Showing 9001 words to 12000 words out of 64206 words
Chapter 4 - HARAMTACCIYAR SOYYAYA Compelet Book by Nafisa Sani Hussein.txt
Safeenar yana gani yasän sistern tace .
Yasamu kanshida ajiyar zuciya yakumayi river da motar har yabar layin Anty zaliha bata ganshiba Amma ita Safeena tasan yana binta .
Harta koma gida tana mamakin wai me gayen nan ke nufi da ita ne haka saikace shine mijinta?
Ko mijinda aka aura mata baruwanshi da ita saishi can ta janyo jakarta tareda bude ledarda Anty zaliha tabata wai tasha Hmm ita batasan mijin ko kallo bata isheshiba Hmmm. Bare ayi zancen tasha ķayan harka tab ita bama zata iya shasuba koda mijin yakulata bare ba daya,
Haka ta tattarasu ta tura durowa tarufe ,
Shikuwa Sageer ba abinda yake tunani irin meya hadata da wannan gayenda takema fara a jiyayi kawai yana bukatar Amsarta kuma yanzu tafadamai kawai ko zai îya bacci yau.
Yamike yadaga labulen dakinshi tareda leka harabar garden din acan ya hangota tana waya tareda murmushi mai tsayawa azuciya yasaki labulen yafita da sauri
Batasan da zuwanshiba kawai jitayi anfisge wayař tareda bugatada kasa .........🖊opps
*me sageer yakeyi haka saikace matarshi?Hmmmm*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
Maman Ammar
💫
*FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION* 💫
_idan nace godiya to nayi kadan saidai ince Allah yabar kauna da Amana kinsan bawata saike FIRDAUSI MUHMD MAINASARA wato marubuciyar bamu dace ba_
*tareda ke DOCTER ASHAM marubuciyar makirin zama kunyi komai Allah yabar kauna da Amana ina mugun yinku*
8⃣
Wayar tabi da ido tsabar mamàkin shi don tasan saishi don tariga yanzu tafara fahimtar baya kaunarta da zaman lafiya.
Cikin zafin zuciya ta mike tareda mai mugun kallo wai meke damunka? Yace tanbayana kikeyi? dawaye kike waya? Oh wannan katon ne dana ganku tare shine yakira kike mai irin wannan dariyar ko?
Ita ai imani cika mata ciki yayi tamakasa cewa komai tãce yes ko ban isa bane? Amma kinsan ke matar aure ce ko. Kwarai kuwa shiyasa nakeson kafita hanyata saboda bakai nake aureba.
Saida zuciyarshi takusa fitowa da yatuna ita matar Auncle dinshi ce wai meke damuna ne? Har yajuya zai tafi yakuma dawowa wayeshi? wai me kake nufine dawayeshi kai ubana ne ko mijina?
Yaruntse idoñshi đon yatsani yaji tana fadar wai mijinta. Ya ce look just tell me who the hell is he cikin tsawa yake mata magana harsaida tafirgita wanda har yajanyo hankalin Menal dake fitowa daga cikin falon zata fita dasaurinta ta isa wurin alokacin har yasa hannu zai janyota.
Menal tace bros meke faruwa yayi saurin juyowa tareda barin wurin batareda yakuma cewa komai ba. Sai Alokacin Menal ta kalli Safeena tace why did you hurt him i no my bros baya shiga harkar kowa .
Cikin zafin abinda yamata tace hey just shut up ok and get the hell out of my side cikin fushi ai nan Menal taji takara tsanar matar dadyn nata nafarko tabatã ma ruhinta rai nabiyu kuma tamata tsawa how there she? Shout at her like this.
Karfe takwas nadare yana kwance agadonshi ba abinda yakeyi sai tunanin ta dakuma tunanin waye suke waya shifa hankalinshi yaki kwanciya baisan meyasa ba wai yaushe nazama haka ne ? Wannan yarinyar gab takeda ta haukatañi ina gab darasa natsuwata Ahnkali yafurta why did you comé in tõ my life? gaba daya jiyake kamar bashiba shi rayuwarshi tada da mutane ke ganin baya cikin walwala tafimai wannan rayuwar.
Yadafe saitin zuciyarshi so yake yataushi zuciyarshi tacire mai tunaninta Amma ina abin yafi karfinšhi. He need some one to talk to tunanin Yusuf wato Aminin shi yafado mai da sauri ya dauki waya tareda dialing numbanshi.
