Showing 33001 words to 36000 words out of 37846 words

Chapter 12 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt

25 Oct 2025

370

ina ma ace mafarki yake yi? Da kuwa ya mallakawa duk wanda ya tashe shi abinda yake da shi a duniyar nan. Wannan wace irin bakar rana ce ta zo mishi? Ta yaya hakan zata faru da shi farat daya?' Yana cikin wadannan nazarce nazarcen ya fara jin sautin ihun mutanen dake wajen kotun suna jefo shi da munanan kalamai marasa dadin ji. Tamkar an yagi fatar kirjinsa an murza masa gishiri, haka ya ji wani irin zafi da radadi sun ziyarci zuciyarsa. Ya rumtse idonsa da karfi yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Habib na cuci kauna". Ya fada lokacin da yake dafe kansa da hannayensa guda biyu cikin matsananciyar Dana sani.


A cikin kotun ma hayaniyar ce ta kaure mutane suka mimmike tsaye suna la'antarsa suna nunashu da hannu kamar zasu rufe shi da duka, a cikinsu hadda manyan abokanansa 'yan siyasa da sanannun 'yan kasuwa. A kokarinsu na ganin sun wanke kansu kar a zarge su kan wannan mummunan laifin nashi da basu ma san yana aikatawa ba.

Lokaci mai tsayi aka dauka a hakan, yayin da jami'an tsaro suka dawo kokarin kare Shugaba daga fushin 'yan kallon shari'ar dake cikin kotun. Dakyar alkalin ya samu nasarar tsawatarwa game da hayaniya da rudanin. Alhaji Habib kuwa ya yi tsuru tsuru a gaban jama'ar da a da suke daukarsa a matsayin jigonsu kuma uba, jagira ga ragamar rayuwarsu. Alkalin ya yi gayaran murya, sannan ya maida kallonsa ga lauyoyin Alhaji Habib yace "ko a cikin ku da akwai wani mai ja game da wannan shaida da ta gabata?". Dukkansu suka yi kasa da kansu cike da jin kunyar kasancewarsu masu kariya a gareshi. Suka ce "babu". Alkali Musa ya kalli Fadwa dake tsaye yace "zaki iya ci gaba da gabatar da shaidannunki yarinya". Ta yi godiya ga kotun sannan ta dora da kiran sunayen 'yan matan nan. Wadanda dukansu babu boyayya a cikinsu. Manya ne kuma sanannun karuwai, wadanda mafi yawan mutane suka sani a cikin garin Kano. Daya bayan daya suka gabatar da kansu da ayyukansu, da kuma alakar dake tsakaninsu da Alhaji Habib. A karshe suka rufe da bada gamsassun hujjojinsu masu bada tabbacin abinda suka fada din. Na faro hotuna ne da video wadanda suka yi dauka a sace idan suka hadu da shi Alhaji Habib din. Kamar yadda suka saba. Wato zaman kasafi na kudi da suke yi da shi, inda yake fidda musu nasu ihisani kan ko wace fita da suka yi a karshen wata.

Sai voice record da suka dauka na umarnin da yake basu na suje nan, su je can a kan waya. Da kuma wadanda suke dauka na turawan nan da ake turasu wajensu. A karshe ta rufe da cewa "ya mai girma mai shari'a wadannan sune tsayayyun hujjojin da nake da su game da wannan mutumin. Ina kuma rokon kotu da ta taimaka ta duba hujjojina da kuma shaidannun da na gabatar, da kuma halin da mai laifi ya nuna karara a bainar jama'a. A taimaka a yanke masa hukunci daidai da laifinsa". Ta gama tana mai hada hannayenta waje daya tana rokonsa, hawaye na bin kuncinta. Alkalin ya sadda kai kasa yana 'yan rubuce rubuce. Yayin da kotu ta kaure da wata hayaniyar ta 'yan kallo ciki da waje. Alhaji Habib kam kansa ya gagara dagowa, ba zai iya kallon jama'a da wannan zunubin ba. Ya sunkuyar da shi kasa yana zubda hawayen nadama. A daidai lokacin ne kuma Hajiya Laurat da yaranta suka kunno kai cikin kotun. Wata sabuwar haniyar ce ta koma kaurewa ana fadin "ga yaransa nan, ga su nan yace bai san inda suke ba". Hajiya Laurat ta tsaya tangaram a gaban kotun tana karewa mijin nata kallo cikin cunci da kunan rai. Yaransa kuwa gaba dayansu kuka suke suna sharar kwalla.

