Showing 93001 words to 96000 words out of 114314 words

Chapter 32 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5284

mai ta shafa kafin ta dawo gefen gadon ta zauna ta fara warware gogaggun kayan, wani sassanyan ƙamshi ne yake tashi daga jikinsu, Atampa ce mai laushin gaske kai kana ganinta kasan mai tsada ce, Hajar ta ringa shafa kayan kafin dai ta warware ta saka a jikinta, sosai sukay mata kyau dass dass, riga da skirt sosai yake fito da ainahin shafe dinta, ɗan kwali da mayafi sai pendant necklace da ear rings ne kawai bata saka ba, da sauri ta fara ƙoƙarin rufe kanta ganin Mami ta shigo, ɗan kwalin ta yafa a kanta ta rufe gashinta, Mami ta zauna gefen gadon itama ta riƙo hannunta tace "Yau kuma sai gidanki insha Allah", wani darammm Hajar taji a ƙirjinta, Mami tace "Allah yayi miki albarka tare da zaman lafiya madauwami, maza ki ƙarasa shiriyawa...", hawayen da suka cika idanunta suka fara zarya bisa kuncinta wanda bata shiryawa hakan ba, Mami that was very surprised da ganin tears ɗinta tace "what happened Hajar...?, akwai abinda yake damunki..?", Hajar tasa bayan hannu ta goge hawayen ta girgiza kai a hankali tace "A'a, kawai dai ni bansan waye wanda aka aura min ba, ni dai nasan Baba na yace yamin aure amma ban san waye ya aura min ba..", ta fara kuka a hankali, Mami tayi ajiyar zuciya ta tausasa murya tace "dear he is my son wanda aka aura miki, yayan Noor ai kin ganesa ko", Hajar na kallon Mami da jajayen eyes ɗinta ta gyaɗa kai, knn dai shi ɗin ne ko, Mami tace "Stop crying kinji, he will not harm you i promise..", Hajar dai ta rasa a wani position zata ajiye zuciyarta don ji take tamkar an tsireta da tsinken tsire ana gasawa a tukuba, Noor ce ta shigo, ganin yadda idanun Hajar suka kumbura tace "subhanallah kuka kike..", Mami ta tashi tace "she is not, gyara mata fuskarta ina zuwa" da haka ta buɗe ƙofa ta fita, Noor ta saka mata ear rings da necklace snn ta mata ɗauri mai kyau, saida ta ɗauki kwalbar turare dake kan mirror ta sake baƙaƙa mata ajiki duk da irin ƙamshin da kayan suke, biyar da ƴan mintina Hajar na zaune main palourn tare da Noor, Mami ta fito daga part din Abba ta kama hannun Hajar suka shiga part din, 5minutes da shigarsu suka fito bayan Hajar ta gaida Abba, don daman bai taɓa ganinta ba sai yau. Mami na kallon Noor dake zaune main palour tace "Nurain din bai fito ba har yanzu..?", Noor tace "Eh bai sakko ba", Mami ta kalli stairs kafin ta wuce ta fara hawa, knocking door ɗin ɗakinsa tayi, ya buɗe ƙofar yana kallonta, tace "baka gama bane..?", yace "yanzu zan sauko" da haka ya mayar da ƙofarsa ya rufe, yayi ajiyar zuciya, ya ƙarasa buttoning rigarsa ya saka links, shi kaɗai yasan abinda yake ji a zuciyarsa kawai jurewa yake, down stairs ya sauka bayan ya kulle ɗakin nasa, part din Abba ya shiga ya masa sallama, ya yiwa Mami ma dake zaune main palour daga haka ya fita compound, packing space ya isa ya buɗe motarsa ya shiga, Noor riƙe da tagomishin kayan arziƙin da Mami ta haɗawa Hajar na turaruka ta fita compound, Noor ta saka turarukan a back seat, ta dawo ta riƙe hannun Hajar zuwa wajen motar, front seat ta buɗe mata, a hankali Hajar ta shiga motar, Noor tace "sai nazo sister" da haka ta rufe motar taja baya, Nurain ya ƙurawa steering