Showing 27001 words to 30000 words out of 41738 words
Chapter 10 - Aishah-Saddiqa book 4 end complete by Takori Kabara .txt
ya qara zama yaro. Prince yayi dariya kawai yace “ai Oummana Aishan tace ita sai tayi jamb zata koma don neman magana. Su Nenne kuma sun bi bayanta ni kamar bani da mai bin bayana sai Babanta”.
Nani Oummana tace “ai jan aji ake maka, ka san Indo Aisha ba daga nan ba”. Hamma ya girgiza kai yace “ai na shaida. Ayi jarrabawa lafiya.” Tace kai dai yau ka shirya kaje zance, daga nan ka gwada sa’ar ka, yace “uhm….”.
Aisha ana can gida, tun jiya dama da suka tafi iyayenta suka sake yi mata nasiha ta zaman aure suka ce kuma ta gode Allah ya bata surukai na kwarai da mijin da yake matukar son ta.
Dan an gwada shi ta ko’ina kuma yaci gwajin. “Duk wasu experiments da suka dora jikan Akanni bai fadi ko daya ba!”.
Dan haka suka ce ta kawar da maganar Taiwo daga ranta ta fuskanci aurenta da mijinta da iyayen mijinta. Ta kyautata musu ta kuma rike su da kyau.
Baba Barau yace “tunda naga ya matsa ma Indo ko zaki hakura ki bar jamb din ne? Ban ga amfaninta ba tunda kasar zaku bari fa.” Tace “Baba gara inyi, ko ba komi dole zan koma makaranta, ina so in cigaba”.
Baba Barau yace “toh bakomi”.
Addar Kumo tace “gara dai ki kara satin kema, sai ayi miki shirin amarya, kamar yadda akayi ma ‘yar uwarki Maryam. Yanzu ne za mu kai diya, dan wancan kaiwar daman dai yin sa kawai akayi”.
Ummanta tace “nima zanfi son haka”. Aka ce “toh shikenan. Allah ya masu albarka”.
Toh dazu bayan azhar tana tsakar gida sai ga Baban ta ya shigo yace Hamma ya kira shi yace zai zo anjima ya musu sallama sabida gobe daga Litinin ze wuce Lagos, jibi zai tafi Argentina. Aisha tace “toh” tayi ciki.
Ta ma rasa me take ji. She is happy, kuma har ranta abin da ya faru ya wuce, amma kuma sai tana jin haushin Hamma yace zai tafi. Wato bai ma damu ba, da tace baza ta bishi ba. Hmmm! Da Haseena ce kila kuka zai yi tayi…mtsw…..
Satin nan da tayi a gida, quite sure tasan Hamma bashi da laifi, amman kawai dukansu taji sun bata haushi daga Taiwo din har shi. But daga baya tana dan missing dinshi.
Amman jiya yadda taji Baba Barau yana bata labarin nacin da yayi tayi akanta, ya dawo Gombe ma gabadaya duk sai ta ji tausayin shi da so me girma.
(She always want to be loved) sosai irin haka, toh gashi itama dai kamar Prince ya fara sonta.
Amman wannan cewa da yayi zai koma be matsa su tafi tare ba, ya bata haushi. Ta sake kwana a gidan Baba Barau dai, ta dawo gidansu tayi kwance har akai magrib.
Daman tun yau da safe aka fara mata gyaran jiki itama. Ummanta tasa an mata halawa dazu dasu dilka, tace baza a qara ba.
Toh yanzu ana ida magrib Umma ta miqa mata diye tace taje ta durje jikinta dashi ta hada mata lalle da khumra kuma tace ta dauraye jikin dashi. Aisha tace “toh”. Ta shige toilet tayi ta gama ta fito. gaba daya dakin har waje kamshi ke tashi. Tace “Umma nidai mura zanyi in kullum zan wannan wankan”. Haj Zainab bata tanka ta ba dai, tace “yi ki shirya ko Hamma yau zai zo zance” tace “kai Umma, ina tsoho ina zance” Umma tace Patel kenan, ana so ana kaiwa kasuwa. Ni je ki shirya kyaji da gulmar ki”. Ta wuce ta barta a wurin.
She is so nervous, a haka ta tashi tai sallahr isha. sai ta dauki kulaccen da Ummanta ta bata ta shafa, da tasa undies dinta black ta ma rasa kayan da zata sa, akwai wata abaya da Ummanta tazo mata dashi daga Hajj bata taba sakata ba daman suka tafi Lagos da Nenne. Ita ta dauka tasa, white and silver haka kuma cif-cif jikinta. Sai ya kwanta lubb! A jikinta, kugun nan nata ya fito masha Allah.
