Showing 15001 words to 18000 words out of 64206 words
Chapter 6 - HARAMTACCIYAR SOYYAYA Compelet Book by Nafisa Sani Hussein.txt
ganin kirar jikin ki bare wani namiji
Sai alokačin ta tuna cewar nitie ce ajikinta da sauri ta janyo hijabin da take sallah dashi _Hmm niko nace bayan tanaso tai kisan kai daga baya kenan_
Duk yafita hayyacinshi cikin dauriya ya mika mata ledar da yashigo da ita yace gashi kisa caji nasa wani layin Aciki
Tabi ledar da hannu tace kabarshi kawai gobe zanje insiyo wata wayar ya hade rai yace kï karba nace taki yamike tareda karasawa kusa da ita yace take ganin yanda yake kallonta yasa ba Arziki ta kar ba _wai ummu jiddah anji maza_
Tana karba taja da baya yamata kallon relâxed bazan janyoma kaina wata damuwar ba bayan wadda naķe ciki tana kallo cikin tangadï yabude dakin yafita tareda cemata good night yana fita ta danna key a kofar tana Ajiyar zuciya.
Har yakarasa dakinshi yana dafe da mararshi gaba daya yarinyar kashe shi taķe sonyi dole yane moma kanshi mafita don wallahi yana gab da halaka yasamu yasha yan tablet dakyar bacci barawo ya daukeshi
Tabude kwalin wayace mai shegen kyau da kuma tsada wadda hartafi tata haduwa da girma tanata juya wayar don Akalla zatayi dubu dari tayi pluging caji sannan ta kwanta tana ta faman tunanin rigimammenta
Tana tashi da aAsuba ta kunna wayar kafin ta jetayi Alwala tana fitowa tàji karan wayar tasan ko waye don tasan saishi tashare dakiran ta tada sallah har ta idar yana ķan kiranta dole tamike ta daga kiran
Ajiyar zuciya yayi kafin yace next time inkika kuma har dakinki zanzo bana kira aki daga min bare kuma mace kinci Arzikin sonda nake miki but wallahi kika kuma zanbaki mamaki ita kam yanzu ta gane bayan rashin tsoro harda rashin kwakwal wa yake da ita
Yace kinajina ? tace ka gama? Zankwanta bacci bai isheniba , ok inzo muyi tare koke zaki zo nan Nima kwantawa zankuma yi kafin gari yawaye kit takatse kiran don batada Amsa saida ta kuma taba kofarta tajita rufe kafin ta kwanta don sanin zaï aikata....🖊
_shedar mänyan gobe kenan Safeena abi ahankali fa_
[2/19, 2:40 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)
Śtory writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar
💫FAGEN MARUBUTA WRITERS
ASSOCIATION💫
_(gidan zaman lafiya da yarda da juna🤝insha Allah)_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
1⃣3⃣
Da safe kuwa har kusan karfe goma bata fitoba don tanaso sai yabar gidan kafin ta fito ta karya don har aikowa anyï taki ta fito tace bayanzu zata karya ba,
Sageer kuwa tun karfe bakwai yafita saboda kwana biyu baileka office yasan ayyuka na jiranshi sosai shiyasa yafita da wuri,
Koda tafito ba kowa duk sun kama gabansu har Anty Nena ma ta tafi aiki daga ita sai masu aiki data gama karyawa tasamu wuri tafara danna wayarda Sageer yasiyo mata,
Tana kokarin bude wtsp kawai message ýashigo tasan waye harta share saikuma ta bude (hope kintashi lafiya my prety natafi office naso ganinki before in fita amma kina bacci please take care of yourself for me see you soon i love you)
Shiru tayi tana mamakin karfin halin wannan bawan Allah gaskiya ita yanaso yajefata cikin damuwa gashi wani irin mugun sonshi yake shigarta batareda ta shiryaba gaba daya tasa ni cewar itama ta kamu da sonshi,
Yanzu take fahimtar kuskurenda ta tafka narashin tsayawa ta saurari wa inda suke sonta da Abinda keshirin faruwa da ita da bai faruba da kila bazata hadu da shiba har yajefata cikin wannan yanąyin
Sai karfe hudu yasamu yafito daga office zuwa gida duk ya gaji ba abinda yakeso irin yaganshi agida tsabar gajiya drivern office yasa yadawo dashi gida yana shigowa falon duk suna zaune har Aunty Nena da yaran duka
Menal na zaune agefe tana copyn hànd out Safeena na koyawa su Ammar home work yaran naganinshi suka ruga oyoyo bros akasalance yakarasa ķan kujera tareda yaran yana gaida Aunty Nena tãce ya aiki? Yace akwai sosai wallahi har yanzu bangama ba na dawo nekawai,
Tace Allah yataimaka Ameen Anty bari inyi wanka yadan dubi gefen da Safeena take gaba daya tayi kamar batasan dashi Awurin ba nan kuwa duk Hankalinta nakanshi
Menal kuwa ranta ya sosu yanda baiko damu da itaba afalon yanuna ma baisan tana wurinba, kuma agaskiya hankalinshi yatafi wurin pretty
yanda ta dauki wanka da wani doguwar rigar code less lemon green rigar A shape wow takasa kasa yake kallonta jiyake dama tamike yanda źai gänta da kyau,
Saida Anty Nena tayima Menal maganar hada mai Abinci sannän yalura da ita tareda cewa little sis ba magana? Cikin turo baki tareda jin haushi tace to ai kaine baka ko ganni ba.
