Showing 21001 words to 24000 words out of 114314 words

Chapter 8 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5281

dinta ta zubasu a jaka, wayar ma ta wurgata a jaka, a lokacin aka fara announcing jirginsu zai boarding, ta miƙe tabi queue akay checking dinta sannan ta shiga Flight, ta zauna a seat dake kusa da window ta jinginar da kanta ta lumshe ido, wata mata da take gefenta ce ta taɓota jin anata cewa kowa ya saka belt dinsa jirgi zai tashi amma bata motsa ba, Ruqayyah ta buɗe idonta da sukay jajur ta kalli matar, matar tayi mata murmushi tace "fasten your seat belt lady", Ruqayyah tace "thank you" da dasasshiyar muryarta, ta janyo belt ɗin ta ɗaura, Jirginsu ya sharara gudu akan runway kana ya ɗaga zuwa sararin samaniya.


★Da wani irin expression Anty Zulaiha ta kalli Mami jin abinda ta gama faɗa tace "innalillahi wa'inna ilayhirraji'un, yanzu yarinyar da Nurain zai aura ce ta gudu", Mami tayi ajiyar zuciya tace "wai neman me kike min ne tin ɗazu?", Anty Zulaiha tace "ai magana ma ta wuce, yanzu where is my Son", Mami tace "yana ɗakinsa, Allah yasa ma bai fita ba, he will be okay", Sakeena ta shigo tare da Noor, Noor ta kalli Mami tace "wai me yake damun yaya ne, kamar naga bashi da lfy lokacin da nazo kiranki?", Mami ta kalli Sakeena tace "ina abincin Abba da nace ki ajiye?", Sakeena tace "yana nan", Mami tace "toh ki kai masa yanzu", Sakeena tace "ai sun tafi wajen ɗaurin Aure", Mami tace "ai ba wani ɗaurin Aure da za ai an fasa" ta miƙe ta fita, Sakeena da Noor suka bi bayanta da kallo domin suna buƙatar concrete explanation ne akan maganarta, tana fita sai suka juya a tare suka kalli Anty Zulaiha da ta wayance da buɗe foil papern da aka rufe peppered chicken da ita, Na reception din Nurain ne wanda za a ƙara akan wanda akay order, Sakeena tace "Anty nifa bangane me Mami take nufi ba", Anty Zulaiha tace "Eh an fasa auren", Noor tace "but why?", Anty Zulaiha ta gaya musu komai. Sakeena taji zafi sosai, her only brother wanda take jinsa tamkar shaƙiƙinta, ita har mantawa take ba mahaifiyarsu ɗaya ba, indai Nurain zai kaiwa Ruqayyah wata kyauta kamar Ramadan basket da sallah gift ko kuma dai wani abin haka itace take shirya masa, ko jiya da ta ganshi da daddare a balcony yana waya da Ruqayyah saida ta tsokanesa, duk irin crush dinsa da ƴan mata suke amma ita ɗin dai yake so kuma bai haɗata da ko wace mace ba yana dating, shin her brother yayi deserving irin wnn yaudarar daga Ruqayyah. Biki dai ya mutu ƙurmus, ƴan biki da ɓaki kowa ya ɗaɗe gida ya koma sai ƴar cikinsa daga Anty Zulaiha sai Sakeena ne suka rage, Nurain all this while yana room ɗinsa bai sakko ba kuma Anty Zulaiha ta hana kowa yaje gunsa tace abarsa zuciyarsa ta huta, sai dare da misalin ƙarfe goma sannan Sakeena ta zuba abinci da drinks ta ɗora akan tray zata kai masa, Noor da Khausar ne kawai a main palour, Sakeena tazo zata wuce da abincin Noor tace "amm na yaya Nurain ne?", Sakeena tace "Eh", Noor ta miƙe tace "wait a minute" ta shiga kitchen, few minutes ta jona coffee maker ta haɗa wani yummy coffee ta tsiyaye a Mug, ta fito da Mug ɗin mai ɗauke da coffeen ta ɗora akan trayn hannun Sakeena tace "idan ma bai ci abincin ba I'm very sure zai sha coffeen ko yaya ne", Sakeena tabi stairs zuwa room ɗinsa, a hankali tayi knocking sai kuma ta kara bakinta jikin ƙofar tace "brother