Yusuf nadauka yafara fada haba dude saunawa nakiraka yau no respond meke damunka ne? me i dnt understand you this time.yabude baki cikin slow yace mai nikaina bansan meke damuna ba plss help me plss dude cikin tashin hankali Yusuf yace subuhanallah kana ina ne yanzu? gida. Ok am coming yakatse wayar.
Koda Yusuf yashigo baimasan inda yakeba don gaba daya numfashinshi fita yake da karfi cikin tashin hankali yakarasa bakin gâdon tareda furta meke damunka haka dude cikin dauriya irin ta maza yace itace.
Wacece? Safeena yafada cikin fisgar magana, wacece Safeena? Dude ina sonta kishinta zai kasheni ina kishinta meyasa? Why why why? Dude idan naci gaba dazama Anan gidan zan iya mutuwa help me please gaba daya Yusuf yarude donshi baima fahimci zancen ba.
Yace Sageer please kamun bayani yanda zan fahimta yace bani drinks mai sanyi a firij please yamike yakawo mai yakafa kai saida yasha rabi sannan ya ajiýe a gefen side drower Hmmm yayi ajiyar zuciya.
Cikin natsuwa yafaraba Yusuf labari har yakai karshe cikin kidima yusuf yadafe kai tareda cewa Dude nasan ba laifinka bane bakai kasama kanka soyayyar ta azuciyarka ba haka Aĺlah yaso Amma kasan wannan HARAMTACCIYAR SOYYAYA ce tunda matar aure ce kuma matar Auncle mutumin da yama komai Arayuwa.
Yace nasani Yusuf i tried to forget her but i cnt i realy lõve her i love her somuch help me please gaba daya jinake duk soyyayar danake mata ba laifi bana ganin HARAMCIN SOYYAYR
da nake mata gabadaya jina nake idan ban kasance da itaba zan iya rasa rayuwata ko kuma hanka lina.
Gaba daya tsoro yacika Yusuf yana mamakin Abokin nashi dan baitama tunanin zai iya yin haka ba soyyaya tarufe mai ido gaba daya har tanaso tasashi a muguwar hanya.
Yusuf yace looķ Dude kayi kokarin fita hanyar yarinyar nan. Ina shî gaba daya he lost his mind saboda tsabar kishi yace kasan meyafi bata min rai? I saw her with some body.
I even ask her she refused to tell me why tasan yana keji kuwa akanta? What hurt me the must she hate me she dont have feelings for me.
da abin mamaki yakeba Yusuf amma yanxu yafara bashi tausayi wai Sageer ne da ko lokacin da suke school baruwanshida yan mata shine yakamuda soyyayr mace kuma matar Aure.
Duk ko da irin farin jinishi da yanda yan mata kesonshi hmmm.
Yana wannan tunanin yaga gaba daya numfashinshi yafarã fisgarshi irin yana gab da fita da gudu yaduro yafito falon don neman ceto da Safeena yafara karo yana ganinta yasan itace matarda keson illata mai aboki cikin sauri yace plsease Sageer call Aunty Nena.
Cikin tashin hankali tace meyasa meshi don ta tuna yanda taganshi da safe aiko sauraren Yusuf batayiba tafada dakin derect wurinshi tanufa bata tsaya tunanin komai ba ta sa hannu tadago kanshi tareda dorwa saman cinyarta takuma rike hannunshi.
Jin kamshin turaranta da kuma jin lallausan hannuta acikin nashi yasa yabude idonshi dasuka kada yana kallon cikin idonta tareda kare tamke hannun cikin nashi Ahnkali numfashin shi ke dai daita.
Ahankali yafurta waýeshi? tace u are seek please just keep quit. Yace i cant tell me kina sonshine? Meýasa kika Auri Auncle ? Meyasa kike sa kaya irin wannan? Da sauri yatashi tareda kallon ta don ko yanzu doguwar rigar baccine ajikinta sai net akanta dakuma zani data daura akai amma tamai mugun kyau haŕ yasauke idonshi akirjinta da suka kunburo kamar sufito itakam hankalinta duk yatashi batamasan kare mata kallo yajeyiba.
Saida yakuma cewa kirika sa hijab ko falo zaki fito sannan tadawo hankalinta takuma tuna bai dace ba itafa matar wanice yazata damu da wani namiji har take täbashi tayi istigi fari tasauke kanshi tamike amma yaki sakin hannunta.
