Showing 30001 words to 33000 words out of 37846 words
Chapter 11 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt
fatar kasancewa mai irin wannan dabi'ar". Kotu ta sake kaure da ihun masoyansa, suna fadin "sai Shugaba. Allah ya kare ka".
Bayan sun lafa da maganganun Bar.BB ya kalle shi da murmushi yace na gode Alhaji zaka iya komawa ka zauna". Ya fada a lokacin da yake taku zuwa gaban masu laifin nan. Alhaji Habib kuma ya sauka daga inda yake ya koma mazauninsa bayan kotu ta bashi iznin hakan. Bar.BB ya sami iznin tambayoyi ga masu laifin ya fara da tambayar su ayyukansu. Kamar ba zasu fada ba sai kuma suka yanke shawarar su fada kawai su tona asiri a nemo duka ragowarsu kar su wahala su kadai. Hali (maiki) ne ya fara magana. "A wannan al'amarin fa ba mu kadai bane. Muna da yawa, kuma muna da shugaba. Bamu da wani aiki da ya wuce ta'addanci shugaban namu shi ne yaron wancan Alhajin... Ya nuna Alhaji Habib. Sannan ya dora ...Shi yake kira a duk lokacin da yake bukatar mu yi masa wani aiki na ta'addanci kamar kisa ko tsorata wasu mutane dake neman bijire masa. A iya rayuwar shashancinmu bamu taba rika bindiga ba sai da muka fara aiki da shi. Shi ya saya mana makamai a kokarinsa na ganin mun kawar masa da ita wannan 'yar gwa-gwarmayar da yace ta addabi rayuwarsa. Wanda a kokrinmu na yin hakan ne aka kama mu." "Mene ne shaidarka game da hakan?". Bar.BB ya tambaye shi. Abokanen aikina sune shaidana. Zan iya fadawa jami'an tsaro inda suke domin su ma a kamo su a gurfanar da mu tare. Kirjin Alhaji Habib ya buga da sauri ya yi kasa da kansa. Bar.BB ya yi godiya ga alkali sannan ya koma ya zauna yana 'yan rubuce-rubuce kan takardar dake gabansa.
Saida alkalin ya gama rubutunsa sannan ya dago yana kallon jama'ar dake cikin kotun yace "bisa yadda zantuka suka gabata daga bakin masu laifi, sun kara tsunduma Alhaji Habib Inawa a cikin wannan shari'ar. A saboda haka kotu ta daga wannan shari'ar zuwa mako mai zuwa, tare da bawa jami'an tsaro iznin kamo ragowar masu laifin domin samun tabbatacciyar shaida a kan wanda ake zargi. Saboda haka... "Wannan Shari'ar ta rana daya ce ya mai girma mai Shari'a". Wata murya da ba a san mamallakiyarta ba ta katse alkalin da fadin haka a cikin wadanda ke zaune bisa jerin kujerun dake cikin kotun. Hakan ya ja hankalin alkali da lauyoyin tare da ilahirin mutanen dake kotun zuwa ga mai maganar. Mace ce zaune bisa kujera, fuskarta yane da karamin mayafi. Cikin 'yan dakiku ta sauwaka ma masu son ganinta ta hanyar mikewa ta tsayu a gaban kotun tare da bude fuskarta gaba daya. Fadwa ce! 'yar gwa-gwarmaya.
Tirkashi... Keep following.
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*β
_*WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£*_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
```Page 25```
Ai kuwa a take kotun ta kaure da hayaniya ciki da waje. Dubbanin mutanen dake jin labarin 'yar gwa-gwarmaya da hatsabibancinta suka marmatso dan ganewa idonsu wace ce ita?. Cikin matsananciyar kaduwa da tashin hankali Alhaji Habib ya mike tsaye yana fadin "Gata nan Fadwa ce ku kama ta kashe ni zata yi". Ya fada cikin bada umarni ga daukacin ma'aikatan dake wajen. Gaba daya suka mike suka nufi inda take suka yi mata kawanya. Kawunan bindigoginsu na fuskantar kwakwalwarta. 'Yan kallo na ciki da waje suka dauki ihu "ga 'yar gwa-gwarmaya, ga 'yar gwa-gwarmaya, yau dubunki ta cika, ku harbe ta! Ku harbe ta!!" Abinda da yawa suke fada kenan. Ganin kotun ta kacame da maganganunsu yasa alkalin buga gudumarsa domin dawo da nutsuwar kotu. Tsit! Kake ji ba wani mai magana ko dogon motsi, jami'an tsaro kuma suna nan zagaye da Fadwa alamar ta shiga hannu. Ita kuwa ko a jikinta ballatana ta nuna wata alama da zata nuna ta ji tsoro.