Mai shari'a Musa ya tsawatar ga masu tace nacen dan ci gaba da shari'a. " ke kuwa wace cs ke, kuma mene ne alakarki da wannan case din?". Hajiya Laurat ta share hawayen da suka kasa yankewa daga idonta ta amsa. "Sunana Hajiya Laurat kuma ni matarsa ce. Wadannan dake tare da ni kuma duka yaransa ne". Alkalin ya kalleta shekeke sannan yace "to meke tafe dake ne, ko kina da wata hujja da zata wanke mijin naki daga zargin da ake masa?".

Hannayenta na rike da wajen tsayuwar ta sauke idanunuta bisa gare shi, tare da nannauyar ajiyar zuciya. Tana mai kara jin tsantsar tsana da kyamar halinsa tace "na zo nan dan in kara tabbatarwa kotu da abinda ta ji a bakin wannan baiwar Allah. Ta fada tana nuna Fadwa. Babu ko shakka mijina munafikin mutum ne wanda ya dade yana cutar al'uma da fuska biyu. Ni nan shaida ce game da hakan. A karshe ina rokon kotu da ta yaimaka yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Domin 'yaya mata su sami salama da nutsuwar rayuwasu. da haka ne kadai zamu iya yakar ta'addanci da wannana safarar yaranmu mata a wannan kasar. Ganin an hukunta wannan mugun bawan ne kadai zai sanya salama ga rayuwata, domin kuwa shi ne sila kuma dalilin lalata rayuwar 'yata". Ta kai karshen maganar hade da kuka mai ban tausayi.


Alhaji Habib kuwa ido ya zubawa Hajiya Laurat cikin tsananin mamaki da ya shafe duk abinda ke ransa. Yaushe ta san yana safarar mata, kuma me ta sani game da hakan nan?". Kamar ta san abinda ke ransa ta zayyane masa komai a bainar jama'ar. Tsananin kunya da dana sani sun dada lullube shi. Nadama mara amfani ta baibaye rayuwarsa. Kansa a sunkuye ya amsa tambayar alkali Musa da ya yi masa kan cewa "ya yarda ya aikata wadannan laifuffukan da ake zargin sa da su?". "Eh". Ita ce amsar da ya bayar cikin rishin kuka. Allahu Akbar! Fadwa ta fada lokacin da take dora kanta bisa tsayayyen katakon dake zagaye da ita a inda take tsaye. Godiyar Allah take a zuciyarta inda ta kara tabbatarwa kanta cewa komai na duniyar nan yana da karshe. Ta yarda ikon Allah ne kadai zai dore koma ya dauwama. Tun da take gwa-gwarmaya bata taba kawo wa a ranta zata samu irin wannan gagarumar nasarar a nan kusa ba. Yau gashi Allah ya kawo karshen zalumcin Alhaji Habib. A gaban dubannin jama'a kuma da bakinsa ya amsa laifinsa.


Wasu siaran hawaye ta ji suna bin kuncinta ba tare da ta ji fitowarsu daga idonta ba. Ta dago kai tana kallon jama'ar dake cikin kotun wadanda ga baki dayansu suka yi sanyi lakwas kamar wadanda aka zarewa laka. Kotun ya yi shiru, baka jin komai sai kukan Alhaji Habib da na yaransa. Yayin da alkalin ke aikin rubutu bisa farar takardar dake gabansa...



















