Showing 3001 words to 6000 words out of 37846 words

Chapter 2 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt

25 Oct 2025

365

da kuma amfani da kayan kwalliya. Al'amarin da ya yi matukar daure kan daliban. Basu kara tsurewa ba sai lokacin da aka tilasta su yin ado, suka saka wasu dangalallun kaya masu kama da tsirara. Aka dauke su hotuna. Da wadan-nan hotunan aka tallata su a kasuwar kana-nan 'yan mata masu budurci a jiki. Nan da nan aka fara zuba daloli a kan su. Basuda labari ana can ana cinikinsu kamar wata haja. Bayan an karbi kudadensu ne aka debo su, aka danka ko wace a hannun wanda ya biya kudi mafi daraja a kanta.

Nan fa hankulan 'yan matan suka yi mummunan tashi. Babu yadda suka iya, a wannan ranar aka raba dukkaninsu da rigunan budurcinsu. Bala'i wanda ba a sa mishi rana. Tabbas wannan ranar ta zama bakar rana wadda har abada ba zata kau daga idon Fadwa ba. Wasu a matsayin karuwai aka bada su haya, wasun su kuma duka aka siye su kamar bayi. Fadwa tana cikin wadanda aka siyar duka. An kuma saida ta ne ga wani busashshen bature mai suna James. James bisa manufa biyu ya sayi Fadwa, wato ya biya bukatar kansa kuma ya yi kasuwanci da ita. Wannan ne yasa ta sha wahala sosai a wannan takin. Ta zama baiwa ta gasken-gaske. James yana cikin jinsin jarababbin mazajen nan da basa gajiya da mata. Kusan ko wane lokaci yana tare da ita. Zai iya amfani da ita sau biyar ko shida a rana daya. A hakan kuma zai tura ta biyawa wasu tasu bukatar ya karbi kudi.















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________







```Gare ki 'yar Uwa ta gari``` *Ama Alh. Kabir* ```Nasmat tana yin ki sweet Sis Allah ya raya mana zuri'a```








```page 4```








Rayuwa ta yi wa Fadwa zafi, ko kadan bata samun hutu. Sun maida ita tamkar sex machine. Nan da nan ta ra-rake ta dawo kamar wata babbar mace.


*Bayan shekaru Uku*
Tun tana cikin firgici da tsoro har ta gaji ta bada kai. Ta zama cikakkiyar karuwa, wadda take ji babu wata macen da zata iya yi mata tunkaho game da juriyar aiki. Ta zama kwararriya wajen sarrafa maza da iya amfani da kwayoyin kara kuzari, da magun-gunan mata na karin ni'ima da juriyar sex. Haka turawa suka ci gaba da jagwal-gwalo da ita. Ta sake sosai har ma tana karawa da gyaran jiki. Kamar yadda yake kasancewa ga sauran wadan-da ake kaiwa irin wannan wajen.


Ta fara fadawa shaye-shaye dan ragewa kanta damuwa da yawan tunanin Ummynta. Wadda kullum take kwana take tashi da tunaninta. Babu shakka Fadwa ta bautu ta kuma ci kwa-kwarta kafin ta saba din. Daga baya kuma ta fara kasawa.


*Bayan wasu hekarun uku.*
Sai ta tsinci kanta a wani yanayi na yawan yin mafarki da Ummynta. Tana yi mata fada da gargadi a kan ta gaggauta barin rayuwar da take. Koda zata mutu ne to ta mutu a kan hanyarta ta komawa gida Najeri. Nan fa hankali Fadwa ya fara komawa gida. Ta fara shiri cikin sirri da kwarewarta. Satar hanya ta fara yiwa mai gidanta James tana kula wasu mazan ta gefe tana karbar kudin. Ta bude asu-sun ajiya (bank account). Ta fara ajiye kudinta, kafin ka ce me Fadwa ta tara biliyoyin kudi. To a hankali kuma a sirrance ta yi passport (visa) ta fara shirin biyan kudin jirgi zuwa Najeriya.


