnn zazzafar wainar da ake toyawa Maama da ƴaƴanta sun ƙule ɗaki saidai fa komai akan micimicin idanunsu tinda laɓewa sukay jikin labule da window suna leƙe. baƙin ciki da hassada ainun suke nunawa, Anty sai ɗaɗɗaga kaya take tana saka albarka, wasila kuma na rangaɗa guɗa, da baƙin ciki ya ishi Maama da sauri ta bar bakin labule ta zauna ƙasa daɓas ta dafe kai, Sa'adatu kam tsaki tayi ta koma gado tayi kwanciyarta tace "ko sha'awa", Maama tace "ƙarya kike munafuka, wane mai zuciyar ne zaiga uban kayan nan yace basu birgesa ba..", Nabilah ta rage murya tace "haba Maama kiyi magana a hankali kar ace baƙin ciki muke", da ƙarfi Maama tace "Eh aji ɗin mna" sai kuma ta miƙe ta gyara ɗaurin zaninta ta saɓi hijab tayi waje, da sauri Maama ta fice daga gidan zuciyarta na tafarfasa ta saɓi hanya........✍️


🔔*WEDDING BELL*🔔
Ehen it's ringing...... ƙalalannnn 🔔


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche.


{28..}
Can cikin lungunsu ta shiga, bayan tayi tafiya ba mai nisa ba tazo ƙarshen lungun, ta gangara can ciki, wani tsukun layi ta shiga mai wawakekiyar kwata, ƙudaje da ƙwari sai shawagi suke, wari kam ba a cewa komai sbd kwatar ta Engine markaɗe ce kuma mara gudana, wani kuturun gida na laka Maama ta shiga ta zabga sallama daga soro, ta kutsa kai ciki, wata mata ce ta fito wacca za su kai shekaru ɗaya da Maaman daga wani ɗaki, ganin Maama ta riƙe baki tace "lale lale maraba da baƙuwar yamma", Maama tace "bani ruwa na sha maƙoshina a bushe yake", wata randa dake can gefe matar ta buɗe ta kantamo ruwa a cup ta kawo mata, daga tsaye Maama ta moɗe ruwan, tayi ajiyar zuciya tana hura tukubar hanci ta miƙawa matar kofin tace "yawwa Balaraba, da zance nazo", Balaraba tace "Atoh mu shiga ɗaki ko mu zauna nan waje tinda ba kowa, duk basa gidan", Maama tace "mu zauna nan tsakar gida yafi iska", Balaraba ta shiga ɗaki ta ɗakko wata yagulamun tabarma duk ta zare ta shimfiɗa musu, suka zauna, Balaraba tace "lfy dai Aminiya", Maama ta sharce zufar da ta tsattsafo mata da ƙasan hijab tace "Balaraba ƴaƴana gaba ɗayansu sun wurgar da zuciyoyinsu a ƙasa kare ya lashe". Balaraba tace "me ya faru?, shaƙamin mana", Maama tace "kinsan dai ina zaune bazan bari ƴaƴan faɗima sufi nawa ba, wai wnn shegiyar ƴar Hajara itace yau aka kawowa lefe", tayi shiru ta riƙe baki tace "ke baki ga uwar dukiyar da aka lafto ba", Balaraba tace "babbar magana, toh su kuma yara meye haɗin su da wnn lamari kika ce kare ya lashe musu zuciya?", Maama tace "kwanwar su ce fa duka, gaba ɗayansu gaba suke da ita, ni bama wnn ba wnda shegiyar zata aura ne matsalata", Balaraba ta taɓe baki tace "ɗan gidan waye?", Maama ta juya hannu tace "oho ni bansani ba, amma dai wai malamin makarantarsu ne, yaran nan da yake sun sansa shine suka ce min wai faƙiri ne bashi da komai, wai ƙaramin shagon chajin waya yake dashi, uwarsa ɗan wake take jefawa a ruwa, kin san me?", Balaraba tace "yo ina zan sani ai sai kin gayamin", da wani irin takaici Maama tace "hmmm arziƙi da rashinsa ai basa ɓuya, wllh in gaya miki lokacin da malam ya kwanta a asibiti ke baki ga