Showing 96001 words to 99000 words out of 114314 words

Chapter 33 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

09 Dec 2024

5285

ƙarfen napep din ta matsa baya, Mu'azzam yayi kwafa ya koma ya shiga ƴar ƙurƙurar, mai napep yaja napep dinsa suka hau saman titi, bayansu su Mu'azzam suka bi tinda su za su musu jagora, Maimuna ta kalli kuɗin dake hannunta ɗari tara, tsayar da mai napep din da yazo wucewa tayi, da sauri ta shiga ta nuna masa motar su Mu'azzam wacca tayi nisa tace "yi sauri malam ƴar ƙurƙurar can zaka bi karsu ɓacemin", mai napep yace "tom" ya bawa babur ɗinsa wuta daman kuma sabo ne, Maimuna ta ringa azalzalal mai napep kar ya bari su ɓace masa don idan suka ɓace babu yadda zatay, gashi dai ta taɓa zuwa gidan amma kuma bazata gane ba sbd dulhu dankali ce, daga farkon layin Maimuna tasa mai napep ya ajiyeta tinda zata iya gane gidan daga nan, bill dinsa ta tambayesa, direct yace "dubu ɗaya zaki bayar hajiya", zaro ido tayi tace "duba ɗaya kuma, gsky ɗari biyu da hamsin zan baka..", yace "ɗari biyu da hamsin taɓɗi", Maimuna tace "nidae haka zan baka..", yace "haba malama duk wnn tafiyar, Shata fa kika ɗauka don baki bari na ɗauki wani pasinjan ba..", mai napep da yaga tana ƙoƙarin ɓata masa lokaci tini ya kashe babur din ya fito, yace "ko ki bani kuɗina ko na haɗa miki jini da majina, ce miki akay ruwa na zubawa babur din, ko baki san yadda fetur yayi tsada ba..", tini jikin Maimuna ya hau zikiri don kwa layin tsit babu kowa, hannunta na rawa ta fito da ɗari tarar data rage mata tace "dan girman Allah yi haƙuri ka amshi wnn, wllh su kenan a hannuna", da magiya da komai ya haƙura ya amshi ɗari tarar bayan ya mata Allah ya isan ɗarinsa ya burga mashin dinsa ya tafi. mai gadi ya buɗe gate da ake knocking ya tsaya yana kallon su Anty, gaisheta yayi ya bata hanya ta wuce, Hafsah tabi bayan Anty zuwa cikin gidan, mai gadi da mai ƴar ƙurƙura sai Mu'azzam ne suka sauke kayan suka shigar dasu ciki, Mu'azzam yayi mamakin ganin gidan da aka kawo ƙanwarsa, Inuwa sai duban kayan yake yana gyaɗa kai, da ake cewa babu kuɗi a gari ashe dai kuɗi suna nan inda suke, Hafsah ta danna bell ɗin main door ta shiga gidan bayan knocking da tayi, Anty ta ciro wayarta ta shiga kiran layin Hajar, tana dai ringing amma no respond, Anty tace "ikon Allah, ko basa nan ne, munyi waya fa da ita ɗazu tace min tana nan", Hafsah tace "toh bari a tambayi mutumin da ya buɗe mana ƙofa", Hafsah ta ƙarasa wajen da Inuwa ya koma kan white plastic chair ya zauna, tace "mutanen gidan basa nan ne...?", mai gadi yace "Alhj ne kawai ya fita", Hafsah tace "mu gashi nan sai bubbuga ƙofa muke amma shiru", mai gadi ya tashi yace "bari na nuna muku ta baya sai ku shiga" ya wuce gaba Hafsah tabi bayansa, har ƙofar kitchen dake backyard ya rakasu kafin ya koma bakin aikinsa, Anty ta murɗa ƙofar tashiga taga ashe kitchen ne, ta kalli Mu'azzam tace "a shigo dasu nan kawai, ba a barsu yashe a tsakar gida ba", har sukay minti goma da shiga palourn basu ga alamar Hajar ba, daga karshe dai Hafsah ta tashi ta haura sama, a hankali tayi knocking ƙofar ɗakin da tasan an kai Hajar, murɗa ƙofar tayi ta shiga, ba taga kowa ba saidai taji ƙarar ruwa daga toilet, tsaye Hafsah tayi tana jiran fitowarta, few minutes kam sai gata nan ta fito tana tafiya a hankali......✍️