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________








```Page 28 second to the test page```













Ya jima yana rubutun kafin ya kammala ya dago ya fuskanci al'umar dake wajen ya fara magana. "Alhmdulillah, da wadannan shaidannu da kuma amsa laifi ga masu shi muka zo karshen wannan shari'ar. Duba ga yadda mai laifin ya amsa laifinsa ba tare da wahalar da shari'a ba, kotu ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na tsayin shekaru ashirin da biyar, tare da horo mai tsanani. Da kuma tarar kudi Naira miliyan dari uku da dubu dari shida a matsayin diyya ga wadanda ya zalumta". Ko da jama'a suka ji haka sai suka cika da farin ciki suka kaure da ihun murna suna tafi, yayin da wasunsu ke daga murya suna fadin "daidai kenan". Wasu kuwa cewa suke "da ma kashe shi aka yi". Alhaji Habib ya fashe da wani irin kuka mai tsananin kafin ya gurfane a wajen, hannunsa dafe da zuciyarsa, saboda irin masifaffen ciwon da yake ji a cikinta. Yaransa kuwa sai suka kara tsananta kukansu, duk kuwa da yadda suke jin tsanarsa a zukatansu. Domin dai sun riga sun san har gaban abada yana nan a matsayin mahaifinsu duk kuwa irin ta'asar da ya shuka. Hatta hajiya Laurat sai da ta zubda hawayen tausayinsa duk yadda zuciyarta ta bushe. Da kyar alkali Musa ya iya tsayar da hayaniyar mutanen nan sannan ya dora da fadin "su kuma wadancan biyun da suka amsa laifinsu na aikata ta'addanci har ma da kisan jami'in tsaro. Kotu ta yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, tare da umartar jami'an tsaro da su gaggauta kamo ragowarsu a gurfanar da su gaban shari'a. Domin su ma su karbi hukunci. Sai magana ta karshe game da ita wannan 'yar gwa-gwarmayar Fadwa. Kotu ta wanke ta bisa zargin da aka dade ana yi mata na batawa wannan mutumin suna. Haka kuma kotu na umartar hukumar kare hakkin mata da kananun yara ta jiha da ma ta kasa baki daya da su karrama wannan yarinyar da ta yi aikin da ya kamata a ce su ne suka yi shi. Sannan daga karshe su yi koyi da ita wajen gudanar da ayukkkansu. Allah ya kara daukaka duk wani mai son taimakon al'uma".


Ya dasa aya tare da buga gudumarsa bisa teburin dake gabansa alamar kotu ta tashi. Gaba daya jama'ar suka mike tsaye saboda girmamawa. Sannan ne kuma alkalin ya fice ta karamar kofar da ya shigo, wato kofar ofishinsa. Jama'a suka fara bi gefen Alhaji Habib dake zagaye da jami'an tsaro suna wucewa tare da jefa masa munanan kalamai kamar su
"ka dai ji kunya Alhaji".
"Alhmdulillahi an yi walkiya mun ganka, Allah ya ci gaba da tonawa ire irenka asiri".
"Allah ya isa bamu yafe maka ba azzalumi".
"Mugu bakin kumarci".
"Allah ya kara bayyana mana duk mai irin halinka".


Kowa da abinda yake fada. Haka jama'ar dake cikin kotun suka yi ta fadar albarkacin bakinsu game da shi. Yana nan sunkuye a inda ya gurfana kan guiwoyinsa baya ko motsi. Jami'an tsaron dake tsaye a kansa kuwa ganin zai bata musu lokaci yasa suka kai masa cafka da nufin su mikar da shi tsaye su fita da shi. Luuu... Suka ga ya tafi tim! Ya kife kasa. Sakamokon tabinsa da suka yi.

Da sauri suka dago shi suna girgiza shi. Yayin da Baffa da kannensa ma suka yo kansa cikin kaduwa da tashin hankali. Hajiya Laurat na tsaye a inda take duk tsoro ya baibayeta.


"Shikenan ma jama'a sun huta da turaddadi da kuma saka ran zaka fito ka koma addabarsu". Cewar wani dan sanda da yake mikewa tsaye bayan ya dafa kirjin Alhajin ya ji shiru. Cikin rashin fahimta Faisal ya cakumo rigarsa yana fadin "me kake nufi?". "Sai hakuri, mahaifinku ya riga da ya mutu. Ba mamaki zuciyarsa ce ta buga". Sai a lokacin Hajiya Laurat ta iya motsawa daga inda take. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Alhaji ya mutu?". Ta tambaya tana dago kansa dake kasa kamar mai shinshinar kasa. Gaba daya jikinsa ya saki, babu alamar rai a tattare da shi. Su duka suka dafe kai suka fara runtuma kuka, daidai lokacin da 'yan jaridun dake waje suka fara kunno kai cikin kotun dan tabbatar da abinda suke gani a waje. Nan fa suka shiga daukar hotunansa da kokarin yin magana da iyalan nasa. Abinda basu samu ba kenan. Domin hankalinsu ya kai kololuwar tashi.


