Showing 24001 words to 27000 words out of 37846 words

Chapter 9 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt

25 Oct 2025

374

lokacin ta san maganar ciki ta fito fili. Sam bata san a fili ta furta kalaman ba, amma a ganinta laifin Alhaji Habib ba abin boyo bane. Matsalarta daya ita ce ta yaya zata sanar ta kuma fahimtar da yaran laifin mahaifinsu?. Cikin kunci da tsantsar takaici ta jijjiga kai "kwarai kuwa shi, mahaifinku nake nufi Faisal. Babanku mutumin banza ne, azzalumi mai boye aibu da alkhairai. Shi kare ne da fatar kura, fuska biyu ke gare shi. Wannan halin na mahaifinku abin tir! Da Allah wadai ne". Ta kai hannu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa. Sannan ta ci gaba "ya zama dole in gaya muku babban aikin mahaifinku shi ne safarar 'yan mata. Kananun yara 'yan kasa da shekara ashirin yake diba yana sayarwa turawa suna yin abinda suke so da su". Ido waje Faisal ya gurfana gaban gadon da Momy take kai yana kallon fuskarta. A lokacin ji yake kamar ta saki murmushi tace duk abinda ta fada wasa ne. Ko kuma ma a ce wata zautuwa ce ta kamata ta fadi hakan a kan amintaccen mijin nata mafi soyuwa ga zuciyarta. "Momy!" Ya kira sunanta a razane yana jijjiga kafarta wai ko Allah zai sa ta dawo hayyacinta ta karyata abinda bakinta ya fada a kan Dadynsu.


Ganin babu sauyi ko alamar karaya a fuskarta yasa ya saki kafar tata da sauri ya koma gun yayansa da ya gani zaune daram kamar bai ji abubuwan da Momyn take fada a kan Dadynsu ba. Hannayensa ya kama cikin wani yanayi yake girgiza shi "yaya shin kaima kana jin abinda take fada ko da kunnuwa ne suke gaya min karya?" Ganin yayan nasa bashi da niyyar yin magana yasa ya juya ya koma kan kanwarsa "Anisa, Anisa baby kina ganinsu ko? Ita tana fade-fade shi kuma ya yi shiru. Shin ba zasu yi min magana ba? Kanwata kema kin ji me Momy take fada ne?". Wani matsanancin kuka Anisa ta fashe da shi ta fada jikin Faisal ta rungume shi ta tabbatar a yanzu su ababen tausayi ne. Bakin ciki kuwa su duka sun daura aure da shi. Tsoro da fargaba sun hana shi iya motsa gabban jikinsa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Abinda ya shiga furtawa kenan a lokacin da ya fahimci al'amarin da'iman ne. Kansa ya yi masa nauyi, dakyar ya kai hannunsa ya dafe shi. Ganin zai sami matsala ya sanya Baffa saurin mikewa ya janyo shi jikinshi da shi da Anisa duka ya hada ya rungume su. A ransa yake kwatantawa shikenan sun shiga maraicin rashin uba. Cikin tattausan lafazi yake kara tabbatarwa kanin nasa maganganun mahaifiyarsu. Ya dora masa da wadanda ya ji kuma ya gani. Haka ita ma Momy ta tabbatar musu babu ko shakka halayyarsa ce domin ita ma ta ji da kunnenta yana waya kan zai tura yaran ga wani bature dan kasar rasha.


Dukkaninsu kuka suke suna jajantawa kansu. Tsananin tsana ta bakin cikin halin uban nasu ya cika zuciyoyinsu. Momy ce ta yi karfin halin tsayar da nata kukan ta soma rarrashin su.


