Showing 36001 words to 37846 words out of 37846 words
Chapter 13 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt
suke hankalin Baffa baya jikinsa, a duk wani bugu na zuciyarsa tana yinsa ne tare da tunanin Fadwa. Ya yi juyin duniyar nan amma ya kasa cire tunaninta a zuciyar tashi.
Fadwa kuwa tana can aiki ya kankama. Kamfani ya ginu har an fara gudanar da ayyukan sarrafe sarrafe. Domin kuwa bayan kudin diyya da kotu da umarci iyalan Alhaji Habib su basu. Su yaran da kansu suka ware kaso mai tsoka a cikin dukiyar suka mallaka musu. Haka gwamnatin jiha ma a madadinta ta basu ruwan kudi naira miliyan biyar, domin a cewarsu wannan aikin su ya kamata su yi shi. Ta haka ne suka sami wadataccin kudin da suka yo odar manyan injuna da ragowar kayan aiki daga kasashe dabamdaban. Cikin wata daya suka kammala daukar yawan ma'aikatan da suke bukata suka fara aiki babu kama hannun yaro. A wannan kamfanin suna buga zannuwa iri iri wato atamfa. Suna buga takalmi na mata da na maza da jakunkuna. Suna yin mayafai. A bangare daya kuma ayyakan takardu ne. Litattafai ake bugawa manya da kanana. Kafin kace meye kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA* ya bunkasa ya yi fice a fadin najeriya. Ya zamana bayan 'yan kasuwa ma gwamnati da kanta tana yi da su sosai wajen basu kwangila ta buga zannuwa da litattafai a lokutan siyasa suna rarrabawa ga mata da makarantu a matsayin campaign.
Madalla da wannan tsarin na Fadwa, hakika maganarta ta bayyana gaskiya ta yi halinta. Mata masu zaman kansu a garin Kano sai kawo kansu suke gare ta manya da kanana har ma da wadanda zasu kai sa'ar hihuwar wasu a wajen. Sun fada sun maimaita cewa wahala da tsananin rashin gata ga masu barin gidajen iyayensu su suke saka su yin karuwanci ba dan suna da ra'ayin yin hakan ba. Sannan kuma babu yarinyar da take barin gidajen iyayenta bisa son ranta sai dai ta barshi dan dole wanda mafi yawa duk ta sanadin auren dole suka fi fitowa, sai kuma wadanda ake korowa idan kaddarar yin cikin banza ta fada musu.
Jin wadannan maganganun daga garesu yasa Fadwa ta ware wasu manya daga cikinsu ta hada su a matsyin komitin wayar da kai ga iyayen yara mata. Wadanda suke zagayawa cikin kauyuka da birane suna wayarwa iyaye kansu game da hatsarin dake tattare da korar 'ya mace daga gidansu. Da kuma illar shi kansa auren dole.
Ai kuwa da yake abin yinsa ake da gaske kafin wani dan lokaci fadakarwar ta baza ko'ina na birni da kauyukan dake cikin jihar Kano.
Fadwa kam tsakaninta da Allah sai godiya, domin kuwa ya gama mata komai a wannan rayuwar burukanta sun cika, rayuwarta ta haska, sunanta ya tumbatsa a cikin duniya. Ta kara gogewa ta yi fresh ta kara haske. Kwanciyar hankali ta samu, jiki ya murje tai bul bul abunta bata da matsala da kowa. 'Yan mata marasa gata da karuwai daga ko wane yanki gargadowa suke zuwa ga wannan rahamar da Allah ya aiko musu. Kuma duk wadda ta zo wannan kamfanin babu ita babu karuwanci har abada, sannan kuma ba zata nemi abu ta rasa shi ba. Fadwa ta zama wata fitila da ta haska rayukan mata da iyayensu. Matsalolin da ake yawan samu na korarar 'yaya mata a gidajensu ta ragu kashi tamanin da biyar bisa dari. Haka kaso cas'in a cikin dari na karuwan da a da suke zube a cikin Kano suna saida kansu sun koma ma'aikatan kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA*. A yanzu karuwanci baya burgesu. Burinsu shi ne su hana masu yi, kuma su dakatar da masu shirin fitowa su yi. Duk wata sabuwar jaridar da zata fita kasuwa sai an sako maganarsu irin shahara da gagarumar nasarar da suka samu farat daya.
