Showing 6001 words to 9000 words out of 37846 words
Chapter 3 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt
boye miki ba 'yata, bana ji wannan ciwon zai bar ni. Saboda haka na baki dukkanin goyon bayana. Ina goyon bayan manufarki, na kuma baki dama ki fara gwa-gwarmaya. Ki tunkari duk wani azzalumi ki toni asirinsa. Kar ki barsu, kar ki sassauta musu. Rike wannan..." Ta karashe maganar tana damka mata wata karamar laya a hannunta na dama. Tace "wannan layar ta bata ce. Gudummawa ta farko da zan baki, saboda na san wadan-nan maha'intan zasu fara farautar rayuwarki. A duk lokacin da kika matsu, aka rutsa ki. Sai ki matsa ta da bismillah. Da iznin Allah zaki bacewa ganinsu, zaki bayyana a duk inda kika yi ra'ayi. Sannan abu na gaba da zan gaya miki shi ne, ki tsarkake kanki da zuciyarki, ki yi watsi darayuwar da kika yi a England ki buda wata sabuwa a nan. Ki zama mai yawan ibada da kaiwa Allah kukanki. Ki dage da bincike a kan abinda kika sa gaba. Ina kaunarki Fadwa. Ina jinki kamar 'yar da na haifa a cikina.
Na gama magana da shugaban gidan nan, duk wasu kudade da na shafe shekaru ina tarawa, na aiki da ma na gudumawa da ake bamu, na mallaka miki su. Ki yi amfani da su wajen tafiyar da aikinki. Ina da wani karamin gida a mai-tama na san kin gane gidan da nake nufi. Shima na mallaka miki shi. Domin ya zama dole ki bar gidan nan, ki nisanta kanki da wadanda suka san ki.
Kar ki yarda da kowa sai kanki. Kar kuma ki nemi taimakon kowa sai na Allah. Ke ta daban ce, ni na rene ki. Na sani zuciyarki ta musamman ce. Zaki iya duk abinda kika sa a gaba. Ina miki fatan alkhairi 'yata. Zan zama mai alfahari da ke, idan kika zama *fitilar 'yan-cin mata.* Fadwa ta rungume Ummy cikin tsananin murna da farin cikin goyon bayan da ta samu daga gareta. Ta fara kwarara mata godiya da kyawawan adduo'i. Haka suka kasance har zuwa asuba. Inda ta tashi ta shiga bayi ta dauro alwala, ta fito ta tashi salla bayan da ta lura cewa Ummynta ta samu yin bacci.
Ta dade da kammala salla da adduo'inta, amma Ummy ko motsawa bata yi ba. Tunaninta ya bata ramakon bacci take yi, tun da jiya duk basu yi baccin ba. Karfe bakwai dai-dai ta yanke shawarar tashin ta dan ta yi salla a yadda take lallabawa tana yi kullum. Amma inaa. Abinda bata sani ba shi ne Ummynta ta dade da amsa kiran buwayi. Ta tafi inda ba a tafiya a dawo. Tayi bacci ne irin wanda ba a farkawa a doron kasa.
Allahu Akbar! Fadwa ta da'da shiga kunci, ta yi kuka kamar ranta zai fita. A karshe aka kai Ummy Amina gidanta na gaskiya. A lokacin ne Fadwa ta san maraici, a lokacin ta san zafin rabuwa da iyaye. Bayan lokaci mai tsayi ta aiwatar da duk abubuwan da Ummy ta bar mata wasiyyar ta yi. Ta karbi makudan kudaden ta loda su a account dinta. Ta hada su da nata. Sannan ta tattare ta bar gidan marayu ba tare da sanin kowa a gidan ba.
Kamar yadda Ummy ta bukata bata yarda ta sanarwa kowa shirinta ba. Kawai dai an wayi gari aka ga babu ita a gidan.
Hukumar gidan da marayun da suke gidan har zanga-zanga suka yi, saboda batan dabon da Fadwa ta yi. A tunaninsu Shugaba ne ya tura aka sace ta.