Cikin wannan yunkurin ne asirinta ya tonu. James ya gano shirinta na son guje masa. Nan fa ya rikice ya kuma sauya mata. Ba imani balle tausayi ya shiga azabtar da ita. Ya hanata fita ko'ina. Daga gidanshi sai gidanshi. Ya saka ta aiki ya kuma yi amfani da ita. Duk lokacin da zai fita kuma sai ya kulle ta a gida. Haka ta shafe watanni biyu babu mafita. Ga mafarkin Ummynta sai kara matsanta mata yake. Ta matsa mata ta je gareta ko ta halin ya'ya.


Rayuwa ta yi tsanani, ta fara tunanin bin umarnin Ummy ta fita ko da James zai kashe ta. Wata ranar lahadi da safe James ya tafi Church wajen ibadarsa kamar yanda ya saba. Ita kuwa sai ta fara shirin barin gidan kafin lokacin dawowarsa duk da gidan yana kulle ne.


Tana cikin tunanin ne Jack ya bude gidan ya shigo. Jack abokin James ne na kud da kud. Shi kadai yake da makullan gidan James saboda amintar su, kuma shima ba aure ne da shi ba. Ya kan yi amfani da wadan-nan ranakun ya zo gurin Fadwa a wasu lokutan. Ya biya bukatarsa da ita.


Fadwa na ganinsa ta shiga farin ciki sabanin sauran lokuta da yake zuwa gareta. Ta tarbi Jack cikin murna ta bashi hadin kai, irin yadda bai taba samu ba. Sosai ta gajiyar da Jack sannan ta zare jikinta, ta bar shi zube a kan gado ta fada bayi na sashenta ta yo wanka. Sauri-sauri ta gama shirinta, ta tattaro kayan da take bukata, ciki hadda passport dinta. Da sanda ta lallaba ta yi ficewarta. Ta bar Jack can zube kamar kayan wanki.

Lokaci mai tsayin gaske ta dauka wajen fafutukar tafiyar ta'ta. Kasancewar bata shirya komai ba. Jirgin ma sai a lokacin ta nema. Hakan ya sa bata tafi ba sai karfe shida na yamma jirgin ya tashi.


Wohoho wannan ranar kam ku zo ku ga yadda murna da bakin ciki suke haduwa wa mutum daya a lokaci daya. Murmushi take a cikin jirgin kuma tana kuka. Cikin dare suka sauka birnin Kano. Bayan cire rai na shekaru shida, gashi ta dawo garin haihuwarta. Ta lumshe ido a hankali ta shaki daddadar iskar mahaifarta. Ta taki kasar da dukkan karfinta, zuciya cike da bururruka dabam-daban.


Babban abinda ya tashi hankalinta shi ne ganin Shugaba Habib a sahun masu jiran jirgin zuwa Holland. Yana tare da wasu 'yan mata goma sha daya. Sai murna suke suna zumudin barin kasarsu da nufin samo ci gaba.


A take abubuwan da suka shude suka fara dawo mata. Ta tuna da wan-can ranar. Ranar da ta kusa zamar mata ganin karshe ga Jihar Kano.


Ranar da ta zamo sila ga tarwatsewar shiryayyar rayuwarta. Ga kuma wannan azzalumin tsohon da ya yi mummunar illa ga maraicinta. A lokacin ta fahimci wannan ita ce sana'arsa. Fataucin mata, saka su karuwanci da kuma saida su tamkar bayi. A ranar ta sha kuka bayan ta yi kokarin boye kanta ga Alh. Habib tana kallo har jirginsu ya tashi. Inda ita kuma ta nemi taxi ta shiga zuwa babban gidan marayun, inda ya zama gida gareta. Kuka take sosai a cikin taxi din, tana takaicin yadda ta bar gidan tana cikakkiyar mace, yau gashi ta dawo cikakkiyar karuwa. Tausayin kanta ya kara kama ta. Ta tuna nasihohi da jan kunnen da Ummynta ta yi mata kafin tafiyar. Sai ta koma rushewa da kuka. Haka dai ta kasance har zuwa lokacin da mai taxi din ya shaida mata ya kawo ta inda ta bukata. Ta sauka ta kuma fidda kayanta. A lokacin babu kudin Najeriya a hannunta, dollars ta cire ta bashi ya karba yana murna ya tafi. Ita kuwa ta ja akwatin tana taku dakyar kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi gate din gidan nasu cikin matsanancin kuka...















