Showing 24001 words to 27000 words out of 41738 words

Chapter 9 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt

24 Nov 2024

2293

ma suce ‘show off’ ake masu, su sake boye ta a daki?"
Nenne da Oummana me zasuyi ba dariya ba.
Uban kasa ma da Dade sai da suka dara. Wato duk Taiwo ta jawo ya zama a darare yake da duk abinda zai sa a ce ya raina azikin su Siddiqah. Uban kasa yace "ai dai an gayyace ka daurin aure ko?" Hamma yace "eh" Uban kasa yace "toh ni nace ka wakilce ni. Gara yau dai a gan ka a ainahin gaskiyar ka. Sarauta ai ba karya bace Abdulrasheed".
Prince yayi murmushi. Nenne tace "gaskiya kam. Allah dai ya bada sa’a, in an gama daurin aure ka shiga ciki ku gaisa da su Umman Aysha, kace ina gaishe ta". Hamma ya ce "toh Nenne".
Daman Kuma karfe 12:45 ne daurin auren, da an idar da sallar Juma’a za a daura. Ai kuwa kan kace meye wannan sarkin dogarai ya cika aiki, an sanar da maganar zuwa daurin auren, Galadima da Waziri sun shirya, ga dogarawa da motoci na alfarma nan uku an ware, sai motar Uban kasa itama an fito da ita. Cikin ta Prince zai shiga.
A gefe ga masu algaita.

Daga cikin gida kuwa Prince ne zaune za'a nada masa rawani, sai kira yake "shi fa baya son rawani, zafi ne dashi Oummana".
Nani Oummana tace "ai kuwa dole kaso rawani, don kuwa kayi gadonsa hawa biyu". Hakanan Hamma ya zauna aka nada masa farin rawani, an masa irin rufin bakinnan, ya dau 'black Gucci shades' kalar dark brown' ya saka, ga hannun nan na dama yana juyawa yana sheki. 'Patek Philippe Grandmaster Chime' ya saka, not extravagant but extremely classy. Yau sai jinin fulatancin gabadaya ya fito. Masha Allahu kawai za'a ce saboda Nenne tana zaune tana kallon sa ya tashi zasu wuce bata san sanda tace "fa tabarakallahu ahsanal khaleqeen. U'izu bi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq". Ta tashi ta tofa ta shafa mashi. Wallahi tama manta basu kadai bane. Oummana tace, "je ka Allah ya tsare" yace "amin Nani".
Suka fito tare da Uncle Abdulmajeed shima yasa rawani. Amman Kehinde ya haska. Dogarawa an samu abin so, shi dama gashi miskili kuma rawanin ba so yake ba, ai sai shan kunun da yayi yasa komi looks more regal. Suka hau kirari kamar makoshin su ze fita aka shige mota. Hamma yace don Allah a rage convoy din. Sarkin dogarai yace "ai yayi hakuri tunda sarki yake wakilta baza su fita qasa da haka ba.
Ya shige motar Uban kasa shi da Uncle Abdulmajeed sai sarkin dogarai a gaba. daya motar kuma Galadima dayar Turaki da Waziri. Sai ambulance da kuma bus ta dogarai da masu algaita. Aka wuce tiryan_ tiryan zuwa Jeka da fari.
A hanya Prince ya kira Baba Yunus, yace “yazo zai fito Uban kasa yace lallai ya wakilce shi a daurin aure, to dai gashi nan a hanya Allah yasa kar yayi wa Baba Barau laifi”. Ashe a ‘hands free’ yake, Baba Barau na kusa da Yunus yana jinsu, sai Baba Barau yayi masa gyaran murya yace "wato Abdulrashid kallon sarkin bala'i kake mani ko?"
