Showing 9001 words to 12000 words out of 41738 words
Chapter 4 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt
“Nenne ke uwace mai adalci a wurina, babu abinda zaki sani in ki yi, amma don Allah ki barni naje gun Ummata. Nayi rantsuwa a gidanmu zan kwana yau. Kar kisa nayi kaffara.
Ni Nenne wallahi Allah tun ranar da kika kawoni Lagos da niyyar zaki kaini asibiti, har aka kai ga maganar aure, aka yi aka dawo, duk da banaso har raina, ban taba jin zan iya yi muku gardama ba. kuma na karbi kaddarar auren a haka, nima ai da wanda yake so na din nake kuma son shi aka raba mu amma ban yi bore ba.
Amma Nenne yau Maman Kiki ta tabo martabar wadanda ba’a iya taba su in hakura, inna hakura ma ji zan yi kamar nayi gagarumin laifi ga iyayena, don haka Nenne don Allah zan tafi, na rantse bazan kwana garin nan ba”.
Jikin Nenne yayi sanyi kalau, at the same time she is so proud of Aisha, domin ta haifu, ta cika diya.
Prince na kallon Nenne da dukkan hope na cewa zata lallashi Aisha ta shawo masa kanta ta saurareshi. Shi meye laifinsa a ciki? Amma sai gani yayi Nenne ta dauki wayarta tayi kira.
Bai dai san wa ta kira ba yaji tana “lallai-lallai a nemo jirgin zuwa Gombe yanzu, idan ma babu direct a nemi na Abuja daga nan sai ta kara shiga wani”.
Sai Prince ya dubi Nenne a firgice, yace “Nenne me kike nufi? Gidan zata tafi da gaske? Ta gama auren fa tace, ni kuma fa Nenne?”
Gabadayansa a daburce yake, kansa da duk wani lissafinsa ya kwance, duk wani azanci da tsinkaye da kunyar idanun mahaifiyar tasa sun kwace daga hannunsa.
Nenne bata ko bashi amsa ba tace “Aisha dauki kayanki kinji, muje driver da Dade suna waje suna jira zasu saka ki a jirgin Gombe”.
Dadi sosai ya kama Aisha sai lokacin ta samu hawaye suka zubo, tafe da wata sassanyar ajiyar zuciya, tace “nagode da uzuriki, amma ni Nenne yadda nazo haka zan koma Gombe, ko tsinke bazan dauka ba”.
Ta dauko wayarsa da ya bata daga jakarta ta russuna ta ajiye a gabansa ba tare data kalli yanayinsa ba. Saura kadan Prince yayi hauka a cikin kansa, musamman ganin Nenne tasa hijab ta kama hannunta suka fice suka barshi tsaye a wurin.
Sai kawai ya fito daga dakin shima a matukar fusace, ya san yayi kadan ya dakatar da Nenne yanzu, a yadda yaga fushinta da bacin ranta irin wanda bai taba gani ba, to balle kuma Dade mijin tace din Nenne, wanda sai abinda Nenne tace yake amfani dashi. Don haka maimakon yabi bayansu, dakin su Taiwo ya nufa. Yana tafe da sassarfa yana tambayar ransa me zai yiwa Taiwo ya huce?
Ance ba’a raba hanta da jini, ance blood is thicker than water… wai ba’a batawa da ‘yan uwa saboda mace, komin son da ake yi mata. Amma shi yadda yake jin matukar bacin rai da soyayyar Aisha data bijiro masa yanzunnan, mai raba shi da Taiwo dinsa yau sai Allah.
**** **** ****
Tun kafin su Nenne su karaso jikin motar daya daga cikin direbobin Emirate da Dade ya kira ya bude musu kofar gidan bayan wata jibgegiyar mota baka wuluk suka shiga har Aisha wadda hannunta ke cikin na Nenne. Direban ya ja motar cikin nutsuwa suka bar fada. Har sai da suka dauki hanyar airport din Ilorin sosai, suka yi nisa fintinkau da masarautar ta Ilorin, sannan ne Aisha ta ji ta (at ease) kuma bugun kirjinta ya soma lafawa, Aisha ta yi ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali, saboda abinda take so Nenne ta yi mata nan take, Nenne ta dubi halarci, kauna da amana ta yi mata kan ta rufe baki. Me za ta ce da Nenne Sappa? Ban da Allah ya ja kwananta?
Tana jin Nenne da Dade suna magana amma da harshen Yoruba suke yi, (which means) ba su so ta fahimta sosai, don kuwa yarbancin mai zafi da sauri da sauri sosai suke yi. Amma a cikin dan abinda take tsinta yanzu a harshen ta fahimci kamar Dade na rokon Nenne ne akan ta bari a yi komai a hankali kada ta biyewa fushin Siddiqah, ta bata hakuri su wuce Lagos don yana so ya fahimci meye matsalarta data sa aka taso tafiya Gombe haka bagatatan, suna tsaka da sabgar biki, kuma daga ina matsalar take?”