ido bai bari ya kalli inda take ba, saida ya gama warming motar snn ya fara driving a hankali ya fita daga gidan, tinda suka hau babban titi Hajar ta juyar da kanta side glass din ƙofa kawai kallon waje take, sanyin Ac ya ringa shigarta ga kuma abinda yafi tsaya mata a maƙogoro scent dinsa, ita dai bata san ma ina suka bi ba kawai gani tai sun tsaya a bakin gate ɗin wani katafaren gida, Nurain ya danna horn, mai gadi ya buɗe gate da sauri, Nurain ya parker motar a parking space kafin ya kashe ya zare key daga Ignition, buɗe murfin motar yayi ya fita, a hankali Hajar ta buɗe motar ta fito, ya buɗe back seat ya ciro ledar da Noor ta ajiye ya rufe motarsa, dire ledar yayi nan bakin motar yayi wucewarsa ciki, a karo na farko data ɗaga kai ta kallesa, ta taɓe baki ta sunkuya ta ɗauki ledar tayi hanyar da ta ga yabi, tsaye tayi bayan ta shiga palour, ta ajiye ledar hannunta, ta ƙarewa palourn kallo tass, direct Nurain upstairs ya haura ya shiga ɗakinsa bayan ya kunna Solar, trolleyn kayansa tin wacca ya kawo last week ya buɗe, arranging kayan ciki ya fara yi awajen da yake so, duk yawanci ma kayan aikinsa ne aciki ba sutura ba don on Monday yake da shirin rusuming work, yana gama arranging kayan yaji ana kiran sallah, huge bathroom dinsa ya shiga yayo alwala, da sauri ya gama ya fito, fita yayi ya sauka down stairs, Hajar na rakuɓe daga bayan kujera har ta gaji da tsayuwa ta samu guri ta zauna, kallo ɗaya yayi mata ya fita zuwa masallaci wanda akwai tazara kaɗan tsakaninsa da gidan, Hajar ta miƙe tsaye tana tunanin ina ne alqibla don da alwalarta sallah kawai za tay, kallon stairs tai wani tunani yazo mata, bayan ta gane gabas tayi sallar ta, har sallar isha'i Nurain yayi kafin ya dawo gida wajen takwas da ƴan mintina, muƙullin motarsa ya ɗauka ya fita, eatery ya fita ya siyo abinci ya dawo, wai yau shine da siyar abinci a waje, abinda bai taɓa sha'awa ba knn, kan Centre table ya ajiye ledojin da ya shigo dasu kafin ya haura sama, Hajar da bacci ya fara kwasarta ba tama san ya shigo ba, Sha ɗaya da rabi ya sakko with Pajamas mai sweat pant, ledojin dake kan Centre table ya ɗauka ya bar guda ɗaya, har ya fara hawa stairs sai kuma ya dawo baya, tsayawa yayi yana kallonta, jingine take da kujera bacci yayi awan gaba da ita, maganar Abba ce tayi hitting brain dinsa, kallonta ma da yake wani maƙaƙi ya ringa ji a zuciyarsa, ya taka a hankali ya tsaya gaban kujerar da ta jingina da ita, kujerar ya bubbuga yace "hey"......✍️


Arewa book @feenerhfeeche02


💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche


{43..}
Saida ya sake buga kujerar snn ta motsa, daman ba wani daɗin baccin take ji ba, buɗe idanunta tayi, yana ganin haka ya bada distance a tsakaninsu yace "hey, you better find a place to sleep, nan ba wajen bacci bane", ta buɗe idanunta tarwal ta mutsuttsukasu da hannu, taɓe baki tayi tace "what concern you da wajen dana kwanta..", ta mayar da kanta jikin kujerar ta lumshe ido, sake bubbuga kujerar yayi this time around da ƙarfi yace "you are not serious, ki tafi wani wajen malama amma banda nan", miƙewa tayi tsaye ta gyara yafen mayafinta, ledar data rage akan Centre table ya ɗauka yace "follow me...", ɗauke kanta tayi kamar ba taji me yace ba, yayi controlling tempern