follow my account on Arewa book to stay connected @ feenerhfeeche02


💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche


{44..}
Tamkar wata munafuka haka Mainuna ta ƙarasa bakin gate din gidan ta bubbuga, mai gadi ya buɗe ƙofar, tsayawa yayi yana kallonta, Maimuna tace "zan wuce ko", mai gadi yace "hajiya daga ina...?", tace "tare muke da mutanen da suka shigo yanzu, na tsaya ne akan hanya na amshi saƙo..", mai gadi ya sake kallonta sama da ƙasa don sam ba tayi kama da mutanen ba, fuskarta sai kace horror duk ta ɗashe sbd azabar shafa mai, ga kuma uban ƙuraje da barni da mugu, kayan jikinta ma ba kanta don wani yagulamun hijab ne sanye ajikinta duk ya ƙoƙƙone ya farke, matsa mata yayi ta shiga ya rufe gidan, wani kallon baƙin ciki Maimuna take bin compound din dashi, tsaye tayi ta rasa ina ma zata dosa, Inuwa da har ya koma ya zauna ya sake tashi ganinta a tsaye, yace "bari na nuna miki ta baya tinda naga tanan a rufe take..", gyaɗa masa kai kawai tayi don tsoro ya fara shigarta, wai ta yaya ma zata iya zuba shinkafar ɓeran, haka tabi mai gadi har ya nuna mata hanyar baya, kasa shiga tayi don tsoro ya kamata fa ainun, shi dai mai gadi tinda ya gwada mata ƙofar ya koma bakin aikinsa, shahada kawai tayi ta tura ƙofar a hankali, tinda dai ta riga da tazo babu yadda za suyi da ita, saɗaf saɗaf ta shiga da wani suɗaɗɗen takalminta, cak ta tsaya tana kallon kitchen din ganin kayan garar zube a nan, wani daɗi ne ya tsarga mata a zuciya, da sauri ta fito da ledar da take ƙunshewa a hijab. Tare da Hafsah Hajar suka sauko ƙasa, Hafsah ce ma ta riƙota don da kyar take tafiya sbd ciwon kan, ga kuma yunwa da ta mata illa don rabonta da abinci tin jiya da yamma, sosai Hajar taji daɗin ganin Anty da Mu'azzam, saida suka gaisa gaba ɗaya snn ta samu waje ta zauna ta jingina da kujera, Mu'azzam na kallonta yace "ke lafiyar ki kuwa..?", Hafsah tace "kanta ne yake ciwo..", yace "Sannu, Allah ya sauwaƙe", Anty tace "Ayya sannu kinsha magani..?", Hajar ta girgiza kai tace "babu maganin ai", Anty tace "tin yaushe kan naki ke ciwon..?", Hajar tace "tin safe", Anty tace "akwai panadol a jakata, Hafsah buɗe ki ɗakko mata", Mu'azzam ya tashi yana ciro wayarsa da tay vibrate daga aljihu, ƙofar kitchen ya murɗa ya shiga, a gigice Maimuna dake tsugunne gaban jarkar mai ta ɓalle murfin tana shirin zazzaga shinkafar ɓeran data buɗe ta ɗago kanta, wani irin juyawa ƴan hanjinta sukay ganin Mu'azzam, tsabar gigicewa sai ta saki ledar shinkafar ɓeran a ƙasa, daɓas ta zube a ƙasa tana raba ido tamkar ɓera a buta, da mamaki Mu'azzam yake kallonta, mayar da wayar yayi aljihu ya fasa ɗaga kiran, ledar da ta wurgar ya ɗauka, ƙurawa ledar ido yayi, ya dubi Maimuna da tayi tsilli tsilli, wata mummunar zuciya ce ta ɗebesa ya haɗa kanta da cooking gas, wata razananniyar ƙara ta fasa sbd ji tai kamar raba mata kan gida biyu yayi, tini zufa ta fara tsattsafo masa a goshi, Anty ce ta shigo kitchen din, still tay tana kallon Maimuna da goshinta ya wanke da jini, Mu'azzam ya goge zufar goshinsa yana kallon Anty yace "Why, ƙoƙarin kashe min ƙanwa take Anty" ya juya yana nuna Maimuna da yatsa yace "so take ta kashe min ƙanwa...", Anty ta ringa kallon Maimuna sai kuma ta dubi Mu'azzam, bata kai ga cewa