Showing 105001 words to 108000 words out of 114314 words
Chapter 36 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
abinda ya faru ta gaya mata, Sa'adatu ta ringa jinjina kai tana hura bubble da chewing gum din bakinta, Maimuna ta kwashe cinya tace "kinga walmukalafatun da Baba yayi min..", Sa'adatu tace "karki yarda wllh tllh, toh aiko shinkafar ɓeran kika zuba iya abinda za a miki knn, karki haƙura wllh..", Maimuna tace "ke ko ce miki akai zan haƙuri zaki yarda ne, dan na rantse da zabbatin Ubangiji bazan yarda ba..", Sa'adatu ta karyar da kai tace "wllh karki haƙura wannan halittar da ya mayar dake ai ya cuce ki, fuska duk ta suntuma, ji fa yadda idanunki suka koma ciki sai kace fuskar biri bukka, kibi dare idan ya kwanta ki rusa masa taɓarya a ka..", Maimuna tace "A'a ni bazan taɓasa da hannuna ba, dafa kuɗina a ƙugu, ƴan daba zan biya su lakaɗa masa duka su sassara banza su jefar a layii", Sa'adatu ta sheƙe da dariya tace "hakan yayi... wai ina Maama da waccan mai kai a tukunyar...?", Maimuna tace "Maama ta fita bansan inda taje ba, Nabilah kuma ta fita auno shinkafa...". babu jimawa Maama ta shigo gidan bayan ta dawo daga gidan Balaraba, ganin Sa'adatu Maama ta yaƙe haƙora tace "Sa'adatun Maama kin dawo...?", Sa'adatu tace "nadawo Maama..", Maama tace "ai kinga haka yafi kin cika alƙawari, kinga gobe ma sai nasan ƙaryar da zan shiryawa malam idan ya tambayeki, ina ƴan albarkar ƙawayen naki kuwa...?", Sa'adatu tace "suna nan kalau Maama sunce ma na gaisheki..", Maama ta washe haƙora tace "Ahh ina amsawa kuwa..", Nabilah ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda, kallo daya ta yiwa Sa'adatu ta ɗauke kanta, hijab dinta ta cire zata fita Maama tace "haba Annabilatuwa biki ga ƴar uwarki ba", Nabilah ta juyo tace "Au sannunta toh" da haka ta fice a ɗakin, gawayi ta zuba a kurfotu ta tashi wuta, tana fifita wutar Naseer ya shigo, ta masa sannu da zuwa ya amsa a taƙaice, Maama ta leƙo tace "A'a Nasiru sannu da zuwa..", Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita ya russuna ya gaisheta, Maama tace "lfy lou, ya wajen aikin..?", yace "Alhmdllh an gode Allah..", bai tambayi Baba ba sbd yasan dai a wnn lokacin Baba ya fita aiki, ganin haka yasa Nabilah tace "Yaya Baba yana nan fa..", yace "toh" ya shiga ɗakin Baban da Sallama, Maama ta zabgawa Nabilah wata harara tace "naga ranar da wnn munafikin canjin naki zai ɗore..", bayan Naseer sun gaisa da Baba yace "Baba ko dai jikin ne..?", Baba ya numfasa yace "Nasiru duk ranar da kuka wayi gari bani toh mahaifiyarku ce sila..", Naseer ya kasa cewa komai tsabar ydda mgnar Baba ta dakesa, can dai yace "Ayi haƙuri Baba, Allah ya huci zuciyarku..", Baba yace "haƙuri ai ya zama dole tinda ta gama zubamin virus ta haifeku...", Naseer dai kawai haƙuri ya ringa basa duk da cewa bai san me ya faru ba.