Ganin haka yasa ta aika musu wasika a rubuce, cewa su kwantar da hankalinsu bata hannun kowa. Kuma a inda take tana cikin koshin lafiya.
Daga wannan lokacin ne ta fara binciken sirri, da bibiyar duk wasu ayukka da Shugaba Habib yake aiwatarwa. Daga lokacin ta daura damarar *gwa-gwarmaya* da yakar azzaluman mutane irinsa a cikin kasarta.
Zuwa lokacin kuma al'amarin shugaban ya kara habaka. Ya ma daina dibar dalibai da 'ya yan talakawa, ya koma kan karuwan gari. Irin wadan-da suke samun matsalar Auren dole da iyayensu, su baro gidajensu. Da masu haduwa da kaddarar cikin banza, iyayen su kore su. Kasancewar zuwa lokacin sun yawaita sun cika ko-ina. Suna neman mafaka da abinda zasu ci su biya bukatunsu. Sai ya zamana aikin ya daina bashi wahala. Yarje-jeniya yake kullawa da su yana kai su kasashe suna karuwanci. Idan aka dawo sai ya basu dan ihsani a cikin abinda ya samu da su din.
A haka yake kara bude musu idon. An fara hawa jirgi ana harka da turawa. Sai suke jin kansu kamar wasu hamshakai.
Hakan yasa ya tara karuwai yarurruka dabam-daban. Ya rarraba su a wasu gidajensa na sirri. Sai dai wannan duk a cikin sirri ne. Amma ita Fadwa duka ta san komai game da shi.
Wannan shi ne tarihin rayuwar *'Yar gwa-gwarmaya Fadwa* da musabbabin 'yar tsamar dake tsakaninta da shugaba Habib. Mutumin da al'uma suke wa kallon Uba, adali, mai so da tausayin talakawa. Hakan yasa duk garin suka tsani *'yar gwa-gwarmaya* a ganinsu abinda aka fada game da ita gaskiya ne. Wato wasu'yan siyasa ne suke amfani da ita wajen ganin sun shafa masa bakin fenti. Lokacin da ayyukanta suka fara bayyana kuma, sai suka dawo yi mata kallon 'yar ta'adda.
*Ci gaban labari...*
Washe gari da safe Fadwa ta koma daura damarar shiga gari neman wata damar.
Kamar yanda a can ma Chaka (dan ta'addan Shugaba) da yaransa suka shirya tsab dan nemanta bisa umarnin Shugaba. A cikin garin Kano.
Haka bangaren Asp Sauwam ma ya tashi da tsare-tsaren gudanar da bincike na musamman a cikin garin dan nemanta. Tun da ya samu tabbacin tana garin.
Hotel din nan na sharaton ta kuma komawa, saboda hasashenta ya bata Suhaima kwana zata yi a can. A bangaren cin abinci ta tsaya, inda ta yo odar abin karyawa ta fara ci. Hankalinta na kan mashigar wurin, kasancewar wajen gilas. Daga inda take zaune tana iya ganin duk wanda zai shiga ko zai fita harabar hotel din.
Wasa-wasa har karfe sha biyun rana ba labarin ta. Sai ta fara tunanin ko dai tun jiya ta bar hotel din ne? Da wannan tunanin ta mike ta biya kudin abincin da ta ci, sannan ta kama hanyar ficewa. Ranta ya sosu, sam bata ji dadin rashi ganin Suhaima ba. Domin shirinta na yanzu duk a kan karuwansa ne. Tafe take tana sake-sake a ranta.
Karaf! Ta ji ta yi karo da mutum wanda bata ma san daga ina yake zuwa ba...
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
```Wannan shafin tukuici ne ga babbar masoyiyar wannan labarin na``` *'yar gwa-gwarmaya* ```na gode sosai``` *Ikram* ```sakonni da yawan comment dinki sun nuna karara irin so da kikewa labarin. Ba ke kadai bace Iki, nima ina yinki sosai. Ina son mai sona. Allah dai ya bar so da kauna.```
```page 7```
Babu tsoro ko alamarshi a tattare da ita, ta dago. Sabanin wanda ta yi karon da shi. Alamu sun nuna ya tsorata matuka. Suka kafe juna da ido kowannen su na kokarin tuna inda ya san daya.
