Showing 27001 words to 30000 words out of 37846 words

Chapter 10 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt

25 Oct 2025

377

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________











```Page 23```







Cikin tsawa ta katse masa tunani da fadin "ka dakatar da wannan karamin tunanin naka ka saurare ni tukunna. Na san yanzu ta riga ta kare maka kai kanka ka san da hakan, saboda haka nake gargadinka a kan ka tabbatar ka fadawa duniya da kotu gaskiya a tsayuwarka ta gobe gabanta. Ina mai shawartar ka da kar ka yi kokarin yin karya a goben domin ni na riga da na gama shirina. Ko da ka yi karyar na tanadi gaggan hujjojin da zasu tabbatar da gaskiya, saboda haka ka kula. A karshe ina maka albishir cewa gobe ce ranarka ta karshe da duk wani mahaluki zai kalleka da mutunci a ciki da wajen jihar Kano. Karshenka ya zo Shugaba..." Ta kece da dariya tana karasa maganarta "tabbas na fada kuma zan cika burina zai cika."


Alhaji Habib a matukar razane ya fara magana "ke tsinanniya 'yar gidan marasa mutunci, goben da kike cewa ta kare min to ke ce ta karewa baki sani ba. Ke har kin manta da yadda jami'an tsaron jihar nan suke nemanki ruwa a jallo? To ki sani har yanzu ni Alhaji Habib Inuwa Shugaba ne. Kina yin kuskuren bayyana kanki a goben kin zama gawa ko da kuwa a cikin kotun ne. Shashasha mara hankali" ya katse wayar a kufule ya shiga kai komo a dakin yana share gumi. Cike da neman mafita game da wannan masifar da ta tunkaro shi.


*A maitama*
Karfe shida na yamma Ab'ha ya farfado daga nannauyan baccin da ya yi ta dalilin wata fauda dake jikin kyallen da Hameeda da shaka masa. A firgice ya farka yana kokarin tan-tance inda yake. Ganin kansa a cikin dakinsa ya yi matukar girgiza shi. Zumbur ya mike ya bude kofar ya fita yana dube-dube. Babu kowa a falon sai TV dake ta faman aiki ita kadai. Ya dauki remote ya kashe TV sannan ya zarce izuwa dakin Fadwa.

Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga, tana zaune bisa kujerar gaban madubi tana daure gashin kanta da band. Ya ja ya tsaya a jikin kofa yana tunano abubuwan da suka faru da shi. Ya ma rasa ta inda zai fara magana. Shi dai ya san ya dauki Hameeda amma bai sami kaita inda ta bukata ba, ya kuma san ta yafa mishi wani kyalle a fuska. Daga nan kuma bai koma sanin komai ba sai yanzun da ya farka ya ga kanshi a gida.


"Meye ya rage wanda baka gaya min ba kuma Ab'ha? Naga ka yi shiru. Ka fada mana, kana sonta, ka yarda da ita, ba zata iya cutar da kai ba ko?". Tana maganar tana ci gaba da shirin da take. Ya yi kasa da kansa cikin matukar nauyi da jin kunyarta "ki yi hakuri Fadwa ni na dauki so kamar iri daya ne. Ashe abinda ban sani ba shi ne yadda nake ji game da ita daban yadda itama take ji game da ni daban. Na yi nadama Fadwa na kuma bar so bari na har abada. Na yarda soyayyata ta zo a sahu na marasa sa'a a duniya. Domin kuwa shi so daya ne, kuma ita kadai nake yi wa shi. Ta cuce ni ta ci amanata. A yadda ta nuna zata iya kashe ni.." Wasu zafafan hawaye suka biyo bayan kalaman nashi, kafin ya ci gaba "zata iya kashe ni Fadwa, saboda haka yanzu na tsane ta, na tsani duk wani abu da ya shafi so!". Allah sarki Ab'ha tausayinsa ya kama Fadwa shiru ya ratsa na dan lokaci kafin ta nisa tace "shikenan ka manta da ita kawai, ka ga, da ban je da wuri ba da sun lalata duka shirinmu. Nufinsu shi ne su azabtar da kai har sai ka fada musu shirinmu, su san inda nake su kashe mu duka da ni da kai. Amma Allah bai basu iko ba. Ka manta kawai komai ya wuce, na san Allah ba zai taba basu wannan damar ba".