Alkalin ya kara daidaita zaman gilashinsa yana kare mata kallo. Yasha jin labarinta a gidajen radio da tv, jaridu da kuma bakunan al'uma. Amma bai taba tsammanin haka take ba.
Yariya ce shar da ita, siririya mai matsakaicin jiki, wankan tarwada mai karamin kyawu da yake tattare da sirruka. Da kallo daya zaka gane hakan a tattare da ita. Kada kai ya yi, ya yi sabon rubutu bisa takardar gabansa sannan ya yi gyaran murya ya fara da bawa jami'an tsaron umarnin su matsa gefe kutu tana son ji daga gareta.
Nan fa 'yayan cikin Alhaji Habib Shugaba suka duri ruwa. Ganin 'yan sandan sun matsa bisa umarnin alkali yasa ya mike cikin marairaicewa da kaskantar da kai. "Ya mai girma mai shari'a, a taimake ni a kama wannan mai laifin wallahi guba ce mai bata zukatan al'uma, ta sace min 'yata ta kuma baza video yadda ake keta mata haddi ana wulakanta ta a duniya. Ta kuma sace min babban yarona har yau ban san inda suke ba. Ta kuma sanar cewa nima yau zata kashe ni". Alkalin ya gama kallon Alhaji Habib da kuma nazartar kalamansa ya maida kallonsa ga Fadwa. Yana mamakin Kasancewar wannan yarinya dunkule da wadannan laifukan. Ya tsaida idonsa kan Alhaji Habib kana yace "da kai da ita duka kuna gaban shari'a yanzu. Saboda haka ka kwantar da hankalinka kotu ba zata taba barin mai laifi ya sha ba.
Ya juya ga Fadwa dake tsaye a inda take tamkar wadda aka dasa ya jefa mata tambaya "yarinya zamu iya sanin wace ce ke da kuma dalilin sako kanki a cikin wannan shari'ar? Shin mene ne alakarki da su dukan?" Babu wani jinkiri ta daga fuskarta daidai ta fukanci al'umar dake wajen sannan ta fara magana. "Dafari dai sunan Fadwa wadda a yanzu aka fi sani da 'yar gwa-gwarmaya. Kuma ni marainiya ce da ta tashi a gidan marayu na gwamnati mai lamba 3 a nan cikin garin Kano. Tun lokacin da na fara wayon sanin matsayina na tsinci kaina a matsayin marainiya maras asali da tushe. Hakan yasa na kuduri aniyar sayawa kaina kima da nemawa kaina makoma ta gari ta hanyar dagewa in sami nagartaccen ilimin da zai saya mini 'yanci a rayuwata ta gaba. A saboda haka ne na zamo daliba mafi kwazo da maida hankali a makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da nake zuwa. Wannan ya saka gaba daya malamai da shugabannin makarantar suke alfahari da ni. A shekarar 2005 na sami nasarar kammala karatuna na sakandire. Inda a wannan lokacin ya zamana nice dalibar da tafi kawacce maki a matakin karshe. Wannan ne ya saka na sami damar kasancewa a cikin dalibai goma da wancan azzalumin yake dauka da sunan tura su kasashen duniya su ci gaba da karatu. Farin ciki sosai iyayen rikona suka yi a lokacin da labarin ya zo garesu. Bayan duk wasu shirye-shirye muka bar Nigeria muka tafi American da zummar ci gaba da karatu. Amma kash rana ta farko da muka shiga kasar ba a barmu mun kwana da mutuncinmu ba. A ranar ya saida mu duka ya karbi kudinsa ya dawo Najeriya. Mutanen nan basu duba karancin shekarunmu da maraicinmu ba a wannan lokacin, haka suka yi ta ci mana zarafi tun muna wahala har muka dawo muka saba.
A karshe da na sami kubita na dawo da zummar tona asirinsa karyata ni ya yi. Aka ce biyana aka yi in bata masa suna. A lokacin har ya gabatar da yan matan da ya fidda mu tare a matsayin shaida a kotu da takardun karya masu nuna alamar cewa lallai karatu suke yi a can". Ta sarara tare da matse kwallar idonta.