Ta kuma umarce su da su yi hakuri su danne zukatansu su ga karshen gudun ruwansa. A yadda tace bata bukatar ko-wannensu ya nuna a fuska ko a bayyane cewa ya san wani abu game da shi. Tana bukatar karin lokacin da zai yi dai-dai domin tarfa shi. Cikin kunan rai ta karkare zancen da cewa "idan har Alhaji bai fuskanci hukunci kan laifinsa ba to nima ban can-canci in amsa sunan 'ya mace kuma uwa ba". Gaba daya yaran suka jinjina kai cikin jimami. Karfe tara da mintuna ya dawo Asibitin dauke da ledoji masu kunshe kayan marmari da drinks. Mamaki ne ya bayyana karara a fuskarsa na ganin yaransa biyu da suka bata sun dawo a lokaci daya.


Bai iya boye farin cikinsa na ganinsu ba duk kuwa da yana cikin damuwa. Haka ya zauna da yaran sama-sama domin hankalinsa ya riga ya kasu kashi-kashi. Kasancewar yau ta kama assabar, washe gari kuma lahadi, yayin da rana ta gaba zata kasance litinin kuma ranar da alkalin babbar kotu yake bukatar ganinsa a gabansa domin ya kare kansa bisa zargin da ake masa. A gefe daya kuma ga babbar barazanarsa Fadwa, wadda ta gagare shi, izuwa yanzu kuma bai san me take shirya mishi ba. Wannan ne yasa ga baki daya ya rasa nutsuwarsa domin kuwa shi mara gaskiya aka ce ko a ruwa gumi yake yi. A daddafe ya samu ya yi musu sallama ya bar Asibitin bisa bada uzurin cewa zai shiga wani zama na gaggawa da shugabannin kananan hukumomi.


*Mai tama*
Fadwa ce tare da Ab'ha a dakinsu na harhada bayanai da ajiye duk wani abu mai muhimmanci. Sun dukafa sosai ga aikin da suke yi na tattara bayanai da bidiyoyin da suka samu daga wajen 'yan matan nan na Alhaji Habib da ya tura kasashen duniya. Dukkaninsu suna cikin gagarumin farin ciki na samun nasa, wanda akalla sun san ko ba a sami wasu ba wadannan hujjojin kawai sun isa su daure Shugaba.


'Kirrrr...!' Wayar Ab'ha dake ajiye a gefen hannunsa ta dauki ringi, alamar wani yana son magana da shi. Ganin number bakuwa bai bashi mamaki ba kamar yadda ya ganta da alamar kari (+) wato dai number ta kasar waje ce. Shiru na dan lokaci kafin daga bisani ya daga wayar da sallama. Zumbur ya mike tare da dora hannunsa kan kirjinsa, saboda bugawar da ya ji yana yi. Fadwa ta zuba mishi ido kawai tana kallon shi. Shi kuwa muryar Hamidarsa daya ji cikin kuka tana ambaton sunansa yasa gaba daya ya rasa nutsuwarsa. "Ha'ab?!" Ya kira sunanta cike da son tabbatarwa. Ta amsa da sauri tana share hawaye kamar tana gabansa. "Abba ka yafe ni ka yi mini aikin gafara. Hakika na aikata kura-kurai da yawa a rayuwata, amma a cikinsu babu wanda ya kai kin ka da na yi. Na yarda kin masoyi babbar masifa ce, Ab'ha na tuba ka yafe min. Na san zaka yi mamakin ji na a wannan lokacin to ba yadda na iya ne. Alhaji Habib ya cuce ni. Ya maida ni baiwarsa mai bautar da rayuwarta a banza. Duk iya zaman da na yi da shi bai gani ba. A kan wani karamin kuskure da na aikata masa yasa ana farautar rayuwata. Ni yanzu ban damu da kaina ba, damuwata daya ita ce juya maka baya da na yi a lokacin da kake matukar kaunata. Na dauki alkawarin sai na tozarta rayuwarsa kanfin ya cimma nufinsa a kaina. Gobe zan shigo Najeriya, zan kuma zo da gagga-gaggan hujjojin da zasu daure shi iya rayuwarsa. Ka tare ni karfe bakwai dai-dai jirgin safe zan biyo". Duk wannan dogon zancen ta yi shi ne wani na bin wani. Sam bata bada wata dama ga Ab'ha ya yi magana ba har saida ta zo karshe.


