Showing 1 words to 3000 words out of 37846 words

Chapter 1 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt

25 Oct 2025

366

ο»ΏπŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________








```Da sunan Allah mai rahma, mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah!. Dubun salati kuma ga Ma'aikinsa fitilar alkhairi, shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w.)```




*Sallama da fatan alkhairi ga daukacin masoyana. Masu jimiri da kwazon bibiya ta a ko wane littafi da shafukansa. Ina godiya my fans. Sam ban ga laifinku ba, na matsanta min da tambaya a kan ina sabon labarin nan. Ku yi hakuri kun san jiki da jini. Na tsaya in dan huta ne. Yau kam ku motsa, ku mutsutstsuke idonku. Ga labarin 'Yar gwa-gwarmaya nan ya faso. Da iznin Allah zaku ci gaba da samun shi a ko wace rana.*



```Labarin namu ne mata.ku mu je zuwa 😍```



*Jinjinar ban girma, gare ku, zakakurai kuma jarumaina. ZAMANI WRITERS, kuna sanya ni alfahari. Nasmat tana kaunarku sosai da sosai. Allah ya kara daukaka min ku.* 🀝






```Page 1```






A hankali take tafiyarta cikin isa da iya tako. Babu wanda zai dauka wata take bibiya a yanayin tafiyar tata. Domin ta fi maida hankali ga wayar hannunta, wadda take tafe tana lallatsawa. Sanye take da bakar riga doguwa, sai mayafin rigar da ta yi rolling kanta da shi. Kyakkyawar farar fuskarta ma'abociyar kwarjini ta bayyana. Yanayin lumshin da ake yi a garin shi ne ya karawa lallausar fatarta kala da armashi ga mai kallonta. Fadwa kenan. Ja'jirtacciya, kuma tsayayyar mace. Mai kafiya a kan ra'ayinta.


Duk abin nan da take idonta na kan abin harinta, wato Suhaima. Wadda take bibiya ba tare da saninta ba. Wannan karon ta gama yanke shawara. Mai kan-kat, take so ta yiwa babban makiyinta Alh. Habib. Wanda duk duniya bata da makiyi kamar sa. Bata da burin da ya wuce ganin iyakarsa, da shi da mummunar harkallarsa.


Ta sadaukar da rayuwa da duk wani jin dadinta. Ba dan komai ba sai dan shi. Dan ganin ta kawo karshen abinda shi ne silar rugujewar ta'ta rayuwar.


Ta yi amanna cewa ita ce zata yi gyara a wannan fannin.


Ta dade da tattara duk wasu bayanai game da Alh. Habib, amma aka yi watsi da su. Daga karshe aka maida ta rikakkiyar mai laifi kuma abar nema ga hukumomi. Saboda rashin cikakkiyar shaida kuma bayyananniya, ga kokarinta na bayyana ma duniya boyayyiyar fuskarsa da mummunan halinsa, da kuma tarin ta'asar da yake tafkawa da shi da ire-irensa a rayukan bayin Allah 'yan kasarsu.


Wannan ne yasa hankalinta ya koma kan Suhaima. Babbar yarinya mai tashe a kasuwarshi ta yanzu. Kuma ta hannun daman shi. Ta tabbata muddin ta sami hadin kan Suhaima, ta shawo kanta har ta fito fili ta bada shaidar gaskiyar abinda yake aikatawa, to ba makawa duniya zata yarda. Saboda sanin kusancinta da shi.


Ta dade tana jiran wannan ranar, da zata sami Suhaima ta fito ita kadai. Amma bata samu ba sai yau. Wannan ne yasa gaba daya hankalinta ya tafi gareta. Ta ma manta da tarin jami'an tsaro da 'yan barandar da aka baza suna farautar ta..


Bangare daya kuma Dodonta ne, a's'p Sauwam yake bin sawayenta daga nesa yana murmushi, zuciyarsa cike da farin ciki. Yana mamakin wannan wace irin nasara ce Allah ya bashi haka cikin sauki? Yau ga shi ga gagararriya Fadwa. Ya tabbata a wannan karon kamar ma ta shiga hannu ne. Dan kuwa babu abinda zai sa ya rasa ta kamar sauran lokuta.


