Showing 216001 words to 219000 words out of 237912 words
Chapter 73 - MAKAUNIYAR KADDARA!! BY BILYN ABDULL CE.txt
kuwa da biyu suke zuwa barkar ƴan biyun amaryar baba dansu sake tabbatar da zancen ciki da halin da Inna ke ciki na samun ciwon ɓarin jiki a silar faɗuwar da tayi.
Ga ƴan uwan amaryar baba sun cika gida daga jiya zuwa yau dan ana haihuwa baba ya kirasu ya sanar musu. A safiyar jiya saiga kusan mutane shidda sunzo, sauran kuwa sai daren suna. Duk abinda ke faruwa kuwa akan idonsune sai mamaki sukeyi kamar almara ko hikayoyin marubuta.
Cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan maigari ya cika taf da jama'ar gari saboda kiranye da aka saka sanƙira yayi musu. Ciki kuwa har dasu Sa'a a ƴan kallon zuwa ganin maimartaba. Sai da guri ya nutsa sannan maimartaba ya fito. A take waje ya ruɗe yau gasu ga maimartaba. Farin ciki duk ya bayyana a fuskokinsu kamar shima yanda yaji daɗin yanda suka amshesa duk da basu da wani cigaban kirki a garin, zaima iya cewa baisan da zamansuba saita wannan silar. Sai yaji zuciyarsa ta ƙara rauni da karaya akan nauyin al'umma dake kansa.
Bayan Matawalle ya isar da saƙon gaisuwar sarki a garesu ya gabatar da hajji lanti a gabansu tai bayani akan silar ɗaukar Zinneerah zuwa birnin katsina. Itama Hajiya Haule tayi bayani kamar yanda tayi a kano. Kafin Zakiyya ma da takejin tamjar ranta zai fashe tai nata bayanin akan gaskiyar dasama Zinneerah ciki da sukai ba ta hanyar iskanci ta samosa ba.
Take gurin ya ƙara ruɗewa da al'ajab da mamaki. Ɗunbin tausayi da nadamar cin kashin da suka dinga ma yarinya ya ringa dawo musu a rai harda masu kuka. Kafin wani dogon lokaci labari ya ƙara kaiwa ga mata dake cikin gida da jama'ar sauran ƙauyukan gefensu da duk sukasan da labarin cikin na Zinneerah. Abinka kuma da ƙananun gari babu wanda ya manta musamman daya kasance ba'a jima da zuwa akai bikin Zinneerah ɗin ba. Bakajin komai sai ALLAH wadarai ga Inna asabe dasu Zakiyya. Dan su maimartaba kan sun tafi sunbar abin faɗa ga mutane. Musamman daya kasance yanzu ALLAH ya bama Zinneerah cigaban rayuwa. Ga kuma samakon nan a jikin Tinene da ita kanta Innar dake kwance rijif ita ba gawaba ba kuma rayayya ba.
Ita kanta da labarin yaje mata sai gata tana hawaye zuciyarta na ƙara hauhawar zafi. Daga ƙarshe jikintane ya ruɗe sai da aka kwasheta zuwa asibitin cikin kusada..............✍
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
_________________________
*Page 65*
............Ganin dare ya fara yasa Hajiya Iya tada Zinneerah, shima AK taje ta tasoshi akan suzo su wuce gida haka nan. Badan Zinneerah taso hakanba ta miƙe, shima AK ɗin ya fito yana faman dafe kai. Kowa bai kallaba a falon yay ficewarsa duk da yasan akwai su Mammah zaune. A waje ya samu su Haneef da little a hannu, aiko ya maƙale masa. Amsarsa yay suka shiga motar da Khalipha zai jasu dan shi bazai iya tuƙinba. Zinneerah ma da Hajiya iya ta rakota dasu Meenal ta shiga baya.