Babu shakka Fadwa ta yi gwa-gwarmaya kuma ta yi nasara. Sannu a hankali ta fara kokarin sada matan da suke karkashinta da iyayensu. Wasu su koma gidajen nasu wasu kuma iyayen da kansu suke cewa su zauna a nan tare da ita har Allah ya fiddo musu da mazajen aure. Munanan ayyuka sun ragu fiye da kima a cikin garin da ma wajensa. Domin kuwa karuwai sun yi wuyar gani, babu su babu alamarsu a duk guraren da aka saba zuwa a same su. Hakan ya sanya matan aure suka sami sa'ida a gidajen aurensu. Domin da yawan mazan sun watsar da matayen da suke gidajensu sun rungumi karuwai. Amma a yanzu rashin karuwan yasa duka sun maida hankalinsu ga iyalansu. Wannan bun ba karamin dadi yayi wa matayen sunna ba. Kuma sun tabbatar wannan duk ta dalilin 'yar gwa-gwarmaya ne. Hakan kuwa yasa duk wata salla da zasu yi sai sun rokar mata rahamar Allah da kwanciyar hankali ga ilahirin rayuwarta.
Baffa ya kasa hakura da Fadwa, zuciyarsa ta Gaza daurewa kan tsananin sonta dake addabarsa na tsayin lokacin da ya santa. Ya isar da bukatarsa gareta kuma alhmdulillahi ta amshi rokonsa. Ta aminta da soyayyarsa dari bisa dari. Ko babu komai tana son ta yi aure domin karawa kanta daraja a duniya da lahirara. Kuma tana son daukacin matan nan da suke tare da ita suma su yi koyi da ita su yi aure tunda ba zasu dauwama a nan ba.
Farin ciki ya cika gidan marigayi Alhaji Habib a lokacin da suka ji kulkuwar alaka ta soyayya tsakanin Fadwa da Baffa. Wannan ne yasa ba wani bata lokaci ba aka shiga shirye shiryen biki. Zuwa lokacin kuma Abba da Hameeda sun koma daidaita kansu. Wata sabuwar soyayya suka koma ginawa kansu, idan ka gan su sai ka rantse basu taba samun wata matsala ba. Bayan gwaje gwajen asibiti su ma Fadwa ta fara shirin nasu auren da kokarin sada su iyayensu. Wannan abin kuwa ba karamin taba zukatan ragowar matan nan ya yi ba. Hakan yasa suma wasu shida daga cikinsu suka daidaita da tsofaffin mazajen dake neman su a baya aka fara maganar aurensu.
Alhmdulillah wanan abu ba karamin faranta ran Fadwa ya yi ba. A lokaci daya aka saka duka bikin nasu. Daurin aure takwas a rana daya. Daurin auren da ya sami hartar manyan manyan jagororin gwamnati da jigajiganta. Sun kuma sami tallafi daga gwamnati da wasu daidaikun mutane da ma kamfanoni masu zaman kansu.
Bayan auren ko wacce ta tare a gidan mijinta. Watanni biyu kuma Fadwa ta koma bakin aiki bisa amincewar mijinta abokin rayuwa, wanda take jin samun kamarsa zai yi wuya a duniyar nan. Baffa da mahaifiyarsa da kannensa sun karbe ta hannu bibbiyu babu wani bambanci babu canjin fuska. Sun kuma nuna goyon bayansu dari bisa dari kan aikin da take na taimakon al'uma.
*Bayan shekaru uku.*
Kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA* ya kara samun daukaka, sunansa ya tumbatsa a duniya. Duk matan da aka fara kafa kamfanin da su sun yi aure sun tafi gidajensu. A yanzu sai sababbin fuska da aka dauka. Kuma dukkansu Fadwa ce ta yi musu komai da aurensu. Ab'ha da Hameeda na can suna rayuwar aurensu cikin farin ciki. Bayan ta daidaita tsakanin ko wannensu da iyayensa.
Yau ta kama ranar week end ne asabar. Fadwa tana gida tare da mai gidanta da kuma karamin Fawad dinta. Yaron da ta haifa a shekaru biyu da suka wuce. Muhammad (Fawad) mai matukar kama da mahaifinsa. Yaro dan shekara biyu a duniya. Ya zama farin ciki kuma sanyin idanunsu. Falon ya yi tsit! Baka jin komai sai dariyar yaron ya yake ta yi yana wasa da teddynsa tare da mai renonsa Hannatu.