Cikin sarkewar murya yake amsa mata da "Sikenan Allah ya kai mu goben". Dif! Ya katse wayar ya zauna kan kujerar da ya tashi a kanta. Idonsa a kan fadwa cike da murna yake sanar mata Ha'ab ta yi nadamar abinda take zata kuma dawo gida. Ya gaya mata duk abinda ta fada masa.


Fadwa ta jijjaga kai, tana nazarin maganar. Kafin ta kalle shi tace " Allah ya kai mu goben lfy". Iya abinda tace kenan ta ci gaba da aikinta.


Washe gari tun da ya yi salla zumudi bai bar shi ya koma kwanciya ba. Shi kansa a wasu lokutan yana mamakin irin yawan so da kaunar da yake yi wa Hameeda. Duk da ya san halin da take ciki dai-dai da rana daya bai taba jin sonta ya ragu a zuciyarsa ba. Yau yana cikin farin cikin da ya debi shekaru bai yi kwatankwacinsa ba. Duk rawar kan da yake yi Fadwa na lura da shi, amma bata tanka shi ba. Haka ya kammala shirinsa karfe bakwai saura kwata ya fita gidan ya nufi airport.


Karfe bakwai dai-dai jirgin Dubai mai dauke da fasijoji dari da sittin ya dira a babban filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Kano. A cikin jerin mutanen dake fitowa daga jirgin ya hango ta cikin shigar doguwar riga baka hade da mayafinta. Ta kara kyau ta murje, ta cika bul-bul da ita gwanin sha'awa. Ab'ha ji ya yi kamar ya ruga ya rungume masoyiya abar so da hangen ruhi da gangar jikinsa. Amma sai ya daure ya jira isowarta. Tana ganinsa ta fara sharar kwalla sannan ta saki jakar hannunta ta isa gareshi ta rungume shi tana ambaton sunansa cikin raunin murya.

Ab'ha kam kusan rasa ji da ganinsa ya yi a lokacin, saboda wani irin shauki na masoyan da a baya suka cire rai ga samun ababen son nasu. Dakyar ya iya raba jikinshi da nata yana dai-daita tsayuwa ya yi mata barka da isowa. Har zata tari taxi ya dakatar da ita yana sanar mata cewa ai da mota ya zo. Hakan yasa ta bi bayansa zuwa inda motar take a ajiye.

Tafiya mai dan tsayi ya yi kafin ya tamyeta game da abinda ya ji ta fada "me yasa kika zabi ki sauka a hotel madadin ki wuce gidan iyayenki kai tsaye?" Hameeda ta marai-raice fuska ta soma magana "ina so ne sai na fara tura wasu dattabai su rarrasar min su, ina so zuciyarsu ta yi sanyi kafin na tunkare su. Ka san suna fushi dani saboda dadewar da nake ban zo gida ba". Ya jinjina kai yana auna kalaman nata. A lokacin kuma sun fara shiga karamar hanyar da zata sada su da karamin hotel din da ta bukaci ya kai ta. Kasancewar lokacin lokaci ne na sanyi kuma da safe, yasa layin ya yi shiru baka ganin giftawar mutum ko wani abin hawa a kan kari. Shiru ya ratsa tsakanin masoyan biyu. Ab'ha ya dukufa kan tukin da yake, ita kuma tana duba jakarta kamar mai neman wani abu. Ta saka salati tare da dan fiddo ido alamar ta rasa wani abu. Da sauri ya taka birkin motar yana kallonta da kuma jiran jin abinda ta yar ko ta manto a can. Cikin wannan yanayin ne ya samu ta shammace shi ta rufe masa fuska da wani karamin kelle. Kafin ya yi wani yunkurin tuni ya rasa kuzari a gabban jikinsa, kafin daga bisani kuma numfashinsa ya tsaya ga fita a kai-a kai ya dawo daya bayan daya.