Yace òh come on little nagaji ne please ki hadamin ruwa zanyi wanka da sauri Safeena ta kalleshi cikin jin wani iri Abin ya sosa mata rai sosai cikin haka message yashigo mata
_(Ko zaki hadamin ruwan ne my pretty ince tabari?)_cikin sauri tadaga kai ta kalleshi yakashe mata ido ta dauke kai tareda kallon Anty ko taga meyayi Amma ita Hankalinta nakan yara suna maganar su
Wani massege yakuma shigowa _muje kitayani wankan baby_ ai kawai mikewa tayi batareda takuma kallon gefen da yakema kirjinta na halbawa tayi daki yayi murmushi sannan yamike dai dai lokacinda Menal tadawo
Tace bros na hada yace tanx sis yana shiga daki ya kirata Awaýa kamar bazata dauka ba har saida takusa tsinkewa _kizo baby na please inason ganinki tayi shiru don batada tacewa yace kinaji na?wallahi yunwa nakeji tun safe banci Abinciba_
Baby! Ki taimaka idan kina kusa ne kawai zansamu natsuwarda zan iya cin Abinci ko inzo dakinki pretty inason ganinki please ta katse kiran yabi wayar da kallo tareda tura mata text
_please my happyness mu hadu ko a garden ne leter_
Ita duk yasata cikin wani yanayi yazatayi da wannan mutum wai ?dole ta takamai birki gaskiya yau
Karfe takwas na dare duk sun gama diner suna zaune Afalon har Alhajin gaba daya Anty Nena lamarin zaman Safeena da dan uwanta yadameta gaskiya yana shiģa hakkin yar mutane dole tayi wani Abu Akai
Suna wurin har Sageer yashigo baiji dadin yanda yasameta Afalon ba ga Auncle yagaida su tareda samun wuri yazauna Suna magana da Alhaji Anty tace Safeena muje daģa ciki
Zamuyi magana, saida gabanta yafadi sannan tamike shima sageer yaji wani iri meye Anty źata fada mata da sai sunshiga ciki
Suna shiga Anty cikin hikima take tanbayarta dakuma nuna mata cewar harda laifinta mijinta ya banzatar da ita cikin dabaru da kuma na siha ta koyamata dabaru da kuma nuna mata yanda zata janyo hankälin megidanta
Har tabata wata hadaddiyar humra tace tariga Amfani da ita idan zataje gurin Alhajin tunda suka wuce yarasa natsuwa saida yaganta duk jikinta asanyaye tashige dakinta tana tunanin mafita
Ta dade azauʼne tana saka da warwara kafin ta mike ta sheko wanka tashafe jikinta da mayuka dakuma turaruka masu kamshi daga karshe tasaka wata guntuwar nitie ta dora dogon hijab akai kafin ta tsaya tana tunanin
Taje ko karta je ?idan taki zuwa Anty zatace bata dauki shawarar taba haka ta janyo kofar tafito Alokacin bakowa haka tafara takawa cikin sanyin jiki zata nufi dakin Alhaji
Batareda ta shiryaba taji anfisgota cikin mugun zafinshi kafin tace me yasata cikin dakinshi cikin muguwar kaduwa da kuma tsoro take kallon yanda jikinshi ke rawa ga idonshi yakada yayi jawur
Duk ta tsure cikin fusata yace ina kike shirin zuwa Safeena? Yafada cikin kidimewa itama cikin kosawa ďa lamarinshi tace dakin mijina zanje cikin hasala yace mezakiyi acan?