A dakin Baffa kuma shi ne a kwance ya yi dai dai bisa lallausan gadon, idonsa a lumshe tamkar mai yin bacci. Ta tura kofar dakin ta shiga da salla. Cikin wasu kaya na atamfa dinkin doguwar riga buba. Ta yi matukar kyau kamar a sace ta a gudu. Ta kara cika ta yi bul bul gwanin sha'awa. Hannunta dauke da basket na abinci. Ta isa gaban gadon ta jere komai a kasan tails din inda ta shimfida wani zagayayyen farin kyalle, ta kalle shi da dara daran fararen idanunta tace "sweet husband ur break is ready". A hankali ya bude idonsa ya zube su a kanta kamar yau ya fara ganinta. Shi a kullum Fadwa sabuwa take zamar masa. Duk wata shiga da zata yi sai ta yi mishi kyau. Ya lushe idon ya koma budewa yana fadin "to a zo a dauke ni". Ya yi maganar a shagwabe da sigar wasa. Ya bata dariya sosai ta kuwa dara sannan tace "ai ko Fawad dinka ya wuce dauka yanzu balle kuma kai ubansa". Ya waro ido kadan "au haka ma zaki ce? To shikenan ki ci abincinki ke kadai". Jin hakan yasa ta marairaice fuska "afwan sweet husband tuba nake zo in dauke kan". Ta isa gareshi tana kokarin daga kansa ya tashi zaune. Shi kuwa sai dada narke mata yake yana dandara kansa da filo.
"Allah Dadyn Fawad rigimarka ta yi yawa, yanzu ya kake so a yi?". Ta tambayeshi lokacin da take daidaita zamanta bisa gadon. Ido daya ya kashe mata yana daga bargon da yake rufe da shi alamar ta shigo. Ta gane wayonsa da kuma manufarsa saboda haka ta makale kafada "ka bari mu fara yin break to". Ta fada a marairaice. Shi kuwa gogan sai ya saki blanket din ya juya mata baya. Wai a dole ya yi fushi. Da sauri ta kwanta a bayansa ta yi masa kyakkawar runguma tana rada masa a kunnensa "kar ka yi fushi da ni masoyi. Ni da duka abinda nake da shi naka ne hakak malak. Gani gareka hasken raina". Baffa da ya kasa jure salonta da yadda take maganar ya juyo da sauri ya kankame da yana fadin "Fawad zai iya girma a idonki Fadwa amma ni ba zan taba girma gareki ba. Ki sani ni ne asalin Babynki mai matukar bukatar kulawarki. Pls take a Gud care of me kin ji Fadwana?". Ta kanainaye mijinta cike da so da kauna da kuma jin dadin yadda yake gaya mata gaskiyarshi tace "yadda ka so haka Fadwa zata kasance..." Bata karasa ba ya mirginata suka shige blanket aka hau musayar... Nasmat kam na tattare litattafai da birurrukana nace "fatan alkhairi ga ilahirin rayuwarki 'yar gwa-gwarmaya ".
Tammat bi hamdillahi. A nan na kawo karshen wannan labarin mai cike da darussa ga rayuwar al'uma. Shakka babu labarin kirkirarre ne, amma abubuwan dake cikinsa asalin zahiri ne. Babu wanda ba a aikatawa a cikinsu. Fatana a kullum shi ne rubutuna ya yi tasirin canza rayuwar koda mutum daya ne daga mummuna zuwa kyakkyawa. Allah ta ala yasa mu dace amin. 🙏
Godiya mai tarin albarka ga daukacin masoya masu kokarin bibiyar wannan labarin wadanda ba zan iya kirga dukkaninku ba. Ina son ku duka kuma ina kaunarku. Fatana shi ne ku amfana da duk abinda na zo da shi. Na san kuna tare da ni, to ku ci gaba da kasancewa da ni zaku yi farin ciki.
Ina muku albishir da sabon littafina na gaba mai suna *BAN SAN SHI BA* karamin labari mai dauke da babban sako. Zai fadakar ya wa'azantar, sannan ya nishadantar da ku masoyana.
*Jinjina ta musamman ga kungiyar*
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.
Da daukacin marubutan dake cikinta. Allah ya kara hasken kwakwalwa jarumaina. 👍😇
Na barku lafiya 🙏
*Nasmat* ✍