uban kayan da ya kawo masa ba na dubiya, tin daga lokacin zuciyata ta fara wasiwasi akansa, wai sai Sa'adatu tace min kayan haya ne, wai shi Opay, in gaya miki aka zo aka kawo kuɗin aure, nidai tinda nake ban taɓa ganin kuɗi masu aukinsu ba, to sai wnn kayan na lefe da aka kawo, shknn fa akasa muƙeƙiyar sanda aka bajar dani a ƙasa, kinji fa lukutar masifar da nake ciki..", Balaraba ta jinjina kai ta riƙe haɓa tace "amma baki taɓa sanar dani ba Rabi", Maama tace "ai yaran nan ne sukai ta juyar min da kai da tunani, suka ringa cewa matsolo ne kuma faƙiri shiyasa ban damu ba, nidai yanxu ki bani shawara me zanyi?", Balaraba tace "ai kwa dai bazaki zauna ba kina ji kina gani ƴar faɗima tafi naki ƴaƴan, yanxu dai yaushe ne bikin?", Maama tace "naji ɗaxu dangin mijin suna cewa saura wata biyu", Balaraba ta washe haƙoranta da suka gama dafewa sbd cin goro tace "yo wnn ai me sauƙi ne, munada lokaci isasshe, wata biyu ai da yawa", Maama tace "kar dai muyi sake, ta ina zamu fara?", Balaraba tace "toh wai me kike so ayi ne?", Maama tace "A'a haba ke kuwa Balaraba ai kinsan me nake so", Balaraba ta ɓarke da dariya tace "Azzaluma Rabii", Maama tace "har na kaiki", Balaraba tace "gidansu yaron zamu fara nemowa, ai bazai wuce unguwar Dala ba tinda kince malamin islamiyya ne", Maama tace "to wa zai nemo gidan nasu?", Balaraba tace "haba Rabii sai kace baki san ko ni wace ce ba, nice larabe uwar kwakkwafi da bin diddiƙi", Maama tayi ajiyar zuciya tace "yawwa, na bar komai a hannunki, sai zuwa yaushe zan ji ki?", Balaraba tace "har gida zanzo na sameki ai wnn abu nima ya shafeni, bazan bari kiji kunya ba Rabii", sai ynxu zuciyar Maama ta sake, taji daɗi har cikin ranta tace "to bari na saɓa, wai ƴar tafiyar nan da nayi ba kiji yadda ƙirjina ya riƙe ba sai kace wata wacca ta tara kitse, yo Allah na tuba ina naga maiƙon", Balaraba tace "ai da anci maiƙon, yanzu ne dai babu, amma da gidan Malam Adamu ai baya rabo da maiƙo, ke kanki maiƙon kika gani kika liƙe masa..", Maama tace "gsky dai sai bayan da aka haifi autar gidan arziƙi ya yanke mana, malam yana riƙon gida sosai, yanxun ma yana bamu daidai ƙarfinsa, kin san ni ba ruwana in mutum yayi abin arziƙi bazan kushesa ba, shiyasa nima nayi masa halacci na zauna dashi a babu", da haka Maama ta miƙe, soro Balaraba ta rakata, sukay sallama Maama ta wuce, har ta koma gida jama'a basu baje ba, ynxu ne suka fara shigowa, abinka da unguwar tsuku wato gheto, wnn gayawa wnn haka suka cika gida suna kallon abin arziƙi, sai bayan Sallahr magrib aka samu masaka tsinke, Anty ta riƙe haɓa tana kallon Umma tace "Adda mutane akwai gulma", Umma tace "uhmm bare ƴan lungun nan", Anty ta kalli boxes ɗin da Mu'azzam ke jigilar shigowa dasu tace "Alhmdllh gsky kaya sunyi kyau sai san barka Allah yaci da ƴan baya", Umma tace "Ameen, zan tambayi mal nanda kwana biyu sai a kai kayan gidan ki", Anty tace "toh shknn, wnn tururuwar jama'a haka ai ba a rasa mai dogon hannu ba, yanxu sai ki ga kaya na ɓata, haka kurum su cuci yarinya mutanen yanxu ba imani", sai takwas da ƴan mintina Anty ta tafi gida.