Prince ya zaro ido yace "subhanallahi, ko kadan Baba. Na dai fada ne kada muzo baku sani ba". Yace "to wa ya taba mayar da wakilcin Uban kasa? Wato don na rike maka Indo, shine kake so ni a kore ni daga kasar Gombe ko?" Yace "ah Baba, tsaya kaji.....". Ai kuwa Baba Barau ya fashe da dariya, Mal Yunus yace "wasa yake maka ka ji! Sai kun iso".
Du duk a tunanin su shi da wani aka turo. They have no idea it’s the whole convoy.

Nan aka fito aka shiga rumfuman canopy da aka kakkafa a gaban gidan. Aka zazzauna, aka ce sarki yayi wakilci, wa zai daura aure wakilin Sarki bai iso ba?” Haka nan aka dan tsaya aka dan ware wuri kamar na mutum hudu da zasu zauna.
Ba jimawa saiga ga jiniya, motar escort na wi-wi-wi-wi. Mata ma daga cikin gida jin jiniya sai aka hau leke, sai ga Bus din dogarai ta tsaya a gefe, suka fice.
Baba Barau sai da ya dan firgita. Ya mike tsaye shi da malam Yunus da Malam Hassan wato Baban tsohon saurayin Aisha Ishaq, don shima Mal. Hassan yazo daurin auren. Bakidayansu suka tashi don sun dauka sarki ne yazo.
Kafin su tantance komai sai tashin algaita duk inda ka hanga police ne da dogarai, sai ga motar Uban kasa har gaban ‘tent’ din da iyayen amarya ke ciki, dogarai suka zagaye ta ana kirari “Barka da sauka magajin garin Ilorin, barka dai sarki dan sarki jikan sarakuna. Gaba salamun baya salamun. Abdulrashid dan Idrisu jikan Akanni. Jikan Ummaru Jalloh Uban kasar Gombe…”.
Abdulrashid yana mota jin ana masa wannan kwakwazon ji yayi kamar ya nitse, cewa yake “don Allah sarkin dogarai kace su bari” yace masa “toh kawai”.
Sai ya yunkuro zai fita, dogarawa suka baje riga aka bude kofar, ya fito. Uncle Abdulmajid ma ya fita, yara ‘yan unguwa da matasa sai ihu ake …. kyau kam iya kyau Hamma Prince ya sheka shi.
Baba Barau da Baba Yunus suna inda suke zaune kowa yana tasbihi ga Allah a zuciyar su, dan lallai ya bawa diyar su miji nagari, wanda bashi da makusa. Ga nasaba ga addini. Kuma Allah ya mallaka mata zuciyar sa.
Sai kawai Baba barau yaji sanyi a zafin sa da yake ji. Ya tashi suka wuce suna nuna masu wurin zama.
Sarkin dogarai ya wage baki da murya yace “mai martaba Uban kasar Gombe ne ya wakilta dan sa yazo ya wakilce shi a wannan daurin aure na Maryama. Ya kuma bayar da auren a madadin sa”. Da ya kai aya sai dogarawa suka wuce dasu goro da dabino alawa ana ta jibgewa.
Ashe a cikin gida ma ana ta sauke su lemu da ruwa da dai kayan daurin aure. Baba Barau ya tabbatar cewa lallai an karrama shi, an karrama autarsa Maryam.
Nan aka zauna Abdulrashid ya gaishe su, zai duqa kenan Sarkin dogarai ya tare shi, ya ce “Yallabai Uban kasa fa kake wakilta, kai ne sarki yau”. Baba Barau yace kul ka tsugunna, muje”. Aka wuce ciki aka bashi waje duk suka zauna. Sarkin dogarai a ran sa yace. “wannan Yarima na zamani, ba abinda ya sani a kan sarautar gidansu”.
Nan dai aka fara shirin sallar Jumma’a. Liman yace gudun kada yayi laifi, ko Galadima zai yi limanci? Sai Uncle Abdulmajid yace da Prince yayi. Nan kuwa Prince ya tashi yayi huduba mai ratsa jiki, sannan ya tayar da sallar jumma’a.