Shiru ya koma ratsa tsakaninsu. Ganin haka yasa ya dago kansa dake kasa yace "na gode da ceton rayuwata da kika yi Fadwa". Murmushi kawai ta yi mishi ya juya zai fita.

"Ab'ha". Ta kira sunanshi, ya juyo yana dubanta tare da fadin " aa Fadwa ki kirani Abba kawai." Sai da ta dan sarara saboda tausayin shi da yanayin yadda ya yi maganar. Sannan ta kauda kanta tace "sorry Abba. Ka kasance cikin shiri gobe komai zai zo karshe". Ya gyada kai alamar ya gamsu sannan ya fice jikinsa a sanyaye.


Bayan ya kammala waya da lauyoyinsa ya koma kan gadonsa ya zauna tare da hada uban tagumi da duka hannayensa biyu, ya ma rasa abin yi. Yana cikin wannan halin wata bakar sakar ta zo masa a rai. Ai ko cikin azama ya daga wayarsa ya kira lambar Acp Sauwam. Har wayar ta yanke ba a daga ba. Ya koma danna kira itama dai kamar zata yanke sannan aka daga da
"Hello".
" Hello Sauwam kana ji na?".
"Ka yi hakuri ba zai sami damar amsa wayar ba yanzu yana meeting".
Aka fada da wata kakkaurar murya.
"Ok idan ya kammala a sanar masa na kira kuma ina neman shi gidana".
"To yallabai".
Dukkaninsu suka kashe wayar.


Karfe takwas na daren Acp Sauwam ya isa gidan Alhaji Habib domin amsa gayyatar da ya yi masa. Bai sha wata wahala wajen shiga gidan ba, kasancewar shi sananne ga dukkan securitys din. Yanayin da ya ga Alhajin ya tabbatar masa cewa yana cikin damuwa. Bayan gajeruwar gaisuwa aka gabatar masa da abin motsa baki. Sai dai bai ci komai ba idonsa na kan Shugaba. Ya fara magana "yallabai kamar kana cikin damuwa, ka kira ni nan ko lfy?". "Lafiyar kenan Sauwam, na tabbata a irin wannan aikin da kuke sam baku can-canci a kiraku jami'an tsaro ba". Asp cikin rashin fahimta ya kalli Alhajin yana neman karin bayani. Shugaba cikin fada-fada yake magana. "Banda lalacewar aikin dan sanda a yau, ta yaya za'a ce mace daya ta gagari ilahirin 'yan sandan dake jihar Kano? Ta sace min 'yata sannan ta watsa video yadda ake tozaratar da ita. Ta koma sace min dana, shima ta sako video yadda ta wulakanta shi ta kashe shi. Har yanzu ban san inda suke ba. Saboda jin dadin duk wannan abin da ta yi ba a kama ta ba yau ta kira waya tana shaida min gobe a tafiyar da zan yi kotu zata kashe ni a bainar jama'a. Wannan shi ne tsaron da kuke bawa kasa?"


Sauwam jikinsa ya yi sanyi, sai yanzu ya fahimci inda maganganun Alhajin suka dosa. Ya gyara zama yana fadin "ka gasgata ni Alhaji har yau muna kan binciki a kan wannan mai laifin. Ina tabbatar maka idonmu-idonta ba zata sha ba. Yaranka kuma da iznin Allah zaka same su cikin koshin lafiya. Ka kwantar da hankalinka babu abinda zai same ka, muna tare da kai. Babu shakka wannan wata dama ce a garemu da zamu sami damar kama ta. Barta ta zo gaben, babu makawa karshen ta'addancinta ne ya zo". Ya mike a fusace ya yi wa Alhajin sallama ya fita, a ransa yana sakawa muddin Fadwa ta bayyana kanta gobe to ko shi ko ita, sai ya tabbata kwato wa 'yan sanda mutuncinsu da take neman zubarwa a idon duniya.


Alhaji Habib ya bi bayansa da wani shu'umin murmushi ya tabbata ya kwanto mata kura, ta zo goben. Mikewa ya yi ya shiga cikin gidansa yana umartar Baffa da Anisa a kan kar su yarda su fita gidan nan balle har wani ya gan su ya san sun kubito daga hannun Fadwa. Yana gama maganar ya wuce sashensa ya barsu da kallon juna cikin wani al'ajabin.






Mugun shiri πŸ€”
Keep following, mu ga me suke shirin yi wa jarumarmu? πŸ˜’



Zan ci gaba.



















*Nasmat* ✍
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

Β©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________






