Showing 15001 words to 18000 words out of 37846 words
Chapter 6 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt
daya kamar na wannan dake gabansa ba. A ransa yace "tsarki ta tabbata ga mahaliccin wannan kakkyawar halittar". Ya dauke kansa dakyar, zuciyarsa na raya masa ya samu abinda shi da iyayensa suka dade suna nema wato matar aure. Babu shakka wannan 'yar sanda ta tafi da imaninsa...
Bai kai karshe ga maganar zucinsa ba ta katse shi. "Kai karamin mara kunya, shin ka san inda kake kuwa?". Baffa cikin sanyin muryar da shi kansa bai san yana da shi ba yace "ranki ya dade, na san ina hannun jami'an tsaro ne".
Fadwa ta fashe da muguwar dariyar nan ta'ta mai ban haushi ga wanda ya san manufarta tace "shakka babu uban da 'yayan duka kwakwalen jakai ne da su". Maganar ta tunzura Baffa kasancewarsa mai saurin daukar zafi. Sai dai sanin muhimmancin wadda yake maganar da ita a zuciyarsa yasa ya danne "ban gane me kike nufi ba". Ya bukaci karin bayani. Ta girgiza kai "yaro, yaro ne. A yadda naga zafinka a gidan TV sam ban kawo haka zaka yi sanyi a gaban abin nemanka 'yar gwa-gwarmaya ba".
Maganar ta saukar masa kamar almara. Kansa ya buga da karfi, lokaci daya tare da ziciyarsa. Ya kura mata ido yana neman gasgata abinda ta fada. Kasancewar duka video da ta sake babu fuskarta sai dai murya. Tabbas ita ce. Yanzu muryar take dawo mishi.
Cikin karaji da matsanancin zafin bacin rai ya zaburo mata...
Zan ci gaba.
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
*Alhamdulillah na ji dadi na kuma gode da yawan comments da privete test naku a kan wannan labarin. Hakika kuna karawa Nasmat kwarin guiwa matuka. Ku ci gaba da bibiya ni kuma cikin farin ciki zan ci gaba da antayo muku shi.*
~The great gift in this life is a *love* and *care*. U guys give all those to me. I hav no one like u my fans keep following~ π€
```page 15```
Jin ya kasa mikewa daga kan kujerar ne ya tuna masa a daure yake. Ya zubawa sarkar da ta daure shi da ita ido, yayin da bakin ciki ya mamaye zuciyarsa. Ya sake dago da jajayen idonsa ya kalleta yana cewa "banza karamar tsagera. Wannan daurin da kika min ya tabbatar min kina jin tsorona ne, in ba haka ba ki kwance ni ki tsaya a gabana mana. Wallahi kisan da zan miki shi zai zama kisa mafi muni da aka taba yi a cikin duniyar nan". Ya saka aya yana ciccika kamar wani mayunwacin Zaki. Fadwa ranta ya yi masifar baci, ita ma a take launin idonta ya canza. Jikinta har bari yake ta fara magana "lallai kai jahili ne. Kallon me kake min ne? Ka dauka 'yar gwa-gwarmaya kamar ko-wace mace take? To bari a kwance ka din ka yi abinda zaka iya". Ta fice daga dakin a matukar fusace ta nufi nata dakin a ranta cewa take lallai yau ko bata kashe wannan yaron ba sai ta hada masa jini da majina. Ba jimawa ta fito tana huci hannunta rike da daurin makkulansu.
Ab'ha dake zaune a falo yana kallon shige da ficenta ya miki ya rufa mata baya, saboda ganin yanayinta. Da isarta dakin kai tsaye ta isa gaban kujerar tana kokarin kwance shi.
Tsabar yadda ya kagu ya kashe ta, tun kan ta gama kwance hannunsa daya ya yi amfani da kansa ya buga a nata. Ji kake gum! Dai-dai da shigowar Ab'ha kenan. Ta tsaida abinda take ta dago ta wanke kuncinshi da wani rikitaccen mari, wanda ya sa idanunsa suka fara gani bibbiyu. "Banza mai karamin tunani, ka bari na kwance ka mana. In yaso sai ka fito da dukkan karfin da kake da shi ka kashe ni".