Sai taji Nenne na cewa, “A’ah Dade, yi hakuri ka barta ta tafi, ni a wurina tafiyar Siddiqah Gombe yau ba makawa sai wani babban ikon Allah mai karfi da ya gagari iyawata, matsalar daga Taiwo take, zaka fahimci komai daga baya don ba yau matsalar Maman Kiki ta fara akan Siddiqah ba, na yau din na fahimci yayi tsamari ne tunda har kaga Siddiqah tayi fushi, amma a halin yanzu bazan iya yarda da komai ba banda cikawa Siddiqah burinta”.
Ta Lawanti International Airport. Dade ya yi ma Siddiqa tikiti, babu ko waya a hannunta haka ta shiga jirgin, Nenne ta gaya mata tana sauka Malam Buhari direban Nani Oummana zai zo ya dauke ta daga gidan Sarki. Ya kaita har zuwa nasu gidan.
In kaga idanun Siddiqah a lokacin a soye suke kamar gyada marau-marau, babu ko kyallin hawaye a cikinsu. Na Nenne ne fal kwalla, suka yi sallama ta shiga jirgin Mangal. Dade dai yana gefe yana kallonsu ya rasa abin da ke masa dadi, don Nenne har zuwa lokacin ba ta yi masa wani cikakken bayani da zai gamsu da tafiyar Siddiqah Gombe kuma ita kadai ba, don ta ce ita ma ba ta gama fahimtar matsalar ba kawai ta yi wa Siddiqah abin da ta ke so ne kada hawan jini ya kama yarinyar, a yanayin da ta ganta kamar mai tashin iskokai sanda ta ke rokonta ta maida ta gida. Hakika Nenne ta tsorata, kuma ta dauki laifin duka ta dora a kan Abdulrasheed, duk da a hargitsatstsen bayanin Aisha ta fahimci ita dasu Taiwo ne.
Siddiqah na sauka a Gombe ta tarar da direban Nani Oummana watau Buhari ya dade yana jiranta, wanda dama ta sanshi, duk zuwan da suke yi Gombe da ma shi yake daukarsu zuwa gida haka in zasu koma Lagos shi yake kaisu airport.
Suna tafe a hanya Siddiqa banda ajiyar zuciya ba abin da ta ke yi. Wata irin ajiyar zuciya mai tafe da numfashin fushi da bacin rai. Ji ta ke a ranta, daga yau aurenta ya gama karewa da Prince Abdulrasheed ko za’a mutu ko za’ayi rai.
Nenne kuma a sanyaye ta kira Hajiya Zainab, bayan tasowar Siddiqah sukuma suna hanyar komawa Emirate, ta gaya mata komai a sakaye. Inda ta ce (murya ba karsashi) “Zaynaba ga Siddiqah nan zuwa, ki yi wa Mallam Yunus bayani, Siddiqah ce ta daga hankalinta sai ta taho gida, muna tsaka da bikin twins a Ilorin.
Ta ce ba ta bi ba’asin maganar ba tukunna sai sun koma gida daga raka Siddiqah, ta dai biye wa Siddiqa ne don kada ta yiwa kanta illah, in ta koma gida daga airport din zata bincika ko me yake faruwa kuma za ta dauki matakin da ya dace, insha Allahu.
Nenne tace ma Umman Siddiqah. “For now Zaynaba, ba don ni ba ina so ku taimakeni, ku tausasawa bakuncin na Siddiqah zuwa gareku, ku karbeta babu tambaya babu tuhuma, naga kamar tana da iskokai idan ranta ya baci, ku karbeta da hannu bibbiyu kada ku ce mata don me, yanzu zan koma gidan Kakannin nasu Hammansu, in binciki Taiwo da Firdausi inji me ya faru, saboda na tara al’umma ciki da waje suna jirana da ni da kaina zan rakota, in yaso idan an gama biki an kai amare dakunansu zamu san kwakkwaran matakin dauka.
Tun daga nan Hajiya Zainab ta san cewa ba lafiya ba. Bata san Siddiqah da wasu iskokai ba amma tana da fushi in an kaita bango mai wuyar sauka. Don a saninta Siddiqah ta gama kwantar da hankalinta da auren Prince. Kullum ta kira ta sai ta ce “Hamma na gaisheta, Hamma kaza da kaza.
