Showing 12001 words to 15000 words out of 37846 words
Chapter 5 - Yar gwagwarmaya complete Book by Yar Autar Arkilla.txt
bin gidaje na 'yan uwa da abokaninta har karfe dayan dare ba wani labari mai kama da samunta. Sai suka juya akalar neman zuwa asibitoci da police station. Nan ma shiru a ranar Momy Baffa da Faisal ba wanda ya iya rumtsawa. Gaba daya layukanta a kashe sai kuna suke.
*Mai tama*
Mamaki ne ya kame bakin Fadwa a lokacin da Ab'ha ya isa gidan da Anisa. Farin ciki ya tirnike ta, ta rasa bakin magana ta rasa kalmar furta masa. Wannan wace irin nasara ta fara samu haka? Sai kawai ta rungume shi lokacin da idonta suka kawo kwalla. "Abba kai din na daban ne, wannan wace irin sa'a ce? 'Yar Shugaba a hannunmu? Babu shakka lokaci ya yi da zai dan-dana zafi irin wanda iyaye suke ji game da 'yayan da yake bautar musu ta hanyar safara. Ab'ha ka gama min komai. Fadwa ta jinjina maka. Hakika tarena da kai haske ne, kai fitila e mai haska hanya ga 'yar gwa-gwarmaya. Na gode Abba."
Ab'ha wanda ya kusa fita hayyacinsa yace cikin duburburcewa "bab...ba..komai Fadwa ai yi..wa...kai ne."
Yanayin da ta ji shi ne yasa ta yi hanzarin raba jikinta da na shi. Tana murmushi ta dauki cup na tea ta shige dakinta. Ya zubawa kofar da ta shiga ido, domin har zuwa lokacin bai gama dawowa hayyacinsa ba. Tun da yake a duniya mace bata taba rungumarsa ba. Haka shima bai taba ba. Amma duk da haka sai ya ji Fadwa daban. Bai taba jin kansa a yanayi kamar yadda ya ji shi yau ba. Wannan ne ya kara tabbatar masa hakikanin mazantakarsa. Ya lumshe ido yana kokarin kawar da abin a ransa. Ya juya shima ya shige dakinsa zuciya dauke da abubuwa.
*washe garin*
Hajiya Laurat da yaranta sun kasa jurewa lokacin da suka hadu a gurin cin abinci babu Anisa. Tunanin halin da take ciki yasa kuka ya kwacewa dukansu. Uwar da 'ya yan ba mai rarrashin wani. Shugaba kam ido ya zuba musu cike da rashin fahimta yana tambayarsu "lafiya?". Hajiya ce ta yi masa bayani cikin kuka. "Innalillahi wa inna ilaihi raji-un." Haka ya dinga fada kamar wani mutumin kirki. Jikinsa na bari ya lalubo lambar commissioner of police ya fara rattafa masa. Ya katse ya kira Sauwam shima ya gaya masa. Ya kashe ya nemi gidajen TV nashi da na kasuwa ya gaggaya musu. Nan da nan labari ya bazu cewa "an sace Anisa 'yar gidan Shugaba." Talakawa da al'umar gari suka shiga taya su da addu'ar Allah ya bayyana musu ita. Sai raba hotunanta ake a ko ina. Wanda bai san ta ba ma yau ya san ta.
Shugaba ciwo ya dawo sabo kwanciyar gida ta gagara dole sai asibiti aka kwantar da shi.
*Bayan sati daya*
Faifan video mai ban al'ajabi ya bayyana ya kuma yawaita a Jihar kano da kewayenta. 'Yar gwa-gwarmaya ce ta bayyana kanta a matsayin wadda ta sace matan nan masu zaman kansu, wadanda ta bayyana a matsayin ajiyar Shugaba. A ciki ta nuno fuskokinsu duka inda suke ta kuka suna neman ceto. Sai kum maganar Anisa tace su hutar da kansu da wahalar neman ta domin tana hannunta. Tana kuma yi wa Shugaba albishir da cewa ya shirya kallon videon dillancin 'yarsa nan da sati daya. Inda za'a yi cinikinta a sayar kamar yadda yake saida'ya yan al'uma. Daga karshe a lalata rayuwarta kan idonsa. Duk a cikin video na gaba.