Hameeda ta saki wani shu'umin murmushi na samun nasara, sannan ta dauko wayarta ta fara laluben wata number ta danna kira. Ba jimawa wanda take kiran ya daga wayar kamar dama can ita yake jira. Ba ko sallama ta fara magana. "Da girman kujerarka, aikinka ya kammala. Yanzu ina kake so a kai shi?". Ban san me aka gaya mata ba, ta dai amsa da cewa "an gama". Kawai sai ta katse wayar.

Ta fita ta zagaya ta yi wa kanta mazauni a bangaren driver. Ta tashi motar tare da juyar da kanta ta cillata bisa babban titi...







Babbar magana. πŸ€”
Ku ci gaba da bibiya, zan ci gaba.



















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________








```Page 22```









Ab'ha yana sunkuye bisa kujerar motar kamar mai bacci. Yayin da Hameeda take ta sharara gudu bisa titin kasancewar babu yawan zirga-zirgar ababen hawa a kan titin. Tafiya mai nisa ta yi kafin ta fara fita garin Kano. A lokacin ta fara hango inda ta nufa da shi, wato tsohon gidan gonar Alhaji Habib Inuwa. Zuciyarta ta fal da farin cikin cika aikin uban gidanta. Wani mahaukacin birki ta taka lokaci daya ta rike motar iya karfinta tana mai kife fuskarta bisa sitiyarin motar a matukar tsorace. A zatonta motar zata kife ne. Hakan kuwa duk ya faru ne a dalilin ganin mutum da ta gani ya diro mata tsudum a tsakiyar hanya ta gabanta, ba tare da sanin ta ina ya fito ba. 'Kuuuuuuuu...' Kake ji karar birki da kokarin tsayar da motar da take tsaka da gudu lokaci daya. Wani irin ihu Hameeda ta saki ganin motar zata bi ta kan wannan bakon mutumin da ya dirar mata a kan hanya sanye da bakaken kaya fuska a rufe. Sai dai kafin ta kai karshe ga tunaninta ta ga ya bace bat! Kamar bai taba wanzuwa a gurin ba. Sannan kuma motar ta tsaya lokaci daya.

Hameeda ta shiga waige-waige tana ware ido, ajiyar zuciya take saukewa wata na bin wata. Cikin sauri-sairi ta fara yunkurin yi wa motar key hannunta na rawa. "Wai shin ina ne kike kokarin kai shi Ha'ab?". Ta juyo da kallonta zuwa sit din motar na baya inda ta ji sautin na fitowa a matukar tsorace.

"Na shiga ukuna waye kai?...". Ta fada tare da dafe kanta cikin tsantsan tashin hankali da rudewa, saboda ganin wannan mutumin da motar ta bi ta kansa zaune a kan kujerar motar ta baya. Tunda take bata taba jin kanta a yanayin tsoro kwatankwacin wanda take ciki a yau ba. Mai bakin kayan nan ya saka hannu ya yane hular roba dake rufe da ilahirin fuskarsa zuwa wuya. Ga mamakin Hameeda sai ta ga gashi ya zubo ya rufe fuskar mamallakin kayan. Tsoronta ya kara hau hawa zuciyarta ta shiga sake-sake, a yanzu kam ta tabbatar gamo ta yi da aljan. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Ta fada cikin matsancin razani tana neman balle motar ta fita. Cikin zafin nama mai bazajje gashin nan ya yunkura ya kife ta da mari. Ji kake tas.! Ta tsandara kara tare da dafe kuncin nata da ta ji kamar zai cire saboda zafi, idonta a kan wannan aljani kamar yadda ta dauka.