Koda suka iso Khalipha ne ya buɗe musu ƙofar falon, daga haka ya juya yana musu sai da safe. AK ya ɗauka Little suka wuce sashensa batare daya kula Zinneerah ba. Itama ɗin ba kulashi taiba ta shige nata sashen. (Faɗan masoya hutu😂😝).
Ko wanka kasa zamanyi Zinneerah tayi, tana shiga gado ta faɗa tai kwanciyarta dan barcin tafi bukata. Musamman daya kasance maganin da Granny ta bata yana saka barci.
Shima a ɓangaren AK kwantar da little dayay barci tun a mota yayi, ya samu yaɗan watsa ruwan yasha tea dan yanajin yunwa, duk yinin yau ya gagara sakama cikinsa abinci, basket ɗin abincin da suka bari a gidan tunna safe ya ɗauka ya bubbuɗe. jin babu abinda abincin yayi ya sashi ɗauka ya fita dashi ya kaima maigadi yace ya badashi kar ai asararsa. Daga haka ya dawo shima yay kwanciyarsa bayan yaɗan leƙa Zinneerah yaga harma ta kwanta.
*_WASHE GARI_*
Da safe sun tashi Alhmdllh, musamman Zinneerah batajin ciwon komai a jikinta. garama AK dai jikin nasa sam baya masa daɗi. dan ko sallar asuba a gida yayi abunsa ya koma ya kwanta. Sai kusan ƙarfe bakwai da little ya farka yana damunsa ya miƙe da ƙyar ya ɗakkosa gaba ɗaya yayo sashen Zinneerah da shi. A lokacin tana cikin saka turaren wuta dan ta gama gyaran ko ina.
Sanye take cikin wando da riga na kayan barci farare tas, yanda suke da santsi yasa suka manne mata a jiki sosai, gashi ko bra babu a jikinta. Kallo ɗaya yay mata ya kauda idanunsa, itama cike dajin kunyar yanda ya sameta dan batai zaton shigowarsaba takai ƙasa tana gaidashi cikin girmamawa batare da ta yarda sun haɗa ido ba.
Amsa mata yay a daƙile yana dire little kusa da ita dan haushinta yakeji, har itace zata buɗe baki tace zata barsa saboda wasu. Wannan magana tai masa ciwo, tanama cikin masa ciwon. Juyawarsa yay ya fice ta bishi da kallo zuciyarta na raya mata yana fushine saboda matarsa da aka wuce da ita. Haka kawai sai taji ranta ya sosu. Ta ɗan taɓe baki tana miƙewa da ɗaukar little ɗin dake mata ƙorafin shi tea zaisha.
“Dalla yima mutane shiru abinda ka iya kenan sai cin tsiya kamar ubanka”.
Kuka ya sanya mata saboda dungure kansa da tayi. “Malam yimin shiru ALLAH kona huce a kanka”. Daga haka ta ɗaukesa suka nufi ciki dan ta masa wanka sannan tazo tanadar musu abinda zasuci dan tacema Granny abar kawo musu abinci zata fara girki.
Wanka tayi masa itama tayi sannan, tura little tayi wajen AK ya amso kayansa, ita kuma tai ƙoƙarin shiryawa a gurguje ta fito. Sai da ta haɗa ma little tea ta fara nema musu abinda zasuci yanda bazata takura ba. Harta gama bataji ɗuriyar little mai kukan yunwaba, hakan bai dametaba dan tasan wani abun ya samu acan.
Kamarko ta sani dan AK na gama saka masa kaya tea ɗin ya haɗa masa da ruwan dispencer, ya haɗa masa da biscuits. Shima wankan yayi dan yanason yaje asibiti kar abin yay masa nisa. Koda ya fito wankan rashin ƙarfin jikin ya sakashi sake komawa ya kwanta har takai barcin ya sake figarsa.