Tace ta san dai tayi kiba saboda abayan kamar yanaso ya matse ta, karin kibar nata har haka ne? data gama ta dauko ‘yan hannun gold din da Nenne ta bata na Makkah ta saka su, tasa ‘yan kananan ‘yan kunne na gold suma ba sarka. Tayi parking kitson ta tayi gammo da gashi. Sai ta dau gyalen abayar ta yafa. Tana zaune taji ana gaisuwa a tsakar gida, gaban ta ya fadi….
Shi kuma Prince tun da akai magrib ya dau wanka. Ya dai ma kasa cin abinci. Yayi sallah yana zaune da jallabiya har akayi isha, sannan ya shigo cikin sassan Oummana, Nenne tace yazo yaci abinci yace a koshe yake. Bari ya shirya zashi gidansu Aisha zai masu sallama tace “toh” ya shiga ciki ya dauko kananan kaya sai kuma ya mayar, yace gidan surukai ne. Sai ya dauko wata baqar (voile lace) na maza. tana da shara shara haka sai daukan ido kyallin ta yake. Wando da riga irin iya cinya dinnan cip jikin sa dinkin. Sai karamin hannu haka ba dogo ba iya gwiwar hannu. Haka Hamma ya shirya tsab, ya dauko hular sa Tonak ya saka baka itama, da design din silver a jikinta, ya zuba turaren ‘Tomford Oudwood’ ya kuma dauko ‘Francis Kurkdjian Baccarat Rouge’ ya fesa.
Wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikin Prince ya dauko ‘black hermes’ ya saka ya daura ‘rolex’ dinsa ya fito.
Ai yana fitowa sai Taiwo tasa guda har ma dai yaji kunya, su Nenne duk suka juyo, yace “meye haka Taiwo?”, tace ko dai mu dauko mayafi mu bika naga daukar amarya zaka yau” yace “kash!” Ya wuce.
Nenne da tayi murmushi dan tun bai fito ba suke jin kamshi. Lallai Aisha Siddiqa ta ciri tuta. yau Kehinde ke ta wannan rawar kafar haka zai je zance. “Alhamdulillah” Nenne ta gode ma Allah.
Yace musu se ya dawo ya fita. ya dau mallam Buhari suka wuce.
Prince ya yi sallama gidan su Aisha, Mallam Yunus yana tsakar gida suna zaune da Umma, ya amsa ya ce “shigo mana Abdulrashid”. Ya shigo ya gaishe su. Sun burge shi. Domin sun shimfida katuwar dadduma ga abinci nan a gefe, ga sallayar Umman Aisha da hijabinta akai. Nan tayi sallah kenan.
Tana gefen Mal. Yunus suna hira tana dama fura. Shikuma ya kishingida haka kan tuntu. They look so simple and very in love. Masha Allah kawai yace a ransa, ya karaso suka gaisa yace Oummana na gaishe su. Mal. Yunus yace suna amsawa ina Dade? Yace ai ya koma Lagos tun dazu. su Nenne suma jirgin safe zasu bi gobe. Suka ce “toh Allah ya kai su lafiya”. Akayi shiru, Umma tace “shiga palo Hammansu, bari in kira Petel”.
“Petel!!!!”
Umma ta kwada mata kira, ta amsa daga cikin dakinta tace “na’am” tace ga “Hammanku yazo, ki debo ruwa da abinci ki kai masa. Hammansu akul kayi min fulako” yayi dariya yace “Umma ai daga gida nake, furar kawai zan sha”. Tace “toh bari ta kawo maka” yace “toh”.
Ta nuna masa kofar falo ya shiga, ya zauna yana jiran gimbiyar tasa.
Can sai gata ta fito, Ummanta tace “dau fura da yamri a fridge da kindirmo duk ki tafi dashi, wanda yafi so sai ki dama masa”. Tace “toh Umma”. Umma duk sai ta ga wani kyau diyarta yau ta tatso, tace “uhm lallai… Aisha dai an girma, masha Allah”.
Tayi sallama ta shigo, fuskar dai a gimtse, da dan nisa tsakanin falon Baban nata da cikin gida. Prince ya amsa mata, ta shigo, ya daga ido yana kallon ta.
Tashi yayi don ya taya ta da kayan hannunta amman sai ya kasa. Wani kamshi takeyi da ya rasa wane iri ne tun shigowarta, ta qara cika, ga wata abaya nan ta saka ta kwanta jikin ta, gabadaya surarta ta fito waje…. shi yarinyar nan take so ta jiqawa aiki a gaban iyayen ta.
Tana shigowa tayi sallama taji ya amsa tunda ta fito tsakar gida take jin wani irin kamshi yanzu da ta shigo kamar tana aljanna….