Ko kwanaki biyun bayannan sun yi waya ita da Siddiqah tana farin ciki tana dariya ta ce mata sun sauka a Lagos ita da Hamma Prince. Bikin kannensa Princesses. Amma bata jin zasu biyo ta Gombe in an gama, don yace daga gama bikin immediately Qatar zasu wuce bakin aikinsa don hutunsa ya dade da karewa. Har tace ma Umman da zata yarda da ta sa Hamma ya kawo mata Umma har Qatar taga muhallinta. Umman tace mata a lokacin “ashe ni Zaynaba kenan na zama ba bafullatana bace tunda zan biki gidan miji”. Siddiqah tayi ta dariya tana fadin “Umma fulani fa sun waye, sun daina irin wannan yanzu, balle ni Petel dinki wadda ni ce ta fari nice auta, bakiga yadda Nenne take kula da Hamma ba shi da yake babban dan ta ma, bata iya wuni guda bata san me yake ciki ba”.
Haka kawai kuma ba za ta zo lokaci guda suna tsaka da biki mai muhimmanci irin wannan ta dagawa Nenne hankali ta ce lallai a maido ta gida ba. Ruwa dai baya tsami banza. Koma dai mene ne za ta jira isowar Siddiqah lafiya, ta gaya mata me akayi mata ta ji.
Mallam Buhari direban Oummana yana kashe motar a kofar gidan su Siddiqah, tayi wuf ta bude kofa ta fice. Siddiqah ko sallama ba ta tsaya yi wa Malam Buhari ba ta shige gidansu ba godi bare an gode. Shi kansa Malam Buhari yayi mamaki don ya san ba haka yasan yarinyar ba. A tsakar gida suka yi kacibus da Ummanta, wadda jin dirin tsayuwar mota ya sa ta tasowa da sauri har tana tuntube. Da wata irin azama Siddiqah ta shiga gida tayi karo da Umma, ai kuwa ta rungume Ummanta sosai, Umman ma ta rungumeta tana hamdallah na saukarta lafiya.
Sai a lokacin Aisha ta samu kuka dan gaske ya balle mata. Umma na cewa cikin fillanci, “Petel dina, mi ya hwaru? In ji dai lafiya lau kike, ba wasu iskokai, kuma kin zo lafiya baki samu matsalar komai a hanya ba?”
Aisha babu baki sai na kuka, wanda tun a Ilorin ya tokare mata a makogaro, sai yanzu da ta ji ta a kirjin Ummanta, ta samu ‘yanci da sukunin fitar da shi, ko ta ji sakayau da sanyi a kirjinta.
A haka suka karasa cikin falon Umma, Hajiya Zainab na rike da ita ta zaunar da ita a doguwar kujera, itama ta zauna a gefenta. Siddiqah an samu abinda ake so, wato anzo inda za’a yi shagwaba son rai, a kuma biye mata, nan ta yi ta rusawa Haj. Zainab kuka, tana cewa auren ta da Hamma ya kare, Umma ko za’a yankani ba zan koma ba.
Ita gara a ce ita aka taba aka ciwa mutunci basu ba, da ko daga ido bazata yi ba kuma abin ba zai dame ta haka ba.
Hajiya zainab ta ce, “Yi shiru Petel ki gaya min Abdulrasheed din ne ya yi miki laifi ko waye? Me yayi miki haka? Mutumin da na lura yana da kirki sosai”.
“Babu abin da ya yi min Nenne sai kyautatawa ta alkhairi da mutuntawa cikin alfarmarsa”.
Umma ta kara shiga duhu tace “to Petel din Umma, gayamin menene ko wanene?”
Daidai lokacin Malam Yunus ya shigo gidan, yana ta sauri kamar ya tashi sama, don har ya fita wajen aiki Prince Abdulrasheed ya kira shi a waya, yana tambaya cikin jin nauyi da murya mara amo da karsashi, bayan ya gaisheshi yadda ya saba kira lokaci-lokaci ya gaisheshi tun bayan rasuwar Emir da suka hadu a wajen makoki a Ilorin, sai ya tambayi Malam Yunus din,
“ko Aisha ta iso gida lafiya?”
Abban Aisha ya ce masa, “Siddiqah kuma? Ba dazu aka ce min kuna Ilorin ba? Ita da wa tazo? Kai ban san komai ba, amma bari inyi hanzari in karasa gidan in duba”.
Sallamar Malam Yunus ta sa Aisha tashi zaune daga jikin Umma. Ta sauko kasa tana gaida Babanta shikuma ya zauna a kusa da ita. In ta tuna irin kalaman Aunty Taiwo a kansa bata sanin sanda ta ke jin sababbin hawaye sun bulbulo mata. Ta durkushe gaban Malam Yunus tana ta sabon kuka.
“Petel in ki ka yi haka ba ki kyauta mana ba, ba ki kyauta wa Hajiya Sappa ba, in wani laifi mijinki ya yi miki ai tsakaninki da shi sulhu ne, bai kamata ki daga musu hankali ki ce komai dare sai kin taho gida ba, zo mu zauna zo mu saba shi ne aure.
