Showing 18001 words to 21000 words out of 127052 words
Chapter 7 - Abnal Part 1 Complete Hausa Novel by Bilkisu Qazeem .txt
dan kwali babu?" sai a lokacin Nadia ta tuna cewa ashe babu komai akanta, sai ta dawo ta dauki hulan turban pink colour, dan pink and white flowery material half flaired high waist skirt ne ajikinta wanda ta siya daga MEEDAH'S COUTURE AND MORE (DM 09013851300), da farin top ne ajikinta, dama ita ba ma'abociyar kwalliya bace ba, but she looked cute, tana gama sa hular, sadiya ta kuma dauko turare ta fesa mata sannan tace
"dan Allah ki nutsu, now you go down there and behave just like the classy lady that you are"
"okay, I've heard you" Nadia ta amsata a takaice. Nadia kadai ce ta fita daga dakin while sadiya ta staya gyara gadon Nadia, Marwan ne yafara lura da ita yace
"your royal highness, sai yanzu kikaga daman saukowa" Nadia bata amsa shiba, sai zuwa tayi ta zauna kusada laila, laila tace
"dan Allah barta, lil sis please take your time, infact if you're not through with what you're doing upstairs, you can go back and continue, muna nan muna jiranki" dariya dukkansu sukayi banda Abnal daya kurawa cinema ido as if he's soo much enjoying the movie he's watching that baima san mai suke cewa ba, Nadia na lura dashi amma batace komai ba, anty faty ce tayi magana tana cewa
"ai indai Nadia ce, kaima Marwan kasan cewa yar ganin dama ce" shagwaba fuska Nadia tayi ta kalli laila tace
"anty kina jinta ko?" murmushi laila tayi tace
"karki amsata kinji, zanyi missing dinki ba kadan ba" rungumeta Nadia tayi tace
"same here anty"
"ai karki damu, nan da watanni zata zama tamu din din din" anty faty tafada cikin raha, sunkuyar da kai laila tayi tana murmushi, nan gidan sukayi sallar azahar, dasuka tashi tafiya, anty faty ta hadawa laila kaya iri iri, danginsu kayan kwalliya, gowns, perfumes, mai da sabulu, har inner wears sai data bata, Abnal kuma envelop ta bashi tareda kara mishi adduan samun sauki, godiya laila taringa mata kamar zata ari baki, Abnal Shima godiya yayi mata, rakasu har parking lot anty faty da Nadia sukayi while Marwan shi yana ciki receiving an official call, anty faty da laila ce suka tsaya suna hira while Abnal shi kuma ya jingina da mota , cos all this while baiyiwa Nadia magana ba, Nadia ce taje gaban shi ta tsaya tace
"nawa oo, tun baka barnan ba har ka fara shamun kamshi, kace inka tafi muka hadu a hanya, yi zakayi kamar baka sanni ba" fuskantar ta Abnal yayi yace
"please i beg you, ba kince in muntafi, antynki kadai zakiyi missing ba, ni ko oho?" dariya Nadia tayi tace
"inji wayace maka haka?" Nadia ta tambayeshi while still smiling
"uncle, kodai you want to deny it ne?" Abnal Shima ya tambayeta, murmushi Nadia tayi sannan tace
"kai, matarka ta shiga uku" Abnal najin abun datace yayi murmushi yace
"why would you say that?"
"because of your jealousy" Nadia ta amsa shi
"na you know that one" Abnal replied, tsaya kallon shi Nadia tayi, sannan tace
"you know I'm gonna miss you, expecially your troubles" murmushi Abnal ya kumayi sannan yace
"wato nice trouble maker kenan?"
"A mana,ai ba karya nayi maka ba, you enjoy looking for my trouble" Nadia ta amsa shi
"kuma zan cigaba ba, ai you're stuck with me" Abnal ya kuma fada mata
"how am i stuck with you? Sai kace wani mijina? Ai daga yau shikenan" Nadia itama tafada mishi, dariya Abnal yayi sannan yace
"baga waya nanba, I'm gonna disturb you like hell, even your so called boyfriend will have to endure me", haka suka cigaba da neman tsokanan juna har Marwan yazo ya samesu, Amma kafunnan saida Abnal ya takurawa Nadia cewa ta bashi digits dinta, saida Nadia ta gama ja mishi aji sannan ta bashi, Marwan na zuwa su uku suka shiga mota, chauffeur yajasu suka bar gidan.