```Page 24```








*Daren lahadi*
Wannan daren ya kasance mai tsayi kuma mai cike da buruka ga mutane masu yawan gaske. Ilahirin jama'ar jihar Kano sun kagu gari ya waye a je kutu, domin su ji me Shugaba zai fada domin kare kansa a gaban kotu? Musamman 'yan siyasa masu ban-bancin ra'ayi. Haka talakawa da suke masa kallon inuwa kuma mafaka ga irinsu. Sun kagu garin ya waye su ga me ake shirin kulla masa? Abin ya yi kamari a zukatansu domin wasu daga cikinsu ji suke kamar zasu iya bada rayukansu domin kare Shugabansu.


Haka bangaren 'yan sanda sun riga sun gama yin kwakkwaran shiri domin ganin sun kauda tarihin wata 'yar gwa-gwarmaya a birnin Dabo. A ganinsu wannan shi kadai zai sa su ci gaba da amsa sunan jami'an tsaro cike da izza. To Fadwa ma ba a barta a baya ba ta gama shirinta tsab, da kuma hada duk wasu ababen da take da tabbacin zata bukata goben a cikin kotu. Duk da cewa abokin aikin nata baya cikin nutsuwarsa, Ab'ha ya kusa rasa tunaninsa duka. Saboda ganin soyayyar da ya shafe shekaru yana tarairaya ta ruguje a rana daya. Ya rasa mafaka ko mafita, shi kansa bai san takamaiman yanayin da zuciyarsa take ciki ba. Ya zama tamkar wani hoto abin jinginewa. Babu um ba um...um. Sai ido da yake binta da su a duk shiga da fitarta.


Hajiya Laurat da yaranta ma a ranar basu bari an barsu a baya ba, domin kuwa su ma sun gama yin shiri tsab dan yakar zalumci da son zuciya irin na Alhajin, sun gama yanke hukunci a matsayinsu na al'uma sun tabbata barin mutum irinsa a sarari ba karamin illa bane ga duka kasa. Duk da suna cikin matsanaciyar damuwa hakan bai hana zukatansu son bayyana gaskiya ba.

A wannan daren mai sarkakiya Alhaji Habib baccinsa ya tika hadda minshari, domin zamansa gogagge kuma masanin siyasa da tuggunta, ya san ya riga ya hadawa Fadwa kashin da ba zata iya rabe shi ba. Wato ya dana mata tarkon da ba zata taba tsallakawa ba. Bisa wannan dalilin ya tattare duk wata damuwa ya yi watsi da ita gefe. Domin dama Fadwa ita ce babbar damuwarsa.


*Washe gari*
Kasancewar ranar litinin ce, yasa zirga-zirga da kai komon jama'a da ababen hawa ta yawaita. Duk da cewa ana tsuga sanyi hakan bai dakile al'uma ga fitowa da sanyin safiyar suna nufatar guraren ayyukansu ba. (Monday) litinin kenan aka ce ko Nasara na tsoronta.