Ganin ta shiga kofar Hotel na sharaton. Yasa ya dan tsaya daga nesa, sannan ya ciro wayarsa ya danna kiran lambar ofishinsu.

"Hello! Yallabai, Abbas ke magana." Aka fada daga can inda ya kira din.

"Gud Abbas maza ka debo jami'an tsaro, ku same ni a Sharaton Hotel. Ku yi da jikinku, Fadwa ce na rutsa, kuma na tabbata wannan karon sam ba zata sha ba."

"To yallabai." Abbas ya fada yana sarawa mai gidan nashi, kamar yana kallon shi.


Duk wannan wainar da ake toyawa Fadwa bata sani ba. Ita kam, kanta tsaye take bin Suhaima. Bata da burin da ya wuce ta riske ta a wani lungu na wajen, kafin ta fada dakin da zata shiga.


Ita kuwa Suhaima ko alama bata san ana bibiyar ta ba. Tana isa cikin Hotel din ta hau lifta ta danna lambar hawa na shida. Da isarta ta fita, ta fara tafiya a duguwar hanyar da zata sada ta da dakin da ta zo. Cikin azama Fadwa dake bayanta ta sha gabanta. Turus ta tsaya, suka shiga yiwa juna kallon-kallo. Ita dai Suhaima kallon rashin sani take mata. Da kuma mamakin yadda ta tare ta kai tsaye. Ita kuwa Fadwa kallon kyau da tsarin Suhaima take, da kuma tsan-tsan tausayinta. Domin a yadda take sam rayuwar da take bata kamace ta ba.


"Baiwar Allah lafiya?". Suhaima ta tambaye ta fuska a daure. Har ta budi baki zata yi magana suka ji maganar 'yan sandan dake waje. Ta cikin lasifika suna cewa "Fadwa! Fadwa!! Na san kina ji na, kar ki yi taurin kai. Ki fito kawai ki mika kanki ga hukuma. Wannan wajen duka a zagaye yake da ma'aikatanmu. Baki da wata hanyar guduwa. Ki mika kanki kawai 'yar gwa-gwarmaya."


Murmushin nan nata na musamman ta yi. Tare da lumshe ido. Wannan ne ya tabbatar wa Suhaima cewa da ita ake maganar. "Yar gwa-gwarmaya?". Ta mai-maita sunan tana kara karewa Fadwa kallo. Hannu ta daga ta nuna ta da shi "dama ke ce 'yar gwa-wagwarmaya? me yasa kike bibiyata nima? Wai me muka tare miki ne kike neman raba mu da jin dadinmu?".


Fadwa bata kai ga yin magana ba, jami'an tsaron suka fito daga cikin lifta suka nuna ta da bindigoginsu. "Kar ki motsa Fadwa! Kin shiga hannun ma'aikata." Ta ji muryar a's'p Sauwam ta fada cike da gadara.


Idonta a kansa. Sai murmushi yake yana tunkaro ta da inkwa. Da kallo daya zaka gane irin farin cikin da yake ciki. Fadwa ta kuma lumshe ido a karo na biyu, ta yi murmushi. "Kai babban jami'i ne Sauwam, amma me yasa kake goyon bayan rashin gaskiya? Na sha gaya maka ni Fadwa a kan gaskiya ta nake. Ba kuma zan daina gwa-gwarmaya ba har sai burina ya cika."

"Gaskiyarki da rashinta ba ni ko ke ne zamu fada ba. Shari'a ce zata bayyana." Yana maganar yana dada tunkararta. "Ka yi gaskiya Sauwam. Tabbas kotu ita take bayyana mai gaskiya. Amma ba irin wadannan kotunan da muke da su yanzu ba. Hujjoji a kan makiyana suna da wahala. Amma ni tuni kun gama hada hujjoji a kaina. Wannan ne yasa ba zan taba baku damar kamani ba."


Ta fashe da dariyar nan ta'ta da suke kira ta 'yan iska. Tace "Sai wani ganin a's'p Sauwam." Ganin haka da kuma sanin wace ce ita yasa a's'p ya fara sakar mata harbi. Sai dai kash! Fadwa kam ta bace bat!. Ta bar shi da harbin iska...












*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________







*Ina tare da ku masoyana. Sakonninku na fatan alkhairi na zuwa gareni. Na gode! Na gode!! Na gode!!!. Ubangiji ya bar so da kauna su yi karko. πŸ™*