Lokacin da Zinneerah ta shigo falon da kayan abincin little kawai ta samu a falon ya barbaza filos ɗin kujera yayma falon kaca-kaca. “ALLAH ya shiryeka” kawai ta iya cewa ta ajiye abincin a dining. Kayan shara ta ɗakko ta fara a tunaninta AK yana wani abunne a ciki. Waje ɗaya ta saka little zama harta kammala kimtsa falon tasa turare. Ganin har lokacin shiru babu motsin dadynsa ga goma harta gota ya sata nufar bedroom ɗin a ɗarare danta sanar masa ga abinci. Kusan sau uku tai sallama babu amsa. hakan ya sata tura ƙofar ta ɗan leƙa kanta a tunaninta koma dai baya gidan ne.
Zaune ta hangosa a bakin gado dan dai-dai ya tashi kenan saboda sallamarta. Hannunsa dafe da kansa dake masa tsananin ciwo. Jitai tamkar ta juya da baya dan da ga shi sai boxer ne, amma ganin yanda ya dafe kansa yasata tunanin ba lafiya ba. tunda jiya dai ga a yanda suka dawo su duka, kuma tanaji sanda yake sanarma Khalipha kansa na masa ciwo a jiyan.
Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin ɗakin, sai da tazo kusa da shi sannan ta rissina tana gaishesa batare data sake yarda ta kallesa ba. A yanda ya amsa ɗin kuma sai tsoro ya sake kamata, cikin damuwa tace, “Yayanmu baka da lafiya ne?”.
Shiru kamar bazai amsaba har kusan mintuna biyu sannan ya ɗago idanunsa da sukai jajur yana dubanta. Kwalliyar tata tayi masa ƙyau, dan haka yaɗan lumshe ido ya sake buɗewa a kanta da cewa, “Kaina ke ciwo. Haɗamin ruwan wanka inason naje asibiti”.
Sosai damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta. ta shiga jera masa sannu kamar zatai kuka. Shi dai kallonta kawai yake dan duk da yana cikin halin ciwo yanda takeyi ɗin tada masa tsigar jiki take. Ga mayatattun turarurrukan ta da ƙamshinsu ke ɗaga masa hankali zuwa ga buƙatarta. Ya ɗan cije lips ɗinsa yana komawa da baya a saman gadon ya ɗan kwanta kafin ta kammala haɗa ruwan.
Sai da ta tsaftace masa toilet ɗin duk da ba wani uban datti yay ba sannan ta haɗa ruwan, ta fito hanunta da tissue data warwaro daga can tana gogewa. Da ƙyar ya iya yunƙurawa ya tashi zuwa bayin.
Ta ɗan sauke numfashi da fara ƙoƙarin gyara masa gadon, daga haka ta zarce da tsaftace ɗakin gaba ɗaya. Ɗan jimawa da yake a wanka yasa harta kammala kafin ya fito, tana fesa fresheners take jiyo little na ƙwala mata kira daga falo. “Aunty! Aunty!!”.
“Oh ALLAH! Na'am”. Ta faɗa tana ajiye gwangwanin freshener ɗin. hakan kuma sai yay dai-dai da fitowar AK daga bayi. Bata yarda ta dubesaba, sai sake amsama little kiran da yake mata tayi. Ta ɗaga ƙafa zata nufi hanyar fita taji an ruƙo mata hannu. cak ta tsaya dan tasan dai shine.
“Idan kin tafi wazai shiryani”. Ya faɗa a hankali yana jawota ta juyo tana fuskantarsa. Kasa kallonsa tai dan dagashi sai guntun towel. Ganin yanda taketa sinne kai ya ɗago fuskar tata da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata. “Nazama surukinki ne?”.
“A'a” ta faɗa a hankali tana ɗan murmushi.
“Hum” ya faɗa da kama hannunta yajata suka ƙarasa gaban mirror ɗin. Duk yanda taso zamewa dole tabi umarnin sa. dan dolenta ta shafa masa mai da kanta, ta kuma ɗakko masa kayan da zaisa wanda bazai takura ba. A gaɓar shiryawane dai kam ta kasa duk yanda yaso dole ya barta ya shirya da kansa.
