Showing 78001 words to 81000 words out of 114314 words

Chapter 27 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5271

tace "tin ɗazu nake gyara mata sai ya kuma zamewa, bari nasa mata hula kawai" ta cire hular kanta ta rufewa Hajar black silky hair dinta da aka yarfawa siraran kitso. Babban private hospital aka kai Hajar, tini doctors suka amsheta, a Amenity room aka kwantar da ita aka saka mata drip, cikin mintinan da basu wuce uku ba ta zama stable, fever din ta sauka, akai mata allurar bacci sbd ta huta, Mami ta fita reception ta cigaba da kiran Nurain da tin ɗazu take kira baya picking, wajen Hajiya da ke zaune kan silver chair ta nufa tace "Hajiya, driver zai mayar dake gida...", Hajiya tace "ina fa zan koma gida ga ƴar mutane rai a hannun Allah, yanxu wnn kyakkyawar yarinya ɗanya shagaf Usuman zaice baya so, kyan fuska dai ya samu Allah yasa zuciyar ma me kyau ce, ni babu inda zani sai ƴar mutane ta farfaɗo", Mami tace "ai ta samu lfy, bacci take zata huta daga ta farka shkn. zata tashi sumul", da kyar Mami tayi convincing Hajiya ta yarda zata koma gida, Hajiya na tafiya tare da driver Mami ta kira Anty Zulaiha ta gaya mata abinda ya faru, bayan ta gama waya da Anty Zulaiha ta sake kiran Nurain, ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba da baya picking.


★Nurain kam daman kai tsaye gidansu Farooq ya wuce, yana parking motarsa ya zagaya ta bayan gidan inda zai shiga part ɗin Hajiya direct ba sai yabi ta main door ba, anan kusa da part din Hajiya ɗakin Farooq yake, Nurain yayi knocking ƙofar ɗakin Farooq, Farooq ya buɗe ƙofa ya kallesa da sleepy eyes ɗinsa sai kuma ya ƙanƙance ido yace "brother, me ya fito da sabon ango this early morning?..", Nurain da yake moody yace "move", Farooq ya basa hanya ya wuce, yana shiga Farooq ya rufe ƙofar ya bisa da kallo, Nurain ya zaune kan executive coach dake ɗakin gami da lumshe ido, Farooq ya zaune gefen gado yana facing dinsa yace "what's up..?", Nurain bai tanka masa ba saima ya kwanta kan coach din yayi pillow da hannunsa, Farooq yayi kwanciyarsa don bacci bai ishesa ba, weekends ne kawai yake samun hutu ba fitar sassafe zuwa work, Nurain kam gaba ɗaya mind dinsa a cunkushe take, meyasa bashi da sa'a ne wajen aure, Ruqayyah betrayed him and now an aura masa mara manners, tashi yayi ya zauna ya dafe kansa, Farooq ya miƙe ya zuro ƙafafuwansa ƙasa yana kallon brother din nasa yace "wai me yake damunka ne Nurain?, aren't you here to tell me..", Nurain yace "auren da akay min ne banaso wllh, am not happy with it..", Farooq yace "why?, naga dai jiya lfy na maka rakiya, and it seems like you were happy that time..", Nurain yayi ajiyar zuciya yace "damn it, ko a lokacin bana farin ciki kawai dai i was calm to accept it as my destiny, but now bazan hakura ba gsky, ban taɓa tunanin akwai ranar da zan turning Abba down ba sai wnn karon, turning din kwa shine wllh sakinta zanyi, waccar rigimammiyar tsohuwar ce ta mayarmin da agogo anticlockwise, wllh da tini na wuce