Cikin bushewar zuciya tace zanbashi hakkinshi da yakamata inbashi tun farko cikin bugawar zuciya tareda zafin rai yace jikin naki zaki mallakâ mai?
Kafin kace me sai hawaye yafara bin kumatunshi cikin rage murya da kwantarda zuciya yace Safeena please don't wallahi inkin bashi kanki zan iya mutuwa ina kishinki ina bala in kishínki
Meyasa kike kallon idona ki fadamin zakiba wani namiji jikinki Safeena you are mine only please don't ke tawace cikin kasa da murya yakara matsawa kusa da ita zai riketa tace
Karka tabani yace why? Ni bankai namiji bane um look at me Safeena meye nakeyi wanda bakyaso tell me i will stop just tell me duk jikinshi narawa yake fada mata maganaŕ
Ga hawayenda yakeyi da duk yabatatausayi don itama tana sonshi amma yazatayi itafa matar aurece ta yaya zata rika biyemai idanshi idonshi yarufe ita da sauran hankalinta dole tayi controling kanta
Cikin ajiyar zuciya tareda kallon cikin idonta yace kina sona Safeena? Cikin kidima tace ni insoka ina matar aure? No way and please kafita hanyana ka hana ni sakewa
Har addu a nakeyi dama bantaba ganinka ba arayuwata katakurani ka hanani sakewa kabaŕni haka takarasa tana fitarda hawaye cikin sanyin jiki dakuma damuwa yake binta da kallo
Harta gama fadar abinda taga dama yana mata wani irin kallo cikin rashin kuzari yace shikenän jeki amma duk Abinda yasameni kece sanadi yabude mata kofar tafita sannan yakoma ciki tareda fara wasu hawayen masu zafi
Gaba daya bataji dadin kalamanda tafada maiba amma shine kawai mafita ita kanta tasan idan tace bata sonshi tayi karya shine dai dai da ita shiyaka mata ta aura sai yanzu tagane kuskurenta.
Dama Abinda Aunty Zaliha ke kokarin nuna mata kenan? Hmmm.
Washe gari har dare bata sa Sageer a idonta ba tayita sintirin yawo afalo har zuwa waje har wayewar gari duk ta damu saida kowa yafita tayi karfin halin zuwa dakinshi domin taga ko lafiya Amma kofar Arufe wanda ya nuna mata bama ya gidan
Yinin ranar kamar mara lafiya haka tawuni har wani zazzabi yafara shigarta tsabar damuwa da tunã ni koda mutanen gidan suka dawo dakyar tafito cikin dauriya Anty tace lafiya kuwa Safeena ?
Cikin sanyin jiki tace kanta keciwo tamata sannu Menal ma ta mata su Al ameen ma suka mata sannu Aunty
Menal ce tace Aunty bros tunjiya bai kwana agidaba ko yashigo yau? Cikin bugawar zuciya da tsoro tace Aa bai kwanaba? To ina yaje? Cikin zuciyarta take tunani
Wasa wasa har kwana uku shiru saida taji Aunty Nena tana fadama yara dazu ma sun hadu a office tasan cewa itace bayason gani bayan yasa mata sonshi sannan ne zai nemi kaura ce mata gaskiya bazata iya dauka ba
Allah kadai yasan halinda zucyarta take ciki kwana ukun nan dabata ganshiba cikin damuwa tafita garden tana zama tafara bin wayar hannunta da kallo tareda karanta messages dinda yake turomata kafin yayi fushi da ita
_ina kake ne?please come back i realy missed you.i love you too please come back tafada cikin damuwa_
Realy my pretty? Kamar daga sama taji muryarshi tamike akidime tareda kallonshi yana tsaye sanye cikin riga da wandon jeans yayi wani irin kyau, cikin shaukin so da kuma rufewar idanu ta nufeshi tana mai kallon don me zaka shiga hakki na daya wa
Cikin karyewar zuciya tana isa tafara dukan kirjin shi tareda fadin meyasa zakamun haka? Saida ka koyamin sonka sannan zaka juya min baya meyasa ka kaura cewa ganina kwana biyu?kasan halinda ka jefani kuwa?