Ta koma dukawa da nufin ci gaba da kwance shin.
Ab'ha ne ya yi wuf ya rike hannunta tare da mikar da ita tsaye. "Me kike shirin aikatawa haka Fadwa? Ta ya kike tunanin hada karfinki da na namiji? Wannan kuskure ne karki soma pls". Wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare mata a makogwaro, wai me maza suka dauki mata ne? Bata san lokacin da ta kai wa Ab'ha wani mugun naushi a fuska ba. Ya yi baya taga-taga ya fadi kasa. Daga lokacin ya daina ganinta sai maganganun da take cikin fushi, da yake ji sama-sama. "Ina namijin yake? Wannan ne namijin? Me kake tunanin samu a jikin da aka gina shi da haramun? Dole in ganar da wannan kuskurensa. Dole ya san ni din ba kamar ko-wace mace bace, burin ramuwa bai bar ni sakankancewa na san dadin jikina ba". Ta juya ta ci gaba da kwance shi.
Baffa ya zuba mata ido yadda take zuba masifa. Bangaren zuciyarsa na kokarin yabon yadda fadan ya yi mata kyau. Bangare mafi rinjaye kuwa Allah Allah yake tagama kwance shi ya yi mata kisan gilla. Hakika yau zai kawar da abinda ya hana mahaifinsa da duka familynsa sukuni da walwala, abinda ya jefa rayukansu a cikin bakin ciki.
Sai da ta gama kwance shi sannan ta ja da baya ta yi wani irin juyi, lokaci daya rigar nan dake jikinta ta nadi-diye. Ta sa hannu ta daure ta a inda ta taru. Ta daure gashin kanta waje daya ta zuba masa ido tana cewa. "To me kake jira? Bismillah man zo ka kashe Fadwa". Baffa ya yi saurin kauda yabon yadda ta kara kyawu a zuciyarsa. Tsana da kiyayyarta suka mamaye a lokacin da ya tuna video da ta dauka na yadda ake lalata rayuwar gudar kanwarsu Anisa, wadda a sanadinta har yau basu san inda take ba. Ya yi wani rin karaji ya nufe ta da gudu zuciyarsa dauke da mugun nufi. Haka itama ta tare shi cike da burin jiyar da shi asalin karfinta. Nan fa aka kaure da fada babu ji babu gani. Ba wanda yake rike da wani makami a cikinsu, sai dai ko-wannensu na kokarin nuna asalin karfi da kuma kwarewarsa. Burin ko-wanne ya illata abokin fadansa.
Naushi da yakuci suke kaiwa junansu ta hannu da kafa, kafin kace me Baffa ya fara jigata. Duk abinda ake dukansa daya bai sami taba Fadwa ba. Da kwarewarta take kare harinsa kuma ta dake shi. Tun yana taga-taga har ya kai ga faduwa, baki da hancinsa duka jini suke fitarwa. Ga wasu manyan gurare uku da ta kumbura masa a ka.
Sai a lokacin idon Ab'ha suka dawo da ganinsu dai-dai. Saboda mugun naushin da Fadwa ta masa. Ganin Baffa a kasa tana ball da shi yasa shi hanzarin mikewa. Wannan karon da rarrashi ya je mata.
"Dan Allah ki dakata Fadwa, hakan ai kashe shi zaki yi. Ya isa haka pls". Ya rike ta yana jijjigata. Bata ce da shi komai ba ta fizge jikinta ta fice daga dakin, ta bar shi da Baffa ranga-ranga.