Karfe takwas dai-dai makeken agogon dake manne a bangon barandar kofar shiga high court din ya buga. Dimbin jama'a maza da mata yara da manya sun gama cika wajen har ba masaka tsintsiya. 'Yan jaridu daga kafafen yada labarai iri-iri sun bayyana har sun fara gudanar da ayyukansu. Duk inda ka gifta ji kake suna fadin "masu kallo da saurarenmu kamar yadda kuke ji kuma kuke gani, wato filin babbar kotu ya gama ciki da batsewa da jama'a, masu son ganin yadda wannan murdaddiyar shari'ar zata kaya. Lauyoyi daga ko-wane bangare sun bayyana, yayin da masu laifin ma tuni aka kawo su cikin kotun. Yanzu ya kasance kowa a nan yana dakon isowar Shugaba Alhaji Habib ne da kuma ainihin babban alkali na wannan jihar tamu mai albarka."


Suna cikin wadannan bayanan ne suka jiyo wurin ya kaure da karar jiniya ta motocin jami'an tsaro. Nan da nan mutanen suka fara darewa da kansu suna bada hanya ga jerin gwanon motocin suna wucewa. A filin suka yi farking sannan suka fara dirowa kamar tsinukka suna bin sahu, ko-wannensu dauke da zungureriyar bindiga da hular kwano. Fuskokin nan nasu babu ko annuri. Haka suka yi leshi suka zagaye motar da Alhaji Habib yake cikinta. Acp Sauwam ne a kan gaba cikin gagarumar shiga irinta ma'aikacin da ya shiryawa fita filin daga. Da gudu wani dan sandan ciki ya zo ya bude masa kofar. Cikin mutumcin nan nashi da nuna kamala ya fito daga motar fuskarsa dauke da murmushi. Nan da nan jama'ar dake wajen suka dauki ihu da sowa suna daga mishi hannayensu alamar suna bayansa. Da murmushin nan yake daga musu hannu yana jinjina kai. 'Yan jarudu ko suka yo masa caaa! Da tambayoyi. Ji kake suna "Ranka ya dade me zaka ce game da wannan zargin da ake maka? Dan Allah Alhaji kace wani abu mana. Mutane suna son ji daga gareka". Kowa da irin tambayar da yake jefa masa, sai dai tuni jami'an tsaro suka killace shi ta hanyar saka shi tsakiya suka zagayeshi. Wasu a gaba wasu a baya suna ture mutane suna buda hanya. Bai amsa tambaya ko daya ba har suka shigar da shi cikin kotun. A can ma basu daga suka barshi ba, layi daya aka ware duk na masu bashi tsaro ne, kujerarsa na tsakiya.


Basu jima da shiga ba aka sanar da isowar alkali. Mutane kam ko rabi basu sami shiga ba kotun ta cika. Ganin hayaniyar na wajen ta yi yawa yasa aka yi gaggawar samun mafita ta hanyar jona camera da babban majigi dake make a gaban kotun ta waje, yadda duk wanda yake waje zai iya ganin komai da ake gabatarwa a ciki. Sai da aka tabbatar kotu ta sami nutsuwa sannan aka bude karamar kofar, bayan kowa ya mike tsaye ne alkali ya fito ya zauna a mazauninsa. Sannan kowa ya koma ya zauna. Saida aka fara da gabatar da karar sannan aka gabatar da masu laifin su biyu. Shiru kotun ta yi a lokacin da kan alkalin yake kasa yana gabatar da 'yan rubuce-rubuce a kan wata farar takarda. Sai da ya kammala rubutun sannan ya dago ya bukaci lauyoyin dake dakin su gabatar da kansu. Daya bayan daya lauyoyin Alhaji Habib guda biyar suka gabatar da kansu, sannan daga bisani barrister Bashir Bayo. Ya mike ya gabatar da kansa a matsayin lauya mai kare masu laifin. Al'amarin da ya bawa kowa dake wajen mamaki musamman masu laifin da basu san sun dauka ko wani ya daukar musu lauya ba. Amma saboda jin yace zai kare su ya saka basu musa ba suka yi shiru. Ragowar lauyoyin Alhaji Habib kuwa tuni suka fara kus-kus-kus domin duka sun san Barrister BB kamar yadda ake gaya masa. Lauya ne mai kafiya da dagewa kan abinda yasa gaba. Baya shakka ko tsoron case ko na waye, domin shi din lauya ne mai zaman kansa kuma korarre. Wanda zai iya fafatawa da kowane lauya a fadin duniya. Bayan gajeren rubutun da alkalin ya yi kan bayanan gabatar da kai na lauyoyi ya dago ya fara da tambayar masu laifi a kan waccan maganar da suka fada a zama na farko.