Wannan videon ya haifar da rudani ga dangi da iyayen Anisa. Haka kuma ya haifar da tace nace tsakanin jama'ar gari. Inda wasu daga cikinsu suka fara yarda da gaskiyar Fadwa, wasu kuwa har yau gani suke wasu makiyansa ne suke dauke da nauyinta. Mafi yawan al'uma dai su kan ce Allah ya taimaki mai gaskiya. To fa an jangwalo masu gari. An baza jami'an tsaro a ko-wani filin jirgi da tashoshin mota. Haka a kan tituna awanni ashirin da hudu suke suna binciken duk wanda zai shiga ko zai fita garin Kano, babu kakkautawa.
*Bangaren Fadwa da Ab'ha kuwa*
Zan ci gaba.
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
*Keep following...*
```page 13```
*Bangaren Fadwa da Ab'ha kuwa*
Abinda masu neman nasu basu sani ba shi ne kwanaki hudu kenan da suka fitar da Anisa daga kasar. Fadwa ce ta tafi da ita ta ganyar kasa suka tsallaka ta kasar Niger. Ab'ha kuwa ya tsaya yana kula da matan da suka kamo din nan.
*A kasar Morocco*
Zuciyar Fadwa ta gama dakewa duk wani tausayi na 'ya ya mata bata jinsa a kan Anisa, saboda mugun hali da mummunan aikin mahaifinta. Zaune take bisa wata kasaitacciyar kujera, manyan mutane da suka saba da harkar ta dade da saninsu. Sune ta gayyato mutum uku sai Anisa dake tsugune a tsakiyar su tana rusar kuka.
A hankali Fadwa ta fara magana da harshen turancin England da ya shiga bakinta ya zauna kamar a nan aka yi shi. Tace "budurwa ce fil a leda ba a taba saduwa da ita ba. Ina uzuri maza ku fara tayi. Ba kuma na son tayin wulakanci. Da akwai sharadi kan wannan danyar yarinyar. Duk wanda ya siye ta zai bani dama na daukar video na saduwar farko da za'a yi da ita. Wannan sharadin wanda ya yarda da shi ne kadai zan saidawa hajata."
Ta saka aya tana sararonsu.
Abinka da turawa sai duka suka amince. Aka fara ciniki. Kukan Anisa sai kara tsananta yake. Wannan wane irin tashin hankali ne? Ta yaya hakan zata kasance da ita?. Tana ji tana gani aka kammala cinikinta a gabanta aka zubewa Fadwa kudinta kasa ba check ba. Ta dago da narkakkun idanunta ta zuba su bisa yarinyar, ta fara magana a hankali da harshen hausa. "Tun da nake a duniyata ta farko ban taba yarda da ana safarar mata ba, balle kuma in kai ga yin ta da kaina. Amma sanadin mahaifinki na sani. Kamar yadda kike jin kanki yanzu haka na ji a lokacin da ya saida ni ya karbi kudi. Gashi yau nima na yi. Kuma bana fatan kuma aikatawa, sai dai dakatarwa. Idan Allah ya yi miki tsawon ran da kika koma hannun shi sai ki tambaye shi me yasa ya rasa sana'ar yi sai ta raba 'yaya mata da abinda suka fi so? Wannan shi ne raddina farko ga mahaifinki. Yanzu ne zai fara jin asalin dafin saran 'Yar gwa-gwarmaya".
Tana gama fadin hakan ta mike tace su tafi. Mutumin yayi gaba hannunsa rike da Anisa, wadda jikinta ya yi sanyi mutuka, yayin da tsoro da tashin hankali suka kara kanainaye ta. 'Yar gwa-gwarmaya! Ta mai-maita sunan a ranta, sai kawai ta fashe da kuka. Domin kuwa ta san ta'ta ta kare.
Wani mugun murmushi Fadwa ta saki, sannan ta mike ta bi bayan wanda ya siye tan wato Mr. Mike. Wanda ya tabbatar mata cewa "yanzu-yanzu zai kauda budurcin yarinyar."