Ahaka Yusuf yashigo saida gabanshi yafadi ganin yanda abokinshi duk yasusuce Akan matar Aure shiķam cikin fushi yacema Yusuf wait Outside Dude Yusuf ya girgiza kai don yaganoshi wai kar yakalleta sai wani kakkareta yakeyi.
Yace Nakira Auncle yana zuwa yaje ýa kira Aunty Nena so behave your self yafada mai hakane don yasake mata hannu Amma ina Shidai kawai Yusuf yafita kar yakalleta.
Ita Safeena kallon wanda yatabu tafara yimai tafisge hannunta tareda kama hanyar fita yasha gabanta don baisan lokacinda wani irin karfi yazo mai ba. Yace dont go plsease stay here, please stay with me cikin fushi ta tureshi tareda ficewarta tana fita yana faduwa akasa.
Wanda yayi daidai da shigowarsu Auncle da Anty Nena harma da Menal itama jin karar salatinsu yasa tadawo da gudu..........🖊
*_bawanda yafi karfin kuskure inda nayi ba daidai ba ku gafarceni dan Adam din kenan ina yinku fans muje zuwa takunce dai Maman Ammar*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYAYYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar
💫FAGEN MARUBUTA WRITERS
ASSOCIATION💫
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
_(Gidan Aminci zaman lafiya da yardar juna, insha Allah🤝)_
*wannan nakine maman khausar kince kiji khausar a next page to gashi nan na mallakawa khausar wannan page duka Allah yaraya mana ita Akan sunnah*
9⃣
*Bismillahir rahamanir rahim*
Duk sukayo kanshi da sąuri nan take Menal tafara kuka tana kiran sunan shi, bros katashi don Allah itakuma Safeena ai gaba daya tarikice takasa koda karasawa kusa dashi Alhaji da Yusuf su suka kamashi Anty Nena ta ruga ta dakko key din mota,
Duk sunrude musamman Safeena batama tsaya daukar hijab ba tafada mota Menal ma tabita Anty Nena ce mai karfin halin acikinsu Sai Yusuf Alhaji ma duk ya firgice yana tunanin dan Amana,
Koda suka isa Asibiti da gudu Akã nufi emagency dashi dón gaba daya numfashinshi baya tafiya, Safeena jitake kafarta ma bazata iya daukarta ba komai ya tsaya mata ita tarasa maike shirin faruwa ne da ita sam takasa fahimtar halinda take ciki,
Meke shirin faruwa ne da ita don gaba daya jitake kamar nata numfashin zai tsaya Alokacinda taganshi a sume,
Menal kam ba Abinda takeyi sai kuka don gani takeyi idan har wani Abû yasami Sageer itama tata takare don ita kadai tasan irin Azabtuwar da takeyi saboda sonshi, Addu a take Allah yabashi lafiya gaskiya zata fada mai Abinďa ke cikin zuciyarta ko zata samu sauki,
Saida doctor yabasu umarnin shiga suganshi kowa na rige rige tsakanin Alhaji da Sãfeena harma da Menal tana shiga takasa karasawa ciki Abakin kofa ta tsaya tana kallon yanda yake fitarda numfashi Ahankali andaura mai drip Ahannu ta Mēnal da gudu takarasa tafada jikinshi wanda saida Safeena taji wani iri har cikin ranta bataji dadin yanda yarinýar ta taba mai jikiba, Amma wani sashi na zuciyarta na cewa ina ruwanki, tayi saurin dauke kanta don batason ganin yanda Menal tawani rukun kume mai jiki,
Saida Alhaji yayi magana cewar Yusuf yama yarda su gida dare yayi sosai shizai tsaya Amma ina yace aa shine yaka mata yatsaya badamuwa su sutafi daga Menal har Safeena basuji dadin cewa da akayi sutafiba Amma sun san tunda Alhaji yace dole sutafi,
Alhaji yama Yusuf godiya sannan suka wuce gida suna hanya suna tattauna ciwoň na Sageer shida Anty nenã Akan doctor yace Akiyaye bacin Abinda kesashi cikin damuwa kuma yaka mata Amai Aure amma mekike gani? Yakamata ayi wani Abuakai. Wai meke damunshi ne ma har yasa tunani yakeson cutar da shi Anty Nena tace to saidai yatashi zangwada tanbayarshi,
Har suka isa gida suna tattaunawa akan ciwon Dakuma damuwa, wanda awani gefen Safeena kamar ta zuciyarta zata fito tsabar bugawa, Aure meyasa za amai Aure? Menal kuwa taji dadi har cikin zuciyarta don tasan Sageer baida wata budurwar da yakeso Dama Humaida ce ita kuma yanzu ta fita hanyarshi aganinta don haka ita zata fadamai kawai suyi Auren su kawai don tafi kowàce mace dacewa dashi, nikam nace Hmmm.