dake taso masa yace "i said follow me", ta sake juyar da kanta tayi folding both hands dinta tace "kayi mgana da yaren da zan gane..", yace "haka ne fa, ohk, duba da irin localityn da kika taso bai kamata a miki magana ta masu ilimi ba, cewa nayi ki biyo ni", bai jira cewarta ba ya fara hawa stairs, bin bayansa tay da kallo kafin ta haura saman, a daidai ƙofar ɗakin dake matsayin nata ya dakata, ya murɗa door handle ya buɗe, ajiye mata ledar yayi a gefenta ya koma ƙasa, ta yiwa ledar wani kallon hadarin kaji ta shiga ɗakin ta barta a nan, Nurain ya kashe duk bulbs dake kunne palourn, ya haura sama da ledar abincinsa a hannu, tsayawa yayi yana kallon ledar da ta bari inda ya ajiye, ya ɗaga kafaɗa ya wuce part ɗinsa, a palour ya zauna ya buɗe ledar, abinci ne mai rai da lafiya jollof rice da taji kayan lambu sai quartern kaza da soyayyen plaintain, spoon ya ɗauka ya ɗebi rice din ya kai baki, ajiye spoon din yayi yana kallon abincin, ya koma yayi resting da kujera don taste din bai masa ba, kwata kwata baya son abincin waje, rufe abincin yayi ya buɗe bottle water ya sha, daga ƙarshe dai ya tashi daga palourn ya shiga bedroom, ya rage hasken fitulu ya bar dim ta bedside, ya ɗauki Mac phone dinsa dake kan bedside ya kunna. Hajar ta gama ƙarewa ɗakin kallo kafin ta taɓe baki, da sauri ta isa gaban gado ganin handbag dinta, ta ɗauki handbag din ta buɗe, wayarta ta fara cirowa tana jujjuyata, kunnawa za tay taga ta mutu, acikin hand bag din ta zaro charge tayi plugging wayar a socket da ta gani a room din, zama tayi kusa da wayar har saida tayi 10% ta kunnata, bayan wayar ta gama booting taga missed call da yawa wanda sune ma suka sa wayar ta mutu tinda ba wani charge ne da ita ba lokacin da aka kawota gidan, call log ta shiga ta kira Ummanta, ba tama damu da dare yayi ba, don a lokacin sha biyu na dare ake magana, har kiran ya katse Umma bata ɗaga ba, Sake kira Hajar tayi, daf da kiran zai katse aka ɗaga, wani ajiyar zuciya Hajar ta saki tace "Umma na..", Umma ta tashi zaune don bacci take kiran wayar ya farkar da ita, Umma tace "Hajara..", tini hawaye ya ciko idanun Hajar tace "Na'am Umma", Umma tace "ina kika saka wayarki anata kira ba a samu..?", Hajar tace "a gida na barta kuma babu chaji..", Umma tace "Okay, toh ykk ya zaman sabon waje?", Hajar da already hawayen idonta sun fara tsiyaya tace "Ya Baba da Sabra da Yaya...?", Umma tace "kowa lfy alhmdllh..", Shiru Hajar tayi ba tace komai ba don wata ball ce ta tsaya mata a throat, jin tayi shiru Umma tace "ya jikin naki..?", da kyar tace "naji sauƙi sosai..", tayi shiru kafin tace "Umma..." sai kuma ta kasa cewa komai don ta rasa me zata ce, daga ƙarshe dai tace "Umma seda safe nasan ma kin fara bacci na tashe ki" da haka ta kashe wayar ta fashe da kuka, har cikin ƙasan zuciyarta bata san auren nan, saida taci kukan mai isarta har kanta ya fara ciwo, ta goge hawayen da ya jiƙa mata cheeks kafin ta tashi daga tiles da ta zauna, bathroom ta shiga ta wanke fuskarta ta fito, pillow ta ɗakko daga kan gado ta wurgar kan lallausan carpet dake room din, ta kware duvet din gado shima, tayi kwanciyarta kan carpet ta rufa har ka da duvet din don wani irin sanyi ne yake ratsata na Ac, har uku na dare idonta biyu ta kasa bacci sai