Da aka idar aka daura auren Maryam da Angonta Yusuf, Kehinde yayi walicci aka bayar da Maryam bisa sadaki naira dubu dari lakadan. Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya
Ana gamawa kowa yana so ya gaisa dashi, nan duk ya tsaya aka gaisa akayi hotuna, Prince ya matsu su wuce gida saboda cikowar jama’a irin wadda bai zaba a ciki ba, ga rawanin nan ya ishe shi da zafi, duk ya gaji kamar yasa kuka.
Zasu shiga mota kenan sarkin dogarai yace wa Mal. Yunus zasu shiga su gaishe da Umman Aisha da matar Baba Barau. Malam Yunus yace “toh ba matsala”.
Su mata acan cikin gida al’ajabi ya ishe su, ance sarki yazo daurin auren Maryam, toh ta yaya? Ita dai Aisha jikin ta duk yayi la’asar. tun da taji ana “jikan Akanni” kuma ta jiyo muryarshi yana khutbah…Mal. Yunus ne ya shigo yace da matar Baba Barau da manyan Aunties din Aisha su kimtsa Uban kasa ya turo ai musu Allah sanya alheri. Ai sai suka yafa mayafai, aka taho falon.
Suna shiga ya koma yayi musu iso, masu algaita zasu fara kirari Hamma ya daga hannu sai suka yi shiru, da algaitar suka shigo gidan.
Amman babu wanda bai ce masha Allah ba, wanda suka gansa shekaranjiya ma basu gane shi bane, suka shiga falo dasu Galadima aka gaisa, da su Baba Barau duka, aka kuma sake fatan alkhairi, sannan suka ce zasu wuce. An karramasu, sun gode.
Karaf! Hamma sai ji yayi Waziri yace “toh a bisa al’ada, in sarki ya bada aure, komi na gararauren shi zaiyi, dan haka ga kayan gara nan na Maryama Uban Kasa yace a kawo….”.
A dari da sittin Abdulrashid ya kalli Waziri, sannan ya kalli Baba Barau, sai kawai ya rufe ido, a ransa yace “shikenan, daman can Taiwo tayi masu gorin arziki, toh yanzu Baba Barau cewa zai yi shi da kansa yayi musu, amma dai ba’a kyauta masa ba…”.
Prince yana cikin wannan tashin hankalin sai ya ji Mal. Yunus ya ce, “sun gode”, ya kara da cewa ayiwa Uban kasa godiya, Allah ya kara girma, ya saka da alkhairi”.
Ya kuma kallon Baba Barau, sai yaga dai fuskarsa normal. Suka mike daganan aka tashi za’a shiga mota.
Suna gaba sun fito kenan kamar ance ya kalli gaban sa, sai ya hango Aisha da wasu ‘yammata biyu suna dawowa.
Cak! Hamma ya tsaya ya dan kalle ta, duk da hijab ne jikin ta amman abinka da farar fata lallen nan ya fito, yatsun nan sunyi jajawur kamar jini, ita ashe tunda taji muryar sa ta fice ta tafi gidansu, tace taje dauko wasu kaya.
Shine Furairah matar Baba Barau tayi waya tace ace Aisha ta dawo bakin sun tafi. Tsayawa sallama da mutane yasa har suka dawo suka cimmasu a kofar gida.
Ba wanda ya lura ita yake kallo, don tana daga nesa. Amman Prince ya ganta, itama kuma ta ganshi. Da kyar ya shige mota dai suka wuce
Hamma yana shiga mota yace ma Kawunsa Abdulmajeed bazai yarda a qara saka shi wakilci ba, Uncle Abdulmajeed da Sarkin dogarai suka yi ta dariya.
Da suka koma gida Prince ya kwabe Rawanin a falon Oumana ya shige nasa dakin dake sassanta yayi wanka ya kwanta. Zuciyar sa na hasko masa Aisha. Shi a idonsa kamar ma kiba yaga ta kara.