Sageer why ?takarasa tana mai fashewa da kuka da kuma fadawa cikin faffadan kirjinshi batareda tayi tunanin ai HARAMUN bane tana matar aure soyyaya ta rufe mata ido har tamanta da rashin dacewar hakan
Duk tarukunkumeshi tana gursheken kuka kuma tana kan mai mitan meyasa zaigujeta ?meyasa zai wahalar da zuciyarta haka?
Cikin damuwa dakuma farin ciki yace relaxed my pretty am fine cikin kaďawar ido take kallonshi tana mai wani irin kallo tareda cewa yes i see you are fine, but what About me? Kasan irin halinda ka jefani kuwa ?
Yakuma janyota cikin rashin kuzari tareda mannãta akirjinshi yana shafa bayanta pretty Am sory kece kika nuna bakya sona zaki bama wani jikinki bayan kinsan ke mallakina ce dasauri ya kuma dagota tareda cewa
Pretty kinje dakinshi? Please yatabamin ke tell me? Kifadamin baki bari ya tabamin jikin nan nakiba yana fada yana kare mata kallo baby! Kin san irin halin da nashiga kuwa nima cikin kwana uķun nan
Daurewa kawai nakeyi amma banda wani choice ne bayan hakan kidaina min zancen wani namiji baby zuciyata zata buga inada mugun kishi musamman Akanki.
Bazan daure ganinki awajenshiba banason ganinki kusa dashi pretty shiyasa na daìna zaman gidan nan Amma kinsan bazan taba daina sonki ba sonki yariga yashiga cikin jini na tundaga ranarda nafara dora idona
Akanki
cikin murmushin tsokana yace ranarda nafara ganin Safeena real dinta ranarda ta hana ni bacci baby kinsan aranar nasan inada sha awar kasan cewa da mace baby look at your structure yana me bin jikinta zuwa kugunta da kallo dasauri tayi baya tareda rufe ido tunawa datayi Aranar daga ita sai towel Sageer yaganta
Dagudu tayi cikin gida tana maijin kunyar Abinda tayi Aranar dakuma yau batareda tasaniba tajitayi karo da mutum cikin hanyarta tashigowa falon cikin firgici ta ja da baya ganin wanda ke tsaye yana kuma binta da wani irin kallon da takasa gane me hakan yake nufi?
_Shin yaganta ne Ajikin Sageer ko yaji Abinda suķe cewa? ........_🖊
*SANNU BATA HANA ZUWA FANS MUJE ZUWA*
[2/19, 2:43 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)
💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar
*godiya mara adadi HARAMTACCIYA SOYYAYAR FANS Kunayin yanda yakamata*
_UMMU JIDDAH.. mema zance miki ne kincika masoyiya ta hakika Allah yabar mu tare Yaraya mana JIDDAH_
1⃣4⃣
Duk tarude Abinka da mara gaskiya ya kalleta yace ina zakije haka Safeena kiķe gudu haka?
Hmm Ajiyar zuciya tasauke saboda tagane baigansuba kafin tace wani Abu shima yashigo cikin falon sai takuma tsurewa,
Abinka danamiji sai yawani waske tareda rabewa zai wuce yana cewa sannu Auņcle, yabishi da kallo kafin yace son inason ganinka yanzu,
Yace ok Auncle da sauri ta karasa cikin dakínta tareda dafe kirjinta gudun abinda zai faru kodai Auncle yagansu shiyasa yake kiran Sageer ?
Suna zaune Alhaji mu azzam yakira Aunty Nena Awaya itama tazo duk sun natsu wanda shi Sageer ko Ajikinshi baya shakkar duk Abinda zai faru Ahalin yanzu.
Indai Akan zancenshi da Safeena ne saida Alhaji yace Khadija! tace na am.
Kinsan watan nin baya kafin Sageer yakoma new york nayimai maganar Aure Anan surin ko?
Tace kwarai yaya yace ok zaki tuna meya fadamin Alokacin? Eh yace kayi hakuri har yadawo nija gaba daya. Alhamdulillah yanzu yadawo.
Kuma idan ban mantaba kanada yarinyar da kuke soyyaya da ita cikin tsunkewar zuciya da kuma kaduwa yama kidime yarasa ta cewa.