★Kamar yadda Nurain yace kafin 12noon zai iso hospital, 11:40 ya isa hospital din, yana shiga office dinsa yasa Haleema ta kira masa his team members, har zai wuce sai kuma ya dawo yace "exclude A Nurse, call Nurse Amina instead..", Haleema tace "yess sir", ta ɗauki landline ta shiga kiran members din, babu jimawa kam All of them suka hallara a office din, Nurse Amina ce kawai ba tazo ba, briefing dinsu Nurain yayi akan surgeryn da zasu shiga, daga nan suka fita to get ready, Nurain na wanke hannunsa kafin ya shiga surgery room din Khaleel ya da already dressed up in surgeon gown da nose mask a fuskarsa amma bai rufe hancin ba ya iso wajen yace "Boss everyone is here banda Nurse Amina, kuma i informed her tace tana zuwa..", Nurain na cigaba da wanke hannunsa yace "lets wait for her since the surgery is not yet started...", Khaleel yace "sure..", Nurain na gama wanke hands daman already ya sanya surgical Scrub. Surgery room din ya shiga, wani Nurse dake riƙe da surgeon gown ya ƙaraso kusa da shi helping him to wear the gown, Nurain ya saka nose mask da hand gloves kafin ya isa position dinsa na head of the surgery ya tsaya, patient din daman tintini aka masa anesthesia. Ruqayyah na zaune Nurse station duk abin duniya ya isheta, tinda tazo babu wani aikin arziƙi da tayi kawai safa da marwa take tsakanin Nurse station da Office din Nurain, taje office din yafi sau biyar saita tarar baizo ba, Nurse Amina ce ta shigo station din in a hurry tace "please Ruqayyah ki kulamin da ward C ina dawowa..", Ruqayyah tace "ina zaki haka..?", Nurse Amina ta dafe goshinta tace "Dr Uthman ne yake nemana a surgery room..", miƙewa Ruqayyah tayi tace "surgery zaiyi knn..?", Nurse Amina tace "eh..", wani irin ɗaci Ruqayyah taji ya taso mata daga zuciya, she is part of the team toh me yasa ake neman wata Nurse din bayan gata, Nurse Amina tace "Please Rukky..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "A'a gaskiya bazan kula miki da ward ba saidai ke ki zauna in shiga surgeryn", Nurse Amina tace "ai kwa da na fi son hakan ma, nagode sosai..", Ruqayyah tace "don't mention" da haka ta bar station din walking fast, surgery gown ta ɗora kan uniform dinta ta saka nose mask da gloves kafin ta shiga surgery room din kanta a ƙasa, with respect ta ɗan russuna tace "sorry Dr..", Khaleel yace "come closer..", ta ƙarasa ciki tana satan kallon Nurain, surgery tray ta dauka ta tsaya position dinta, ta ɗauki Scalpel ta miƙawa Nurain, da haka aka fara surgeryn, kawai aikinsa yake cike da nutsuwa yayinda Ruqayyah ta kafa masa idanu tamkar zata cinyesa, wani sa'in ma sai yace ta basa instrument snn take basa sbd rashin nutsuwa, a haka dai har suka gama surgeryn, bayan an fita da patient din sauran doctors din ma sun fita Nurain ya cire hands gloves yayi disposing, sauke nose mask din fuskarsa yayi ya wuce zai bar room din, Ruqayyah tace "Dr...", ya juyo yace "yess Nurse Amina...", idonta yayi rau rau ta kai hannu ta zame nose mask dinta....✍️
Arewabooks @ feenerhfeeche02
💛 HAJAR 💛
Feenerh feeche ce
{47..}