Ab'ha ya tallafa masa ya mikar da shi ya maida kan kujerar da yake kai ya zaunar da shi. Ya yi laushi sosai har baya gane komai. Kansa ma ya kasa tsayuwa sai lilo yake kamar dan mashalo. Da gudu Ab'ha ya nufi dakin Fadwa. Ya tura kofar ya shiga yana kiran sunanta. A lokacin tana tsaye gaban karamar freezer dake dakin tana kora ruwan sanyi. Sai goge gumi take da wani karamin kyalle dake hannunta. Ta juyo ta zuba masa ido kawai. Shi kuwa cikin rawar murya yake mata bayani. "Guy din nan fa zai iya mutuwa, bai san inda kansa yake ba. Ga baki da hancinsa na zubda jini". Sam bata ji wani tausayinsa ba, amma sai ta ji sam bata so ya mutu ko dan saboda mahaifiyarsa. "Ka je ina zuwa". Iya abinda tace da shi kenan. Ta shige toilet dinta. Shi ko ya koma gurin Baffa da sauri.
Ta dauki mintuna goma kafin ta fito a hakan ma ta hanzarta saboda tausayin uwar yaron ba dan shi ko ubansa ba. Ta shigo dakin cikin wata sabuwar shigar. Hakan ya nuna wanka ta yi ta sauya kayanta zuwa wasu kana-nan kaya riga da wando pink colour. Da flat shoe su ma pink. Ta tattare gashin kanta ta daure shi guri daya bayan ta taje shi. Wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mata, wato a duk lokacin da ta sauya shiga sai mai kallonta ya ga tafi ta dazu kyau.
Karamin akwatin agaji ne a hannunta, ta zuba masa ido cikin wani yanayi. Ita kanta bata san ta illata shi hakan ba. A yadda yake kam babu mamaki zai iya mutuwa. Sai ta ji faduwar gaba ta riski zuciyarta, dan tun da take bata taba yin kisan kai ba. Ga tausayin halinda mahaifiyarsa zata shiga idan shima ta rasa shi. Sai ta ji tana tsoron ta zama wannan mugun sanadi. A dan tsorace tace da Ab'ha "na shiga uku Ab'ha, mahaifiyarsa ba zata yafe min ba in na kashe shi. Pls ka yi wani abu". Ganin ta bashi dama yasa ya dauko Baffa daga kan kujerar nan ya kwantar da shi bisa dogon bancin dake ajiye a tsakiyar dakin. Sannan ya dauko akwatin ya dire. Wani tunani ne ya zo wa Fadwa kasancewar bata da wani makiyi sama da Shugaba a kullum burinta ta saka shi bakin ciki.
"Dakata Ab'ha kar ka masa komai, ina zuwa". Ta fada tana mai ficewa daga dakin. Ab'ha ya bita da kallon mamaki al'amarinta ya fara bashi tsoro. Sai kace mai al'janu? Ya tambayi kansa. Bisa dole ya dakatar da aniyarsa yana kallon mawuyacin halin da Baffa yake ciki na rai ko mutuwa. Ba jimawa ta dawo da wayar hannunta ta dauki hotunan guy din guda biyu sannan ta yi murmushi. "Ka yi duk yadda zaka yi ka ceto shi, bana so ya mutu". Tana gama fadin hakan ta juya ta fice. Dan tana da yakinin in dai ba lokacinsa ne ya yi ba Abba zai iya dawo da shi.
Tana zuwa da hotunan sai ta dora su kan media kawai a groups na Facebook da whatsapp tare da bayanin ga dan gidan shugaba da ya bata yana hannun 'yar gwa-gwarmaya tana azabtar da shi. Abinka da 'yan social net basa sanya wajen yada ire-iren wannan post din, sai nan da nan labari ya game ko-ina, hotuna suka bazu.
Yau ne ranar shiga kotu da sanannun 'yan ta'addan nan da Asp Sauwam ya kama wadanda suka bindige dan sanda daya kuma suka yi musayar wuta da jami'an tsaron. Bayan dogon bincike da azabtarwa sun sanar wa Asp cewa basu da wata alaka da Fadwa basu santa ba sai ta dalilin Shugaba Habib, domin shi suke yi wa aiki. Shi ne ya basu umarnin su kashe ta. Jikin Asp ya yi sanyi sosai, hankalinsa in ya yi dubu ya tashi. Yayinda zuciyarsa ta kasa raba daya biyu. Shin da gaske Shugaba mai laifi ne, ko dan tana neman bata masa suna ne ya yanke wannan hukuncin?. Domin bayan wannan ba abinda 'yan ta'addan suka sani game da shi. Kawai dai yace su kashe masa ita.
