Showing 3001 words to 6000 words out of 64206 words
Chapter 2 - HARAMTACCIYAR SOYYAYA Compelet Book by Nafisa Sani Hussein.txt
nan ba agidan su matar auncle dinshi
*_tofa akwai magana sageer nidai baruwana_*
*_kuchigaba da comnt yanzu aka fara my fans ina godiya musammn hafsaty nasan kinayin wann novel nima inayinki_*
[2/19, 1:51 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammaŕ
*_this ones for you my little sister RASHIDA B.J Allah yarayamin yarana ya albarkace su akan sunnah_*
3⃣
Karfe takwas da rabi nadare ,abbu tareda Anty Zaliha suka yima Safeena rakiya dakin mijinta tareda danka amanrta ahnnun Anty Nena dakuma nasihohi masu shiga jiki daga abbau, saidai muce Allah kade fitina , sai bayn sun tafi sannan hankalin Safeena yafara tashi don duk bidirin nàn batada niyyar yin kuka tsabar tana ganin kauyanci ne wai don zaki samu yanci ki zauna wani kuka,ahankali tayaye mayafinda ke kanta tanabin dakin da take ciki da kallo wow shine abinda tafada saboda ganin yanda Abbunta ya kashe mata dukiya adakinta,
Ahakn har cikin falonta da kuma toilet saida ta leka. tana tafe tana wani rausaya irin na wayayyun mata masuji da boko har takoma kan sofa tadan kishingida janyo wayarta tana latsawa, har zuwa karfe tara ahnkali aka bude kofar tare kuma da yin sallama tadago donjin muryr mace, ahankali ta tashi tareda fadin sannu Anty, yauwa Amarya kidan fito main falo megidan na magana, what? Aranta take wannan maganar yaza ace wai mijin da take aure bazai iya shigowa dakinta yakirata ba saidai ya aiko kuma a first day data shigo gidanshi, saida Anty takuma magana sannan tadawo daga duniyar tunani tareda mikewa tadauki mayafinda ta ajiye agefe ta yafa sannan suka fito, kamshin turarenta da kuma karar takun takalminta su suka sa duk jama'ar dake falon dako kansun don ganin wacece Amaryar gidan? Kamar an doka guduma haka sageer yaji acikin kanshi, kardai ace wannan ce Amaryar auncle dinshi? Ana nufin wannan yarinyarce tayarda ta Auri auncle? Kai ina she cant do dat, no way. Shigowar auncle dinshi tareda yara shiyadawo dashi daga duniyar tunanin da yafada yamike yaje yai hugin Auncle dinshi ahankali tareda mutuwarda jikinshi yayi.
Yace son ya kake? Fine Auncle sai alokacin Safeena tadaga idontã donjin wata murya mai loushi kamar ba muryar namijiba. Saida gabanta yafadi tunawa datayi da wannan gayen da shine yaje gidansu da safe kuma yaganta daga ita sai towel,
Kaddai ace shima danshine. Saurin kallon fuskar mutùmin tayi don ta gasgata tunaninta, saikuma tadukarda kanta Ammar da Al'ameen kuwã dagudu sukayi wurin Anty Nena suka haye jikinta, tace no guys yanzu ga mamanku can kuje wurinta kubarni inhuta kuma.
Dagudu suka sauka suka karasa wurin Safeena tareda rike mata hannu. Anty wai kece maman mu yanzu cewar Al'ameen ?duk da ta tsani yara amma saitaji wa innan sunburgeta sosai ahankali taja ammar agefenta tazaunarda shi shima al ameen yazauna adaya gefen suka sata atsakiya
Shima maigidan yaji dadin yanda tama yaranshi shikuma yazauna akujera daya shida Sageer Anty nena na one seater Alhaji Mu'azzam yace banga Menal ba Anty Nena tace tana cikin dakinta Alhaji yace Al'ameen yaje yakirata , ahnkali take shigowa falon sanyeda kayan bacci riga da wando tana shigowa tasamu wuri akusada Anty Nena tazauna tareda kallon Sageer wanda yayi nisa awata duniya
Alhamdulillah da Alhaji Mu'azzam yafada shiyadawo dashi cikin hankalinshi.son ga Amaryata nasan banda matsala dakai.sannan ke Khadija wato Anty Nena saboda shi sunan ta na gsky yake kiranta dashi
Ga kanwarki nan don saikinsa ido saboda kinfi kowa sanin kan gidan nan don Allah kisa ido sannan My boys su ammar kenaň sukace yes dady ga new mom nakawo muku banda rashin ji resfect her d way u resfect khadija. Suka hadâ baki wurin cewa yeś dady
Sannan ke menal i know u bansonjin wani matsala cos Safeena is my wife understood? Muryarta na sheckin tace yes dady ok
Sannan ke Safeena ki kama girmanki ki hukuntasu kamar yayanda kika haifa ahankali take gyada kanta.