A lokacin duk wanda yake ciki da wajen kotun jikinsa ya fara sanyi. Ta dago da jajayen idonta ta ci gaba. "Bayan wannan lokacin na yi kokarin fita batun maganar in barshi da Allah, amma me? Sai na ga har zuwa lokacin bai daina abinda yake yi ba, bai daina kwasar 'yayan jama'a yana kaiwa turawa suna biyan bukatunsu da su ba. Haka kuma al'uma basu daina kallonsa a matsayin mutumin kirki mai kaunarsu ba. Bakin cikin rayuwar da ya jefani shi ya kashe uwar rikona duk da ba ita ta haifeni ba. Wannan ne yasa na dauki damarar yaki da shi. Saboda tsananin tausayin iyaye duk da ni ban san nawa ba. Babban burina shine ko wace mace ta sami farin ciki ko da ni ban samu ba. Bani da burin da ya wuce in kawar da karuwanci a kasar haihuwata. In kuma dakile ire-iren wannan mugun bawa masu safarar mata domin yin fasikanci, saboda lalacewar abin yanzu har kasa mai tsarki suke kai karuwai suna yin karuwanci. Maganar da ya yi na cewa na sace 'yarsa an keta mata haddi tabbas gaskiya ne. Ni na sace Anisa kuma na saida ta kamar yadda ya sayarda ni aka lalata ni. Amma maganar basu dawo gareshi ba wannan karya ne, a gidansa dukkansu suka kwana. Ina tafe da cikakkun bayanai da hujjoji da zasu tabbatar da laifinshi a fili kowa ya ganshi. Idan kotu ta bani iznin hakan."
Ta saka aya idonta a kan alkalin kotun. Zumbur Alhaji Habib ya mike, jikinsa na kyarma ya fara magana da karfi. "Karya take, mai shari'a wallahi karya take. Ban taba saida 'yar kowa ba. Ban san komai game da maganganunta ba.." Maganar alkalin ce ta katse shi. Inda yake cewa "kutu zata baka damar yin magana idan bukatar hakan ta taso. Yin magana ba da izni ba laifi ne, dan haka ka kula". Saboda tsabar rikicewa da fitar hayyaci kasa zama ya yi. A lokacin ji yake kamar ya rufe ido ya ganshi a gidanshi.
Wani masifaffen ciwon kai ya ziyarce shi lokaci daya. Idonsa suka fara gani dishi dishi. Wani daya daga cikin lauyoyinsa ne ya mike ya taimaka masa ta hanyar zaunar da shi. Gaba daya ya soma fita hayyacinsa. Alkalin ya maida kallonsa ga Fadwa yace "ina hujjojin naki suke? Kotu na bukatar gani da kuma jin su. Farin ciki ya lullube zuciyarta ganin dukkanin matsalointa sun zo karshe. Hannu ta saka ta sauke jakar hannu dake rataye a kafadarta. A cikinta ta fiddo wani faifan CD ta fara mikawa mai gabatar da kara na kotun wato rajistara ko ince muhutin alkali.
Bayan samun izni daga alkalin aka dauki faifan CD aka saka a wata DVD dake ajiye a wurin. Wadda dama an tanade ta ne domin ire iren haka. Jama'ar dake wajen duka sun nutsu, al'ajabi ya cika zukatan wasu. 'Yan jaridu sai kara saura kamarorinsu suke a daidai fuskar TV da suka tabbatar ta cikinta hoton videon zai bayyana.
Ni kaina Nasmat tsayar da idona waje daya na yi dan ganin abinda zai fara bayyana a cikin laifukan Alhaji Habib Inuwa. Readers ku ban lokaci zuwa gobe dan jin me aka fara karo da shi.
Keep following.π
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*β
_*WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£*_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
Na gode! Na gode da kulawa da kuma dimbin comments naku masoyan gaske.
'YAR MUTAN ARKILLA NOVES GROUP
KIN BOY ISAH NOVELS
UMMYN YUSRAH NOVELS
ZAMANI WRITERS FANS
WAHALA BATA KISA FANS GROUP
Nasmat na matukar godiya gareku mambobi na wadannan groups masu albarka Allah ya bar zumunci ya yi karko, ana matukar tare.
```Page 26```
A karon farko hoton Hameeda ne ya fara bayyana, wanda Ab'ha ya yi daukarta a lokacin da yake bibiyarta. Jikinta sanye da irin tsinannun kayan shan iskan nan na turawa irin na hutun bakin ruwa. Tana kwance ta yi plat bisa kirjin wani bature dake kwance a kan farin yashi yana shafa kirjinta.
Daidai nan tace a dakatar. Aka tsayar da CD ta hanyar danna stop. Ta fara magana "wannan da kuke gani wata daya daga cikin takwarorin tafiyata ne. Tare ya fitar da mu america. Amma da yake su suna da ra'ayin karuwancin har yau suna aiki tare da shi. Har yau bata daina yin karuwanci ana bashi kudi ba. Bayan ita yana da 'Yan mata sama da talatin wadanda duk aikin da suke masa kenan." "Ab'ha" ta kira sunan da daga sauti. Ba a ji amsa ba, sai karar bude daya kofar kotun da aka ji, tayayyen matashin ya shigo rike da ita tana ware ido, hannayenta na daure a baya kamar police ya kama mai laifi.