juye juye take, babu kalar tunanin da ba tay ba a zuciyarta, sai wajen huɗu da ƴan mintina bacci ɓarawo ya kwasheta, alarm din wayarta ne ya tasheta wanda tintini take dashi wanda yake tashinta da asuba sbd ɓatan rana, kafin ma ya tasheta take tashi, da kyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta dafe kanta sbd faskarawar da yayi, ta tashi ta kashe alarm din, a hankali ta fara jiyo kiraye kiaryen sallar asuba, ta dai samu ta daddafa ta shiga toilet tayo alwala tayi sallah, tana idar da sallah ta koma ta kwanta don da gaske kanta ciwo yake. Washe gari ƙarfe takwas da rabi na safe Nurain ya sauko down stairs da key din motarsa a hannunsa, saida ya rufe main door din shiga gidan kafin ya wuce parking spaces, Inuwa mai gadi da ke goge motar da soft duster ya gaishesa da ladabi, Nurain ya amsa yace "zan fita amma ba jimawa zanyi ba..", Inuwa yace "toh Alhj Allah ya tsare", Nurain yace "Ameen" ya buɗe motar ya shiga, da sauri Inuwa yaje ya buɗe gate, da reverse ya fitar da motar daga parking space kafin ya juyata ya fita daga gidan, Inuwa ya mayar da gate din ya rufe ya ɗauki watering can yana bawa flowers ruwa, Supermarket Nurain ya tafi, duk wani kayan abinci saida ya siya na tsaba da kuma masarufi, ruwa da lemo ma bai barsu ba saida ya siyo, har da perishable food ya siyo, sai 11 ya gama siyayyan ya wuce gida, yana parker motar ya zaga backyard ya buɗe wata glass door wacca zata kaika kitchen, ya shiga kitchen din, ya buɗe store dake cikin kitchen din, gas ya kunna wanda cylinder dinsa ke can bayan gidan anyi connecting pipes zuwa kitchen, ranar Thursday da yazo giran yasa aka masa refilling babar cylindern, daga haka kuma ya sake fita compound wajen motarsa ya buɗe booth, Inuwa ya saka ya ringa jigilar kai kayan da ya siyo yana libgewa a store, wanda za a ajiye a freezer kamar meat da chicken suma aka zuba a freezer, lemo da ruwa kuma a store aka ajiyesu bayan an zuba wasu a babban fridge dake kitchen din, a section na biyu na fridge din kuma aka zuba kayan miya, kitchen dai ya cika tsaf, bayan an gama shigar da komai Nurain ya buɗe cupboard ya ajiye Coffee powder da ya siyo ma kansa, daga haka ya buɗe ƙofar palour ya shiga, upstairs ya haura zuwa part dinsa, after like 10mins ya fito ya bar gidan mai gaba ɗaya a motarsa.


★Anty Jamilah ta yafa gyalenta tana kallon Umma tace "toh bari mu wuce kar muyi yamma tinda an gama fita da kayan", Umma tace "Amma kina ganin abin nan bazai zama gulma ba bafa wanda aka gayyata kai garar", Anty tace "babu gulmar da za ai wllh, toh Allah na tuba wanda ma yayi gulmar ai shi yaga zai iya yawunsa ne zai ƙafe a banza, yaushe aka gama bikin da zamu sake jajiɓowa kanmu jama'a wani kai gara, yarinya fa za a yiwa ba wani abun kallo bane, ai na ɗebar miki dubulan da Alkaki da gireba da chin chin saiki ƙuƙƙulla a leda a rabawa maƙota da abokan arziki", Umma tace "toh ai shknn, ince dai dangin mijin sun sani..?", Anty tace "mu dai namu kaiwa, ita Hajarar ta gaya musu da kanta..", Umma tace "hakan ma yayi", Anty ta miƙawa Hafsah dake zaune ɗakin hand bag dinta tace "tashi muje..", Hafsah ta amshi jakar ta tashi ta fita ta tsaya bakin ƙofa, Anty ta fito tana kwalawa Mu'azzam kira don dashi za a tafi, ya fito daga ɗakinsu yace "Anty