★Washe gari Umma ta saka Mu'azzam ya kai lefen ɗakin Baba don ya gani, ko gama buɗe box ɗin atamfofi Umma ba tay ba ya dakatar da ita yace Allah ya saka albarka yasa rabonta ne, Umma tace "Ameen" ta rufe kayan, bayan Sallahr la'asar Hajar ta dawo gida, daman gidan Iya taje ta kwana abinta don haka bata san wainar da aka toya jiya ba, tasan dai za a kawo lefe, koda ta shiga ɗaki taga boxes ɗin lefen murmushi kawai tayi ta kawar da kai, ammafa sun burgeta, nace uhmm hajiya Hajar don ma ba kiga abin arziƙin dake ciki ba da sai bakinki ya yage. da yammacin ranar Naseer yazo sbd kiransa da Baba yayi, ya durƙusa ya gaida mahaifin nasa, Baba ya amsa yace "Naseer akan filina dake unguwar Ring road, kasan na sakasa a kasuwa?", Naseer ya shafa kai yace "Eh Baba na sani", Baba yace "toh yawwa, an samu mai siya, anyi ciniki anyi komai, kuma an samu riba sosai, kasan filin yanada girma kuma na daɗe da siyarsa", Naseer yace "Eh", Baba ya gaya masa adadin kuɗin, mazajen kuɗi Baba ya ambata, Naseer ya jinjina kai, Baba yace "yawwa, gida huɗu za'a raba kuɗin, kaso ɗaya na Hajara ne dashi za ai mata kayan ɗaki, ragowar kaso ukun kuma na Nabilah da Sa'adatu da Maimuna ne, suma duk ranar da Allah ya kawo musu mazaje sai ayi musu kayan ɗaki", Naseer ya gyaɗa kai yace "hakan yayi Baba, Allah ya ƙara girma", Baba yace "A Bank account ɗinka za a tura kuɗin", Naseer yace "toh Baba", Baba yace "idan aka ɗauki na Hajara sai kuma a nemi wani filin can wajen gari a siya da kuɗin su Nabilah", Naseer yace "nima ai akwai tawa gudummawar da zan bayar, zan siya mata katifu", Baba ya jinjina kai yace "Masha Allah, Allah yayi abarka ya yauƙaƙa maka hanyar samu, Allah ya baka ikon kula da ƙannenka ko bayan raina", Naseer yace "Ameen", Baba ya ciro wata paper daga aljihu ya miƙa masa yace "gashi lambar mai siyan filin ce, ka kirasa sai ka tura masa da account numbern", Naseer yace "tom" yasa hannu biyu ya amshi papern, tashi yayi ya fita, har karo suka kusa yi da Maama dake musu laɓe, zuciyarsa ce ta buga ganinta tsaye a ƙofar ɗakin, tayi masa wani mugun kallo tayi ƙasa da murya tace "biyoni Nasiru" ta shiga ɗakinta, dole ya bita ɗakin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, wani huci tayi tace "sbd kai sakarai ne wai zaka mata katifu, A'a ba katifu ba kamfanin Royal foam zaka siyar mata, toh wllh bada yawuna ba karka kuskura ko ficika ka bayar a bikin Hajara, idan kuma ka bayar to ban yafe ba wllh, kaji dai na gaya maka", murtuke fuska yayi yace "kiyi haƙuri Maama na riga na siya ai", hangame baki tayi tace "saika mayar kamfanin a baka kuɗinka, ai ba a ciniki dole, idan kuma bazaka mayar ba ni ka kawomin daman tawa ta ruɓe, kannenka duk sun lotse ta", baice komai ba ya miƙe ya fita zuciyarsa duk a dagule. Bayan sati biyu Umma na bakin rariya tana alwala, Balaraba ta zabga sallama a gidan, Umma ta amsa bayan tayi mata kallo ɗaya, Balaraba ta yatsine fuska tace "wai ina mutan gidan ne inata sallama bare na amsawa", da jin muryarta Maama ta fito tace "ai gamu nan, muna miki lale maraba", Balaraba tace "toh daga sallama sai bare su amsa", Maama