komai ba ya nuna mata ledar bomb din ɓeran hannunsa har rawa yake yace "kamata nayi tana ƙoƙarin zubawa a cikin mai", Anty da mamakin ganin Maimuna a nan ya gama cikata tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mun shiga uku, yanzu Shayin ɓera ka kamata zata zuba a mai", Anty ta sakawa ƙofar kitchen ɗin lock sbd bata son Hajar ko Hafsah su shigo ta juya tana kallon Mu'azzam tace "dan girman Allah fitar mana da ita daga nan, marmaza ka fita da ita wnn ai gara annoba da ita, yanxu ke har zuciyarki tayi baƙin da zaki cutar da mutum da bomb din ɓera", Mu'azzam ya iza ƙeyar Maimuna suka fita daga kitchen din, Anty tabi bayansa tace "ka tabbatar bata zuba ba...?", yace "Eh bata kai ga zubawar ba na kamata..", Anty ta koma cikin gidan hankalinta duk a tashe, banzatar da Hafsah dake tambayarta me ya faru tayi, bayan ta nunawa Hajar kayan ta shirya tace tafiya za tay, don gaba ɗaya hankalinta ya ɗugunzuma gwara taje ta zauna da ƴar uwarta, wnn abu ai ba na wasa bane, a nan ta bar Hafsah zata tafi gida daga baya bayan tace mata karta kai dare, sosai Hajar taji daɗin bar mata Hafsah da akai, Hafsah ta shiga kitchen ta dafa mata Noodles, ta ringa mita bayan ta kawo mata Noodles din tace "ga abinci ba zaki dafa kici ba saiki ta zama da yunwa", Hajar na tura Noodles din tace "bana jin daɗi ne", Hafsah tace "yunwa ce fa..", Hajar na gama cin Noodles din da zata iya tasha panadol da Anty ta bari, sosai taji dama dama kan ya dena ciwo, Hafsah taje kitchen ta ɗakko ledar da suka zo da ita wacca ke ɗauke da turaren wuta da sauran tarkace da Anty ta haɗawa Hajar, Hafsah tace "bari na rage miki aiki", upstairs suka haura again zuwa ɗakin Hajar, Hafsah ta buɗe box din kayan Hajar ta jera mata su a wardrobe, kayan lefenta ma saida Hafsah ta buɗe ta mata tsince tsince, kayan bacci da mayuka da perfumes, mirror kam saida ya cika damm da kayan shafe shafe don Hafsah bata barsa haka nan ba, ita dai Hajar kawai kallonta take tana yamutsa fuska, ita sam babu abinda ya birgeta na daga gidan ko kuma kayan cikinsa, garar da Baban ta yayi mata ya fiye mata komai na gidan, daga ƙarshe Hafsah ta shiga bathroom tayi masa jerensa shima, Shower gel Shampoo da conditioner duk ta jera su a cupboard dake toilet din, saida Hafsah ta gajiyar da kanta don har shara tayi ta goge ko ina ta bisa da turaren wuta a burners, da joke Hafsah tace "da fatan dai kin ɗauki course, haka zaki ringa yi kullum", Hajar ta taɓe baki tace "uhmm", Hafsah tayi ajiyar zuciya ta saka serious face tace "Sister i understand your feelings, nasan yadda kike ji, amma ki ajiye komai ki riƙe hakan as one out of your destiny, ke naki ƙaddarar knn, Allah ya rubuta wnn da aka aura miki shine mijinki, nothing can change that, don Allah ki kwantar da hankalinki ki amshi ƙaddarar ki hannu biyu, forget about the past and face the future ehmmm", Hajar tace "idan da ban haƙura na amshi ƙaddarar ba ai bazan zauna ba Hafsah, wllh tllh Baba nake dubawa shiyasa na zauna amma baya ga haka babu abinda zai zaunar dani", Hafsah tace "Eh hkan ma yayi, komai na rayuwa ai sila ne, in Allah ya yarda wnn auren sai ya zame miki jin daɗi da kwanciyar hankali...", Hajar ta rausayar da kai ba tace komai ba, ƙarfe biyar Hafsah ta fara shirin tafiya, tini mood din Hajar yana