wajen..", Farooq da bai fahimci brother din nasa sosai ba yace "wai kana nufin kace sakin matar da aka aura maka jiya za kayi?", Nurain ya shafa fuska yace "yeah, sakinta zanyi sbd bazan zauna da ita a matsayin mata ta ba...", Farooq yace "ban san mene dalilinka ba amma kana ganin sakinta shine solution, what about Abba..", Nurain ya katsesa da fadin "Abba babu abinda yace infact ma cewa yayi ai ya gama role dinsa ynxu option ya rage nawa, ruwana ne na zauna da ita ruwana ne na saketa, so na gama yanke decision zan rubuta takardar sakin na kaiwa Abba tinda ya amince..", Farooq yayi murmushi yace "shi Abban ne ya baka damar ka saketa?", Nurain yace "Sure", Farooq ya sake yin wani murmushin yana jujjuya kai, Nurain ya hade gira yace "meye haka..", Farooq yace "uhmm, are you a kid?, toh wllh Abba testing naka yake, am telling you gwada ka yake punk, taya ya zai baka go ahead direct ka saki ƴar mutane", Nurain yace "Allah ko, toh kwa zanyi failing don bazan ci test dinsa ba..", Farooq ya tashi yace "nidai ga piece of Advice zan baka, indai dalilinka bai kai wanda zaka saki ƴar mutane ba toh ka janye batun nan, ko don reputation din Abba ya ɗaure a idon iyayen yarinyar..", Nurain ya wani galla masa harara yace "oh really, i don't want your Advice ka rike abinka", Farooq ya ɗaga kafaɗa ya buɗe huge wardrobe ensa ya ɗauki button down shirt and dark blue jeans trouser ya shiga bathroom, bayan minti goma ya fito da kayan da ya shiga dasu ajikinsa, Farooq ya tsaya jikin mirror yana goge kansa da hand towel, yayi combing hair din da brush snn ya shafa mai a palm da legs, Farooq ya dubi Nurain yace "am coming" da haka ya buɗe door ya fita, after like 5mins ya dawo dakin da rufaffen plate a hannunsa, ya ajiye plate din akan bedside, mini fridge dinsa dake ɗakin ya buɗe ya ɗakko lemon kwali na raspberry, gefen gado ya zauna ya ɗauki plate en da ya shigo dashi ya buɗe, chips ne da kwai sai satchet ketchup, Farooq yace "ga breakfast", Nurain yace "No, thanks..", Farooq yaci abinci yayi nak abinsa, ya zuba juice yasha daman shi baya shan tea da safe sai dare, Nurain ya tsiyayi lemon yana sipping, wayar Farooq ce tayi ringing, Farooq yayi unplugging dinta daga charge da take, ganin mai kiransa ya dubi Nurain kafin yayi picking ya kara a kunne yace "Na'am Mami..", yay shiru na second uku sai kuma yace "eh yana nan", yana kallon Nurain da shima yake kallonsa yace "okay" ya sauke wayar daga kunnensa, Farooq yace "Mami ce take tambayarka, tin ɗazu take kiran wayarka baka picking", Nurain ya ajiye cup din lemon da yake sha ya tashi ya fita, compound ya fita wajen motarsa, ya buɗe ya ɗauki wayarsa da ya manta kan dashboard, 40 missed calls ya gani daga different people, na Mami duk yafi yawa sai na Noor ga kuma na Abba ma guda uku, sai kuma na wacca tasa ya tsani wayar, ya kare hasken rana dake haske masa ido da hannu, numbern Mami yayi dialing, tana shiga tayi picking, ya lumshe ido yana jin yadda muryarta ta canza tana masa faɗa, Calmly yace "am sorry Mami".