*Nasmat* ✍

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





*Godiya ta musamman ga masu nuna so da kokarin bibiyar labarin 'YAR GWA-WAGWARMAYA babu shakka kulawarku ita take karawa Nasmat kwarin guiwa a dukakkanin al'amuranta. Na yarda babu kamar MASOYI a rayuwa. Ku ci gaba da so na, nima nan mai son ku ce* ```one love``` 😍









```page 5```












Tana da'da nufar kofar kukanta na kara tsananta. Wannan ne yasa mai gadin gidan fitowa da torchlight dinsa mai dogon haske. Ya dalla mata ita daga nesa tun kafin ta karaso inda yake, ya tambaye ta "wace ce wannan?". Cikin kukan ta bashi amsa, dan ta shaidi dattijon tace "Baba nice. 'Yarka ce Fadwan Ummy". "Fadwa?!". Baba Ilu ya tambaya cikin tsananin firgici. "Fadwa mutum ko fatalwa? Domin mu dai wadda muke da ita a nan Allah ya yi mata rasuwa." Fadwa ta koma fashewa da kuka "Baba nice fa, yaushe kuka sami wata Fadwa bayan ni? Yaushe kuka maida ni matacciya?". Ta yi masa tambayoyin da karfi cikin matukar mamaki.


Dattijon ya karasa fitowa daga gate din ya nufo ta, cikin tsananin mamaki. Yana mai kara haska fuskarta da fitilar hannunsa. Tabbas Fadwa ce. "Ya Allah!". Baba Ilu ya fada kana damki hannunta ya ruga cikin gidan, yana kwalla kiran sunayen iyaye da shugabannin gidan yana cewa "ku fito! Ku fito ga 'yar Amina ta dawo bata mutu ba. Ku zo, ku ga abin al ajabi ga Fadwa ta dawo a raye, wallahi bata mutu ba."

Maganganun Baba sun kara ma Fadwa duhun kai. Kenan ce musu aka yi ta mutu?


Kafin kace me mutane sun cika tsakar gidan, yara da manya. Tsofaffi da ma'aikata. Cikin masu son yin arba da Fadwa hadda Ummynta wadda ta kwashe fiye da shekara tana fama da ciwo, na hakurin rashin Fadwa da ta kasa yi. Tun bayan lokacin da labarin mutuwarta ya riske su.


Saboda hasken da yake kewaye da tsakar gidan kowa na iya ganinta, wanda babu makawa sun tabbata ita ce. Sai ko canji na jiki da girma da ta kara yi. Ummy ta fashe da kuka ta ruga ga Fadwa ta rungume ta. "Fadwa 'yata. Dama kina nan baki mutuba? Meya same ki 'yata? Sun ce mana kin mutu. Fadwa sun saka ni kukan da ban taba yi ba. Ashe baki mutu ba 'yata." Ta koma fashe da kuka ta kankame ta jikinta. Haka iyayen suka yi ta shafa fuskar Fadwa suna mamakin ganinta a raye. Daga karshe suka zarce zuwa ofishin shugaban gidan, wanda dama yana cikin ayarin da suka taru ganinta. Shi kuma ya bukaci su bishi zuwa ofishinsa. A can ne bayan kowa ya nutsu suka bawa Fadwa labarin yadda suka sami labarin mutuwarta a bakin Shugaba, Alh. Habib kenan. Wanda suke yiwa kallon Uba ga marayu da marasa karfi. Har ma suka dora mata da gagarumin tallafin da ya basu.


Bayan shugaban gidan ya kai aya ne, ita kuma ta fara basu labarinta tun daga tafiya har dawowarta bata boye musu komai ba. Ciki har da karuwanci da aka tilasta su yi, da kuma shaye-shayen da ta fada yi.