Da taimakon 'yan sandan suka kai shi mota dakyar da tura mutane saboda cinkoso dake wajen. Duk wanda ke wajen burinsa ya ga gawar ido da ido. Ko wace gawa ana raka ta da adduo'in neman rahamar Allah, banda ta Alhaji Habib. Dandazon tarin talakawan dake wajen jifarsa suka hau yi da munanan adduo'i suka bi motar da ta dauke shi.


Duk abinda ake Fadwa da Abba suna gefe suna kallonsu.

Allah Akbar! Illa da kuma matsalar zalumci kenan. Duk yadda ya karbe ka, ka ji dadinsa wata rana karshenka zai zo. Komin girma da tarin alfarmarka Allah ba zai barka da su ba. Karshen ba zata taba yi maka kyau ba. (Ya Allah ka kare mu daga kusanci da zalumci, kar mu yi kuma kar ka bari a yi mana. Amin)


Fadwa ta matse guntun kwallar dake idonta, tana shirin juyawa ta ci karo da zungureriyar lasifika a gabanta. Kyakkyawar budurwar dake rike da lasifikar ta fara magana "barka dai Auntynmu 'yar gwa-gwarmaya. Ina taya ki murnar wannan nasarar da kika samu". Ta yi murmushi sannan ta amsa mata da "na gode". 'Yar jaridar ta dora "in ba zaki damuba ina da 'yan tambayoyi ne a gareki". Ta gyada mata kai "ina jinki". "Duba ga yadda kika sami wannan nasarar a cikin wannan abin da kika kira da gwa-gwarmaya, shin yanzu kuma mene ne burinki na gaba?".


Sai da ta yi murmushi kafin tace "to alhmdulillah a gaskiya yanzu bani da wani buri da ya wuce in kirkiri wata hanya da zata rika samarwa irin matan nan da matsala ke rabasu da gidajensu kudin biyan bukatunsu. Ina nufin in samar da wata cibiya ta musamman da zata zamo gata ga duk wata macen da take cikin hatsarin karuwanci. Cibiyar da zata fara kafuwa daga gobe. Ina so in yi amfani da wannan damar in isar da wannan sakon ga al'umar jihata. Ta dan yi jim kamar mai wani tunani kafin tace "na yi rayuwar bariki ta dole, na kuma zauna da wadanda suka yi ta son ransu. Na gani na kuma san yadda karuwanci yake. Na tabbata babu wadda take yinsa don dadinsa, sai dai kawai su yi shi don neman abin biyan bukatunsu na dole. A saboda haka kafin in kai ga ganin karshen fitowar mata daga gidajensu yawon duniya sai na fara da samawa wadanda suka fiton mafita da madafa. Na gama yanke hukunci daga gobe kuma zan fara zartarwa. *Fitilar 'yancin mata* sunan karamin kamfanin kuma masarrafin abubuwa masu yawa. Wannan kamfanin shi ne zai zama gata ga ko wace macen da ta rasa gata a jihar Kano. Nice jagorar wannan tafiya. Ma'aikatan kamfanin kuma zasu kasance wadannan matan marasa mafaka da makoma. Wadanda dukkaninsu sun riga sun tuba ga abinda suke yi sun mika wuya gareni sun canja rayuwa. Adireshin kamfanin yana nan unguwar mai tama babban layi. Wannan ita ce lambar da duk wacce ta hadu da wannan kaddarar zata neme ni". Ta karkare tana nuna lambar waya ga 'yar jaridar".


Tana gama maganar ta juya ta nufi gun da motocinsu suke, inda Abba da sauran 'yan matan nan suke jiran ta. A cikinsu kuwa hadda Hameeda. Wadda ta gama saduda har ga Allah ta mika wuya ga Fadwa. Abba kuwa kansa na gefe ya tamke fuska ko kalloninda take baya son yi.



Murmushi kawai ta yi ta shiga motar tana maidawa jama'ar dake faman daga mata hannu martani. Suka tashi motocin duka uku suka fice daga harabar kotun cikin tsananin farin ciki.
















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

_*WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£*_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________