15/12/2021, 12:35 pm - +234 704 414 3447 was added
15/12/2021, 12:35 pm - +234 704 479 4111 and +234 802 789 5260 left
15/12/2021, 7:21 pm - ~👸Fatima Ibrahim joined using your invite
16/12/2021, 9:12 am - MEEDAH'S COUTURE AND MORE: I just published "Chapter 8" of my story "ABNAL". https://www.wattpad.com/1107419347?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ummuhamdiyah&wp_originator=NSfRPbQihWV9tqWwGA5%2FSs4NgqLgYqt0k40u4qVd%2FbTdffL%2FNjTW9W2L9oBRQ76upwNNKmVZV0m%2F6JzbKLuB%2B8AS0FcNBOAIws8a8bc6pvIPb0yQq3OWidfY%2FsmsuObO
🔴🔴🔴⚫⚫⚫🔵🔵�
Book by :Bilkis Qazeem (ummu Hameedah)
ABNAL
Chapter 8
THIS BOOK IS ABSOLUTELY FREE 💃 💃 💃
If at all I'm entertaining in any way or form, please do follow me on my Instagram handle 👇�
https://www.instagram.com/meedahs_couture_and_moreÂ
and as you do so may Almighty Allah answer all your hidden and open prayers �, Ameen.
And please share the book to other groups da kuke ciki, *wannan* *ne* *correct* *Instagram* *link* *dina* , *wanda* *nake* *posting* *before* *was* *wrong*, *so* *please* *show* *me* *love* *by* *following*.
A hanyarsu ta zuwa keffi, Marwan yayi branching a wani babban mall yace wa Abnal yazo ya raka shi siyan wani abu, da laila ta tambayeshi mai zasuyi, ce mata yayi duk abun dazasuyi is non of her business, ita dai tayi zaman mota jiransu, suna shiga cikin mall din, direct wajajen da'ake siyarda waya ya nufa, yace wa Abnal ya zabi duk wayar dayake so, musu Abnal ya tsaya yi dashi, dan gaskiya Abnal yasan cewa shi dai bazai iya daukan wani abunba, not after all what him and his family has done for them, expecially him, da Marwan yaga cewa Abnal zai ba'ta musu lokaci, sai kawai shi da kanshi ya fara daukan wayar, iPhone 12 guda biyu ya dauka, daya na Abnal while the second one is for sameera, while laila ita kuma ya daukar mata iPhone 12+, daga nan ya karasa wajen kayan makulashe, rokonshi Abnal yafara yi cewa dan Allah ya isa haka nan, he shouldn't take or buy anything for them again, Amma biris Marwan yayi dashi, sai cewa yake, "haka zaku komawa Mami da sameera hannu Rabbana bakuyi musu tsaraba ba, after leaving home for over two weeks, haba ai that won't be fair", Abnal had no option than to just stand by and be observing him, saida Marwan yayi musu siyayya mai yawa sannan suka nufi counter ya biya kudin abubuwan daya siya. laila kuma data gaji da zaman motar sai kawai ta fito ta jingina bayanta da motar, dan ba daman tace zata bisu, minti biyu da fitowar ta, saiga wani Benz yazo yayi parking a gefen inda take tsaye, familiar scent din cologne din dataji ne yasa tadan waiga dan taga waye wannan mai kamshin, aikam tana waigowa tayi ido hudu da wani handsome guy, laila batasan lokacin data furta sunan 'Ishaq' ba, gabanta wanda aka kira da Ishaq yazo ya tsaya yana mata kallon mamaki sai yace
"laila is that you?" murmushi laila tayi sannan tace
"in bone and flesh", ishaq couldn't believe it dan yanda yaga cewa laila ta changa, and her outfit screams of elegance, and gata jingine a jikin wani expensive ride, sai ishaq ya kuma cewa
"How have you been?"