Hayaniya da koke-koke suka kaure a ofishin. Masu kuka na yi, masu jifar Alh. Habib da tsinuwa suna yi. Tsananin tausayin marainiyar ya kara kama su. A ranar su kam suka yarda da duk bayananta, suka sanya Alh. Habib a layin azzalumai masu ha'intar kasarsu da rigar karya. Ta kuma shaida musu har yanzu bai daina dibar 'ya yan talakawa yana kaiwa kasashen ketare ba. Ta gaya musu ta ganshi yau din-nan ya fita da wasu zuwa kasar Holland.


Ranar kam kowa a gidan sai da ya yi kwanan bakin ciki. Washe gari suka maka Alh. Habib kotu dan nemawa 'ya ya mata 'yanci da kuma nufin dakatar da shi daga wannan kazamar harkallar. Tsoro da firgici suka dirarwa Alh. Habib a lokacin da ya sami labarin wai wata daga cikin 'yan matan da ya fitar waje ta dawo har ma jagororin gidan marayun da take sun saka shi kotu. Sun ce asirinsa ya tonu yarinyar da ya ce musu ta mutu ta dawo gida bayan shekaru shida. Ta bar gida tana nutsatstsiyar budurwa ta dawo musu a rikakkiyar karuwa.


Hankalinsa ya yi mummunan tashi a ranar, sam bai tsaya yin cinikin yaran da ya tafi da su ba. Ajiye su kawai ya yi ya dawo Najeriya. Da saukarsa ya gayyato manya kuma kwararrun lauyoyinsa suka hadu a wani gidan gonarsa. Ya gaya musu cewa shi bai san komai ba game da zargin da suke masa, ba mamaki 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar dan ta bata masa suna. Ya umarce su da su yi, duk abinda ya kamata su lalata wannan case din. Dukkansu sun yarda da zancensa kasancewar duk kusancinsu da shi basu taba ji ko ganin wata alama da ta kusanta shi da wannan ba.


Haka aka fara gwa-gwarmayar shari'a. Shari'ar da ta dauki hankulan dubannin 'yan kasa. Wadan-da da yawan su sun fi yarda da maganar lauyoyin Alh. Da suka ce 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar don ganin sun bata mishi suna.


Shari'a ta yi zafi, shaidannu sun bayyana cewa duk abinda Fadwa ta fada karya ne. Burinta daya, shi ne ta batawa taddijon suna. A cikin shedannunsu kuwa hadda ragowar 'yan matan nan da aka dauke su tare da Fadwa. An zo da su kasar, sun kuma bada shaida kan cewa tun da suka tafi su kam karatu suke. Ga takardunsu nan na ko-wane mataki. Sannan suka bayyana Fadwa a matsayin wadda ta gudu daga inda aka ajiye su, ta tare a wani club ta fara rawa da wokoki. A can ta koyi shaye-shayen miyagun kwayoyi ta kuma kware a fannin karuwanci. Suka ce lokacin da aka fara nemanta kuma sai labari ya zo daga gun da take zaune wai ta mutu.


Domin kwantarwa iyayen rikonta da hankali yasa ba a gaya musu cikakkiyar gaskiyar halinda ta jefa kanta a ciki ba. Wannan shi ne abinda suka sani game da ita.


Duba ga ire-iren wadan-nan shaidannun ne aka yi watsi da karar, tare da wanke wanda ake zargi. A karshe kotu ta daure Fadwa na shekaru uku a gidan kaso, bisa laifin batawa babban mutum kamar Alh. Habib suna.