Sageer bai farkaba saida Asuba yana bude ido yaga Yusuf Zaune, yace mai tana ina? Sai Alokacin Yusuf yalura da yatashi yace wacece? Ahankali yace Safeena'Yusuf yace muna Asibitine fa Safeena nagida yai saurin zabura zaitashi Amma ina yakasa saboda jikin ba karfi.
Yusuf take me to her please I wnt to see her, yafada cikin damuwa wanda saida yatausaya mai don yasan Abokinshi yashiga matsala babba yace sory yanzu karfe hudu na Asuba da safe zanyi kokari tazo kasan da wuya Asallameka yau jikinka ba karfi Haryanzu.
Badan yasoba yakoma yayi relaxed.gefen Safeena kuwa aikamar ta janyo wayewar garin saboda tsabar matsuwa gari yawaye batasan meyasa ta damuda shi har haka ba. Menal ma hakan take burinta kawai taga tashin shi ko tafada mai damuwarta,
Gari nawaye wa tafada kicin dakanta tafara dora mai break fast tanayi mai aikin natayata da shirya na gidan Har Anty Nena tafito tasameta Akicin tareda cewa Yau madan Safeena ce Akicin ?tayi murmushi tareda cewa wallahi kawai naji ina son yin girkin ne,
Takammala duka sannan tashirya na Asibiti A basket sannan takoma dakinta tafesa wanka first time taji tana son sa riga da zani sunko yimata kyau sosai tareda kama gashinta don bata iya dąura dankwalï ba tasamu mayafi fari kasan cewar atanfar blue ce da takalmi farare masu dan tsini ga dinkin yakar beta sosai kasan cewarta mace mai diri ga ko ina yaji masha Allah.
Tafito tana tashin kamshi mai tsada tareda taku irin na matan da suka yarda dakansu, duk suna zaune a dining kowa na cin Abincinshi har da yaran Anmusu shirin school Alhajin ma na zaune.
Takarasa tareda gaida Anty Nena da Alhaji yace kintashi lafiya batareda yadago kanshiba taja kujera tazauna tareda hada tea don ta matsu ta ganta Asibiti
Dontaga halinda yake ciki,
Saida kowa yagama Alhaji yacema Menal tawuce school tareda yaran su zasuje Asibiti tareda Safeena da Anty Nena suma daga can zasu wucé Aiki. Menal bataso Amma tasan bata isa tama dadynta kaddama ba haka ta wuce badon ranta yasoba,
Sageer kuwa gari nawayewa yamatsa ma Yuşuf kace zata zo har yanzu shiru har likita yazo yacire mai drip din yashiga yayi sallah' yana idarwa yamike yana leka window yaga kozai hangota don ďaga dakinda yake yäna hango harabar Asibiti,
Saida yakusa faduwa hangota da yayi tafito gaban motar Auncle dinshi tana murmushi gashi tayi wani bala in kyau, zuciyarshi kamar tafaso tsabar kishi yatsani yaganta da kowane na miji baison kowa na rabarta.
Saida yazauna yadafe kirjinshi har Yusuf na tanbayar yadai? Ko inkira doctor ne yakwanta tareda rufe idonshi bai Ammasa ba kafin yakuma cewa komai sun shigo dakin su uku.Alhaji ne gaba
Yusuf yagaishe su Alhaji yace baitashi bane har yanzu? Yusuf yace yàtashi komawa yayi don Har yayi sallah ma. Ok Abokinka bai fada ma meke damunshiba har yajanyo mai hawan jini?
Yace kasanshi Alhaji da zurfin ciki Amma ni ína ganin kamar stress ne kawai, yace ok Allah yabashi lafiya Anty Nena tace Ameen Safeena kuwa ta Ajiye basket dinda tashigo da shi tareda kallon fuskarshi data kara haske,
Alhaji yace khadija Muje in antashi Aiki zamu dawo kibar ma Safeena motar idan zata wuce ta tafida ita gida muje Atawa tace ok Takuma matsawa tareda shafa fuskarshi Allah yabaka lafiya Son Ameen suka Amsa banda Safeena.