nice" ta murɗa handle ɗin ƙofar, half expected ta jita a ƙulle amma sai taji ta a buɗe, ɗakin dulum dunɗum duk an kashe light, ta wawaki bango ta danna switch ɗin fitilu, a take haske ya mamaye ɗakin, yana kwance akan gado yayi rigingine, farar T-shirt da brown trouser ne ajikinsa ya cire na ɗaurin Auren da basu gama daidaita ajikinsa ba, ga nan wayarsa a tarwatse ko sake bin takanta beyi ba, Sakeena ta kallesa kana ta ajiye trayn akan rest chair tace "brother ga abinci na kawo maka, plxx eat", ya ɗago ya kalleta yace "thank you", tace "ga coffee ma Noory ta haɗa maka", kalmar coffeen da ta ambata tasa yaji wata suya a zuciyarsa yace "sister off the lights", bata ce komai ba ta kashe fitilar sannan ta fita a ɗakin. Bayan kwanaki Biyu Momy da haj Safiyya da kuma Kulsum da Aysha suka zo gidansu Nurain, tamkar babu wani abu da ya faru Mami ta saukesu, bayan sun zazzauna ne saiga Garba nan ya fara shigo da akwatuna, Mami ta kalli akwatin na lefen Nurain ne, Momy ita dai duk kunya ta dameta, saida Garba ya gama shigo da akwatuna sannan Momy ta shigar da abinda ya kawosu, takanas suka zo bada haƙuri akan abinda ƴarsu tayi, Momy ta kalli akwatunan da suke tuli guda kuma shaƙure da kaya tace "ga kayan yaron nan, akwai waɗanda aka ɗinka Insha Allah suma za'a ciko su, dan Allah hajiya a bawa yaron nan haƙuri", Mami tayi murmushin yaƙe tace "ba komai ba sai an ciko ba, anga ita Ruqayyahn kuwa?", Momy tace "da kanta ta fita kuma dan kanta zata dawo, babu wani nemanta da zamu tsaya yi", Mami tace "Aa ai baza ai haka ba, hannunka baya taɓa ruɓewa ka gutsire ka yar, ya kamata a nemeta ai macace", Haj Safiyya ta ciro bunch of keys ta miƙawa Mami tace "mukullin gida ne da yake gurinmu, ai ba kaya ma muka zuba aciki ba ɗan albarkar yaron nan ya zuba komai a gidansa", Mami ta karɓi keys ɗin tana jin daɗi ɗanta ya samu shaida mai kyau, kuma ta godewa Allah da bashi bane ya kawo tangarɗa, basu wani jima ba suka yi sallama suka wuce.


★Da dare bayan Sallahr isha'i Hajar ta gyara fuskarta da oil control powder ta shafa colourless lipgloss a lips ɗinta, ta zauna a gefen gado tana jiran isowar Nura sbd yau ranar zuwansa ce, babu jimawa sai ga kiransa nan ya shigo wayarta ta ɗauka tace gata nan fitowa amma kuma tana zaune daram babu niyyar tashi, saida ta kwashi minti biyar sannan ta miƙe ta sake kallon kanta a mirror tana murza lips dinta ta saka hijab, darduma ta ɗauka guda biyu sannan ta fito tsakar gida, Umma da take bakin murhu ta kalla tace "Umma na fita soro", Umma tace "tom saikin dawo", Hajar ta nufi hanyar soro, tin kafin ta kai soron taji ƙamshin turarensa, ta isa da sallama ba tare da ta dubesa ba ta fara shimfiɗa dardumar, ya karɓi ɗayar yace "bari na taya ki" ya shimfiɗa ɗan nesa kaɗan da ta ta, ya zauna ya tanƙwashe ƙafarsa, itama ta zauna tana wasa da ƙasan hijab dinta suka gaisa, yace "kin taho da takardun naki kuwa?", tace "A'a zan shiga na ɗakko maka idan zaka wuce", ya ɗauki wayarsa da yake haska musu fitilarta, gallery ya shiga ya buɗo wani uncompleted building, ya haska mata screen ɗin wayar yace "kinga abinda ya wahalar miki dani", ta kalli hoton tace "har an zuba dakin?", yace "eh Allah ya bada iko" sai kuma yayi gaba ya buɗo wani hoton shi kuma na windows ne sliding da door irin na gida da ake ƙerasu da inganci, yace "kinga suma waɗan nan na gama da