Ita ce ta fara tunawa, cikin abinda bai fi sakanni ba ta tuno da Ab'ha, (Abba kenan.) Mahaukacin masoyin class mate dinta Hamida a makarantar sakandiren government collage da suka gama. Duk da ya kara darjewa ya zama cikakken saurayi.
"Abba kai ne?". Ta tambaya tana nuna shi da yatsa. Ya gyada mata kai kawai ba dan ya gano wace ce ita ba. Sai kuma ya tuna da abinda yake tattalin da suka zube yayin karon da suka yi. Da sauri ya rankwafa ya fara tattare takardu da wasu hotuna da suka fadi a hannunsa.
Hakan yasa ita ma hankalinta ya koma kansu. Sai dai kafin ganinta ya sauka garesu ya riga ya gama tattarewa, daya kawai ta gani wanda ya dauko a karshe kafin ya saka a file. Ta girgiza, ta kuma cika da mamakin ganin hoton tsohuwar budurwarsa Hamida daga ita sai pant da bra, tare da wani ba'amurke dake sanye da gajeren wando a bakin ruwa. Ta tabbata ba a dade da daukar wannan hoton ba. Ta kuma kallonsa da mamaki tace "Abba har yanzu baka rabu da Hamida ba?" Wanda ta yiwa tambayar ya kuma zare ido. Duk da alamu sun nuna ya tsorata da tambayar sai dai karfin soyayyarsa ga budurwar tasa babba ne.
Ya kalle ta cikin ido yace "in dai ni zaki kira to ki hada sunana da nata. Kamar yadda yake tun farko, ki kirani Ab'ha, bani da sunan da ya wuce shi. Rabuwa da Ha'ab kuma sai dai bayan rai. Na rantse ko zan mutu sai na rabota da wannan kasar da kuma wannan rayuwar. Ba zan daina sonta ba. Still ina sonta a haka".
Yana gama fadin haka ya figi jiki ya yi gaba, kamar a fusace. Da sauri Fadwa ta sha gabansa "Ab'ha wai baka gane ni bane?" Ya kuma kallonta irin kallon da ya mata dazu. Tabbas yana ji ya san fuskar amma gogewarta ta hana shi gano ta farat daya. Ta mari kuncinsa da wasa tace "kai mahaukaci Fadwa ce fa. Class mate din Ha'ab dinka a Government collage".
Ab'ha ya saki dukkan fara'arsa yace "Fadwa?! Dama kina raye?". Bata tsaya bashi amsa ba ta kama hannunsa, ta ja zuwa hanyar fita hotel din, domin ta tabbata abinda yake bibiya nada alaka da bincikenta. Yana da muhimmanci gareta da bincikenta a yanzu. A karamin nazarinta ta lura har yanzu yana bibiyar tsohuwar budurwarsa. Wadda aka fitar da su tare zuwa kasar England. Tabbas zai mata amfan...
Tirjewar da ta ji Ab'ha ya yi ne ta katse mata tunani. Ta kalleshi da mamaki "ya dai?". "Ba zan fita wajen nan yanzu ba Fadwa. Bibiyata ake. Yanzun ma gudowa na yi daga harin wasu 'yan ta'adda". Kafin tace wani abu sai ganinsu suka yi a gabansu.
Wasu tsagerun 'yan ta'adda ne kusan su bakwai. Hannayensu rike da adduna. Ab'ha ya juya da zummar guduwa, Fadwa ta kara damke hannunshi dake cikin nata. Idonta cikin a kan masu bibiyarsa. Hakika ta shaide su, kamar yadda su ma suka shaide ta.