"Alhamdulillah, I've been good, and you?" laila itama ta tambayeshi
"I'm fine" ishaq ya amsata, sai laila ta kalli yar yarinyar da ishaq ya rikewa hannu, the girl will be around 3yrs of age, sai tace
"and who's this little angel? Is she your daughter?" laila ta jera mishi waennan tambayoyin, murmushi ishaq yayi sannan yace
"yes she is, I've been married for over three years now, what about you, are you married?" ishaq ya tambayeta
"wow, I'm happy for you, well I'm yet to be married" laila ta amsa shi, fadada murmushin shi ishaq yayi dayaji abunda laila tace, sannan yace
"i know its not polite to stand you here in the public like this, so please can i have your digits and maybe have lunch one of these days, with that we would be able to talk at length" ishaq yafada mata
"ishaq i don't think that...." ishaq bai bari laila ta karasa maganar taba ya katseta ta hanyar cewa
"please don't say anything, i promise i just want to see you koda sau daya ne, please for old time sake" ishaq yafada mata pleadingly, laila didn't want Marwan to come out and meet them, and tasan cewa indai ba bashi digits dinta tayi ba, ishaq will not leave her alone, sai kawai ta mika mishi hannu while ishaq yasa mata wayar shi, tana gamasa digits dinta tana cikin mikawa ishaq wayar kenan saiga su Marwan nan fitowa, Marwan shine agaba, while Abnal da daya daga cikin securities din mall din dayake jan trolley din da akasa duk kayayyakin da suka siya suna bayan Marwan, Marwan couldn't believe the scenerio infront of him, wai laila ce tsaye da wani tana mika mishi waya, he just hope it's not what he's thinking, ishaq noticed the direction da laila take kallo sai shima ya juyo ya kalli gurin, the only person he could recognize among them was Abnal, su Marwan na karasowa ishaq ya mika mishi hannu, Marwan was a little bit reluctant in shaking his hands but kawai basarwa yayi ya bashi hannu suka gaisa, sai ishaq ya kalli Abnal sukayi musabaha ishaq yana cewa
"longest time bro, how have you been?"
"Alhamdulillah, I've been great" Abnal ya amsa shi atakaice, cos he can already sense the tension radiating from Marwan, kallon laila ishaq yakumayi yace
"okay, let me not take any more of your time, i will give you a call later" laila kasa amsa shi tayi sai kawai tayi mishi ya'ke, juyawa ishaq yayi ya shiga cikin mall din, lokacin security din ya gama sa komai a butt din motarsu, kudi Marwan ya ciro ya bawa security din sannan ya shiga cikin mota, kallon 'what the hell did you just do' Abnal yayiwa laila, sannan Shima ya shiga cikin motar, laila was the last to enter dan harga Allah duk jikinta yayi sanyi, to God who made her, the only reason why she gave ishaq the digits were just so he will leave her alone, maganar lunch din dayakeyi ma, ita tasan ko giyar wake tasha she will never follow him anywhere.