Falo suka fito a tare suka sami little, baiyi tunanin ita tai girkinba, sai dai ya masa daɗi, kaɗan yaci yau kam dan da gaske bayajin daɗi, yana gamawa ya koma falo ya kwanta cikin kujera saboda jiri, wayarsa yace ta ɗakko tai kiran Doctor Mahmud yazo ya dubashi, dan bama zai iya driving ba. Cikin damuwa ta ɗakko ta lalubo masa no ɗin Dr Mahmud ɗin, yana ɗagawa ta miƙa masa wayar yay magana da shi.
Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Doctor Mahmud da Khalipha tare. Bayan ta gaisa dasu ta bar musu sashen saboda kallon da AK ke mata na gargaɗi dan ko mayafi babu a jikinta yau.
Koda ta koma a can tai zaman karyawa itama. Bata sake leƙo sashenba sai da little yazo ya kirata. Hijjab ta zunbula dan hanyar lafiya a bita da shekara. Khalipha kawai ta samu tare da shi sai Huzaifa da batasan da zuwansaba. Ta gaisa da Huzaifa daketa tsokanarta da amarya amarya. Ita dai murmushi ne nata kawai babu bakin ramawa.
Ta ɗan dubi AK da akema ƙarin ruwa idanunsa a lumshe. Sannu tai masa dan ta fahimci idonsa biyune, saboda riƙe yake da hannun little dake tsaye gaf da fuskarsa yana masa maganar da batasan kota micece ba. Khalipha ne ya sanar mata abinda zatayi, dan haka ta juya ta sake fita ta barsu.
★*********★
Abu kamar wasa sai ga AK yasha zazzaɓi kwana biyu, dan sai da takai har Baffah da Uncle Ahmad sai da sukazo dubashi, hakama su Mammah dake shirin komawa gobe idan ALLAH ya kaimu sunzo sun dubata da sake neman gafarar Zinneerah. Yanda Mammah taketa tattalin Little sai ta baka tausayi, gashi shi saima wani ƙiwan wulaƙanci yaketa faman mata.
Shima AK ɗin sun ƙara masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da ƙaddara. Mammah ta sake neman gafararsa duk da ta fahimci fushi yake da ita. Nuna mata yay shifa komai ya wuce, amma ita tasan bai wuce ba tunda ya kasa sakin jiki da kowa sai ɗansa da matarsa.
Yau Alhmdllh ya tashi jikin nasa da sauƙi sosai, dan har fita yay zuwa gidansu shi da little. Bayan sallar la'asar Zinneerah na falonta na biyu zaune tana cire ƙumba ya shigo da sallama. Gaidashi tai da masa sannu da dawowa. Ya amsa mata yana kaiwa zaune. Ita kuma ta miƙe dan kawo masa ruwa. Amma sai jitai ya ruƙota. Duk yanda taso zamewa ya hanata damar hakan. Cikin wani irin kasalalliyar murya yake mata magana a kunne. “Wace irin amaryace wannan mai rowan tsiya nikam?”.
Ɗan dubansa tai dan bata fahimci ina ya dosaba, ya ɗage giransa ɗaya yana kasheta da kallonsa mai sakata nutsuwa. Itama dai yau tayi dauriya da jarumtar kallon nasa cikin idon, da wannan damar yay amfani wajen ɗora lips ɗinsa kan tausasan nata. Sukaja numfashi a tare da lumshe idanunsu. Sai gata luff ta nutsu tana amsa saƙonsa. Sai da labarin ya fara canja salo kuma ta nema raina kanta. Ko saurarenta baiyiba ya ɗauketa cak yay cikin bedroom ɗinta da ita. Ganinfa irin na ranar yake son maimaitawa tuni ta fara tsuma da neman roƙomsa shikam baima jinta ya antaya duniyar kodumo.
Duk yanda taso daurewa yau ma dai kasawa tai, sai da ta kaita da masa kuka, dan wannan yayan nasu bana wasan yara bane, baisan sauƙi ko sassauci ba har sai ya kai boader.