tace "kedai mu shiga daga ciki", Maama ta yaye mata labule ta shiga snn itama ta shiga, Nabilah ce kawai a ɗakin, sauran kam sun tafi makarantar gogi, Maama tace "Nabilatuwa bamu waje kinji", Nabilah ta yatsine fuska tace "toh ni kuma inje ina?", Maama tace "tsakar gida zaki fita", sakkowa tayi daga ruɓaɓɓen gadon tace "tsakar gida akwai rana wllh", Maama tace "ki zauna can kusa da banɗaki ba rana anan", tace "Maama warin kwata fa?", fuskar Shanu Maama tayi tace "ke dalla malama fitarmin daga ɗaki don ma kinga ana lallaɓaki, fita malama", Nabilah ta zumɓuri baki ta zumbula hijab ta fita, Balaraba dake kallonsu tace "gsky Rabii kin sangarta ƴaƴan nan naki", Maama tace "nasan akwai magana tinda naga kin fito rana gatsal-gatsal", Balaraba tace "uhmm, ai bazan iya bari rana tayi sanyi ba maganar cina take", Maama ta samu waje ta zauna tace "toh ya muke ciki ƴar uwa?", Balaraba ta riƙe haɓa tace "uhmm, ai ƴaƴanki basu miki ƙarya ba Rabii, Nura ai shagon chaji ne dashi ammafa a da, dan yanxu a babbar kasuwar saida wayoyi ya mallaki babban shago, uwarsa ma tayi sana'ar sayar da ɗan wake ammafa banda yanzu, tashi ɗaya Allah ya azurtashi daman ance akwai shi da ƙoƙari da neman na kai, yanxu dai babu maganar matsolontaka ko faƙiranci a tattare dashi, Mahaifinsa ya mutu shine yake kula da ƙannensa mata biyu da mahaifiyarsa cikin yalwa da wadata", Maama ta sharce zufar da ta keto mata ta tashin hankali tace "na shiga uku, ynxu ya za ai Balaraba?".........✍️


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{29..}
Wani mugun murmushi Balaraba tayi tace "wnn ai bai kai abinda zaki shiga uku ba ƙawata, karki damu..", Maama ta katseta da faɗin "ya za kice kar na damu.., nace miki fa bana son yarinyar da uwarta su cigaba", Balaraba tayi tsaki tace "ai bazasu cigaban ba, me kike so ayi?", Maama tace "kar ayi auren nan ko ta halin ƙaƙa ne", Balaraba tace "kinxo ta gidan sauƙi, malamin tsamiya shi zai zartar miki da aiki kina zaune hankali kwance, wllh aikinsa kamar yankan wuƙa", Maama tace "yo ai idan ana neman ruwan kashe gobara har na kwata ɗiba ake, sai muje wajen nasa", Balaraba tace "hmm matsalarsa kuɗi, baya aiki sai yaji dumuss", Maama tace "wnn ba matsala bane, kamar nawa zan tanada?", Balaraba tace "Aƙalla ki riƙe dubu hamsin a hannunki", Maama ta gwalo ido tace "dubu hamsin, jar bala'i ina naga dubu hamsin", Balaraba tace "dole kam kiyo kashinsu in kina son burinki ya cika", Maama ta zabga tagumi tana tinanin a ina zata samo waɗannan kuɗi, Balaraba tace "uhmm idan so samu ne ma ace yanxu haka kinada kuɗin, in ban manta ba dududu saura wata ɗaya da sati biyu bikin ko?", Maama tace "haka yake", Balaraba tace "gsky dai ya kamata ki farga, ki nemo kuɗin nan fa", Maama tace "bani kwana uku zan nemosu kuwa", Balaraba tace "A toh kika tsaya bacci dai kwaɗo ne zai miki ƙafa", Maama tace "ke an ma samu fa an gama waɗannan kuɗi", Balaraba ta miƙe tace "to nidai nabi ta nan, daman cewa nayi bari nayi maza na ankarar dake", Maama tace "sai kin jini", Balaraba ta fito tsakar gida Maama biye da ita, a lokacin Hajar ta fito daga bayi knn, ta