Tausayi da imani ranar a gefe Fadwa ta ajiye su. Inda ta saita wayar hannunta tana daukar video yadda Mike ya raba Anisa da budurcinta ta karfi. Tana kuka tana fizge-fizge har ta sume ta fita daga hayyacinta.
A nan Fadwa ta takaita ta bar musu dakin zuciyarta cike da farin cikin da bata taba tsintar kanta a cikinsa ba tun da ta fara gwa-gwarmaya. Hankalinta kwance ta nufo Najeriya inda ta samu ana nemanta ruwa a jallo. Daga boda ta danna layarta ta bata tare da bismilla. Ta kuwa bace bat! Bata bayyana ko ina ba sai a cikin gidanta. Lokacin dare ne sosai Ab'ha ya yi bacci ta leka dakin da matan nan suke suma ta same su suna bacci. Ga abincin darensu nan wanda wasu sun ci wasu kuma basu ci ba. Ta yi murmushi ta rufe su. Sannan ta nufi dakinta. A daren ta tace video nan ta gyara shi ta maida shi faifan CD. Inda ta ci gaba da yin copy-copy nasa tana tarawa har gari ya waye.
Ab'ha ya yi mamakin ganinta ba tare da sanin lokacin da ta shigo ba. Murmushi kawai ta masa ta tambaye shi ya gidan? Ya amsa da "lafiya lau komai normal". Cikin zakuwa ya tambayeta labarin tafiyarta. Ta kwashe duk yadda abubuwa suka tafi fa gaya masa. Kafin ta kama hannunsa suka nufi dakin sarrafe-sarrafensu. Ta kunna video suka fara kallo. Sai a lokacin Fadwa ta dan ji tausayin yarinyar. Sannan a bangare daya zuciyarta ta rage zafi da zogin ciwon abinda wannan azzalumin mutumin ya yi mata.
Ta mike ta nufi dakinta tana tuna Ummynta. Da yadda ciwon abinda ya aikata mata ya zama silar tafiyarta. "Ka shirya mutuwa Shugaba." Ta fada a kausashe lokacin da ta hau media ta fara yada videon. Sannan ta tashi ta fita da sauran CD nan ta watsar a kan hanya, kamar yadda ta yiwa wadan-can. Ta koma gida zuciyarta wasai. Zuwa yanzu ta fara shiryawa mutuwa. Ta san ko da yau Allah ya amshi ranta ta fanshe abinda Alh Habib ya yi mata.
*06:00pm*
Zuwa lokacin ba iya jihar Kano ba, ga baki daya al'umar Najeriya har ma da wajenta sun kalli mummunan videon batsa wanda aka aikata da 'yar Alhaji Habib Inuwa (Shugaba). A ranar gaba daya familyn sai da suka kwana a asibiti. Ranga ranga aka kwashe su a lokacin da suke tsaka da kallon video ko-wannensu ya yake jiki ya fadi sumamme banda Baffa ya rufe kayan kallon nasu da duka har sai da hannayensa suka farfashe.
Shugabanni da masu mukamin gwamnati sun shiga rudu. Sun nunka kudade ga duk wanda ya zo musu da Fadwa ko labarin inda take. Ba dan sun san gaskiyarta ba, kawai dan ta cutar da jigonsu, wanda suke wa kallon adali uban nakasassu. Alhaji Habib kwanansa uku a asibiti bai san inda kansa yake ba. Sabanin Matarsa da 'yayansa maza da tun a ranar suka farfado. Ga 'yan jarida sai zarya suke a asibitocin suna son yin magana da shi. Hankula sun tashi tunani ya jigata. Kwakwalwa ta dauki rudu. Abdul Aziz (Baffa) babban yayan Anisa ya yi magana da 'yan jarida cikin kuka da kunan rai inda ya yi rantsuwa ko za'a kashe shi ne, sai ya kashe Fadwa. Wannan 'yar gwa-gwarmayar yace shi ne ajalinta. Faisal kam banda kuka ba abunda yake tun da ya dawo hayyacinsa.
Tun a ranar Baffa ya mallaki bindiga da harsasai ba adadi. Ya hana kansa sukuni ya koma kamar wani zararre. Ba abinda yake sai yawo a cikin garin ko-wane bangare bi yake, ba tare da ya san inda zai ganta ba. Haka dare ya riske shi, dole ba dan ya so ba ya kama hanyar asibitin da Abbansu yake.