Ahakan yagabatr mata dakowa nagidan har zuwa kan Sageer wanda batasan dalilinda taji faduwar gaba ba dataji sunan shi,
Har aka rufe taroda addu a Sageer tunaninshi yayi nisa
Meyasa zata yarda da wannan auren yama za ayi tana karamar yarinya tayi ruining life dinta bawai yace auncle dinshi nada wani mugun hali bane but yaza ayi tayi haka tayaya zata karaci rayuwarta ahaka sunan tana aure amma suna ne kawai
Nikõ nace Sagir bakyau šhishshigi bayan auncle ya yabeka,
Har yakwanta ba abinda yake tunani sai wannan mahaukaciyar yarinyar nan kodai batada lfy ne ta yarda da wannan auren? Har kusan rabin dare ba abinda yake sai tunani dayaga abin bamai karewa bane ahankali yamike yafada toilet yayi alwala yazo yafara nafiloli. gefen Safeena kuwa itama sai yanzu tafara tunanin wannan wane irin mijine ta aura wanda ko dakinta yaki yaleko baretasa ran harma zai kwanta aciki,
*wai ahaka ne rayuwar auren nata zaikasance ko yaya?shin ahaka zata yita zama daga ita sai yara sai kuma wannan gayen mai miskilancin tsiya kodai shine abinda Anty Zaliha kekokarin fahimtarda ita shin meyake shirin faruwa da rayuwar zaman Aurenta?*
Ahaka wannan dare yakasance awurin mutane guda biyu sageer da kuma Safeena har garin Allah yawaye yana
Karfe 9: kowa nagidan ya hallara a dining kasancewar al adar gidanne cin abinci atare amma ba safeena saida auncle ya tura Menal taje takirata. Ranta baisoba ahaka tamike taje koda tashiga tana kwançe cikin adonta daba arabata da shi akoda yaushe wato kananan kaya don ita batason rayuwae native wear hmmm niko nace Safeena duk wannan kirar da Allah yamiki amma kike sa kanann kaya gsky akwai daukar alhakin maza masu lfy
Doguwar rigace wadda ake yayi ta yanmata mai buterfly hand takamata tsam kamar komai zai yimagana yace aceceshi koda menal tashigo tafada mata sakon dadyn batareda ko ta gaishetaba tajuya ahankali tayi kwafa zanyi maganinki yarinya. takarasa gaban mirrow takara feshe jikinta da turarukanta masu kamshi dakuma tsada sannan tajanyo wani dan karamin gyalen kalan rigan ta yafa niko nace da babu gwara ba dadi amma wannan gyalen meya rufe Safeena? takun takalminta shiyaba Sageer daman dago dakanshi zuwa ga hanyarda yakejin karar dasauri yadukarda kanshi. Tsabar faduwarda gabanshi yayi, this girl is crazy yazata fito ahaka gaban auncle niko nace tofa mutum da matarshi?