Mai bazajjen gashin ya saka hannu ya yaye gashin tare da watsa shi bayan kansa. Me zata gani? Fadwa ce tsohuwar class mate abokiyar gaba. " Fadwa?!". Ta kira sunan cike da mamaki kana ta shiga tunanin gaggawa. 'Anya ma Fadwa ce? To idan ita ce ta yaya take bacewa kamar aljana?' Fadwa ta bushe da mahaukaciyar dariyar nan tata. Kana ta dora da cewa "dama na sani, mugu bashi da sabo Hameeda. Yanzu ke rashin arzikin naki har ya kai ki ga iya cutar da Ab'ha? Shin kin manta waye Abba kuwa? Abba fa shi ne mahaukacin masoyin nan naki, Ab'ha shi ne wanda ya bar iyayensa da 'yan uwansa da kuma duk wani jin dadin rayuwa saboda ke. Kin yi kuskure Hameeda kin yi kuskure na cutar masoyi kamar wannan. Duk muguwar hallaya da mummunar dabi'arki bai taba daina sonki ba. Kullum fatansa shi ne ki shiryu ki dawo gida, ki zama ta gari ku ci gaba da soyayyar da kuka fara a baya. Tir dake, da kuma halayyarki Hameeda".


Hameeda ta sunkui da kanta kasa cikin tsananin jin kunya da nauyin kalaman na Fadwa. Hakika bata fadi karya ba ita kanta shaida ce, tafi kowa sanin irin son da Abba yake mata. Ita shaida ce game da hakan tunda ya shafe shekaru yana bin bayanta a kasashen duniya... Tunaninta ya katse ne lokacin da ta ji an buda kofar motar dai-dai inda take an fizgo ta waje. Naushi daya fadwa ta yi mata ta nisanta ta da shaka da kuma fitar da numgashi dai-dai. Ta sumar da ita, sannan ta watsa ta bayan motar ta rufe, ita kuma ta shiga mazaunin driver ta tayar da motar ta nufi gidanta da su.


A ranar da karfe bakwai da rabi na safiya aka sallami Hajiya Laurat daga asibiti saboda ta sami sauki. Haka suka dunguma ita da yaranta wadanda take ganin su kadai suka rage abinda ke faranta mata a duniya, suka koma gida. Zukatansu dunkule da sabon yanayin kunci da jimamin da ya zame musu abokin rayuwa a 'yan kwanakin. Gidan ma sai ya zame musu wani fanko kamar ba asalin gidansu ba, sai suke kallon komai dake gidan kamar haramtacce ne a garesu. Haka kawai suka tsani gidan da komai dake cikinsa, sun tabbata duk wani jin dadi da suka yi an gina shi ne haramun. Mummunan haram na sayar da mutuncin 'yayan mutane.


Alhaji Habib kuwa yana can ya kebance kansa a daki yana jiran kiran Hameeda, domin ta sanar masa ta kai Ab'ha inda ya bukata. Manufarsa a kan hakan kuwa shi ne ya san in dai Ab'ha yana hannunsa to zai san duk wani shiri da Fadwa take yi a kansa, sannan ya wargaza shi. Zai kuma san sirrinta da inda take rayuwarta wanda hatta jami'an tsaro duka suka gagara sani. Ya tabbata idan ya sami duka wadannan zai iya batar da ita, ya shafe tarihinta da duk wasu muradai nata na nemawa mata 'yanci bisa kasuwancin da yake da yi su.


Yana cikin wannan dakon ya jiyo kiran ya shigo wayarsa da number tata. Cikin azama da ya daga wayar yana fadin "kin jinkirta da yawa Hameeda, ina nan ina ta zullumi". "Ka ci gaba da zullumin Shugaba, domin ko har yau baka fita a cikinsa ba". Fadwa ta gayar masa a zafafe ta cikin wayar. Alhaji Habib ya zabura kamar tsinke aka saka aka zungure shi. Ya kalli wayar, ya kuma kalli number. Babu shakka number Hameeda ce, amma muryar kam ya fi kowa sanin mamallakiyarta. "Fadwa?!". Ya fada a lokacin da gabansa yake dukan uku-uku, kansa na fitar da gumi. Ya tabbata ya rasa komai, ya rasa Hameeda ya rasa na hannun damanta Abba. Anya wannan mutum ce? Ta yaya ta gano shirinsu? Ya ma aka yi ta kama Hameeda bayan ta tabbatar masa ta kama gayen...?'



















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login