```Page 29 last page``` πŸ‘









Da isarsu gida suka fara shirye shirye a matsakaicin wajen nasu da take kokarin mayarwa kamfanin dogaro da kai ga matan hanya. Farin ciki a ranar kam ba a magana. Hameeda ta zama daban a cikinsu domin kuwa su 'yan matan nan tuni sun riga da sun saba da su. Ita kadai ce take jin kanta bakuwa.

To dama dai haka rayuwa take aka ce lokacin murnar wasu lokacin kukan wasu. Hakan ce ta kasance a gidan Alhaji Habib Inuwa. Abin duniya ya taru ya yi musu yawa. Shi kuwa Alhaji ya riga ya tafi tafiyar da bata da waige balle dawowa. Bakin cikin iyalansa bai fi mummunan tambarin da ya tafi ya bar musu ba. Domin kuwa duk yadda suka so ko suka ki, shi Uba ne kuma jigo ga rayuwarsu har abada ba za'a taba goge shi a cikin tarihinsu ba.

Abin kunya mutane uku ne kacal suka yi jana'izarsa daga limamin gidansu sai 'yayansa biyu Faisal da Baffa. Gidan nasu ma ba dan ana jin kunya da tausayin yaran nasa ba da tuni an ruguza shi. Mutane ko ta ina tofin ala tsine suke ga mamacin. Fadwa kuwa cewa suke Allah ya kara kawo dubunta, Allah ya shi mata albarka, ya taimake ta kan dukkanin al'amuranta.


Bayan makonni uku dukiya da kadarori wadanda basu taba sanin ya mallaka ba ake ta kawo musu daga kasashe dabamdaban, a matsayin na shi da ake juya masa a can. Ga wadanda yake da su a nan manyan kamfanoni biyu da gidajen man da ba zasu kirgu ba. Haka suka yi ya tara dukiyar da suke ganin ba su ba har 'yayan da zasu haifa sai 'yayansu sun ci ta. Hajiya Laurat da har cewa ta yi ba zasu ci kudin ba, amma da ta nemi fatawa gun wani malami sai yace a matsayinsu na magada wadannan kudin halal ne a gare su. Wanda ya neme su ta mummunar hanya shi suke haramun a wajensa. Tunda suka ji haka suka fara kamfata daga cikin kudin suna gina masallatai da makarantu. Inda ake wahalar ruwa kuma su gina murtsatse. Cikin dan kankanin lokaci suka wanke bakin fentin da ya shafa musu da alkhairansu. Birni da kauye yabonsu ake kai ka ce wasu sanannun 'yan siyasa ne. Duk wannan abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login