Ina ta yabonki sallah kinyi zamanki kin kwantar da hankalin ki a gidan aurenki kada ki kasa alwala mana Siddiqahrmu Petel ‘yar Ummanta. Yanzu dai gaya mana me ya faru? Don Abdulrasheed bai gaya min komai na dalilin tahowarki ba, ya dai kira ni don jin saukarki lafiya? Kuma daga ji yana cikin damuwa a kan tahowarki. Ya ce ayi hakuri yana tafe gobe insha Allah bayan daurin auren kannensa”.
Aisha ta kara sautin kukanta, har da zambarwa tana cewa, “ko Hamma ya zo yayi a banza, don ba zan bi shi ba, na dawo gaban talakawan iyayena kenan, na gama wannan auren tunda a kansa aka ci mutuncin Babana da Ummata da bana hada su da kowa.
Aka yi muku zagin da ba zan iya hakura ba a bainar jama’a. Aka yimin gorin suttura harda na lefe, wallahi ko Hamma shi ya saura da namiji a duniya na bar wa Aunty Taiwo dan uwanta”.
Ta kwashe komai ta gaya musu, jikinta har tsuma yake da tana fadi, ko kalma daya ba ta cire ba cikin muggan maganganun Aunty Taiwo.
Shi kansa Malam Yunus sai da jikinsa da zuciyarsa suka raurawa. Abinki da bafullatanin usuli, sanin kowa ne Bafullacen mutum baya daukar kaskanci da raini ko kankani amma ya kanyi kara da alkunya.
Malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Yunus duka jikkkunansu sunyi mugun sanyi, kuma rayukansu sun yi karshen baci don basu taba jin abinda ya taba mutuncinsu irin wannan ba. Kuma wai daga wadda tafi kowa kusanci da Abdulrasheed din. Amma kokari suke su shanye hakan akan fuskokinsu daga idon Petel, don kar su kara dugunzuma ta.
Sanin kansu ne Petel bata iya bacin rai ba, bahagon hukunci take yi in aka kaita makura, sannan bata da rufi akan komai, bata boye abinda bai mata ba wai don ta faranta maka wannan halinta ne na tun asali keke-da-keke, kuma bata da kara bata kuma damu itama ayi mata ba.
Murya a sanyaye Malam Yunus ya ce.
“Haka abin ya zama? Ashe ana maida manufar alkhairi zuwa ta sharri da wulakanci da tozarci?
Sha zamanki Petel, duk da cewa aure rai ne da shi to ina rokon Allah ya kawo karshen wannan daga yau.
Allah shi ne shaidata na bada aurenki gare su ne darajar mutuncin Hajiya Sappa, ban yi la’akari da dukiya, sarauta ko wani abu nasu ba, karewar ma da na ji hakikanin ko su waye Akanni, a tambayi Yaya Barau cewa nayi ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba. Na yi tattaki na tafi wajen Malam Hassan a kan maganar ki da Ishaqa shi kuma ya kwance min zani a kasuwa.
A dalilin haka Yaya Barau ya fusata ya ce a basu, ba Yarbawa ba ko Ijaw ne, saboda dalilai masu karfi akan Haj. Sappa. Amma ban da haka wallahi-wallahi na fi karfin kwadayi a wurin kowa, nafi karfin kwadayin sarauta ko mulki ko neman suna, ita ma Hajiya Sappa ta sani, banida wata manufa a kan auren nan sai ta tunanin zasu rike min ke da mutunci da martaba tunda su suka zo suka ce suna so cikin mutunci.
Amma tunda haka suka ce, to Petel share dakinki ki zauna, su kawo min takardar sakinki, dama Ishaqa ya dawo Gombe, ki gama iddah ki auri daidai ke.
Petel ke kadai muke da, ke kadai Allah ya bar mana, bayan ‘wabi’ na ‘ya’ya goma! Ta yaya za mu yarda ki wulakanta a gidan aure ko a duniya? Bayan ba wai bamu da abinda zaki ci ki sha ki suturta bane? Aure ne kawai wanda ya zama dole akan diya mace? Ko da muke talakawa a kansu, su masu mulki da dukiya wallahi bazasu kira matsiyata ba, ba kwadayayyu bane mu da zuri’ar mu duk fadin garin Gombe kowa ya san masu wadatar zuci ne, masu sana’ar da zasu dogaro da Allah da kuma kansu”.
Ran bafillacen ya baci, yana fulatanci yana gamutsawa da Hausa. Umma dai kasa magana ta yi, don ta tsorata sosai da yadda Malam Yunus ya fusata, ya sa Petel a gaban motarsa nan take suka dauki hanyar gidan Baba Barau suka bar Hajiya Zainab ta rasa abinda ke mata dadi.
Ba ta so a ce Petel dinta