Marwan baice mata kala ba, Amma inka kalleshi, one will know that this guy is upset, kasa ce mishi komai laila tayi cos ko kallon inda take Marwan baiyiba, he was just operating his MacBook. Har suka isa keffi Marwan bai bawa laila fuska ba, Abnal was the one that was directing the chauffeur har suka isa kofar gidansu, tun lokacin da motar ya shigo unguwarsu yan unguwar suka kurewa motar ido tsabagen yanda motar ta hadu gashi basu saba ganin irinshi ba, bin motar da ido sukayi dan ganin gidan da motar zai tsaya, they couldn't believe it dasu kaga gidan daya tsaya, dan a nasu tunanin babu mai irin wannan kudin dazai sosu, Marwan was more than shocked dayaga unguwar dasu laila suke, though yasan cewa they're from a humble background amma bai taba zata cewa their level of poverty ya kai wannan ba, Abnal ne ya fara fitowa daga motar, Sameera dake serving din wani customer abunci ne tafara hango Abnal, rugowa tayi da gudu tazo ta rungume shi, cos she wasn't expecting them today, so is Mami, zuwa lokacin Marwan da laila suma sun fito daga motar, barin Abnal sameera tayi taje ta rungume laila cos she has really missed them, gaida Marwan sameera tayi Marwan yace
"where's my own hug?" ya tambayeta jokingly while smiling , sunkuyar da kai sameera tayi tana murmushi, laila ce ta tambayi sameera inda mami take, sameera ta amsa dacewa tana cikin gida, shiga sukayi cikin gidan while Marwan shi ya tsaya a zaure yana jiran ayi mishi iso, umarni ya bawa chauffeur dinshi cewa yafara kwaso kayan dake cikin booth zuwa zauren gidan. Mami da fitowar ta kenan daga bayi ce ta hango laila da Abnal, daskarewa tayi tsaye cos she wasn't expecting them, basu gaya mata cewa zasu dawo yauba, rungumeta laila da Abnal sukayi dan ba karamin missing sukayi mata ba, daga fuskar Abnal Mami tayi tana kallon shi hawaye na fitowa daga idanuwar ta, dan bata taba zata cewa Abnal ya samu lafiya irin haka ba, share mata hawaye Abnal ya farayi yana cewa
"Mami dan Allah ki daina asarar hawayenki haka nan" murmushi Mami tayi sannan tace
"hawayen farin ciki ne Abnal, bansan ka samu lafiya har haka ba, godiya ga Allah" Mami tafada, laila ce tace
"Mami ki dauko hijab dinki, doctor Marwan yana zaure"
"wai tare kuka zo dashi?" Mami ta tambayeta
"A, shi yakawo mu" laila ta amsata
"shi ne kuka shanya shi acan, maza kiyi mishi iso" Mami tafada tana shiga cikin daki dan dauko hijabinta, sameera laila ta aika ya shigo da Marwan dan uptill now bata san ya zasu karkare ba, sameera na zuwa tace ance ya shigo, tare su biyu suka shigo cikin parlor din gidan, parlor din babu komai acikin sa, ko irin leather carpet dinnan babu sai cement, iya cushion chair guda biyu ne a parlourn, da one seater da three seater shikenan, ko TV babu, but if there is one thing that really impressed Marwan is how neat and tidy everywhere is, no dirty or any funny stench, Marwan na shiga , mami ita kuma ta saka hijab dinta ta fito parlor, sai Marwan ya durkusa ya gaidata, rasa inda zata sashi Mami tayi cos kallo daya mutum zaiyiwa Marwan yasan cewa babban mutum ne, godiya Mami ta fara mishi bayan ya zauna, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Marwan shima yasan cewa yasha godiya da adduoi daga bakin Mami, ruwa Mami ta gayawa laila ta kawo mishi amma sai Marwan yace
"A'a Mami ni yunwa nakeji" ya fadi haka ne dan yana son Mami ta saki jiki dashi sosai, cos he noticed cewa kunyar shi take ji, Mami najin abun dayace, sai tadanyi jim kadan dan ita gani take basuda irin abuncin da Marwan zai iya ci, da Marwan ya lurada reaction din Mami sai ya kuma cewa
"Mami karki damu duk abun da kike dashi zanci, infact ko daga abuncin da kuke siyarwa ne, i want it" da Mami taji abun dayace sai tace
"kai anya zaka iyaci kuwa? Ba irin abuncin daka saba ci bane ba" murmushi Marwan yayi ya kalli sameera yace
"dear dan Allah ki ibarmun shinkafa" sameera na kokarin tashi kenan laila tace
"don't worry, let me do It" tafada tana tashi, kallon ta Marwan yayi yace
"no, i prefer your sister to do it" yana gama fadan haka ya kuma kallon sameera yace
"please do me the honor and serve me" yafada mata with a very sweet smile on his lips, sameera had no option than to go do what she's been ask of, Abnal sai murmushin mugunta yake mawa laila, maka mishi harara laila tayi. Bayan Marwan ya gama cin abunci, sameera ya kuma kira ta kwashe kwanukan sannan ya kalli mami yace
"Mami dan Allah inasonyi magana dake" sannan ya kalli su Abnal yace
"bruh can ya'all please excuse us?"