canza, Hafsah tayi kamar bata fahimta ba ta cigaba da shirinta, tana gama shiryawa ta ɗauki jakarta, har bakin gate Hajar ta rakata, bayan ta tafi ta koma ciki. Hafsah tsaye bakin road tana jiran napep bayan tayi ƴar tafiya ta fito daga layin gidan, napep biyar ta tare kuma duk basu ɗauketa ba wai ba za suyi hanyar ba, har ta fara gajiya da tsayuwa, wata lafiyayyiyar Mota ce taci taya a gabanta, ganin motar ta kare mata titi ta matsa daga wajen, driver seat aka buɗe, wani gentleman ya fito his eyes covered with shade, ta cikin shade din ya ringa kallonta kafin ya rufe murfin motar ya isa inda take, Calmly yace "Assalamu alaikum...", Hafsah ta juyo tana kallonsa ba tare da ta amsa sallamar ba, sake matsawa tayi ta haɗe gira, cire shade din yayi yana kallon side view din face ɗinta yace "Young Lady", juyowa tayi ta ƙura masa ido, tsuke ido tayi bata kai ga magana ba ya rigata yace "it is me Ahmad..", ta zaro ido tace "ohh Sannu ai ban gane ba da farko", yayi murmushi yana shafa kwantaccen beard dinsa yace "how are you...?", tace "am fine alhmdllh", yace "masha Allah..", ya kalli road din da yake tamkar an sharesa babu motoci sosai ma bare kuma napep yace "where are you heading to...?", tace "Gida zani", yace "toh bari na ajiyeki ko", a fakaice ta dubesa sai kuma ta girgiza kai tace "No thank you...", yace "me yasa ba zakizo na ajiye ki ba..?, zafa ki iya kai Magrib anan tricycle basu wucewa sosai tanan", ta sake girgiza kai tace "i can wait....", da kyar yayi convincing dinta ta yarda bayan dai taga tabbas zata iya kai magrib don tin zuwansa wajen babu napep din da ya sake wucewa, da kansa ya buɗe mata front seat ta shiga a hankali ya mayar da ƙofar ya rufe kafin ya zaga ya buɗe driver seat ya shiga, ita dai ta maƙale daga jin window, gaba ɗaya she isn't comfortable ta takure waje ɗaya, Ahmad ya kunna motar ya fara driving da minimum speed, Silence ne ya ɗauka a motar, bayan sun fita daga unguwar Ahmad yayi breaking silence ɗin da faɗin "ya school...?", tana kallon handbag dinta dake kan laps ɗinta tace "alhmdllh ai mun kusa gamawa..", yace "University fa", tace "No secondary ne..", ya jinjina kai yace "as expected you are a teenager", zaro ido tayi tace "A'a fah", his eyes fixed on the road a hankali yace "how is she..?", ɗaga kanta tayi ta kallesa, a lokaci guda ya juyo sukay ido huɗu, da sauri ta ɗauke kanta ta kalli window tace "tana lfy alhmdllh...", yayi ajiyar zuciya yace "Ohk" da haka bai sake cewa komai ba, ita dai tana jiran taji ya tambayeta hanyar unguwar tasu don sai take ganin kamar ya manta, amma sai taga beyi hakan ba kuma tiryan tiryan hanyar unguwar yake bi, Hafsah tana ganin sun shigo unguwarsu zuciyarta ta buga, basu ƙarasa gidansu ba tayi saurin cewa "amm drop me here zan ƙarasa", slowing down yayi yabi gefen titi ya tsaya, tace "nagode" ta fara ƙoƙarin buɗe motar taji a ƙulle don bai buɗe lock ba, ta juya za tace masa ya buɗe taga ashe kallonta yake, da wani irin expression bisa fuskarsa yace "Sorry, one minute please", ta sauke hannunta dake riƙe da handle din ƙofar tace "Okay", yayi ajiyar zuciya still looking at her yace "the last time i met her ta gayamin cewa she is getting marry soon, at that time na yarda amma bayan wani lokaci sai mind dina taƙi yarda..", yayi shiru