Ba abinda yake aika mata dashi sai mugun kallo. Koda taja kujera tagaida kowa amma batako kalli gefenda yakeba cos she haté him da shida wannan fitsararriyar yarinyar duk zata saita musu zama basu san wacece Safeena ba har aka gama cin abincin ba abinda Sageer yaci amma bawanda yalurada halinda yake ciki. Har kowa yawatse dasaurinshi yamike yafada dakinshi taredã daukar makullim motarshi cos he needs some fresh air yana fita wani restourant yanufa yai odar fresh milk da cheese cake yasha gaba daya yakasa ganema kanshi har wayarshi tai kara yasa hannu yadauka hello dude can dayan gefen yusuf ne yace wat is wrong dude bangane makaba ne wannan karon?tunjiya da muka rabu i thought zaka nemeni amma shiru yanzu kuma nazo gidan baka nan meke faruwa? Noting kawąi stress ne but am fine yanzu kana ina ?yace kajirani gani nan zuwa yanzu yai cutin wayar tareda mikewa yabiya bill din sannan yawuce
Yana isowa suka shige cikin gidan yana tura kofan falon yayi saurin komawa baya tareda cema yusuf muje garden dude saboda ganin safeena da yayi tana kishingide akan kujeranda kesaitin shigowa falon yana tafe yana cewa dis girl is crazy baisanma maganar tafito ba saida Yusuf yace wai Menal sai sannan yasan maganar tafito yasamu kanshi dacewa eh ita metayi maka ne wannan karon don Yusuf yasan yanda Menal keson shigema Sageer, yace wai yamaganar wannan bussines din na texas dude yace yana tfy yanada akeso don muna samun incomes sosai ok dude wannan yarinyar tadamenifa tanaso inbata numbanka wanda takeda bayashiga so gşky nidai nabata, why dude yarinyar nan mayyace wlh rabona da ita tun a paris ok yanzudai kayi hakuri ka saurareta kasani wannan karon koku daidaita. Ya daure fuska dawaye zandaidaita wannan yarinyar da batada natsuwa kainifa natsani mace mai shishshigi dayawa fa ok but meye laifin humaida kawai sonka takeyi plss dude. Ok mubar zancen haka
Abangaren Safeena kuwa gabadaya ita rayuwar tayimata wani iri koda gidansu bawasu mutane bane but tasaba fita koda shoping ne but yanzu kuma ba hali saboda an dauretã da wannan aurenda miji ko kallo baka isheshiba, wai ahakane rąyuwarta zata cigaba wai ahaka źata cigaba da zama da wa innan mutanen masu girman kan tsiya anty nena batada lokaci dama itama aiki take zuwa saimasu kula da aikin gidan wa inda da sungama sunkoma gefensu.
*Godiya gareku fans kucigaba da biyoni yanzu muke shiga labari*
[2/19, 1:55 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar
editing
(Firdausi mai Nasara)
*_inagodiya gareku fans wa inda kekirana ta waya da kuma masu yimin mãgana ta watsp duk ina godiya agareku Allah yabar kauna*
4⃣
Ahaka rayuwar taketa tafiya, waňda ayau Safeena tasamu kusan sati daya acikin gidan Alhaji mu azzam. Ahankali take fahimtar rayuwar kowa dake cikin gidan, su Al ameen sun saba da ita sosai don duk rashin son hayaniyarta yaran sunshiga ranta. Sai menal wadda har yau gaisuwa kawai kehadasu, wanda baidamu Safeena ba kokadan don batason raini daman, agefen Alhaji kuwa bawai bayason kula matarshi bane aa. Saidai yana ganin tayimai karama dayawa ko lokacinda mahaifinta yamai maganar don bazai iya kinyarda bane, sai don yana ganin girman mutumin
Sageer kuwa rabonshida shigowa cikin falon tun ranar farko, don bayason gasgata zuciyarshi don yana ganin bai daceba amma shikadai yasan irin halinda yake ciki yana azabtuwa, bacci kuwa saidai barawo' saukinshima yafara zuwa office da abin zai mai yawa, yanzu hakama yana zaune acikin office dinshi zuciyarshi na tunzurashi da komawa gida. jiyake idan har baiga wannan yarinyarba yau akwai matsala , yau sati daya rabonda yasata a iđo