Sai dai kafin ya kai ga isa asibitin shima ya fada tarkon 'yar gwa-gwarmaya. Fadwa cikin shigar nan tata ta dare as usual. Ta tare hanya a matsayin jami'ar tsaro ta cafke shi da laifin mallakar makami ba bisa ka'ida ba. Sannan ta nufi gidanta da shi a madadin ofishin 'yan sanda. A ransa yana mamakin wannan jami'ar tsaron da ba a iya ganin fuskarta. Bangare daya kuma cewa yake ko ma wace ce su je. Ya san ai dole za'a sake shi ne.
π€ Babbar magana.
*Keep following...*
*Nasmat* β
ππππππππππ
*'YAR GWA-GWARMAYA.*
(Fitilar 'yan-cin mata.)
ππππππππππ
π¨π»βπ»π©π»βπ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
ββWΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£β.
_____________________________________
Β©
'Yar mutan
Arkillaβ
____________
```page 14```
Ranar litinin da sassafe aka tashi da rudanin rashin ganin Baffa. "Wannan wane irin al'amari ne? Alhaji me ka tarewa yarinyar nan ne? Don Allah ka taimake ni ban ga Baffa ba. Kar ace shima ta raba ni da shi". Hajiya Laurat ce mai wadannan maganganun cikin kuka tana zune gaban gadon da Alhaji Habib yake kai. Hankalinsa ya koma tashi, kamar wanda aka tsikara haka ya mike zumbur ya tashi daga gadon asibitin yana mai fiz-fizge robar karin ruwa dake makale a hannunsa.
"Wace irin magana kike haka, ina Baffan ya tafi?". Cikin matsanancin kuka tace "ban sani ba, shima dai fita yayi tun safiyar jiya bamu koma sa shi a ido ba".
"Haba inah! Abin ya isa haka kuma, wallahi ba wanda ya isa ya ga bayana ni Habib, sai dai mu ga bayan juna. Kamar ni za..." Karar wayarsa dake ajiye a gefen gadon da ya tashi, ita ce ta katse shi. Hajiya Laurat ta dauko da sauri ta duba ko zata ga sunan danta. Amma sai ta ga (null) boyayyiyar lamba. Hannunta na rawa ta mika masa. Ya karba yana ganin number ya gaggauta danna receive.
Kaifin ta yi magana shi ne ya fara. "Ke "yar gidan marasa mutunci, ina dana yake?". Fadwa ta lumshe lumsassun idonta fuskarta dauke da murmushi. Amma a kasan zuciyarta ta ji zafin zagin da ya dannawa iyayenta. Sai dai yanayin tashin hankalin da ta ji shi a ciki ya fi mata komai dadi a duniyar nan. Ta bude idanunta a hankali sannan ta fara magana "gud Alhajina. Na ji dadin da ka yi saurin gano danka yana hannuna. Na tabbata daga yau zaka fara killace kayanka saboda tsoron Fadwa. Ina so ka haddace daga yau duk abinda ka nema baka gani ba ka neme shi a gurin Fadwa. Daga karshe ina maka albishir Shugaba. Lokacin bakin cikinka ya soma. Wutar 'Yar gwa-gwarmaya ta fara cin abinda ka mallaka kenan har zuwa lokacin da zaka bayyanawa duniya asalin gaskiyarka. Dole mutanen nan su san boyayyiyar fuskarka. Na barka lafiya Shugaba... Am... Ka ga na manta fa, danka yace yana gaisheka, ni kuma har yanzu ina kan tunani ne. Idan na gama yanke yaddda zan yi da shi zan gaya maka".
Tana kokarin yanke wayar Hajiya Laurat dake sauraronsu tayi wuf ta fizge wayar ta kanga a kunnenta. Muryarta har rawa take ta fara magana cikin kuka. "Dakata mana 'yar nan, dan Allah ki yi min rai ki dawo min da dana. Na san kema 'ya ce kuma uwa a wata rana, ki tuna abinda ke tsakanin'yaya da iyayensu 'yar nan..." Sai kuka ya kwace mata.