babinsu", ya sake buɗo wani hoton na kayan bathroom masu kyau har set biyu yace "kinga 2 bedroom toilets suma na gama dasu", Hajar sai murmushi take suna tsara yadda gidansu zai kasance tare da tanadi mai kyau na futuren su. da wata iriyar tafiya irinta mata ƴan duniya Sa'adatu ta shigo, har ta wucesu sai kuma ta dawo tana yamutsa fuska, Hajar da Nura ko ɗaga kansu su kalleta basuyi ba suka cigaba da kallonsu, Sa'adatu ta zuge handbag ɗinta ta ciro tsaleliyar wayarta da mabaruka ta siya mata, fitilar wayar mai haske ta kunna ta dallare su da ita tana jan dogon tsaki, Hajar ta ɗago kanta tana micincina ido sbd yadda hasken ya kashe mata ido, Sa'adatu ta hura kwai da chewing gum din bakinta sai kuma ta taunesa ya bada sautin ƙass, ta buga wani uban tsaki tace "ke ashe naki iskancin haka yake, wato ke ƴar iska shine kike kawo mana ƙattin banza har cikin gida ko?", Hajar ta ɗauke kanta sbd bata so ta tanka mata a wnn lokacin, Sa'adatu kuma already tayi noticing dinta dan haka ta sake ɗaura ɗammarar ci mata fuska a gaban Nura, ta sake dallare fuskokinsu tace "dalla malam tashi ka fitar mana daga gida, ka bari ta biyoka shago mana, amma bazaku yi mana sheɗanci a soron gida ba", Hajar was burning inside kuma she can't take it anymore, ta miƙe tamkar wacca aka tsikarawa allura tana huci..........✍️


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{13...}
Sa'adatu ta dallare Hajar da ta miƙe da fitilar wayarta, Hajar tayi mata wani irin kallo sai kuma ta wuce cikin gida ta shiga ɗaki, umma tana ganin yanayinta saita bita ɗakin, wardrobe ta buɗe inda take ajiye muhimman takardunta tana dube-dube, umma ta kalleta tace "lafiyarki kuwa hajara?, Nuran ya tafi ne?", Hajar ta cigaba da ɗaɗɗaga takardu hawaye ya cika mata ido tace "umma wnn wane irin masifa da bala'i ne?, Maama da ƴaƴanta wllh annobane, ni kam nagaji da haƙuri dasu, na rantse da girman Allah daga yau duk wacca ta sake shiga harkata saina raunata ta, anƙi ayi haƙurin dasu, idan zaman lfy toh za'a zauna lfy ɗin, idan kuma zaman tashin hankali toh za'a tashi hankalin fiye da kima.....", umma ta katseta tace "toh maza ki ɗauki harama tinda ke kika haifi kanki, yanzu me ya faru?, naga dai zaune kike a soro da Nura", Hajar ta ɗauki envelop ɗin credentials ɗinta ta zauna a gefen gado ta share hawayen da ya zubo mata tace "Sa'adatu ce", umma tace "me Sa'adatun tayi?", Hajar ta gaya mata abinda tayi musu a soro, Umma tace "shknn, dafatan dai biki tanka mata ba?", Hajar ta girgiza kai tace "bance mata komai ba kawai tasowa nayi na dawo gida, wllh nasan idan na zauna za'a iya haifar ɗa mara ido", umma ta zabga mata harara tace "wato har wani cewa kike za'a haifi ɗa mara ido ko?, Hajara ki ringa sanyaya zuciyarki, ki dena ɗaukar komai da zafi, yanzu waɗan nan takardun su kuma me sukay miki da kika birkito su?", Hajar tace "shine yace na kai masa", Umma tace "A'a naga ai kin basa takardun naki kwanaki?", Hajar tace "Eh, ai na secondary na basa, yanzu kuma primary certificate da testimonial zan basa", umma tace "toh, tashi ki kai masa saiki dawo gida gobe kwa ƙarasa". Hajar ta miƙe ta fita da envelope a hannunta, kasa kallonsa tayi tace "ga takardun", ya miƙe ya amsa sai kuma ya nannaɗe dardumar da ya tashi daga kai ya naɗe ta Hajar ɗinma, ita dai kawai wasa take da fingers ɗinta tace "dama ka barshi zanyi ai", yace "na