Ilahirin jama'ar dake kotun duka hankalinsu ya koma kan Hameeda. A lokacin ne kuma Fadwa ta dora da cewa "wannan ita ce kuka gani a jikin videon nan. Mutane suka kara kafa mata ido cike da son tabbatarwa, "tabbas ita ce, wallahi ita ce". Abinda suka shiga ambato a tare kenan. Suna "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Wasu daga cikin na fadin " subhanallahi". Hameeda ta yi kasa da kanta cike da kunya da bakin cikin ganin wannan rana da bata taba saka ran ganinta nan kusa ba.
A take kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai tana fadin "wallahi nima na yi nadama, na yi matukar da na sanin kasancewa haka. A zamana a hannun wannan abokiyar karatun tawa na kwana daya, ta ganar da ni abinda a baya ban sani ba. Ta tunatar da ni abinda na sani kwakwalwata ta yi watsi da shi. Ta ankarar da ni wata daraja da nake da ita wadda ni da sam ban san ina da ita ba". Ta saki kuka wiwi kamar wadda ta rasa uwa da uba lokaci daya.
Cikin matsanancin firgicin da bai taba shiga ba ya mike tsaye bakinsa na rawa hannu na karkarwa. Ya rasa wata kalma, ya rasa ko wace kalma da zata karyata wannan abin da Fadwa ke shirin aiwatarwa wato toma masa asiri. " karya suke, gaba dayansu karya suke. Wane ne ya biya ku ku kulla min sharri? Har nawa aka baku da zaku tsaya ku dage wajen tozarta mutum mai mutunci kamata. Ya mai shari'a walla..." Tasawar da mai Shari'a Musa ya daka mishi ita ce ta tsayar da kalominshi. Alhaji Habib kenan da ya yi matukar fita hankalinsa. Jikinsa ya hau tsuma kamar mai shirin kamuwa da ciwon barin jiki. Ya koma ya fada kan kujerar da ya tashi a kai gumi na bin gefen saje da jijiyoyin wuyansa.
Daga can wajen kotun kuwa kara da kururuwar wani dattijo ce ta cika mutanen dake wajen har yana kokarin hana su jin abinda ake fada daga cikin kotun. Hakan yasa mutanen dake kusa da shi rufuwa kansa suna tambayar dalilin kukansa. Tsohon cikin sautin kuka ya fara magana "mun shiga uku wallahi 'yar dan uwana ce Hameedatu. Tun da ta bar kasar nan da sunan ci gaba da karatunnan ana murna, bata koma dawowa ba. Iyaye na ta nemanta ta dawo ta yi aure ta ki, babu zaryar da bamu yi a gidan Alhaji Habib ba amma atafau yace sai ta kammala karatu sannan zata dawo. Ashe azzalumin ya san abunda take shukawa a can. Allah ya isa munafiki ba zamu taba yafe maka ba". Kuka sosai Tsohon yake yana doka tafukansa a kasa saboda tsabar bakin ciki da takaici. Ya ciro wayar hannunsa ya fara kiran yayansa wato mahaifin ita Hameedan. Mutanen dake wajen kuwa jikinsu ya yi sanyi, hankulan wadanda suka bada imaninsu ga Alhaji Habib sun fara tashi. Domin kuwa sun fara tabbatarwa duk abinda ake zargin nan gaskiya ne.
A cikin kotu kuma mai Shari'a Musa ne ya buga gudumarsa dan neman daidaito da nutsuwarsu. Bayan duka sun tsagaita da maganganunsu ya maida kallon shi ga Hameeda da kanta yake kasa yace "ke yarinya meye gaskiyar abinda wannan ta fada game da ke?". Shiru ta yi hawaye na bin kuncinta, ba tare da tunanin goge su ba ta fara magana cikin nadama marar amfani. "Kwarai haka ne ya mai shari'a, duk abinda ta fada gaskiya ne". Ta kwashe komai game da abinda ya shafi rayuwarta a can ta gaya musu...
Tana dasa aya Alhaji Habib ya yi zumbur ya tsallaka kujerun dake bayan nasa, ya kade rigarsa ya zuba da gudu...
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*β
_*WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£*_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
*Na yarda so shi yake kawo kauna. Abinda kuke nuna min kauna ce ziryan masoyana. Ina sonku ina kaunarku ina matukar jin dadin kulawar da kuke nuna min. Ubangiji ya albarkaci zumuncin dake tsakanina da ku gaba daya amin. π*
```Page 27```
"Arrest him". Muryar alkali Musa ta ratsa kotun cike da amsakowa. Kafin ya kai ga kofar da zata sada shi da wajen kotun jami'an tsaron da suke tsaitsaye a ciki suka zagaye shi. Cak! Ya ja ya tsaya yana maida numfashi da kokarin daidaita shiga da fitar numfashin nasa, yana zare ido kamar wani bokon duniya. A yadda yake tsayen ji yake kamar a mafarki ne, zuciyarsa ta kissima mishi