Jin matar na neman karyar mata da zuciya yasa ta katse wayar, sannan ta zube bisa kujerar dake kusa da ita. Ruf! Ta rufe idonta tana maida numfashi. "Hakika duk wanda ya san darajar iya da abinda ke tsakaninsu da 'ya yensu a bayana yake Hajiya. Ki sani saboda wannan kaunar ta iyaye nake fafutuka. Domin sharewa iyayen da ake fandarar musu da 'ya yansu hawaye. Na sani ke uwa ce. Amma mijinki azzalumin uba ne. Kuma na rantse ba zan bar shi ba".
A fili take maganar cikin zafi kamar tana gaban Hajiyar ne. "Mene ne Fadwa?". Ab'ha ya dake gefenta ya tambaya. Bata ce komai ba ta mike ta nufi dakin da ta kulle Baffa a daren jiya.
Shugaba da ya zama kamar zararre ya kalli matarsa dake rike da waya a hannu tana rusa kuka. Yace "ki kwantar da hankalin...". Bai karasa ba ta katse shi "a a, kar ka bata bakinka da lokacinka, ka sani babu wata kalmar rarrashi da zata isarwa uwar da ta rasa danta muddun ba mutuwar Allah ce ta dauke shi ba. Ba zan iya hakura ba Alhaji, kuma hankalina ba zai taba kwanciya a wannan takin ba".
Shugaba kam ya fara rasa tunaninsa sai zare ido yake, ya ma rasa wata kalma da zai koma furta mata. Can ya tsinkayo muryarta ta ci gaba da magana cikin kuka
"Ni wallahi na ma fara zarginka, ina ji a raina wanda aka cuta ne kadai zai iya aikata wadan-nan abubuwa da yarinyar nan take. In ko da laifinka a sanadin lalata rayuwar 'yata ba zan taba yafe maka b..."
Saukar wani mahaukacin mari da ta ji a kuncinta, shi ya hana ta cikata kalmominta. Ta dafe kunci tana kallonsa cike da mamaki da tsoro.
Cikin karfin hali da 'korewa irin ta mai son faranta kansa, ya fara magana cikin masifa. "Lauratu ashe baki da hankali ban sani ba? Ashe za'a wayi gari ki zarge ni da kanki? Tabbas kuwa mace ba adila bace. Duk duniyar nan babu wanda ya san sirrina sama da ke. Babu wanda ya fi ki kusanci da ni. Amma yau da bakinki kike neman yarda da buyagin makiyana. Kike cewa kina zargina... Ya jijjiga kai, cike da alamar tsabar takaici. Sannan ya dora ...to ke da duk mai bi na da sharri Allah ya fi ku".
Ya fizgi jiki ya fice daga dakin a fusace.
Hajiya Laurat jikinta ya yi sanyi sosai. Sai a lokacin take jin lallai bata kyauta ba, soyayyar 'yaya ce kai ta ga barin hayyaci har take kokarin saka zargi ga adalin mijinta. Nan da nan ta shiga istigfari tana tubarwa Allah. Shugaba kuwa wayar ma a hannunta ya bar ta balle ta yi yunkurin kiransa.
Sannu a hankali ta kai hannunta ga handle na kofar ta mirda bayan ta murza key. Jin an bude kofar yasa ya dago da idanunsa da suka gama rinewa ya zuba ma mai shigowar.
Ras! Ya ji gabansa ya yi wani mugun faduwa a lokacin da suka yi ido biyu da ita. Sanye take da doguwar riga dikin gown, ta wani lallausan yadi ja mai ratsin fari. Ba dan-kwali a kanta sai lallausan gashin kanta da ya sha gyara irin na turawa. Kana-nan 'yankunne ne makali a jikin fari kuma kakkyawan kunnenta. Kalar fatarta chocolate ce mai dauke da sirruka. Duk da cewa babu wata kwalliya a fuskar nan ta'ta, amma ba abinda take sai sheki da daukar ido.
Ya kasa kauda idonsa ga barin kallonta, tun da ya mallaki hankalinsa bai taba ganin macen da komai nata ya burge shi farat