Wannan shi ne rashin adalcin da ya fara fusata Fadwa, ya fara sauya tunaninta. Ta fara nazari a kan neman mafita. A rayuwarta ta gidan kaso kuwa ta kara samun wayewar rayuwa a cikin masu manyan laifuka. Mata ne daga Jihohi dabam-daban. Wasu laifukansu na kisan kai ne, wasu kuma na ta'addanci a ciki ma har da 'yan fashi da makami. Sune suka kara tunzura ta, suka hure mata kunne kan ta yi duk yadda zata yi wajen ganin ta tona asirin Alh. Habib.


Fadwa ta yarda, ta kuma karbi shawarwarin da abokanin zamanta na gidan kaso suke bata. A haka rayuwarta ta yi ta tafiya a can. Yayin da bakin ciki da kunci suka cika gidan marayu. Har zuwa lokacin da aka yankewa Fadwa ya kare ta fito daga gidan kaso. Zuwa lokacin ciwon Ummynta ya kara tsananta har ta kai bata iya tashi. Saboda bakin cikin da take ciki na halin da Fadwa ta shiga.


Jikin kowa a gidan ya yi sanyi. Sun ja'janta mata, a karshe suka ce ta fita hanyar Alh. Habib ta maida hankali ga gyaran ragowar rayuwar da ta rage mata. Sun tsoratar da ita game da abinda zai iya yi mata idan ta ci gaba da neman tona asirinsa.


Ranar bacci gagarar idonta ya yi. Ga tsananin ciwon Ummy ga bala'in matsin da zuciyarta take mata kan kar ta yarda ta bar maganar nan, ta ci gaba da bibiyarta, har lokacin da zata yi dacen yin nasara a kansa.


Da dai tunanukan suka hadu suka yi mata yawa sai ta saka kuka. A lokacin tana zaune gaban Ummynta wadda take tunanin ta dade da yin bacci. Cikin kukan ta fara magana "yanzu shikenan muna ji muna gani zai ci gaba da bautar da rayuwar 'ya yan bayin Allah marasa karfi? Iyayen da suke samun abinda zasu ci dakyar. Su ciyar da 'ya yansu, su kuma tarbiyantar da su. Su tattare duk abinda suke da shi su basu ilmi. Duk wannan kokarin suna yin shi ne dan buri da fatan ganin yaran nasu sun zama na gari. Su sami ingantacciyar rayuwa. Amma a karshe sune ake maida 'ya yansu karuwai. Ababen kasuwanci? Tir! Ya Allah dubi halin da Ummynna take ciki, duk saboda bakin cikin gurbatacciyar rayuwar da aka jefa ni a ciki. Yanzu haka iyaye zasu kare a wannan kuncin? Allah ka amshi raina, ni dai ba zan iya rayuwa ina kallon wannan azzalumin mutum da ire-irensa a cikin kasata ba tare da na dauki wani mataki a kansu ba. Ba zan iya ba."


Ta kara tsananta kukanta...


Ummy wadda ke sauraren maganganun 'yar ta'ta, ta juyo da dakyar. Ta lalubi hannunta ta damke. Sannan ta kakaro kalmomin sunanta ta hada ta kira ta. Ta amsa murya na rawa, saboda tsabar kukan da take.


Ummyn tace "Fadwa ni kaina ban goyi da bayan hakan ta ci gaba da kasancewa ba...














*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________












```page 6```





Ta ci gaba da cewa.. " 'Yata ke nake jiyewa, bana so wani abu ya same ki. Amma tunda har kika yi wannan tunanin na tabbata zaki zama mai juriya, na san zaki ja'jirce. Na baki dama 'yata. Ki dakatar da Shugaba Habib da masu sana'a irin tasa in dai zaki iya. Ni kuma zan zamana mai sa miki albarka ko bayan raina. Fadwa kin fadi gaskiya iyayen irin wadan-nan yaran bakin ciki ne zai ci gaba da kashe su kamar yanda yake daf da kashe ni. Ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login