Sai da ya ga ya samu kansa ya koma tsokanarta da suna ragguwa. Ita ko ta dinga tura baki har a wajen wanka da ya taimaka mata ta kuma gasa jikinta yanda zataji daɗi. Suna fitowa ya gudu sashensa dan kiran sallar magrib ake tayi.
Bata sake ganin ƙeyarsa ba sai bayan sallar isha'i, ta fito domin nema musu abinci shi kuma ya shigo hannunsa ɗauke da leda alamar ya biya ta ɗakinsa kafin yazo nan. Zama yay da kiran sunanta, dan haka ta nufosa zata zauna ƙasa ya nuna mata gefensa. Sai da takai zaune sannan ya miƙa mata ledar. Amsa tai tai godiya duk da batasan minene a cikiba, tana buɗewa taci karo da waya mai ƙyau. Ai tuni jin daɗi yasa ta manta da Yayansu ne fa. Ta miƙe ta ɗane masa jiki tana murna.
Murmushi yalwace da fuskarsa ya karɓe abinsa yana cusa kansa a wuyanta. “Yanzu kin ɗaneni, da an taɓaki kuma ki hau yima mutane raki”.
Kanta ta cusa a ƙirjinsa tana dariya da faɗin “ALLAH akwai wuya Yayanmu, kai dan baka sani bane”.
Dariya ta basa, amma sai baiyiba ya cigaba da murmushinsa yana cusa hannunsa cikin gashinta, “Ni kuma gashi ba wasa zan tsayaba ƙannen little nakeso da wuri, dan naga shikam ba barmana zasuyiba haka zai ringa yawo tsakanin danya, gidan Abba, gidan Baffah, london. Kinga saiki sama mana namu muma”.
Ƙwaɓe fuska tai cikin marairaicewa. “Yayanmu ba yanzuba akwai wahala wlhy”.
Kansa ya ɗan girgiza mata da sumbatar lips ɗinta. “Haba my Neerat ai ke jarumace tunda kika haifo Abdul-Mutallab tun kinada shekaru sha huɗu, yanzu kam ko ƴan huɗu ne zaki iya ai”.
“Sai dai in zaka tayani”.
Ta faɗa tana ɓoye fuskarta a jikinsa. Sosai yanzu kam ya ƙyalƙyale da dariya. “Mizai hana na tayaki nikam Mrs Shira, ai tare zamuyi rainon cikin muyi naƙuda abunmu mukuma rainesa idan ya fito”.
Dariya sosai Zinneerah keyi itama mamaki fal ranta na Yayansu. Ashe haka yake da sauƙin kai da sakin jiki, amma yayta musu mazurai a gida.
Washe gari suna kammala breakfast yabar gidan zuwa jigawa. Da wannan damar ta samu zaman gyara gidan sannan tai zaman kiran ƴan uwa da abokan arziƙi data samu nombobin wasu a wajensa. Wanda bata da shi mmn sadiq ta tura mata da su hajiya iya. Ƴan danya ne ƙarshen kira. Inda tai farin ciki matuƙa dajin muryar babanta.
A wayar tasune yake sanar mata shagalin suna da za'ai gobe idan ALLAH ya kaimu. tare da abinda ke faruwa akan Karima na zancen sarƙa data sata acan Kaduna aka kaita kotu, a yanzu kuma babu sarƙar babu kuɗin ga Babawo ya saketa saki har uku. Ya ɗora da faɗa mata halin da Inna take a ciki da zancen cikin Tinene. Harma da wanketan da mai martaba yaje yayi har danya bayan sun bar kano tare.
Zinneerah tayi kukan daɗi tayi na damuwa tayi na baƙin ciki a wannan yinin. dan har AK ya dawo daga jigawa a jigace ya isketa. A kallo ɗaya ya fahimci damuwar dake tare da ita. Baice mata komaiba harta taimaka masa yay wanka yay zaman cin