gefen ido Balaraba ke kallonta snn tayi soro, ta juya ta dubi Maama tace "itace ko?", Maama tace "itace shegiyar..", Balaraba ta jinjina kai sukay sallama da Maama ta tafi. Washe gari Hajar ta haɗa ƴan kayanta a Jaka zata wuce gidan Anty Jamila, tin ranar da aka kawo lefe Anty taso ta bita gidan amma Umma tace malam bazai bari ba, yanxun ma dai da kyar Baban ya amince, da yamma ta tafi bayan ta gama shirinta, murna wajen Hafsa ba'a cewa komai tace "yanzu fa shknn, ba zuwa gidan nan zaki ringa yi kina kwana ba", Hajar ta juya idonta tace "kin san me?", Hafsa tace "A'a saikin faɗa", Hajar tace "nifa banga lefen ba, ranar da aka kawo bana nan ina gidan Iya, kuma dana dawo ban bi takansu ba kar Umma tace min mara kunya", Hafsa tace "toh yanxu ya za ai?, gani za kiyi ne?, sai Anty tace miki mara kunyar", Hajar tace "A'a ke ni ba gani zanyi ba, ki gayamin mene ne aciki", Hafsa tace "chabbbb ai ki gani da idonki yafi, gsky fa ya sayyadinki ya zuba miki kaya", murmushi Hajar tayi tace "Allah..", Hafsa tace "Anty ta kira wacca za ta ringa yi miki gyaran jiki, ina jin ma jibi zata fara zuwa", Hajar ta gwalo lulu eyes ɗinta tana kallon jikinta tace "Me za a gyara", harararta Hafsa tayi tace "zaki gani ne aii". Humaira ce ta shigo tace "yaya Hajar wai kixo inji Anty", Hajar ta tashi tace "toh", suka fita tare da Humaira, room ɗin Anty suka shiga, Anty na zaune gefen gado ga boxes nan sun cika sararin ɗakin, Anty ta kalli Hajar tace "ki ma kwa ga kayan?", gyaɗa kai Hajar tayi tace "Eh", Anty tace "toh daman kiran da nay miki knn, tinda kin gani shknn", Hajar ta juya ta fita ta koma wajen Hafsa, tace "kiran da tay min tambayata tai naga kaya, ni kuma nace mata Eh", Hafsa tace "kinga kwantar da hankalinki, nasan Anty a wnn week ɗin ma saita fita, tinda bana zuwa schl an mana hutu mu bari idan ta fita sai muje kiga lefenki a tsanake".


★Da daddare Maama ta tarfa Sa'adatu da Maimuna a ɗaki, Sa'adatu tace "wllh Maama ni ba nida kuɗi, ina naga wata dubu talatin, ina ma laifin dubu goma amma shine za kice na baki dubu talatin, wllh ban dasu ba nida dalilinsu...", Maimuna da ta tamke fuska tamkar tsohon baƙin hadari tace "yo kema knn, bare ni, wai dubu ashirin", Maama tayi kwafa tace "duk za kuci gidan ku, dani kuke zancen, toh wllh ko kunƙi ko kun so sai kun bani kuɗin nan, yanxun nan ma kuwa", Maimuna tace "nidai Maama saidai ki yanka ni amma ban dasu eheee", Nabilah dake sauraron su tace "anayi ina cin indomie, ni kam ko ta kaina ba a bi sbd ansan babu, Hajjajai maza ku buɗe lalita hajiya Maama na jiran dumuss", Sa'adatu tace "ai kam dai baxa ta ji wani dumuss ba, Maama nidai kin san in ina dashi zan baki", Maimuna tace "nima dai in ina dashi zan.....", katseta Maama tayi da faɗin "ƙarya kike uwar mammaƙo, a gidan ubanwa kike ban iyee?, toh bari kuji in gaya muku karku zata ban sani ba, sarai nasan cewa ba makaranta kuke zuwa ba daga zarar kun fita sai ko waccen ku ta wuce shu'uninta, ko ku bani kuɗi ko na gayawa Babanku, kuma kun san cewa Nasiru na gida, babu abinda ya shalleni haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login