Yace a ransa wato yarinyar nan babu ma abin da ya shalle ta dani, gashi nan tana ta shan lalle tana yawo a unguwa, shi kadai ake yi wa boyon ta. Takaici hana shi hutawar da yayi niyya.
Yadda tayi kyau dinnan haka nan take ta yawo a cikin unguwa da gari kowa na kallon lalle ya masa kyau kowanne gardi yana kyasawa a ransa.
Ai sai ya mike ya saka jallabiya ya wuce parlon Nani Oummana. Nan ya samu Nenne da Oummana sun idar da isha kenan. Tace “yaya dai Hamman su? Ko a kawo fura? Na ga ko abinci baka ci ba. Yace “Oummana yaushe zaku gidansu Aisha ne?” ta ce “ba ance sai gobe ba yau biki suke tayi?” Yace “ai na ganta tayi lalle sai yawo take a gari kowa na kallonta”.
Nani da Nenne suka hada baki suka ce “kayi hakuri, gobe sai aje, in sha Allah. Amman kar ka fada masu za’a zo”.
Washegari sauran yan yinin biki duk suka watse. Kafin la’asar gidan ya zama ba kowa sai ‘yan tsirarun mutane. Nenne ma ta kira Umman Siddiqah suka gaisa amman bata ce mata tazo Gombe ba. Tayi masu Allah ya sanya alkhairi a uren Maryam, suka gaisa da matar Baba Barau ma. Nan tace “anata yinin biki” Furairah tace “ai tun jiya suka kai amarya. Yau can gidan ta zasu yi yini, nan dai an gama komi. Nenne tayi masu fatan alkhairi sukayi sallama. Nan take ce ma Oummana ga yadda sukayi da Haj. Zainab da matar wan Baban na Aisha. Suka ce toh a bari zuwa bayan isha tunda Uban kasa yace dashi za’a je.
Da aka yi magriba, Hamma ya kira Mal. Yunus suka gaisa, yace “ya gajiyar jiya?” Yace “ai baba akwai ta, saida nayi ciwon kai na rawanin nan, ai nace baza’a qara wakilta ni komai ba” Mal. Yunus yai dariya yace “ayi haka kuwa Abdulrashid?” Yayi murmushi. yace “baba kana gida ne?” Yace “eh, ina gida amman yanzu zani gidan Yaya Barau yace in zo”. Prince yace “toh shikenan Baba a dawo lafiya”.
Ana idar da sallahr isha Uban kasa yayi badda kama dashi da Dade a mota daya da sarkin dogarai sai driver Malam Buhari.
Nenne da da Hamma da Uncle Abdulmajid mota daya suma suka shiga sa Jeka da Fari.
Gabadaya Abdulrasheed ya bade su da sassanyar kamshin turarensa Boss Intense. Yau dai jallabiya ce jikinsa coffee, da hula irin ta saudi dinnan. Ya saka slippers din ‘LV’ da ‘counter’ haka a hannun sa. Sai ya fito yaro sosai, yau kamar ba shine basaraken jiya ba.
Shi yayi sallama gidan Baba Barau. Ai kuwa Auwal ya fito ya ganshi, ya shiga ya fadawa Baba Barau.
Baba Barau yace “kai wannan yaro ya cika naci. In ba bashi yarinyar nan nayi ba cinye ni zaiyi, haba!” Auwal ya rike dariyar sa shi da Malam Yunus. Yace “amman yau sai naci masa kan wannan naci da yake yi min, je ka shigo dashi”.
Baba Barau yana zaune ya bata fuska, yana jiran shigowar Prince, sai ko gashi nan ya ga ya shigo, sai ga Uncle Abdulmajid ma, yace “ah ah, kai ya sake dauko…” kafin ya kai aya sai ganin Uban kasa yayi da Nenne. Yace “la’ila ha illahu…” suka tashi su dukkansu, yace “dan Allah ku zauna. Ai yau ba maganar sarauta, biko nazo wa Da na wurin Baba Barau, ayi mana afuwa”.