na 3secs kafin ya ɗora "i want you to tell me the truth..", ta ɗago kanta ta kallesa kafin ta mayar ƙasa tana wasa da ƙasan mayafinta tace "me yasa kake tambayata wnn...?", yace "bcox i need to confirm it ko na samu rest of mind..", kai tsaye tace "Alright, the truth is since last week Friday akay bikinta, yanxu ma daga gidanta nake...", Ahmad was very shocked and dump founded, yama kasa cewa komai, zuciyarsa ce ta ringa confusing nasa tana ce masa ai Hajar kawai tace masa haka ne to get rid of him amma ba hakan bane, Hafsah dai ganin baice komai ba tace "please open the door one minute has passed..", buɗe lock din yayi da kyar yace "sai anjima..", tace "thank you..", ya gyaɗa kai yace "you're welcome", ta buɗe motar ta fita ta rufe masa ƙofar, ta ƙarewa street din nasu kallo wai ko za taga wani wanda yaga fitowarta daga motar kuma wanda ta sani, Sosai taji daɗi da ta lura babu kowa, tana ƙarasawa ƙofar gida ta juyo, sosai tayi mamakin ganin motarsa bai tafi ba har lokacin, ita dai ta ɗakko keys daga jaka ta buɗe gida ta shiga.


★Umma ta ɗora hannu bibbiyu aka ta zabga wani uban salati tana kallon Anty tace "Jamilah na shiga uku na lalace shayin ɓera fa kika ce", Anty tace "ai ba ɗora hannu a ka za kiyi ba, kuma biki shiga uku ba Adda, wllh tllh zama bai kamace ki ba, idan haƙuri yayi yawa toh cutarwa ma yawa take, abu ne wanda ba yanxu aka fara ba an ɗebi shekaru anayi, ace har an fara farautar raii, gsky ya kamata ki farga cutar tayi yawa, idan da ace Mu'azzam bai ganta ba da shknn sai yadda Allah yayi, wa yasan halin da Hajar da Mijinta zasu shiga idan sukaci oil din nan, gani nai bazan iya shiru ba shine nace bari na dawo na tasheki daga barcin da kike..", Umma da kuka ya kwace mata tace "Jamilah yanzu ya zanyi dan Allah wnn wane irin masifa da bala'i ne, ace yarinyar nan tayi aure ta bar maku gida amma ku bita har gidanta da bita da ƙulli, da tana gida ma baku barta zaman lfy ba ita da gidan ubanta gashi gidan mijin ma an bita, wnn wace irin rayuwa ce..", Anty tace "Ahapp ki dena ɓaɓatu kina ƙarar da yawun bakin ki Adda, tashi tsaye za kiyi ki nemawa kanki salama, ki buga ƴan iska ga hukuma, wnn lamari ai ba na wasa bane, ƙoƙarin kisa fa..", Umma ta sharce hawayenta tace "bari mal ya dawo..", Anty tace "A'a Adda mal ai ba hukuma bane, idan nice ke yanzu ba sai anjima ba zan wanke ƙafa na tafi inda za a nemamin haƙƙina", tini Umma ta zari hijab ta saka ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "a ina zan buga matsiyatan..?", Anty ta tashi tace "muje", da sauri Umma ta fita tsakar gida Anty na biye da ita, banke ƙofar ɗakin nata kawai tayi babu wani batun padlock, tin daga soro kake jin muryar Baba yana kwalawa Maimuna kira, da iya volume din muryarsa yake kiranta har yana ƙoƙarin ƙwarewa, da mugun gudu Maama ta fito daga toilet, har tana fyarɗe hannu da ƙarfen langa langar ƙofar banɗakin, banga banga tayi a ƙofar ɗakinta tana zaro ido, a matuƙar fusace Baba da ya shigo gidan shi da Mu'azzam yace "ina Maimuna..?", Maama da hannunta yake azabar raɗaɗi da zugi tace "wace Maimuna kuma mal, yarinyar dake kwance tin shekaran jiya tana fama da masassara, yau kuma ta tashi cikinta ya tsuru wuni tayi tana fatattaka gudawa, gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login