Prince ya amsa mata ta dan daga kai ta kalle shi, “hasbunallah…” tace a ranta, my husband, yayi kyau. abinki da fari, yasa bakaken kaya, duk ya bar qasumba se ya sake zama yaro dan shekaru 35.
Ta karaso, kamshi cool ya cika ko ina… ta ajiye furar da tray din a table din kusa dashi, sannan ta zauna, duk yana binta da ido. Ta zauna kan carpet tace “Hamma ina yini?” Yace “lafiya lau” da kyar… tace “ya su Oummana da Nenne da Maman Kiki?” Yace “they are all fine, how are you?” Tace “Am fine, Alhamdulillah yace “hmm….” don gabadaya kokawa yake da kansa. Domin data duka yanzu don ajje tray dinnan a gabansa kamar ya kamo ta. Tayi kyau, ga lallen nan ashe har kafa aka yi shi. Wadannan siraran abin hannun gold din data saka sai ya kara masu kyau. Ga wani kamshi da take da ya rasa menene. Kai shi kamar ma har canza kala Siddiqah tayi.
Ya kafe ta da ido, yana yi wa kansa fada, shi fa ba yaro bane, meye haka yake abu kamar sabon balaga? Zuciyar sa ta ce to meye maraba? Tunda dai tuzurun saurayi ne yayi sa’ar samun sweet 16?
Sai duk sukayi shiru, tace a hankali “Hamma a dama furar? Ko yamri za a saka?” Yace “furar dai” tace “to” ta tashi ta dauko sai taga bata dauko bowl ba, sai ta mike zuwa dining din palon, ta duka haka tana neman bowl din tangaran na dama fura, gabadaya shi kuma ya kafe ta da ido, dukawar nan da Aisha tayi kuwa yaga Ali, Ali ya gan sa. Se yaji kamar yasa ihu… Yace waye ya koya ma Aisha seduction haka… Omooo this girl wan kill me…!”.
Ta dauko ta qaraso tana zama sai taji tashin motar Baban ta, tace “ah Abba fita yayi? Ina zuwa” sai ta leka waje ta gan shi tace “Abba ina zuwa?” Yace Baba Barau ne ya kira ni” tace “toh a gaishe su, sai ka dawo” (ta dawo like a child), ta zauna tasa fura a gaba tana ta dama masa, duk sun kasa magana.
Ta gama zata juye a bowl, yace shi a qwarya zai sha, da fulatanci ya fada, sai tace “toh”.
Ta miko masa, sai ya nuna table din gefen sa yace a can zata sa, ta taso zata ajje ya cire hular sa yasa gefe. Ai tana ajje wa yana kama qugun ta, abinki da abaya silky nan ya jiyo jigida fal qugun, ga wata ‘curve besin’ ya fara bi da hannu bayan ya zaunar da ita cinyar sa, Prince yace murya na shaqewa.
“Siddiqqqqqaaaaaa, nazo bada haquri ne, kiyi haquri kinji, it will never happen again in sha Allah.
Sauri kikai… na gaggawa, da ba sai an kai haka bama zaki ga action da zan dauka”. Tayi shiru, tace “ya wuce Hamma”. Yace “ai ba wanda zai taba ki Aisha inyi shiru, I am not like that. Iyaye sun wuce gaban wasa. So ko ba ke ba, ko wani naga an tabawa iyayen sa, I will make a stop to it, balle ke matata.
So again, I am sorry. Tace “wallahi Hamma ya wuce”. Sam Aisha bata da riko. He hugged her, yace “Aisha i missed u so much”.
Siddiqah tayi wani lup ta kwanta a jikin shi tana jin kamshi da shauqi, yace “you didn’t miss me ko? Ai naga har wata kiba kikayi, irin ko a jikin ki, ni ko har rama nayi. I don’t know how much I fell for u, sai a week dinnan”, Siddiqah ta daga kai ta kalle shi, yace “yes, I fell soooo hard! Amman ke ina jin har yanzu ni ‘father figure’ ne ko?”
Tayi murmushi tace “ashe mita ce da kai Hamma? Tun yaushe akayi maganar nan?”
Yace “toh kallo na fa kikayi cikin idona kika ce mun kin gama auren….”.
Sai kawai ta rufe ido. Yace “no matter how I am feeling ba abinda zai sa na taba furta haka….” Ta ce “ai fushi nayi”, yace “toh ki daina magana in kikai fushi kin ji Ayshah, sabida kar ki fadi abinda daga baya zaki zo kina nadama.