★Anty Zulaiha na kallon Hajar dake bacci tace "wai me yake damunta Mami, lafiya lou fa jiya muka barta tare dasu Khausar..?", Mami tayi ajiyar zuciya tace "sai doctor yazo zai faɗi abinda suka gani, ba kiga a yadda muka kawota nan ba, Noor kam cewa tayi lokacin da ta ganta ko numfashi ba ta yi sosai..?", Anty Zulaiha tace "innalillah, Allah ya rufa asiri, shi kuma Nurain ina ya shiga har yarinyar mutane ta shiga wani hali", Mami tace "wa ya sanar masa, da sassafe dai yazo gida wajen Abba, daman Hajiya ta zabga sammako tazo tace a kaita taga Amarya shine ya ɗauketa ita da Noor zata kai musu breakfast zuwa gidan nasa, wai ashe yana ajiyesu ya juya yabar gidan, Noor ta kirani take gayamin wai Hajar en ba lfy, saida naje gidan snn muka ɗakkota muka taho nan, tin ina gida nake kiran Nurain amma bai ɗauki kirana ba, saida na kira Farooq na tambayesa, shine yake gayamin wai yana gidansu, Nurain bai taɓa ɓatamin rai kamar na yau ba, zaizo ya sameni aii", knocking ƙofa akay Dr ya shigo tare da Nurse biye dashi, ya gaisa dasu Mami snn ya wuce gadon patient yana magana da Nurse din, yace "for now kar ay mata amfani da normal saline..", Nurse tace "yess dr", ya duba ruwan da ake ƙara mata snn yayi feeling temperaturen ta, discharging Nurse en yayi ta fita, ya juya yana kallon su Mami yace "me ya faru da ita haka har bp nata yayi high?", Anty Zulaiha ta kalli Mami da weird expression, Mami tace "Bp doctor?", Dr ya gyaɗa kai yace "yess, jininta ne ya hau sosai, Allah yaso kunyi rushing zuwa hospital da ba haka ba zuciyarta zata iya exploding cause jinin ya hau sosai..", Mami ta miƙe tace "what's her condition now?", yace "Alhmdllh everything has been taken care of, ba matsala insha Allah she is stable", Mami tace "Alhmdllh", yace "i will send a prescription right away, a siyo drugs en a bata idan ta farka taci abinci" da haka ya fita daga ɗakin, Mami ta dubi Noor tace "bisa ki amso prescription din", Noor tace "tom" ta tashi tabi bayan doctor, Anty Zulaiha tace "an kwa sanar da iyayenta?", Mami ta girgiza kai tace "A'a, bamu da contact dinsu..", Anty Zulaiha tace "ya kamata a gaya musu kwa, kinga ma a tambayesu akan Bpn nata ko tuntuni tana dashi", Mami tayi ajiyar zuciya ba tace komai ba, knocking akay kafin aka buɗe ƙofar aka shigo, Nurain ne ya shigo shi da Farooq, Mami ta ɗauke kanta ta haɗe gira, tini Nurain ya sha jinin jikinsa, suka gaisa da Anty Zulaiha, Farooq ma haka snn ya juya ya gaida Mami ta amsa masa, Farooq yace "ya me jiki?", Mami tace "alhmdllh da sauƙi", yace "Allah ya ƙara lfy ya mayar kaffara" da haka ya matsa kusa da gadon da Hajar ke kwance, Nurain ya shafa kai yace "Mami how is...", Mami ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, Anty Zulaiha tace "kiyi haƙuri don Allah..", Mami tace "meye dalilinsa da har yarinya ta zama unconscious amma be sani ba, da safiyar Allah ya kama ƙafa ya fita ya barta ita kaɗai duk bance masa komai ba, snn ma da ya kaisu Noor gidan me yasa ya tafi ya barsu haka nan, gashi wayarsa ba tada amfani ko emergency ya taso ba za'a sami taimako daga wajensa ba..", ta kalli Nurain da kansa ke ƙasa zuciyarsa na tafarfasa tace "Uthman, wllh Allah idan wani abun ya samu yarinyar nan you are going to see the other side of me, ai Abba ya gaya min abinda ka tarka mara tushe da kan gado" da serious note ta faɗi hakan, Noor ta shigo da prescription paper a hannunta ta miƙawa Mami, without looking at him Mami tace "bashi ya siyo drugs en", Noor ta miƙa masa takardar, ya warce