```page 2```









Sauwam ya ja wani tsaki. Ya daki goshinsa da tafin hannunsa na dama. Zuciyarsa na masa wani zafi. "Ka kuma rasa ta Sauwam". Ya ji sautin daga kasan zuciyarsa. Ya maida kallonsa ga Suhaima, wadda take tsaye tamkar dasa ta aka yi. Mummunar shigar da tayi ne, yasa ya yi gaggawar kawar da idonsa a kanta. Bai ce komai ba, ya juya ya bar wajen yana furzar da wani iska mai zafi.


Haka yaransa ma suka rufa masa baya cikin takaicin rashin samun nasara. Sun rasa gagarumar kyautar makudan kudin nan da aka saka ga duk wanda ya samu nasarar kamo Fadwa.



Bangaren Fadwa kuwa. Gidanta na mai-tama ta koma. Zuciyarta cike da kunci. Tun da Sauwam yake bibiyarta bai taba bata mata rai kamar na yau ba. Ya bata mata shiri, gashi ta rasa Suhaima. Bata kuma san yaushe zata koma samun dama irin wannan ba. Ta koma jan tsaki a karo na barkatai. Ta dauki kwalin sigari dake ajiye a gefenta ta zaro daya ta cinna mata wuta. Ta hau zuka tana fesarwa. Sai a lokacin ta fara jin kanta dai-dai. Ta jinginar da kanta jikin kujerar da take kai. Ta lumshe ido.

"Fadwa!". Ta ji kira ta da karfi da muryar Ummynta. Kamar dai yadda ta saba. Ta bude idon tana kallon inda aka kiratan. Ummy ce tsaye cikin fararen kayanta (as usual). Fuskarta a murtuke ta fara magana "Fadwa ashe ban gargadeki kan shan taba ba? A haka kike tunanin samun galaba a kan makiyanki? A'a 'yata. Wannan ba ita ce mafita ba. Maza ki tashi ki tsaftace kanki ki dauro alwala. Salla da salatin ma'aiki sune tsayayyar hanya ta yaye damuwa. Karatun alkur'ani mai girma yana faranta ran mumini. Na hane ki da shan wannan shirmen daga yau. In dai kin yarda ni ce mahaifiyarki." Bata jira me zata ce ba ta bace. Da sauri Fadwa ta kashe tabar dake hannunta cikin ash. Ta mike ta nufi bayi. Ba jimawa ta fito da alwalarta bayan ta yi wanka. Ta fuskanci alkibla ta fara nafilfili da kiran sunayen nan na Allah tsarkaka. Tana gaya masa maysalolinta. Kafin daga bisani ta fara karatun alkur'ani.


*A kasar Senegal*
Karfe biyar na yammacin ranar. Wayar Alh. Habib ta hau ruri. Bai wani bata lokaci ba ya kai hannunsa ya dauki wayar, tare da dagawa. "Sauwam, Allah yasa in ji labari mai dadi daga gareka." Sauwam ya sauke kansa kasa yana koma tuna yadda ya rasa damar da Allah ya bashi. "A'a Shugaba. Labarin ba mai dadi bane ta wata fuskar, sai dai yana da muhimmaci. Muhimmacinsa shi ne mun samu tabbacin Fadwa tana Najeriya, cikin Jihar Kano. Mun ganta har mun tare ta, sai dai Allah bai sa muka yi nasarar kama ta ba."

Shugaba. Habib ya mike tsaye lokaci daya gumi ya shiga yanko masa. "Wane irin sakaci kuka yi haka Sauwam? Ka kuwa san hatsarin dake tattare da Fadwa? Ku taimaka min mana. Yarinyar nan nema take ta bata min suna. Nema take ta wargaza rayuwar siyasata fa." Asp Sauwam yace "kwantar da hankalinka Alh. Fadwa ba zata gagare mu ba. Da iznin Allah nan bada dadewa ba zata shiga hannu. Ka huta gajiya."