gani", tace "ko ka fasa zuwa kaga ƙanwar taka ne..?", ya girgiza kai yace "A'a zani", Shi dai so yake yaje yaga halin da ƙanwarsa take duba da irin auren da akay mata, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa tin bayan auren, gashi kuma lokaci da dama ya kira wayarta switched off, Anty tace "toh muje ko" da haka tayi soro Hafsah tabi bayanta, Mu'azzam ya saka takalmansa ya fita shima, a soro suka kusa yin karo da Maimuna dake ƙoƙarin shigowa ta ɓoye wani abu a hijab, ko kallonta beyi ba ya wuceta ya cigaba da tafiya, Maimuna ta taɓe baki ta zabga masa harara ta shiga cikin gida da gudu, ɗakin Maama ta shiga tana zazzare ido ta fito da abinda take ɓoyewa cikin hijab, Maama dake tsaye da ɗaurin ƙirji tace "amma Maimuna Ala wadaran nawarki, daga siyo shinkafar ɓera shine kika je kikai zamanki sai kace an aiki bawa garinsu, wllh kin cuce ni, har an gama fita da kayan..", gwalo ido Maimuna tayi tace "mun shiga uku, har an gama fita dasu..", Umma tace "tin ɗazu ma, ai bakya abu da jiki daman baki so aiken ba..", cikin ɗaga murya Maimuna ta dakawa Maama tsawa tace "wai ke dalla Maama kin san da ya akai na samo bom din ɓeran nan kuwa, saida na fita daga unguwar nan sannan na samo sa fa", Maama ta saki baki jin yadda ƴar cikinta ke mata magana na rashin ɗa'a, Maimuna ta zabga tsaki tace "kuma wllh bazan yi asarar ɗari shida ta ba sai kin biya ni..", Maama tace "toh ai saiki bisu can gidan ki zazzaga bomm din da kanki don ni babu yadda zanyi tinda har sun fita", Maimuna tace "A jarkar mai zan zuba ko?", Maama tace "Eh shine yafi sauƙi tinda dai ba zaki iya farke buhun shinkafa ba amma idan kika ɓalle jarkar mai kika zazzaga saiki rufe kawai", Maimuna tace "bari na bisu kuwa don wllh sai Hajara tayi nadamar cin abincin nan", Maama tace "maza ƴar albarka ki tafi kar su ɓace miki", da gudu Maimuna ta fita daga gidan, Maama ta rafsa wata shegiyar guɗa ta buga cinya tace "sai a koma asibiti kuma bayan an take tumbi da abinci", Maimuna na fita bakin titi ta tarar har an gama saka kayan a ƴar ƙurƙura, Mu'azzam ya shiga gaban ƙurƙurar Anty da Hafsah kuma sun tari napep suna ciniki, Maimuna ta matsa kusa da napep din ta wani haɗe rai, Anty ta kalleta ba tace mata komai ba ta cigaba da kwatantawa mai napep unguwar da zai kaisu, Hafsah tace "Anty muje kawai zan gane gidan", Anty ta shiga napep din Hafsah ma ta shiga, ba kunya ba tsoron Allah Maimuna ta riƙe ƙarfen napep ta fara shirin hawa, Hafsah ta leƙo tace "ke malama ina zaki...?", Maimuna tace "kin fini kusanci ne da gidan wacca zaki..?, dalla malama dakatamin ki tsaya iya matsayinki, ke asuwa banza karan kaɗa miya a jefa bayan gida", Hafsah ta jefa hand bag din Anty dake hannunta a booth din napep, tasa hannu biyu ta hankaɗa Maimuna da ta turo buttocks zata zauna, saura ƙiris Maimuna ta baje a ƙasa, ta kasa yiwa Hafsah komai sbd bomb din ɓeran da take ƙunshewa a hijab, Maimuna tasa hannu ɗaya ta riƙe karfen napep din tana ɓarkawa Hafsah zagi, Hafsah ta taɓe baki tace "ban iya ba wllh, zagi ko toh ni ban iya ba, mai daidaita sahu kawai bi takanta muje", Kawai Maimuna ganin Mu'azzam tayi a gabanta, yace "ke dan uwarki ban nan wajen kafin na ɓarar dake...", Maimuna ta saki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login