kafin ya fita daga ɗakin da speed, Farooq ya ja kujera ya zauna, a hankali Hajar ta fara motsi da hannunta kafin ta kaisa ta dafe goshinta, ta buɗe idonta tana ƙarewa environment ɗin da take ciki kallo, Farooq da yayi noticing yace "ta farka". Mami ta taso ta zauna gefen gadon tace "sorry dear", Hajar ta haɗiyi wani yawu wanda da kyar ta samesa sbd bakinta a ƙafe yake, support tayi da hannunta ta miƙe zaune, ta kalli hannunta mai canular da ake mata ƙarin ruwa, sai kuma ta ɗaga kai tana kallon drip stand din da akay connecting da hannunta, tass ta fahimci a inda take amma bata san mutanen da ke wajen ba, Noor kawai ta shaida, ta lumshe idanunta ta kuma buɗesu murya a dashe tace "Umma.. Umma.. Ummata".....✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{38..}
Kawai Ummata Hajar take kira, Mami tace "Umman ki za'a kira miki?", ta gyaɗa kai a hankali, Mami tace "alright, insha Allah za'a kira miki ita, how are you feeling now?", Hajar tace "alhmdllh", Anty Zulaiha ta taso ta tsaya gaban gadon tace "sannu ko", a hankali ta jinjina kai sai kuma ta koma ta kwanta ta lumshe ido, few seconds bacci mai nauyi ya sake figarta cause allurar baccin bata gama sakinta ba... Nurain na fita ya buɗe prescription paper en ya karanta content en ciki, he was totally confused bayan yayi realizing drugs en dake rubuce, murya can ciki yace "too young, may be inheritable..", wani near by pharmacy ya shiga ya siyo drug en, ya dawo asibitin da ledar magungunan a hannunsa, duk iya ƙoƙarin sa na ganin ya saki fuskarsa kafin ya shiga Amenity room en kasawa yayi, cause da gasken gaske zuciyarsa ba dadi, ya murɗa ƙofa ya shiga kafin yay sallama ciki ciki, Anty Zulaiha ta amsa, nan kan kujera ya ajiye ledan yace "gashi", without looking at him Mami tace "saura abinda za taci idan ta tashi", still yay na few seconds kafin yace "i thought daga gida za'a kawo abincin..", tace "right, amma ita bashi zata ci ba, so ka samo mata nata kafin ta farka", yace "yeah" zuciyarsa kamar zata fashe, ya juya ya fita, Farooq dake zaune kan plastic chair ya tashi yabi bayansa, Anty Zulaiha tace "Mami that was too tough", Mami tace "No Zulaiha, abinda ba halinsa bane yake so ya tarka, ba zai yiwu ba wllh, bazan bari yayi abinda bai dace ba gsky, ko baki lura da reaction ensa bane, bayan ya kulle yarinya a gida harta shiga wani halin, nifa I'm not in support Nurain ya bagarar da yarinya in the name of aura masa ita akay, bazan so ayi ma nawa yayan haka ba don haka nima bazan bari ayima yayan wasu ba..", Anty Zulaiha tace "kin san arranged marriage akan samu irin haka Mami..", Mami tace "ai irin hakan ne banaso..", Anty Zulaiha ba ta sake cewa komai ba. bayan 40mins Farooq ya shigo with bags a hannunsa, ya ajiye snn ya juya ya fita, Mami tace "check.. kiga mene aciki", Anty Zulaiha ta janyo ledojin gabanta ta duba, grilled fish ne na manyan tilaphia with potatoes, sai ƙatuwar bottle of fresh milk da kuma leda guda ta fruits, Mami dai combination na abincin bai mata ba, kifi da madara, kawai dai tayi shiru tinda dai ya siyo. Farooq ya ringa kallon kujerar da ya bar Nurain akay nan reception ganin empty baya nan, toh ina yaje, cewa fa yayi zai jira shi anan ya fito sai su wuce Chinese restaurant suci seafood. Nurain yayi knocking consultation room kafin ya murɗa ya shiga, ya zauna ɗaya daga kujeru biyu da suke gaban huge table da ke ɗauke da nameplate da sauran tarkace na doctor, gaisawa sukay da Doctorn, Dr yace "Dr Uthman right?", Nurain yace "yeah", Dr yace "ya aiki..?", Nurain yace "Alhmdllh ya naku?..", Dr yace "same alhmdllh", Nurain yace "Dr Mansoor bai ƙaraso ba knn?", Dr yace "Eh, sai qarfe biyar zai shigo", Nurain yace "Ohk, amm akwai wata patient da aka kawo.." sai kuma yayi shiru cause bai san sunan da zaice ba, tunawa yayi da numbern room din yace "wacca take Amenity room 2", Dr yace "Ohh, what about her?", Nurain ya sauke numfashi yace "how's her condition, za'a iya dischaging nata kafin dare..", Dr yace "No, her condition is totally not enough for discharge, za'a ɗan riƙeta na some days sbd kula da yanayin Bpn..", Nurain ya jinjina kai yace "Alright, ba damuwa kawai ayi dischaging nata akwai family doctor da zai kula da ita a gida", Dr yayi shiru yana kallonsa sai kuma yace "is she part of your family?", Nurain yace "No", Dr yay jim jin yadda ya basa amsa with repartee, Nurain yace "look, she's the daughter of my father's friend, rashin zuwan family doctor en ne yasa aka kawota nan toh yanzu doctor yazo, he will take over insha Allah...", Dr yace "Ohk", nan ya shiga yiwa Nurain bayanin komai, treatment en da aka fara mata ta yadda kawai Dr ɗorawa zaiyi, da yake shine ya duba Hajar din a take ya rubuta referral letter ya bada amma sai yamma za sallameta under cewar wani dr zai taking over, Nurain ya basa hannu sukay sallama kafin ya ɗauki referral papern ya fita a office en, wnn shine kawai option ensa to get rid of Mami's anger, yasan mene a zaman asibiti ai, ganin dr da gwaje gwaje, All Bp stuffs yana dasu a gida. sai ƙarfe biyu na rana Hajar ta farka, ba kamar ɗazu ba yanxu jikin yafi kwari, sai kace wata qaramar yarinya ta fara kiran ummata, Anty Zulaiha ce kawai a dakin Mami bata dade da fita ba wajen Dr, Noor kuma ta wuce gida Mami ce tace ta tafi sbd Hajiya na can kar tayi zugum ita kaɗai, Anty Zulaiha tace "toh fadi numbern umman taki sai a kirata", ai kam da sauri ta fara karanto numbern Umma dake haddace akanta, Anty Zulaiha ta rubuta snn tayi dialing, har ta katse ba a dauka ba ta sake kira, tana daf da katsewa aka daga, cikin dabara kuma a nutse Anty Zulaiha ta fara yiwa Umma bayani, don haka Umma bata wani firgita sosai ba, daga ƙarshe Anty Zulaiha ta kwatanta mata asibitin tace idan zata zo amma dai ba wata matsala Hajar ta samu lfy, sai a lokacin Hajar ta dan ji relief, ta fara ƙoƙarin sakkowa daga gado, Anty Zulaiha tace "mene ne, akwai inda ke miki ciwo ne?", ta girgiza kai tace "A'a sallah zanyi" tana kallon wall clock dake ɗakin, Anty Zulaiha "Ohk, zaki iya tafiya da kanki", ta gyaɗa kai tace "zan iya", a hankali Hajar ta sakko daga gado ta ɗane hannun da aka saka mata canular, ruwa leda biyu aka saka mata, tana bacci aka cire na biyun ba a saka wani ba sai kuma dare sbd kar tayi swelling tinda ba tada rashin ruwa a jiki kawai na kwarin jiki ne, Anty Zulaiha ta nuna mata door din toilet dake dakin, Hajar ta shiga toilet en tana bin bango tayo alwala ta fito, hannu a ɗane ta fito tana riritasa sai kace wani babban ciwo, Anty Zulaiha ta bata prayer mat da Nurse ta ara musu ita babu jimawa za suyi sallah, mayafinta ta ɗauka ta yafa tinda babba ne snn kuma kayan jikinta was more than decent, ta hau kan prayer mat din ta tayar da sallah, kafin ta idar Mami ta shigo, ba ƙaramin daɗi taji ba ganin Hajar harta samu kwarin sallah, Anty Zulaiha tace "na kira Mamanta na gaya mata..", Mami tace "Ohk, Dr ma yace insha Allah zuwa yamma zai iya dischaging enta, toh kinga kwa Alhmdllh jiki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login