Da mamaki Nurain ya ringa kallonta dan bai taɓa tunanin da ita akay surgeryn ba Nurse Amina ba, Ruqayyah ta sauke idonta ƙasa a hankali tace "the surgery was a success, alhmdllh..", baice mata ƙala ba ya juya ya fita daga surgery room din ya barta tsaye, tabi bayansa da kallo hawayen da suka taru idonta suka fara bin kuncinta, fita tayi daga room din bayan ta gama matsewa, ta cire surgeon gown kafin ta wuce Nurse station, bag dinta ta buɗe ta ɗauki black Abaya ta ɗora saman uniform dinta, daga haka ta saƙala jakarta a shoulder ta yiwa colleagues dinta sallama ta bar hospital din, tana fita titi ta tari napep ta gaya masa unguwar da zai kaita, shiga napep din tayi bayan sun gama ciniki, tafiyar minti ashirin ce ta kaisu unguwar, ya shiga da ita har layin da ta masa kwatance, sauka tayi daga napep din ta buɗe handbag dinta ta ciro kuɗinsa ta basa, ya miƙa mata chanjinta yaja machine dinsa, wani gida mai brown paint da black gate ta dosa ta fara knocking, almajirin gidan ne ya buɗe mata, bayan ta shiga ya gaisheta ta amsa a takaice kafin ta nufi entrance din gidan, ta buɗe ƙofa ta shiga palour da sallama, ƙarewa palourn dake tashi da ƙamshin turaren wuta gauraye da na freshner kallo take sai kace wani baƙonta, ta sake yin wata sallamar kafin ta zauna kan kujera, ƙofar wani room dake palourn aka buɗe, Kulsoom ta fito da 2months old babyn ta goye a baya tana jijjigasa, ganin Ruqayyah tace "Ruqayyatu kece kika ta sallama sai kace wata baƙuwa..", Ruqayyah ta cire ƙaramin hijab dinta tayi resting da kujera tace "ina wuni sister..", Kulsoom ta ƙaraso cikin palourn tana jijjiga babyn dake ƙishi ƙishin kuka tace "mun yini lfy...", Ruqayyah tace "alhmdllh..", Kulsoom na kallon fuskar ƴar uwarta ta da ta lura tayi duhu tace "kin kwaso rana..", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya tace "kawosa naga kamar kuka zaiyi..", Kulsoom ta kwanto babyn ta miƙa mata tace "rigimamme ne wllh.." da haka ta wuce kitchen, Ruqayyah ta ringa kallon Babyn kafin ta lakuce masa hanci tace "shine kake wa sister na kukan banza ko, tubarkallah ga ka dai narkeke sai kace ba watanka biyu ba bare ace yunwa kake ji", ta ringa patting soft cheeks dinsa, deeply in her mind taji dama babyn ta ne, da anyi aurenta da Dearest da tini itama ta kusa haifar baby, Kulsoom ta fito kitchen da tray a hannunta, ajiye trayn tayi kan Centre table tace "toh ga ruwa kisha kafin na gama girki na ga kinyi wani wujiga wujiga...", Ruqayyah tace "na gaji ne, kuma gashi na shiga surgery yau na 3hours", Kulsoom dai ta gyaɗa kai tace "Okay", a ƙasan ranta tasan bayan gajiya akwai damuwa a tattare da Ruqayyah, Ruqayyah ta zuba ruwa tasha tana jin yadda sanyin ruwan ya sanyaya mata maƙoshi, bayan kamar 15mins Kulsoom ta tashi ta shiga kitchen, babu jimawa ta fito da plate da bowl a hannunta, Ruqayyah ta ringa kallon abincin tana jin appetite dinta na dawowa, lafiyayyen dambun shinkafa ne wanda yaji attaruhu da albasa da gyaɗa yana bayar da wani ƙayataccen aroma, sai kuma coleslaw a bowl, Ruqayyah ta janyo abincin tana ci a hankali, kallonta Kulsoom ta ringa yi tana feeding babyn ta, saida taga ta ture plate din alamar ta ƙoshi tace "kin gama....?", Ruqayyah tayi gyatsa tace "alhmdllh, godiya dubu..", Kulsoom na shafa kan babyn ta looking at Ruqayyah tace "now tell me, me yake damunki sister...?", Ruqayyah ta zaro ido tace "Ni.. me kika gani..?", Kulsoom ta saka serious face tace "haba Ruqayyah nifa ƴar uwarki ce na sanki ciki da bai, wllh there most be something troubling you, ji fa yadda kika rame kuma kinyi duhu ai ba haka hasken ki yake ba..", Ruqayyah bata san lokacin da hawaye ya fara zuba cheeks dinta ba, Kulsoom ba tace komai ba kawai kallonta take, Ruqayyah ta share hawayen tace "tin lokacin da na dawo Daddy ya yankamin warning cewa na fito da miji shi aurar dani zaiyi idan kuma banyi hakan ba zai aura min Dauda, Dauda fa wnn mai bacogalar ƙafar, da kyar da maƙyarƙyata na shawo kan Momy ta shigemin a wajen Daddy bayan na shirga mata ƙarya nace ai mun sasanta da Dr, idan ya dawo daga tafiya za a ɗaura mna aure, da haka na samu abubuwa suka lafamin a wajen Daddy, sister wllh na gama sakankancewa ina tutiya da irin son da Dr yake min kawai jira nake ya dawo na basa haƙuri, and now he is back almost 2weeks da dawowarsa, nayi kiran a waya na tura text message amma duk a banza, babu kalar haƙurin da ban rubuta a message na tura masa ba amma he didn't respond to any of it, ke na ƙarƙare miki mgana jiya har office dinsa naje ina basa haƙuri amma yaƙi saurarata, daga ƙarshe ya kiramin security, yau kam he kick me out of the surgery team..", Ruqayyah ta fashe da kuka tace "wllh Allah ina sonsa, i can't live without him Allah kuwa..", Kulsoom ta jinjina kai ta kwantar da Babyn da ta gama feeding tace "gsky kinyi babban kuskure da kika yiwa Momy ƙarya Ruqayyah..", Ruqayyah tace "toh ya zanyi sister dole ce tasa na mata ƙaryar nan, da banyi haka ba da tini an wuce wajen an auramin Dauda bacogala..", Kulsoom tace "ke kika fusata Daddy shiyasa ya kafe sai ya aurar dake, Ruqayyah yau inda ace baki aikata abinda kika yi ba wllh kinji dai har na rantse babu abinda zai sa Daddy ya miki auren dole, zai dauka cewa Allah ne bai kawo lokacin aurenki ba, amma akazo akay komai da komai ranar ɗaurin aure kika kwashi ƙafa kika gudu...", Ruqayyah ta kastseta da faɗin "wllh ba guduwa nayi ba..", Kulsoom ta haɗe gira tace "let me land malama, idan ba guduwar ki kay ba toh uban me ki kai, yanzu dai ina baki shawara kije ki gayawa Momy cewa ƙarya kika shirga mata snn kuma ki haƙura da wani Dr, yo Allah na tuba mazan yanzu har wasu abin so ne, an gaya miki in this era ana yiwa namiji makahon so ne, namiji ya soka ma yaka ƙare da wulaƙancin sa ballantana wanda ya fito ra'ayil aini ya nuna baya sonka, idan Dr ya soki a baya toh yanzu ba hakan bane, ai kin masa narkakken wulaƙanci ba ƙarya duk abinda ya miki ke kika siya da kuɗinki, so wake up malama ki san inda yake miki ciwo, kin zauna kina wani ɓare baki kina kuka shaɓa shaɓe akan wani namiji.... ehen ki ajiyesa a gefe ko shine autan maza", tinda ta fara magana Ruqayyah ta saki baki hanci kunne tana kallonta tamkar wata psycho, idonta har wani wulƙilewa yayi tsabar yadda take kallon Kulsoom cike da ruɗin abinda ta gaya mata, Dearest din zata ajiye a gefe, da kyar ta iya cewa "wai doctorn zan ajiye a gefe..?", Kulsoom tace "yhap shi din mna tinda kinyi loosing opportunity tin farko...", Ruqayyah ba ta sake cewa komai ba ta fara haɗa kayanta, ta saka wayarta a jaka, hijab dinta ta sanya kafin ta miƙe ta fara zura Abaya, Kulsoom ta bita da ido, Ruqayyah na gama saka Abayar ta ɗauki handbag dinta tace "sai anjima", Kulsoom ta taɓe baki tace "mu jima da yawa..", ficewa Ruqayyah tayi daga gidan fuskarta a haɗe, da badan Kulsoom ƴar uwarta bace da babu abinda zai hanata danƙara mata baƙar magana, kuma taci sa'a elder sister dinta ce yau da ace itace gaba da Kulsoom to babu abinda zai dakatar da ita daga kwalla mata marii, wai ta ajiye Dearest a gefe wato ta rabu da shi, never ever babu abinda zai sa ta rabu da shi sai mutuwa, tana isa bakin titi ta tari napep zuwa gida.