"Kuka ce saka ku aka yi ku kashe mai laifi Fadwa ko?". Dukkansu suka amsa da "eh". "Wa ya saka ku?". Kai tsaye suka kara mai-maita abinda suka fada a baya. "Alhaji Habib Shugaba". Shugaba da yake gogagge ne ya zuba musu ido, yana kada kai cike da alamar mamaki kamar bai taba ganinsu ba. Alkalin ya koma yin rubutu sannan ya dago yace "kotu na bukatar ganin Alhaji Habib a gabanta yanzu".


A tsanake babban mutumin ya mike jami'an tsaro suka rufa masa baya. Cikin takun nan nasa na kasaita da amsa sunansa. Ya isa gaban munbarin tsayuwar ya tsaya yana fuskantar al'umar dake cike da kotun. Kutu ta kaure da maganganun mutanen dake daga mishi hannu. Alkali ya buga gudumarsa domin dawo da nutsuwar kotu. Ai ko duk suka yi tsit! Ya kalli Alhaji Habib yace "Alhaji Habib ko zaka gabatarwa kotu da kanka?".


Alhaji Habib ya gyara tsayuwa. "Da fari dai sunana Alhaji Habib Inuwa. Wanda aka fi sani da Shugaba a bakunan al'uma". alkalin ya koma kallonsa bayan ya rubuta bayaninsa yace "ko ka san wadancan mutanen kuma mene ne alakarka da su?". Sai da ya koma kallonsu a lokacin su kansu shi suke kallo. Sannan ya kau da kansa gefe yace "aa, ban san su ba ya mai shari'a". Alkalin ya koma rubutawa sannan ya kalli lauyoyin yace akwai wanda yake da tambaya ga Alhajin? A bangarensa suka ce aa. Amma bar.BB ya daga hannu alamar zai yi tambaya ga Shugaba. Kotu ta bashi damar yin hakan. Ya mike ya isa gaban Alhaji Habib ya kalle shi da guntun murmushi yace "ranka ya dade kace baka san wadannan mutanen ba?" Alhaji Habib ya amsa da "eh, ban san su ba". Yace "haka ne? To in baka san su ba me yasa zasu tsallake kowa dake jihar nan kai katsaye su ambaci sunanka a matsayin wanda ya basu aikin?". Alhaji Habib ya saki fuska a wayance yace "to lauya, ni a ganina wata manufarsu ce kawai ta kokarin ganin sun bata min suna". "Kenan kana zargin suma wani ne ya turo su domin ganin sun bata maka suna?". "Eh haka nake tsammani". "To yanzu kai wa kake zargi game da hakan?". Ya yi shiru alamar yana dan nazari. "A gaskiya ba zan ce ba, dan ban taba rike kowa da mugun nufi ba, balle in yi tunanin shi yake ramako a kaina". "To ko in haka ne me yasa kace kana zargin wani ya saka su?". Tambayar ta zo masa a ba zata, amma kasancewar sa kwararre wajen iya magana ya yi saurin juyeta "to ka san mai hannu cikin lamuran siyasa baya taba rasa 'yan adawa da magauta". Br.BB ya yi murmushi "amma Alhaji na ji ita wannan 'yar gwa-gwarmaya ta zargeka da cewa kana lalata rayuwar yara mata kana dora su bisa turbar karuwanci, sannan ka fara safararsu daga nan zuwa ko-wace kasa turawa na yin badala da su. Ya abin yake?". Nan da nan yanayin shugaba ya canza, ganin dubannin idanu ne a kansa yasa ya yi gaggawar nemo nutsuwarsa "wannan karya ce kawai mara tushe. Ba ni ba, hatta makiyina bana masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login