Sun juya Yusuf ma yabi bayansu ita ma tafara takawa zata bi bayansu da karfi taji Anrikota kafin ta iya cewa komai yatura kofar tareda mannata ajikin kofar.
Ya rike west dinta da hannunshi duka biyu yafara Ajiyar zuciya yana kallon cikin idonta gaba daya takasa ko motsi tsabar mûtuwa da jikinta yayi saboda rike mata kugu da yayi gawani irin kallo da yake aika mata dashi
Ahankali yake karasa cika gab dinda ke tsakaninsu yana kara shige mata tareda shakar ķamshin turarenta duk tafitoda idonta waje tana mamakin me yake shirin yi ne haka?...............🖊
*Nima dai bansaniba muhadu a nxt pàge fans inajin dadin comnt dinku ina yinku sosai masoya HARAMTACCIYAR SOYYAYA*❤
[2/19, 2:19 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar
*ina godiya YAYA HAYATU Allah yakara daukaka*
🔟
Iya kaduwa ta kadu tsabar shõck harta kasa motsawa shikuwa Sageer ganinta kusa dashi gaba daya yarikice bai tsaya bata lokaciba yayi saurin shigewa cikin jikinta tareda matseta gam ajikinshi kamar su zama daya,
Ba inda baya rawa ajikinshi saida taji takasa numfashi da kyau tafara kokarin tureshi tana fadin wane irin iskanci ne wannan kakeyi ? Kana haukane,
Cikin mutuwar jiki tareda dashewar murya yace eh na haukace kuma kece kikayi sanadiyyar hauka cewata. Still yaki sakintã sai kokarin hada fuskarsu yakeyi yana lumshe ido tareda cewa,
Wayace kishigo motar shi? Cikin fushi tace miji nane da karfi ya tureta tareda fadin kidaina fadamin mijinki ne banaso' aiko ban fada ba kowa yasani yace banda ni ban yarda ba ita gaba daya yanzu tsoronshi takeji.
Gaskiyane kanshi yatabu komuma tsabar iskancine zai rika tabata tana matar Aure cikin fushi tace karka kuma kai hannunka Ajikina ni matar Aure ce haramun ne kana taba ni kai ba halali na bane.
Waima meye matsalarka dani ne? Kece zantan baya wayace kishigo rayuwata kin hana ni sakewa kina kokarin haukatani why? Meyasa kika Auri Aùncle dina why?
Bakida hankaline? He did'nt deserv you yafada cikin rada yana kokarin shigewa jikinta again nine dai dai dake. Ni yakamata in mallakeki bashiba taja baya tareda fadin wai meye kakeyi haka ne?
Kiyi hakuri Safeena wallahi ina sonki ! Look i can't even explain look in to my eyes and see. takuma ja dabaya yana kuma binta tareda cewa kar ka tabani nafada maka,
I realy love yôu Safeena i realy do please listing to me gaba daya ta tsure takasa natsuwa. Bata tsayaba saida ta dangana da gadon ta zauna yakarasa tareda zaunawa gab da ita yana aika mata da wani irin kallo,
Duk idonshi yayi jawur tsabar fitina da shaukin so, jin motsin kofar yabata damar mikewa da sauri ta matsa yatashi cikin mutuwar jiki yanufi kofar don yasan waye,
Yusuf ne yashigo tareda kallon Sageer irin na tuhumar nan ya dauke kai tareda matsawa yakoma kan gado yana me tsareta da ido duk taji ta tsani kanta bata son zaman dakin tamike yace kiban Abinci cikin bada umarni.
Ita gaba daya yanzu yadaina bata mamaki sai tsoro don wannan HARAM TACCIYAR SOYAYYA da yake shirin jefasu aciki harta fara nadamar Abinda zaifaru in Abbun su yaji kasheta zaiyi,
Takarasa wurin basket ta duka tana hadamai tea tareda soyyayan kwai da kuma farfesun kayan ciki duk yana kallon bayanta yanda hips dinta gaba daya yakara rikicewa tareda rike marar shi duķ Yusuf na kallonsu,
Yana kuma hango Abinda zai iya faruwa nan gaba saboda yaga Alamar Abokinshi yayi nisa bayajin kira harta karaso ta dan