Ya katse wayar, ya bar Alh. Habib rike da wayar yana saka da war-wara. Kai tsaye ya shiga laluben wata number a cikin wayar tashi, ya danna kira.

Ringing biyu a na uku aka daga. "Allah ya kama ma Shugaba." Aka fada a can inda ya kira din. "Amin amin Chaka. Kana ji na. Wannan ja'irar yarinyar tana Najeriya. Tana nan cikin Kano. Abinda nake so da kai maza ka baza yaranka kaima ka kutsa kai. Lungu da sako, ku nemo Fadwa kuma ku kashe ta."


Wanda aka kira da Chaka ya amsa da "an gama Alh. Ina gaya maka in dai muka yi arba da Fadwa sai dai gawarta." Alh. Habib ya hangame baki, farin ciki ya lullube shi yace "zan kuwa cika maka burukan rayuwarka Chaka...".


Ya kashe wayar sannan ya kira Aysha wadda ya kawo Senegal. Dan a yadda yake ji bai kamata ya koma kwana a kasar ba. Duk da akwai masu bukatar yarinyar da yawa. Saboda muhimmancin maganar Fadwa, yana da kyau ace yana kusa. Har wayar ta yanke bata daga ba. Ya ja tsaki yana fadin "wan-can shegen baya da sauki, har yanzu bai bar yarinyar nan ba?".


Haka dai ya yi ta zariyar kiran layin Aysha har dare. Bayan ya kira waya airport an yi musu komai na tafiya zasu bi jirgin sha dayan daren. (Ka ji manya)


Karfe tara da rabi, Okeke ya dawo masa da Aysha bayan ya yi mata ragas. Dakyar take tafiya. Ya kalli bakin mutumin yana bata rai yace "amma fa baka kyauta ba. Me yasa zaka yi mata haka? Ka kuwa san asarar da ka yi mini? Yanzu fa sai ta dauki lokaci kafin ta koma aiki."

Okeke ya hangame baki "sorry Alh. Yarinyar ce da a kwai sweet. Zan baka kudin jinyarta daban, kuma na yi bunking a dawo min da ita karshen wata mai zuwa." Take a wajen ya tura masa makudan kudi a account dinsa. Alh. Habib ya bashi bannu suka gaisa, sannan Okeken ya fita yana shafa fuskar Aysha.





To fa πŸ€”

*Shin Ina bakin zaren yake? Wane ne Alh. Habib Shugaba? Wace irin kiyayya ce tsakanin shi da Fadwa? Wace ce Fadwa? Mene ne burinta? A kan me take gwa-gwarmaya? Ku biyo Nasmat a shafi na gaba.*















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





```Ina kaunarki``` Kanwata *Amina Auta.* ```kina raina kema``` *Maryam 'Yar Mama* ```ban manta da ke ba``` *Baby Maryam* love you fiye da tunaninku. 😍