Zunbur yamike yadauki key din motarshi. wani gefe na zuciyarshi na tanbayarshi meye kake tunani sageer? yazakayi haka me kakeso ka aikata?amma ina baijin yau zai iya hakura gaskya
Yana isa cikin get din gidan yaga motar Alhaji mu azzam yace aunčle meyadawo yi gida yanzu? Ahaka dai yakarasa ciki, yana shiģa yayi dana sanin dawowarshi gida. Saboda mugun ganinda yayi, Safeena tana sanyeda dogon wandon jeans blue da kuma farar tshirt ajikinta ga gashinta takamashi atsakiyar kanta , tasako jelar fuskarta tasha make up tasa janbaki maroon abinka da farar mace ga hips dinta sunfito sosai ga t shirt dinma ta mugun kamata komai yafito tana fitowa daga kofar sashenta shima Alhaji nafitowa daga nashi gefen wanda hankalin sageer yamugun tashi saboda bayason Alhaji yaganta ahaka, kujimin fa readers mutum da matarshi. dasauri yakarasa cikin falon yatari auncle diň. Sageer mekadawo yi gida by this time ?yana me duba agogon hannunshi. nayi mantuwane nazo indauka kaifa naganka agida?nima mantuwar nayi kuma yanzu dama nakeson kiranka don nasamu urgent call munada comprence meeting a yola so zanbi jirgi karfe shabiyu.yaushe zaku dawo? May be gobe ko jibi duk yanda takama ok Allah yakiyaye, yana gamawa yasakai waje shikuma yafada dakinshi tareda yin ajiyar zuciya mai karfi najin dadin auncle baiganta ahaka ba,
Wayarshice tayi kara yadauka tareda cewa hello auncle yaçemai don Allah kafadama sauran yaran da kuma Safeena nayi tafiya ina sauri ban sallameta ba,
Ita khadija tasani. Ok zànfada mata yafada akasa lance sann yakatse wayar, harya gyara kwanciyarshi kome yatuna yamike da sauri yafito, yanufi gefen safeena wadda ita ko lokacinda yashigo bata ko lurada shiba wucewarta tayi wurin lambu tana danna waýarta tunda ba abokiň hira.
Kõda ya kwankwasa baiji motsiba yakara shiru Ahankali yatura kofar yashiga cikin dakin wani kamshi mai dadi yabugi hancinshi yaduba ko ina tsab tsab amma baiga alamar tana cikiba
Yana fitowa yayi harabar gidan acan gefen lanbu ya hangota zaune tana waya gamai ba fulawoyi ruwa ga masu aiki sunata aikinsu, azuciye yakarasa wurinda take zaune yatsaya zuciyarshi natafasa,
Yace mekikeyi anan? Cikin hasala dasauri tadago kai don ganin waye yake mata íhu haka don tasan bamai gidan bane. Kallonshi takeyi da mamaki don ita tama manta dashi agidan, yakuma cewa dakefa nake magana. mekikeyi anan Ahaka? bakida hankaline kome? Yazaki fito waje da wannan shigar kuma gamasu aiki suna kallonki, meyasa kike wulakanta jikinda yakeda muhimmanci? baki da hanci harda ido tasaki tana kallonshi tareda cewa ikon Allah. Kaikuma waye kai da kakemin ihu haka akai bakasan natsani hayaniya ba, how there you shout at me like this? zuciya takuma ciyoshi yace , i no u don't care har waje ma zaki iya fita Ahakan, wai wayekai ma tukun? ninasan bakai kake aure naba ko mijin da ya auroni bazai zo yanamun ihu har haka ba cikin fushi yace wuce muje ciki, kinajina ki wuce karki bari inkuma mai maitawa duk masu aikinma tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah ganin idon mutane yasa tadauki wayarta tashige tareda zabgamai muguwar harara,
Har tashiga tana me tunanin wannan wane irin mutum ne ko shine megidan saihaka, zanyi maganinshi. Shikuwa yana shiga side dinshi yafada kangado yana fitarda numfashi mai karfi shikadai yasan halinda yake ciki juyi kawai yakeyi agado wannan yarinyar tanaso tamin illah meyasa take wannan shigar mutane naganinta meyasa take bari wanda yakamata da wanda bai kamataba suna ganin tsadadden jikinta?
yana kwance baisan lokaci yayi hakaba saida yaji kiran sallar ázahar yatuna yabar office tun shadaya.
Wai meyasa nadamu da wannan yarinyar meyasa ma namata magana? Karfa tarenani ôh shit ya naushi iska tareda miķewa yafada bathroom yasheko wanka tareda dauro alwala.