hutar dake", ya miƙa mata darduman tare da wayarta da ta ajiye a wajen yace "toh seda safe", ta karɓa kanta a ƙasa tace "seda safe", ya tsaya yana kallonta yace "toh shiga gida", ta juya a hankali ta shiga gida shi kuma yayi tafiyarsa, Hajar ta tsaya daga bakin rariya ta kunna wayarta tana murmushin mugunta tace "idan kinci bulus shegiya nake", ta shiga contact ta lalubo numbern Naseer tayi dialing, bata daɗe da fara ringing ba ya ɗaga, ta sauke ajiyar zuciya tace "Yaya ina wuni", daga ɗayan ɓangaren Naseer yace "lafiya lou Hajar", tace "yaya daman Sa'adatu ce tazo, gata can sai rashin kunya takewa Maama sbd tace karta sake barin gida..", Naseer ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba, Hajar ta kalli screen ɗin wayar tayi murmushi, tasan yanzu haka gida zai taho, daman tasan yana neman Sa'adatu tinda duk zuwan da yake takan ji yana tambayar Nabila ko Maama ina take wani sa'in. ta wuce tsakar gida ta tsaya tana kallon ɗakin Maama da ake jiyo muryoyinsu daga ciki suna hira da shewa, muryar Sa'adatu tafi ta kowa tashi, Hajar ta yamutsa fuska tace "zaki ɗanɗana ne jaka" tayi wucewarta ɗaki. Nabilah ta juya tsaleliyar wayar hannunta tace "yanzu Sa'adatu wnn wayar ta mazajen kuɗi itace a hannunki", Sa'adatu tace "rass ma kuwa ya son ranki, masoyiya Mabruk ce ta siya min", Maama ta karɓi wayar daga hannun Nabilah tace "gaskiya yaran nan suna sonki da arziƙi, nawa ma kika ce kuɗin ta?", Sa'adatu tayi kwai da chewing gum ɗin bakinta tace "dubu ɗari biyar", Maama tace "caɓɗijam", Maimuna da take kan gado ta sakko tace "yawwa Sa'adatu kince zaki faɗamin sunan man da kika koma shafawa wanda yasa kika koma fara gaba ɗayanki", Sa'adatu ta harareta tace "wane irin mai, yarinya wasa ma kike, ni na dena shafa mai sbd ɓata lokaci ne, allura ake min", Maimuna tace "Allura..??", Sa'adatu tace "rass, har fatar kaina da mazaunai na sun koma farare yanzu", Maimuna tace "chab gaskiya bazan iya allura ba", Sa'adatu tace "yo shknn kiyi ta shafa mai yana miki glass a fuska, yanzu ma kalli fuskarki kamar an watsa fitsari duk tayi wani jirwaye, ga wani map of Africa a kumatunki", Maimuna tace "naji, a haka Alhaj ɗina yake so", Sa'adatu ta warce wayarta da take hannun Maama ta duba lokaci, ta ɗauki handbag ɗinta ta ciro maƙudan kuɗi ta lalo dubu ashirin ta miƙawa Maama tace "toh da haka da haka baƙo zaiyi halinsa", Maama ta soke kuɗin a kirjinta tace "Au ƴar nan tafiya zaki yi baza ki kwana ba", Sa'adatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta sai kace wacca ta zauna a sahara tace "la la la bazan kwana ba wllh, kuɗin cizo da sauro suyi min illah", Nabilah tace "Sa'adatu naga kin mayar da kuɗin jaka, ni kuma fa ba ki ɗusheni ba", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "ai kece kinƙi ki waye, yanzu Maimu ba gashi nan ba kullum da ƴan canjinta a ƙugu, miƙomin jakar", Nabilah gaba take da Sa'adatu amma haka ta ɗauki jaka ta miƙa mata da hannu biyu, dubu biyar Sa'adatu ta lalo ta mannawa Nabilah a ƙirji tace "gashi dai mai kai a tukunya", Nabilah ta dafe kuɗin ta linkesu ta cusa a bra. Sa'adatu tace "toh na tafi Maama", Maama tace "karki daɗe baki zo ba kinji", Sa'adatu tace "toh zan duba na gani" ta fito tsakar gida ta saka takalmi ta fita. A soro sukay kaciɓus da Naseer wanda ya shigo a fusace, zuciyarta ta buga da ƙarfi ta juya zata koma ciki, wani