Nan gaba (try and rationalise) kin ji?” Ta ce “toh Hamm…. kan ta karasa sai jin bakin shi tayi cikin nata tare da wata ajiyar zuciya data kwace masa. He kissed her good, se ji yayi ludayin fura dake hannun ta ya fadi kasa, qarar yasa ya kyaleta, don yasan dai a gida suke. Aisha ta sulale daga cinyar sa, ta dau ludayin tayi hanyar dining zata ajiye, har tayi rabin tafiya taji mutum a bayan ta, kan ta juyo ya rungumota ta baya, ya hada ta da bangon dining din a hankali, he is completely a manne da bayanta, he can thoroughly feel her on his body, hannun sa kan flat tummy dinta tace “Hamma…” yace “shhhh…” tace “Umma..” yace “I know…”. Ya sake matse ta yana kissin kasan wuyan ta…a ta a tare suka saki numfashi mai wahala. Al’amarin na Hamma Abdulrasheed (Prince) yafi karfin birona ya rubuta shi, can dai naji yace “Ya ilahi…”. Gaba daya wata kasala Hamma ya saukar mata, basu taba tsintar kansu a irin wannan yanayin ba sai yau… tana cikin wannan halin taji Hamma ya…… bata san sanda tace “Babyyyyy!” Ai babyn nan da Siddiqah tace sai ya kuma kwance masa notika.
Ya juyo da ita ta kalle shi ya kalle ta… ba wanda yake hayyacin sa a cikinsu, he started kissing her lips again. French kiss. Duk dan karatun da ya fara koya mata ya zubar yau, gabadaya ya zuba sababbi. Dan Baby brain din nata ya juye shi tassssss…..a kwarya.
Ba abinda Prince yake so irin yau ya angwance, gabadaya sha’awar da ya dakile sun zubo, ten folds yau!
Siddiqah ita ta fara dawowa tunanin ta, na kada fa Abbanta ya dawo tayi maza ta kwace bakin ta… Hamma yayi lamooo a wuyan ta, ya tsaya a haka yana maida numfashi yana manne da ita.
Bai san sanda ajiyar zuciya ta kwace masa ba sosai…. ita kuwa kunya kamar ta nitse. Sai da duk suka nutsu ma kunyar ta sauko mata.
“Siddiqah u will not kill me…” ya dago yana kallon ta. Da kyar taji me yace, gabadaya muryar sa ta dashe, ita dai ta rufe fuska da hannun ta… Hamma ya qare mata kallo, ya sake gashin ta daya rike dama dankwalin ya dade da zamewa a kasa, ya duka ya dauko mata dankwalin yace “ouchhhh….” tace “Hamma yaya?” Ta tsugunna itama yace “it’s u….” se gani tayi Hamma…. tayi maza ta dauke kai, ta bar jikinsa ta yafa gyalenta, ta koma ta zauna kan kujera kamar ba ita ta gama cewa “babbyyyyy” ba dazu.
Prince ya tsaya ta gyara sannan ya qaraso inda take har wani dingishi taga yana yi, ita dai ta daina kallon sa… he sat close to her, yace “babyyyy!” tayi smiling tace “in miko ma furar?” Yace “ai kin bani fura har da nono” tace “innalillahi….” duk ta daburce. Zata mike Hamma ya janyo ta yana dariya. A ransa yana son kunyar nan tata, amman ya san se ya mayar da ita mara kunyar kwarai. The Prince yayi wani ‘evil smile’. Yace “this baby has no idea what she is in for…..
Tace “menene kake dariyar mugunta?” Yace “baby, tausayinki nake ji, you have no idea what is in store for u…. hmmm….”.
Gabadaya a lokacin fuskar sa ta canza, ya dawo “Yoruba Demon” dinsa yana mata wani arnen kallo, ita ji tai ma kamar period ta fara a lokacin, sai ga horn din Baban ta ya dawo.
Aisha ta zabura ta dauki gyalenta, ta mikawa Hamma hularsa, duk ta rude na rashin gaskiya, shi dai yana kallonta yana murmushi tace “don Allah Hamma ka sha furar nan” ya karba yana sha yana kallonta, sai raba ido take kamar munafuka” tace “Abba ya ce zaka Argentina, ba Qatar kace ba? Ya kalle ta, ya ajje furar bayan ya gama sha, ya goge baki. Yace “kizo mu tafi tare gobe… I need you Babyyyy, kin dai ji irin yadda… it wants u so baaaaddddd…”.
Ya ja baaad din, she felt it har ranta, a ranta tace “yanzu Hamma Abdul ne ke abubuwan nan Innalillahi”. Bata sani ba ashe a fili ta fada, yace “baki ga komi ba, Hamma ya samu abinda yake so… life begins at forty!”
Siddiqah tayi murmushi. Yace mu tafi din?” Tace “Hamma wallahi inaso nayi jamb din, kuma jiya ma bayan kun tafi Ummana tana ta murna zan kara one week kan mu tafi, gashi