Yafito daureda towel menal tafado dakin da gudu bros, saida yadaka mata tsawa bana fadamiki kirika nocking kafin kishigoba ta tsaya taname kallonshi shikuma yana goge jikinshi dawani towel yace kije falo kijirani ínshirya jikinta yayi mugun sanyi sannan tace tom tareda juyawa tana mekara jin feelings sosai a zuciyarta . Agaskiya yakamata Sageer yasancewa tagirma itafa tanajiň da soyayyarshi aka haifeta. tana bala in sonshi har cikin zuciyarta shiyasa ko lokacinda Humaida budurwar shi ke zuwa take jin tatsaneta sosai duk da lokacin bata wuce ten years ba,
Ahankali tafada kan sofa tareda furta i love him somuch har lokacinda Aunty nena ta dawo tasameta afalon batasaniba ta fada tunani saida ta tabata tareda cewa yar gidan Aunty mekike tunani haka inatã magana yau ba lecture ne naganki agida ? Yanzu nadawo Aunty you are welcome tace tank u inasu Al ameen? Basu isoba driver yaje dakko su.
Ok bari inkintsa in fito muyi lunch takarbi jakarta tareda rakata dakinta sannan tafito,
Saida sukazo lunch Anty nena ke fada mata megidan yayi tafiya saida taji wani iri ace mijinda kake aure baida lokacinka. Koda auren bawai yadameta bane amma ko yaya yaka mata yakula da ita itama fa mutum ci tana son kulawa har suka gama Sageer bai fitoba dama tun ranar farkon zuwan Safeena yadaina cin Abinči a dining saidai akaimai side dinshi. Ko yauma menal ce ta kaimai sannan tatsaya adakin yanaci tana gyaramai dakin har yagama takwashe komai shikuma yazari key tareda fita daga gidan direct gidansu Yusuf yawuce dayake dan gidane kai tsaye yashige ciki tareda yin sallama Mamy na zane wato maman Yusuf yakarasa yagaisheta ta amsa cikeda fara a tace nayi fushi sai yau kaga damar zuwa gaisheni? Yace kiyi hakuri mamy abubuwan ne sukayi yawa. tace Allah yataimaka yace Ameen mutumin naciki ? Eh yanzu yàshigo shima ka karasa ciki. yashiga yasamu Yusuf din wanka yazauna jiranshi yana fitowa yace yau ina kashiga naje office dinka baka nan? Yace nadanyi mantuwa ne nakoma gida. Amma nazauna kusan awa daya ina jiranka. Oh sory ina fatan bawata matsala ko yace babu kawai inaso muyi wata magana ne.
[2/19, 2:01 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYAYYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)🏵
Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
Maman Ammar
editing
(Firdausi mainasara)
*_wannan shafin nakune yan grp din feenerh fans kucigaba da posting ina yinku*
5⃣
Har Sageer yadawo gida yana tunanin maganarshi da Yusuf
Meyasa Yusuf yake tunanin zai iya auren Humaida yama zai bashi irin wannan shawarar
Shifa yanzu inhar bazai samu macenda yakesoba tofa ya hakura da auren
Yusuf bazai taba fahimtar halinda yake cikiba yana azabtuwa tundaga raʼnarda yafara dora idonshi akan wannan yarinyar gabadaya zuciyarshi bata fada mai gáskiyà.
Shifa yana bukatar inma bacci yakeyi yasamu wanda zai farkar dashi don yandã yakejin zazzafar soyayyarta dakuma mugun kishinta.
Fitinarda kecikin zuciyarshi bai tunanin akwai mai iyamai maganinta. Sai Allah. Yawatsa ruwa yafi sau goma bayan dawowarshi amma har yanzu bai samu peace of mind ba saida yasanyã kaya yafito falo ko Ällah zaisa ýaganta ko sanyi yaji aransa.
Koda yãfito duk suna falon tareda yara Ammar nakusa da ita yana zuba mata surutû Al ameen kuma yana tareda Anty Nena
Kamshin turarenshi yasa duk suka dago kansu domin sun fahimci waye mai isowar harda ita Safeenar ma cos taji kamshin ajikinshi dazu
Saida gabanta yabuga tsabar kwarjininda yamata saiyau takare mai kallo dakyau yana sanyeda riga amles dakuma tree quter ajikinshi sajen nan yana sheki yana takowa Ahankali irin na isassun maza dasukejin sunkai.
Cikin minti dabai wuce biyu ba takare mai kallo for the first time data taba jin wani namiji yaburgeta arayuwarta,
Yaran suka nufesu dagudu suna mai oyoyo bros Anty Nena tace son dama kana gida? Eh wallahi Aunty nadan hutane,
Ya zauna daidai saitin kujerar datake zaune
Ita kuwa Safeena tunda takalleshi gabanta kemugun faduwa saboda wani irin kallo dayayi mata