Yaran Shugaba ne. Ta san su farin sani, domin sun sha kai mata farmaki bisa umarnins... Kafin ta kai karshe ga tunaninta babbansu ya karaso wajen cike da izza. A lokacin kuma suka fara magana "kai Oga. Ka ga wata sa'a, wlh ga Fadwa nan Yar gwa-gwarmayar nan". Jin hakan yasa Chaka ya fito da karamar bindigarsa, tare da saita ta da ita. Yau kin gamu da ajalinki Fadwa, kwanankinki sun kare abin farauta'ta".
Gaba daya suka saka dariya, kafin ta katse su cikin daga murya.
"Karya kake banza kare, ko da Fadwa zata mutu to ba dai a hannun karnuka irin ku ba". Kafin dukansu su yi wani yunkurin sai suka ji wucewar harsashi da karfi ta kansu. Ya wuce ya daki gilashin kofar shiga sashe na biyu na Hotel din. Asp Sauwan ne da tawagarsa.
A take yaran Chaka ma suka fiddo nasu bindigogin, suka fara maidawa jami'an tsaron martani. Suna kokarin ficewa daga wajen. Sai ko aka shiga musayar wuta.
Ganin haka yasa Fadwa jan hannun Ab'ha suka kauce a gurin.
Cikin sauki suka fice daga Hotel din. Suka bar su nan suna aikawa junansu harsa-sai.
Zan ci gaba...
*Nasmat*
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
*Slm masoya, ma biya labarin 'yar gwa-gwarmaya. Hakika shafina na yau zai kasance na musamman domin zan sadaukar da shi ne ga wata ta musamman. FATIMA USMAN kanwata. Ina alfahari dake da kuma kwazonki. Fatana shi ne Allah ya kara haskaka min haska-kakkiyar kwakwalwarki amin. Ana matukar tare. π€*
```page 8```
Lokaci mai tsayi suka dauka suna musayar wutar, kafin daga bisani 'yan ta'addar su sami nasarar bindige police daya. Su kuma 'yan sandan suka kashe musu mutum biyu suka kama wasu biyun. Hudunsu kuma suka sha dakyar.
Bayan Fadwa da Ab'ha sun fita wajen, bata nufi gidanta da shi ba. Wani Hotel din ta samu suka shiga. Ab'ha wanda gaba daya hankalinsa yake a tashe ya kalleta bayan sun zauna yace "wai dama ke ce 'yar gwa-gwarmayar da nake jin labarinta?." Ta sakar masa murmushin nan nata tace "ni ce." A takaice. Tana kurba lemun da suka saya. Mamakinsa ya kara bayyana yace "kaina yana cikin duhu dan Allah ki bani labarin rayuwarki. Kin san bana kasar ina can ina bibiyar ruhina a kasashen duniya."
Ta yi murmushi mai bayyana sigar tausayawa ga wanda aka yi wa shi. Tace "Abba kana bani tausayi sosai. Hakika so ya yi maka mugun dabaibayi. Yayin da kaddara ta yi wa rayuwarka karan tsaye. Na tabbata ba zaka iya barin ta ba. Amma ta yaya kake ganin zaka iya samunta a wannan rayuwar?".
Ya sauke numfashi kansa yana sunkuye a kasa. Hakika yana cikin damuwa da manyan hadarurruka game da wannan burin, amma giyar so sam, bata nuna mishi zai rasa. A kullum zai samu cikar buri yake gani. Bayan gajeren nazarin maganganunta ya dago kansa cikin sanyin jiki yace "bani da zabi Fadwa. Kaddarata kenan. Ba sai na gaya miki ba, abu ne da kika dade da sani. Son Ha'ab a cikin jinin jikina yake, ba zan iya hakura da ita ba. Ki sani saboda ita na rasa kowa. Abbanmu ne kawai yake tare da ni yanzu. Amma Umma da kannena duk sun tsane ni saboda son ta, da nace matan da nayi. Fadwa na sha yin addu'a, amma son ta bai taba raguwa a zuciyata ba. Kullum hauhawa yake. Bacin sabani da familyna kin ga halin da rayuwata take ciki. Farauta ta ake tamkar nama. Rayuwata ake nema ruwa a jallo."