Wannan ne yasa ya kasa sanarwa kowa sakamakon bincikensa duk kuwa da matsin tambayoyi da yake samu daga 'yan jarida. Baban kotun ta gama cika da batsewa da lauyoyi da kuma masu son jin ta bakin 'yan ta'addan a kotu tunda sun kasa samu a gurin jami'an tsaro. Tuni 'yan jaridu daga bangarori dabam-daban suka hallara.
Hilix biyu aka ciko da ma'aikata tare da masu laifin suka faka a kofar kotun. Asp Sauwam ne kan gaba, sai yaransa dake rirrike da masu laifin suna rufa masa baya. Fitowarsu ke da wuya 'yan jarida suka yo musu caa da tambayoyi. Sai dai tun a can headcoter Ogan ya gaya musu kada wanda ya zanta da su. Hakan yasa ragowar 'yan sandan suka shiga ture mutanen suna buda musu hanya har suka shiga kotun.
Aka tsayar da masu laifin a inda ya dace kowa ya sami guri ya zauna. Kotu kam ta cika makil, ba masaka tsintsiya. Sahun 'yan jaridu dabam na 'yan sanda da masu kallon shari'a dabam. Kowa da abinda yake cewa, hakan yasa dakin kotun ya kaure da surutu. Ana cikin haka aka buga kofar karamin dakin alkali dake bangare daya a cikin kotun. Tsit! Kake ji ba wanda ya koma magana. Ba jimawa sai ga alkalin ya fito "kooot!".cewar rajistara dake zaune a gaban kotun. Gabaki daya mutanen suka mike dan girmamawa ga alkali. Sai bayan da ya zauna, sannan kowa ya koma mazauninsa. Rajistara ya mike ya karanto karar dake kan layi. Karar dake tsakanin hukumar 'yan sanda ta Jiha da 'yan ta'adda biyu Nura tero, da Hali maiki. Shiru ya biyo baya. Sai da alkalin ya gama duba wasu takardu dake gabansa sannan ya dago ya kalli masu laifin. Dukkansu sanannu ne, kuma rikakkun 'yan ta'adda masu kisa. Ya sauke kansa ya yi dan rubutu sannan ya dago ya bada dama ga wakilin 'yan sandan wato furoskito domin ya karanto yadda al'amarin yake.
Furokiton ya mike bayan ya russuna ga mai shari'a ya fara magana kamar haka:..
*Ku ci gaba da bibiyana*
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
```Page 16```
"Ya mai girma mai shari'a, hukumar 'yan sanda ta Jiha tana tuhumar, Nura (tero) da Hali (maiki) da laifin ta'addanci. Karya dokar kasa, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, musayar wuta da jami'an tsaro. Har ma da bindige jami'in dan sanda guda daya Abbas Malik. A lokacin da suka zo kashe wata mai suna Fadwa. ma aikatanmu kuma suna kan kokarinsu na kama ta, kasancewarta mai laifi da ake nema ruwa a jallo, wato Fadwa 'yar gwa-gwarmaya." Ya dasa aya a nan ya koma mazauninsa. Alkali ya ci gaba da rubutun da yake tun lokacin da furoskiton ya fara magana.
Bayan ya kammala ne ya dago ya kalli masu laifin yace "kun ji abun da mai gabatar da kara yake tuhumarku a kai?". Suka ce "eh". Yace "to kun yarda kun aikata duka abinda ake tuhumarku da aikatawa?". Nan ma ba musu suka amsa da "eh".