★Hajar ta gyara ɗakinta fes bayan ta gama cin Noodles da ta dafa, ta rufe ɗakin ta sauka downstairs zata kai plate da cup din da tayi amfani dasu kitchen, gaban sink ta tsaya tana kallon liquid soap dake wajen, ta kunna pampo ta matsa liquid soap din a plate ta tashi foam, sponge ta dauka ta fara wanke utensils din da ta ɓata, tass ta wankesu ta kife a inda ta ɗauka, duk da kitchen din babu datti amma saida ta sake gyarasa, tayi drying hannunta da towel kafin ta fita daga kitchen din, room dinta ta koma tayi zugum sai kace wata prisoner, can dai ta gaji da zaman daƙin ta tashi ta fita, ta kitchen tabi ta fita daga gidan zuwa backyard, through out the day anan tayi zamanta kamar dai jiya sai idan za tayi sallah ne take komawa ciki, bayan ta idar da sallar la'asar ta birkito kayan da ta saka set biyu sai nities da hijab biyu, toilet ta shiga da kayan ta zazzaga detergent a bucket ta shiga wankesu duk da cewa ba suyi wani datti ba, tana gama wankewa ta ɗauraye toilet din ta fito da kayan cikin bucket, can backyard din ta wuce ta shanya kayan jikin flowers, tana cikin shanyar saiga mai gadi da watering can a hannunsa zai bawa flowers ruwan yamma, dan russunawa yayi ya gaisheta ta amsa kafin ta ɗauki bucket din tabar wajen dan ta gama shanyar, tana shiga palour taji kamar ana buɗe main door din gidan, ta ringa kallon ƙofar har aka buɗeta, Nurain ne ya shigo Farooq biye dashi, suna yin ido huɗu tayi sauri ta ɗauke kanta ta wuce zata haura sama taji ance "Amarya..", dakatawa tayi amma bata juya ba, Nurain ya wurgawa Farooq wani kallo kafin ya wuce ya haye sama, Farooq ya ɗaga shoulder ya ƙarasa cikin palourn, a hankali Hajar tace "ina yini..", Farooq yayi murmushi yace "lfy lou amarya.. how are you..", tace "am fine thank you.." da haka ta nufi stairs ta haura sama, Farooq ya zaune kan kujera ya ciro wayarsa daga pocket yana latsawa, after 20mins yana zaune palourn ya daga kai yana kallon stairs, contact ya shiga yayi dialing numbern Nurain har ta gama ringing bai ɗauka ba, babu jimawa saiga shi nan yana sakkowa, Farooq ya ringa kallonsa har ya ƙaraso palourn yace "muje..", Farooq bai motsa ba yace "daga ɗakko paper saika tsaya wanka kuma..", Nurain ya nufi door yace "c^mon let go..", Farooq na fitowa Nurain ya rufe ƙofar da mukulli, shidai Farooq yana so yace wani abun amma dai ya fasa, a tare suka nufi gate, Inuwa dake zaune nan bakin gate din yayi saurin miƙewa har suka ƙaraso, russunawa yayi ya gaidasu duka, shidai bai san lokacin da suka shigo ba sbd a lokacin ya tafi can backyard, Nurain yace "ba wanda yazo..?", Inuwa yace "Eh Alhj..", Nurain yace "Okay, zan sake fita sai na dawo..", Inuwa yace "Allah ya tsare..", Nurain yace "Ameen" ya buɗe ƙofa suka fita gidan da Farooq, motarsa da ya parker nan waje ya bude ya shiga, Farooq ya shiga front seat, tada Motar Nurain yayi ya fara driving out of the street, suna hawa main road Farooq yace "Allah yasa dai ba rufe yar mutane kake a gida ba..", banza Nurain yayi dashi kamar baiji ba, Farooq ya sake cewa "kaga idan ma rufeta kake to ka dena dan naji Mami tayi complain akan hakan a asibiti..", still Nurain bai tanka masa ba kawai driving dinsa yake, Farooq ya gyara zama yace "if i were you banza zanyi da rayuwa wllh, tini zan saki jikina with my cutie wifey, the girl is so cute...", Nurain ya ƙara speed din motar kafin ya juyo ya dubi Farooq yace "really, tinda she is cute idan kana sonta sai in saketa kawai ka aureta punk...", Farooq ya haɗe gira yace "you're not serious...", Nurain yace "am jet serious..", da wani irin expression Farooq ya ringa kallonsa ya kasa cewa komai, Nurain ya juyo sukay ido huɗu, ganin reaction din fuskarsa Nurain yayi murmushi, Farooq ya fara latsa wayarsa