gigitaccen marii ya sauke mata a fuska, tayi taga-taga tamkar zata waɗi ta bugu da bango, tsaleliyar wayarta saura ƙiris ta faɗi daga hannunta, tana dawowa hayyacinta ta ruga cikin gida ya biyota da sauri, takalmin da yake ƙafarta mai tsini ya gurɗeta aikam tayi mummunar faduwa a ƙasa daɓas, wayar hannunta kamar wacca aka fuzge haka tayi tsalle ta daki bango, Sa'adatu ta ɗora hannu a ka ta kurma ihu tace "wayyo wayata", Baba ya fito daga ɗakinsa da sauri yace "Nasiru zane min ita, zaneta nace", Maama ta fito jin abinda yake faruwa tana hura hanci tace "wllh karka kuskura ka taɓa ta", Baba zuciyarsa na masa zafi yace "Rabi idan kika sake magana anan wajen na rantse da girman Allah saina tsinke jemammiyar igiyar aurenki guda ɗaya da ta rage", Maama ta dafe ƙirji ta zaro ido amma ta kasa cewa komai, Saki kuma da girmanta da gemunta ace za'a saketa, dama igiyoyin auren saura ɗaya ce ta rage, Baba yace "Nasiru ka zane min ita", Sa'adatu ta wawaki ƙasa zata miƙe ta afka ɗakin Maama amma ina tini Naseer ya fuzgota. wani mabirki mai kauri na icce wanda ake kaɗa miyar yauƙi dashi ya ɗauka, Naseer ya ringa rankwala mata shi a jiki, saida ya kakkafe mata tsoka tass, ƴan yatsenta kam kamar zasu zube sbd yafi rankwala mata anan, Maama dai kawai kumbura take tana sacewa ita kaɗai, saida Sa'adatu ta faɗawa ƴan garinsu sannan Baba yace "ya isa haka, kullemin ita a can" yayi nuni da kitchen wanda basa amfani dashi sai tara shirgi, gaba ɗaya kitchen ɗin ya mutu, Naseer ya figi Sa'adatu ya dannata aciki ya banko mushiyar ƙofar langa-langar, Baba ya numfasa yace "ka gaji ko kuma da sauran ƙarfinka?", Naseer baice komai ba, Baba ya ɗaga murya da kanaji kasan a ɓace ransa yake yace "Maimuna!!, Maimuna!!", wani irin juyawa ƴan hanjin Maimuna da take laɓe jikin labule sukay, daga ita har Nabila sai suka fara neman gurin ɓuya, Baba yace "Shiga ka zanemin ita itama", wayyo daman Naseer duk kansu yanada cikinsu, ai Maimuna a ɗaki akay mata nata walmukalafatun, itama tasha mabirki daidai gwargwado, Baba yace itama a haɗata da Sa'adatu a rufe, Nabilah ma ta amshi rabonta saidai bai kai nasu ba, ita akai aka rarrankwala mata mabirkin sannan ta amshi maruka biyu zafafa, zuciyar Maama ta soyu iya soyuwa, tanaji tana gani aka zane mata ƴaƴa, Baba ya bawa Naseer padlock yace ya kulle kitchen ɗin anan zasu kwana. Hajar da take jikin window tana hangen duk abinda yake wakana tayi murmushi zuciyarta fess, ai ita dukan da akay wa Sa'adatu da kuma yadda wayarta ta daki bango shi yafi mata daɗi, wayar da aka wulaƙanta ta da ita a soro gashi nan ta fashe. washe gari da safe Hajar ta fito tsakar gida da kayanta da zata wanke, ta deɓi ruwa a bucket ta zazzaga omo ta sunkuya ta fara wankinta tana humming song, a fakaici ta kalli ƙofar langa-langar kitchen da take a garƙame da kwaɗo, har yanzu Sa'adatu da Maimuna suna ciki sunyi bugun sunyi kukan har sun gaji, muryar Maimuna taji tana kuka tana cewa "dan girman Allah Baba kayi haƙuri wllh bazan sake ba, wayyo Maamana, na shiga uku na lalace, wllh kunama ta harbeni dan Allah a buɗe mu, Sa'adatu ta yanke da ƙarfen langa-langa", Hajar ta kyalkyale da dariya tana wankinta, Maama ta fito daga ɗakinta zuciyarta busu-busu ta shiga ɗakin Baba, Baba ya gama shiryawa tass zai fita aiki, Maama tace "mal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login