Ya sarara yana shafa file din gabansa. Bata ce komai ba sai kallo da kara nazarinsa da take yi. Ya ci gaba. "Bayan dogon bincike na gano gaskiya. Da gaske ne Ha'ab karuwanci take yi a can. Sabanin karatun da shugaba yace suna yi. Koda ba ke ce 'yar gwa-gwarmaya ba ina da burin nemanta a matsayina na mutum na farko da ya gano gaskiyarta kuma ya yarda da ita. Wlh Fadwa wannan Shugaban azzalumi ne, fataucin yaran mutane shi ya mayar sana'a. Kin ga Ha'ab yanzu ta manta da kowa. Bata tuna kowa, ta mance da shakuwa da zurfin soyayyarmu. Ta manta Abba mahaukacinta. Kaina ya gama kullewa, na rasa mafita, ina son ta har yau ina kaunarta. Na kasa nisanta kaina da ita. Na kasa ficewa daga lamarinta, duk da an nuna karara za'a kashe ni saboda bibiyarta.
Ki kalli hotunan nan, rayuwarta take cikin kwanciyar hankali. Shekara daya ina bin rayuwarta ba da saninta ba. Rana daya kuma ta farko da na bayyana kaina gareta cike da yakinin zata saduda saboda ni. Tar-bar da ta yi min shi ne sanar da shugaba ina bibiyarta. Tun a England aka fara neman raina. Dakyar na dawo Najeriya, gashi nan din ma ban tsira ba. Kamar yadda kika kudurta nima na kudurta. Koda zan mutu sai na tona asirin munafikin tsohon nan. Sai na sa shi dana sani. Na fara hada gagga-gaggan hujjoji a kansa. Na kuma ji dadin haduwa dake."
Ya dasa aya idonsa a kanta. Murmushi ta yi sannan ta ja hotunan gabanta ta fara budawa. Sai da ta gama sannan ta dago ta kalle shi. "Aiki mai kyu. Kai ka dauki hotunan?". "Eh ni na dauka duka". Ta gyada kai. Takardun bayanai ne a kan yadda suke tafiyar da rayuwarsu a can. Sai hotunan da ya dauka na ita Hamidan a wuraren da take harkokinta da maza dabam-daban. Ta kalli Ab'ha da ya zuba mata ido yana jiran jin me zata ce.
Tace "na yarda da kai. Na kuma yarda zaka iya. Kamar yadda ka so, nima na amince mu yi aiki tare matukar rai. Babu sauyin ra'ayi, babu ganin wahala ko wuya a karaya. Mu yi aiki bisa burukanmu babu makawa zamu yi nasara".
Ya saki murmushi "na ji dadin haduwa dake Fadwa". Ta masa hararan wasa tace "Yar gwa-gwarmaya dai". Gaba daya suka yi dariya sannan suka hada hannayensu waje daya suka damke tare da fadin "alaka ta fara, aiki zai kankama".
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
*Wannan shafin naka ne Autanmu, KING BOY ISAH. Zamanawa da daukacin makaranta litattafan hausa online suna matukar alfahari da kai... Kai din na daban ne. Ubangiji ya kara girma da daukaka Allah yasa ka fi haka amin*
```page 10```
Daurewa ya yi ya lalubo nutsuwarsa. Sai da ya fara da gyara murya tukunna yace "ina jinka Sauwam, lafiya dai ko?". Asp ya amsa "lafiya kalau. Dama zan sanar maka ne mun koma karo da Fadwa, a wannan karon ma Allah bai bamu ikon kama ta ba. Amma a tare da ita mun samu wasu 'yan ta'adda. Ga dukkanin alamu babu jituwa a tsakaninsu. Mun yi nasarar kama biyu daga cikinsu. Insha Allah zamu tsananta bincike a kansu, ta nan ne nake sa ran zamu kara gano wace ce ita, su waye suka tsaya mata? Da kuma manufarta. Alamu sun nuna da akwai 'yar tsama sosai tsakaninsu. Da wannan zamu binciki