Saida yakuma cewa inajinka son lokaci yayi da yaka mata ace ka ajiye iyalinkanka yanzu, tsabar rudewã yace ok Auncle zanyi tunani akai kaban kwana biyu ,
Badamuwa amma fa kasani ina nan Akan bakana idan kashirya sai in samu Aminina muje gidan su yarinyar ko ? Cikin dauriya yace na gode Allah yakara daukaka sannan yawuce
Aunty Nena tace yaya kana ganin yarinyar nan yakamata Ahadata da son kuwa? Meyasa kikace hakan ? Saboda naga ita take sónshi ba shike sonta ba
To ke kinganshi da wata yarinyar ne bayan itan? Aa amma yaya anawa tunanin da anbi ahankali ko.
Khadija ku mata lokuta da dama tunaninku sai Ahankali duk cikin maganar da kikayi baki ban wata kwakkwaran hujja ba
Shikanshi da baya sonta zai fàda Amma baice komai ba so kema kiyi shiru kawai, tace shikenan yaya Allah yashige mana gaba Ameen.
Duk wannan maganar da sukeyi Akunnen menal gaba daya hankalinta yatashi bros zai yarda da Auren Humaida?
To ita kuma fa?meyasa dady zai mata haka? Cikin matsanan cin kuka tasan yanzu dadynta zaice tayi karama da Aure Amma ita gaskiya tanason brothern ta
Duk da yanzu tashiga sixteen years amma dayake goyon hutu ce zaka dauķa takai twenty tsabar cikar da takeyi Ayanzu
Ita ta inama zata iya furtawa Sageer wannan zancen tasan ko banza kallonta yakeyi a karamar yarinya bare kuma har ya yarda Ya Aureta
Kuka takeyi irin mai ban tausayin nan gaba daya tarasa wanda zai taimaketa can ta tuna Safeena tamike da sauri zuwa dakinta
Tana kwance tun lokacinda tashigo dakin tana faman tunanin ya akayi ta kasa controling kanta ne wai har tabari yafahimci itama takamu
Hartakaita ga rungumeshi tafara istigifari cikin zuciyarta tana tuna yanayin datashiga lokacinda tafada cikin kirjinshi
Jitąyi kamar anyi mata rahama gabadaya taji kamar batada wata sauran damuwa Arayuwarta Hmm ta sauke Ajiyar zuciya mai sanyì tana cikin hakan
Menal tafado dakin cikin kuka tareda fadawa kan jikinta saida taji tsoro don bataji shigowarta ba cikin kidima tace Menal lafiya?
Meya sameki? Cikin kuka tace Aunty bros zaiyi Aure🙆♀ dum kirjin Safeena yabuga da karfi cikin firgici dakuma mugun tsoro tace bangane ba kimin bayani please
Cikin kukan take gaya mata komai Ai tashin hankalinda tashiga na Menal wasa ne kafin kace me itama sai kuka tareda rungume Menal
Kukan da Safeena keyi shiyasa Menal tayi shiru cikin matukar mamaki take kallonta tareda sakin baki tasan dai wannan ba kukan tausayinta take ba,
Gaba daya tamanta da wata Menal tausayin kanta takeji tunda Gwara Menal tana da hope Amma ita fa? Menal zata iya Auren Sageer ko A yau Amma ita fa?matar Aure ce da igiyoyin wani Akanta
Saida Menal ta dafa ta tareda cewa Aunty lafiya ? Sannan ta saita kanta tareda saurin wayin cewa tace natausaya miki ne Menal,
Cikin dauriya tace kiyi hakuri hakan bazai yuwuba ma bazai Aureta ba kinji ki daina kuka cikin mamaki tace Aunty Aini nayi shiru Amma ke mezai saki kuka har haka?
Tace banason ganin kukanki ne shiyasa tace ni ai nayi shiru kema kiyi shiru haka nan tana share mata hawaye _tofa wata sabuwa_
Aranar mutum uku sunkwana cikin damuwa ko barci barawo saida yabar Sageer da Safeena Menal dai ita ta runtsa Abinta tunda Auntyn ta tabata hope
Tunda sassafe yafita Agidan sai gidansu Yusuf shima saida yatsorata don rabonda su hadu tun Asibiti dasuka rabu da fada Akan me zai kira mai Humaida shikuma yace yayi saboda gujê mai fadawa halaka
Kuma koyanzu shiyazuga Auncle Akan zancen Auren Amma bai mai baýani bã kawai yafada mai yana soyyaya dawata baturiya don haka gwara Auncle