Baba Barau kamar ya nitse, kunya duk ta kama shi, wato gabadaya kowa kallon bala’e’e yake masa. Yunusa ya zame kansa ya barsa da kunya, yace “Allah ya taimake ka”.
Suka zauna dukkansu aka gaisa, Mal. Yunus yace Auwalu yaje ya dauko Umman Aisha.
Auwalu ya tashi ya tafi, sai matar Baba Barau ma ta shigo suka gaisa, suna ta jinjina saukin kai na wannan sarki, da kuma irin son da suke ma Aisha da Kehinde.
Umma tazo, akai rungume-rungume ita da Nenne, tace “baki ce min kinzo ba dazu da mukayi waya”, Nenne tace ai tun jiya muka zo, da naji ana biki nace sai kun gama.
Nan Uban kasa ya basu hakuri yace ayi wa Prince uzuri. Yace kuma yara ne ka haife su baka haifi halin su ba, amman tun ba’a je ko’ina ba itama tayi dana sani, gashi da ita suka zo. Taiwo ta basu hakuri, tace sharrin shedan ne ayi hakuri. Nan dai akayi sulhu, Aisha ma tace ta haqura.
Zuciyar Hamma wasai yau. Mutuniyar dai ko kallon sa batayi ba. Saida aka gama Baba Barau yace “toh Aisha dai an siya mata jamb form, zata yi anan Gombe sati mai zuwa”. Nenne tace “ba komai, tayi abinta a nitse, bayan jamb din sai ta koma”.
Kehinde dai yayi shiru. Sai Mal. Yunus ne yace Aisha ko zaki hakura kiyi a can, dan nasan Abdulrashid kamar sati biyun da aka debar masa zai kare cikın satin nan mai zuwa”.
Nan Siddiqah tayi maza tace “ah ah Malam don Allah, inaso nayi, dan in samu cigaba da karatu na”. Nenne ma tabi bayanta. Baba Barau ya kallo Hamma, sai ya bashi tausayi, yace “kuyi shawara dai”. Koda Hamma ya kalle ta yaga tana wani cin magani yau shiru bai ce komi ba.
A haka aka gama hirar. Baba Barau yace sunga sakon jiya an gode. Uban kasa yace ai diyar shi ce, an zama daya yanzu. Akayi ta hira ta dattaku kafin akayi sallama, duk suka shige motocinsu suka koma. Kowa tashi zuciyar fessssss.
Aisha ta dauka Hamma zai tsaya ya lallashi ta sai shiru taji ya ware tareda iyayensa.
Prince ya dan ji haushin yadda Aisha ta kafe ita sam sai tayi jamb zata koma. Shi kuma yasan dole ya koma Alhamis sabida Argentina zai fara tsayawa, akwai abinda dole zai dauka ya manta gidan su, inyaso Friday ya wuce Qatar ya dan huta, Monday ya koma aiki.
Yanzu Aisha naso ta jiqa masa aiki. shi kuma (he wouldn’t beg….) don ya ma lura har wani kiba tayi ta kara haske, ba abin da ya dame ta….
Prince ya shiga damuwa, kada fa yarinyar nan ita (nothing has changed in her feelings towards him, shin shi kadai ke rawar sa da tsalle or what….?
Ire-iren tunanin da yayi tayi kenan yau, sai ji yayu ana kiran assalatu.
Yayi sallah ya godewa Allah, kuma ya rokar musu dukkan alkhairinSa.
Da safe sai wajen 11:30 ya tashi. Yayi wanka ya sa kananan kaya ya shigo falon Oummana, ya gaishe su ita da Nenne, sai Taiwo dake zaune itama sun gaisa.
Oummana na tsokanar sa wai daga sulhu sai yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login