"sure" Abnal ya amsa shi a takaice, waje wajen canteen dinsu su uku suka fito suka zauna, sai santin yanda jikinsu yayi fresh suka kara kyau sameera take tayi. da Marwan yaga cewa daga shi sai mami, sai yafara cewa
"na farko Mami, Alhamdulillah cewa Abnal ya samu lafiya, duk dokokin daya kamata yabi na sanar dashi kuma nasan cewa bi iznillAh baza'a samu matsala ba, abu na biyu dana keson in rokeki, indai kinsan cewa kin dauke ni a matsayin da ko ka'ni dan Allah dan annabi wannan alfamar dazan nema banso kice a'a, indai kince a'a toh nasan cewa baki daukeni a matsayin dani na dauke kuba... "Mami ce ta katse shi ta hanyar cewa
" duk wannan taimakon daka yimun banga wane irin alfarmar dazaka nema dazan ce maka a'a ba, bara ma kaji, koma menene dazaka nema, amsana shine A, indai bawai abun ya sabawa addini ba, toh amsar shi A ne, nayarda da koma menene" Mami tafada mishi, hamdala Marwan yayi sannan yace
"ai baima sabawa addini ba, amma naji dadi da wannan yardar da kika yimun, dama ba wani abun bane ba face inason tura Abnal zuwa kasar waje yaje yayi masters dinsa acan, wannan change of environment din zai taimaka mishi sosai wajen kara samun sauki" aikam Mami najin abun da Marwan yafada sai tayi dan jim kadan, dan harga Allah ita bata taba kawo cewa wannan ne alfarmar da Marwan zai nema ba, yanzu kuma babu daman tace a'a, dan that will be her going back on her words, da Marwan yaga cewa Mami batace komai ba sai yaci gaba dacewa
"abu na uku shine, inason laila kuma nayi mata magana ta amince, yanzu amincewarki nake so" Marwan ya karasa maganar shi, numfasawa Mami tayi kafun tafara magana kamar haka
"naji duk bayaninka, nafarko dai godiya zan kuma maka abisa duk abun da kai da yan uwanka kuka yimana, duk laila ta fada mun ta waya, Allah kadai ne zai iya saka muku da mafificin alherin sa, na biyu shine maganar tura Abnal da kake sonyi zuwa kasar waje, Allah ya gani bansan cewa alfarmar da kakeson nema kenan da ban yarda ba, Amma tunda nariga nace A, toh banda zabi kuma, Amma nima ina son kayimun wani alkawari kuma banason kace a'a" Mami itama tafada
"toh wane irin alkawari ne kike son inyimiki?" Marwan ya tambayeta
"so nake kayimun alkawarin cewa, daga wannan taimakon na tura Abnal kasar waje da kake sonyi, bazaka kuma yi mana wani taimakon ba, indai ka yarda toh nima na yarda yaje" Mami ta fada mishi, shiru Marwan yayi na wani lokaci sannan yace
"A nayarda", ya amsata a takaice, sai Mami tace
"madallah, maganarka na karshe dakace kana son laila, maganar gaskiya laila ba yarinya bace ba kuma, amma a matsayina na uwa, bazanso ya'ta tayi aure zuwa gidan da bazata samu kwanciyar hankali ba, kai zaka iya cewa kana sonta koda daga gidan talaka take, iyayenka fa? Ba lallai bane su susota ba, dan irin haka ya taba faruwa da ita, saurayin na mutuwar sonta amma iyayen shi suka hana, babu irin cin mutuncin da basuyi mana ba, toh kaga inda matsalar take" Mami tafada, bayan Marwan ya gama jin duk bayanin Mami, baice komai ba dan ya riga yasan cewa Mami zata iya fadan haka, so already shi ya tanadi abun dazaiyi, sai kawai ya ciro da wayarshi yayi dialing din wani numbar tareda