Nan kana-nun maganganu suka fara tashi kasa-kasa. Kafin alkalin ya dago daga rubutun da yake sai kowa ya kama bakinsa.
Ya koma kallonsu yace "me yasa kuke son kashe mai laifi kamar Fadwa?". Hali ya yi shiru, hakan yasa Nura ya fara magana. "Muma saka mu aka yi". Alkalin ya yi dan gajeren rubutu kana ya dago "wa ya saka ku yin kisan kai?". Kansa tsaye ba ko shakka yace "Shugaba ne". "Wane Shugaba?". "Alhaji Habib Inuwa Shugaba".
Kotu ta kaure da hayaniyar 'yan kallon shari'a inda a nan a take wasu suke fadin "karya ne! Karya ne!". Har sai da alkalin ya buga gudumarsa sannan nutsuwar kotun ta dawo. Ya yi rubutu a takardar dake gabansa ya koma dagowa. "Mene ne alakarku da shi Shugaban?". "Bamu da wata alaka da shi, kawai dai ya kawo mana aiki ne". "Ku din baku da wani aiki sai kisan kai?". Suka yi shiru suna muzurai. Alkalin ya tattara takardun gabansa sannan ya dago ya kalli jama'ar dake kotun yace "an daga sauraren wannan karar zuwa ranar litinin mai zuwa uku ga watan bakwai kenan. Sannan kotu ta bawa hukumar 'yan sanda ta jiha damar zuwa da Shugaba a zama na gaba". Yana gama fadin haka ya mike ya fice. Ya bar kotu da hayaniyar jama'a.
A ranar kam duk jaridun Jihar kusan abinda suka wuni bugawa kenan. "Kutu ta bada damar kamo Shugaba a zo da shi a zamanta na ranar litinin, bisa tuhumar aika 'yan ta'adda su kashe mai laifin nan Fadwa 'yar gwa-gwarmaya. Wanda ya yi sanadiyayyar kashe dan sanda daya". Wannan al'amarin ya razana kowa, inda wasu mutanen suke cewa duk sharri ne. Wasu kuma su ce zai aikata ko dan yadda ta wulakanta 'yarsa, ta yada tsiraicinta a idon duniya bayan ta sace ta. Haka dai mutane suke ta musayar ra'ayi. Da yawansu sun kagu ranar ta zo, su ji me Shugaban zai ce?.
*Gidan Shugaba*
Gidan ya zama tamakar wurin zaman makoki. Su da suka saba da yin rayuwa mai dadi da yin abinda suke so. Yau gasu an tarwatsa su. An dai-daita su. Gidan daga Hajiya Laurat sai Faisal, dukkansu kuma ba wanda yake iya magana zaune kawai suke jugum bakin ciki na cin su. Yau ga su a gida babu Anisa ba Baffa. Babu kuma wanda ya san inda suke. Alhaji Habib kuwa rabonsu da shi tun da ya fita a fusace daga asibiti. Suna cikin haka wayarsa da ya bari a hannunta ta koma yin kara. Mr. Suwat. Shi ne sunan da ya bayyana, wannan kiran kuma shi ne kira na ashirin da biyu da aka yi da layin. Lambar kasar Rasha ce. Hakan yasa ta yanke shawarar daga wayar ta sanar masa mai wayar baya nan. Ta kai hannunta ta yi receive tare da kangawa a kunnenta. Sai dai kafin ta yi magana aka fara daga dayan bangaren a dan fusace a cikin harshen turanci.
"Haba, haba mana Abib. Har yaushe zaka saka ni in yi ta jira? Shi ne ina kiran wayar ma baka dagawa ko? Kaga in dai babu yarinyar nan a kasa kawai ka dawo min da kudina, na gaji da jira". Hajiya Laurat da zuciyarta ke neman bugawa ta daure tayi magana, ita ma da harshen turancin tace "mai wayar baya gida". Mr. Suwat ba kunya yace "idan ya zo ki gaya masa in ba kaya ya bani kudina". Ya kashe wayar ransa a bace. Hankalinta ya yi masifar