```Sadaukarwa ga``` *Mom Heebah* ```fatan alkhairi gareki 'yar uwa. Nasmat na tare da ke. Addu'ata a kullum ita ce Allah ya bawa Babynmu lafiya.``` πŸ™







```page 3```





*Alh. Habib Inuwa (Shugaba).* Haifaffen Jihar Kano ne. Cikakken mai kudi, kuma sanannen dan kasuwa. Wanda ake damawa da shi a bangaren siyasar Kasa. Shi ba mai mulki bane, sai dai shi ne yake nada shuwagabanni. A gaba daya kasar girmamashi ake. Ana mutuntashi, duk wanda ya gabatar a matsayin wanda za a zaba, ba makawa shi zai yi mulki. Alh. Habib yana da mata daya Laurat da yaranta uku. Abdul Aziz (Baffa) shi ne babba sai kaninshi Faisal. Sai kuma autarsu Anisa. Wadan-nan yaran 'yan gata ne gaba da baya, wadan-da basa neman abu su rasa. Masu galihu, masu yin abinda suke so. Mahaifinsu ne ya daure musu gindin yin hakan. Domin a cewarsa idan yana da kudi 'ya yansa basu sake ba to babu amfanin kudin kenan. Yana da yawan kyauta da sadaka. Yana yawan dibar talakawa da 'ya yansu ya biya musu Hajji. Su je saudiyayya su sauke farali. Wasu lokutan kuma ya dibi kana-nan 'yan mata wadan-da suka gama sakandire, ya tura su manyan kasashen duniya da sunan ci gaba da karatu. Wadan-nan halayen nashi ba karamin kima da daraja suke kara mishi a idon al'uma ba. Musamman talakawa. Kasancewar duk wadan-da yake yiwa hidimar su da 'ya yansu ne.


Sai dai a bangare daya Alh. Habib babban azzalumi ne. Makirin mutum, mai fuska biyu. Maha'inci, wanda ya maida 'ya yan talakawa da marayu jarin kasuwancinsa. Ya yarda da safarar 'yan mata sosai, dan yana saurin kawo kudi. Hakan yasa ya maida abin Sana'a. Yana fidda su manyan kasashe da sunan aiki ko ci gaba da karatu. Amma da an je can sai ya tilasta su yin karuwanci. Kudin wahalarsu kuma su dira a asusun ajiyarsa. Kasashen turawa da larabawa suna matukar so da kwadayin bakaken mata, 'yan afrika. Hakan yasa ya dage da tallata hajarsa a kasashen. Kasuwar kuma tana ci sosai. Yana aikin ne cikin hikima da kwarewa. Sam baya barin wata shaida wadda zata bayyana shi a matsayin mai hannu a cikin wannan badakalar.


Hakan ya sa koda zarginsa ba wanda ya taba yi. Sai kwatsam a cikin ja'jibe-ja'jibensa ya ja'jibo ruwan dafa kansa. *Fadwa!* Marainiya Fadwa!!.


Tun daga lokacin rayuwar shi ta shiga rudu. Sirrin da ya shafe shekaru yana binnewa yake neman fallasa. Mutuncin da kasarsa da talakawanta suke ganin shi da shi yake neman zubewa. Ya tabbata idan burin Fadwa ya cika ta fallasa shi, rayuwarsa ma ba lallai bane ya tsira da ita.

Wannan kenan.


*Wace ce Fadwa?*
Itama dai a Kano aka haife ta. Kuma ta zo ne a jerin 'ya yan nan wadan-da basu da takamai-man wanda zasu kira da nasu. A gidan marayu ta tsinci kanta, bayan an reneta tun daga jarintaka. Da aka tsince ta yashe a gefen hanya.


Uwar rikonta ita ce Amina wadda take kira Ummy ita ce ta rene ta tun daga kurciya har girma. Amina macen kirki, mai fara'a da nutsuwa. A karkashin kulawarta Fadwa ta sami cikakkiyar tarbiyya. Wadda ko wadan-da suke gaban iyayensu ba kasafai suke samun irinta ba. Soyayyar dake tsakanin Fadwa da Ummynta soyayya ce kwatankwacin wadda ke tsakanin 'ya ya, da iyayensu.


Nagartacciyar yarinya mai kaifin basira da kwazon karatu. Cikin nasara da saka rai ga ci gaba, ta kammala jarrabawarta ta karshe a babbar sakandire ta gwamnati. A shekarar ma kamar yanda ya saba yaudarar mutane Alh. Habib Inuwa Shugaba, ya sanar da daukar nauyin karatun dalibai mata goma a kasar waje. Marayu da 'ya yan talakawa marasa karfi. A cikinsu ne hukumar makarantar suka saka sunan Fadwa, saboda kwazo da dagewarta ga karatu.


Bayan fitowar sakamako aka fara shirye-shiryen tafiyar 'yan makaranta kasar waje. Allah sarki Fadwa a lokacin duk abokanin tafiyarta farin ciki suke, amma ita kuka take yi. Ba dan ta san wani abu game da tafiyar ba, a'a kukanta na rabuwa da Uwa ne. Wadda take ji kamar mahaifiya, Ummy. Ita ce wadda ta kara karfafa mata guiwa ga tafiyar. Ba dan ta so ba, ranar wata jumu'a jirginsu ya tashi zuwa kasar England. A inda aka ce an gama yi musu bunking na komai game da karatunsu.


Satinsu biyu a wani Hotel ana basu horo game da yadda zasu rika saka kayan turawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login